Faman kwala ma ta kira tare da sauri domin ganin ta ƙari sa gare ta, tunanin da ta ke yi da kuma kuka da ya saka take gani dishi dishi har Batasan inda take jefa ƙafafunta ba, daidai lokacin da ta dakata da tafiyar da take yi ta juya domin kallon Samra a daidai lokacin kuma wata ɓakar mota Highlander ta hawo titin da wani irin matsanancin gudu na tashin hankali gadan gadan saitin wurin da Samara take tsaye tsakiyar titin ba tare da ta ankara ba wannan motar da ta ƙari so ta yi wani irin ɗibar karen mahaukaciya da ta ita kuma ba tare da ta tsaya ba ta yi gaba abin ta yayin da Samara ta zube gefe tana fitar da jini ta hanci da baki kuma kanta ya fashe.
A lokacin mutane suka taru a wurin ana kallon yadda take fitar da numfashi da kyar idanunta a kakkafe nishi tana fita da sauri sauri. Ita kuwa Samra cak taja ta tsaya daga kiran sunan Samara ɗin da take yi tun lokacin da ta hango motar take ma Samara alama da ta matsa ganin bata gane ba shi ne ta buɗe baki domin ma ta magana, sai dai irin bugun rashin imani da mai motar da fuskarsa ta haddatu a ƙwaƙwalwar Samra ya yi ma Samara ɗin shi ne abin da ya sa ta tsaya cak kamar wacca wutar lantarki taja. Wani irin wahalallen numfashi da Samara taja tare da kiran sunan Samra shi ne abin da ya dawo da ita hayyacinta ta ja wani irin wahalallen numfashi da haɗiye wani irin mugun yawu ta watsar da abin dake Hannunta da gudu ta ƙari sa tana ture mutanen da suke taru ana kallon abin da ke faruwa ta ƙari sa wurin tare da kamo ‘yar uwan nata da fuskarta da jikinta gaba ɗaya jini ya gane wanke wa ta ɗaurata a saman cinyarta tana neman a gaji sai da kyar a ka samu ta bari a ka saka Samara a Napep domin kaita Asibiti ita ma ta shiga sannan Matuƙin Napep ɗin yaja.
_Tsugunno bata ƙare ba...😭_
Domin koda suka ƙari sa asibitin ƙiri ƙiri babu irin roƙo da batayi ma Likitocin ba a kan su taimaka su duba ‘yar uwanta karta mutu amma sun yi kunnen uwar shegu domin kuwa Hospital Drivern Napep ɗin ya kai su sun ƙi karɓar Samara su bata agajin gaggawa wai haka tsarin asibitin yake wai har sai an biya tukunna kuma wai aiki za'a ma ta, suka ambaci kuɗaɗen da yawansu suka shallake tunanin Samra.
Haka nan tanaji tana gani tana rungume da ‘yar uwanta a tsakiyar asibitin Mutane da yawa sun taru suna Kallon su amma babu wanda ya iya taimaka musu da komai. Samara tana kwance saman cinyar Samra cikin hali na rai ko Rayuwa numfashin ma da kyar yake fita wai dan ma wasu daga cikin ma'aikatan asibitin sun ji tausayin su an samu wanda ya bada oxygen aka saka ma ta, idanunta a kakkafe tana kallon sama numfashin ma ya dena fita.
Haka Samra tanaji tana gani ‘yar uwanta ɗaya Danginta farin cikin ta rayuwarta ta mutu cikin wannan halin babu wanda ya iya taimaka musu a gaban ta numfashin Samara ya dena fita yayin da ta dakata da ko wani motsi alamu dai rai ya yi halinsa, a take a wurin Samra ta faɗi sumammiya bata ƙara sanin inda kanta yake ba.
Sai bayan wasu kwanaki da ta farka ta ganta a wani irin baƙin gida mai cike da ababen tsoro da mutane kala kala sai daga baya take samun labarin wai suna a Lagos ana ƙoƙarin fita da su daga ƙasar domin a siyar dasu. A firgice ta farka kuma ta sama kanta a wannan halin da ya yi matuƙar Girgiza duniyar ta, tunaninta bai wuce a kan shin ina gawar ‘yar uwanta yake ba, kuma garin ya ya tazo Lagos sai dai babu mai bata amsar tambayoyin..... Haka ta ci gaba da Rayuwa tsawon kwanaki a wanann baƙin gidan kafin a wani dare ta yi ƙoƙarin gudu daga gidan su biyu tare da wata budurwa da ta kasance ‘yar asalin mai duguri ce sunanta Hauwa'u ana kiranta da Maiji. ƘADDARA CE! Ta yi silar haɗuwar su a nan gidan kuma a wancan Daren Allah ya basu damar guduwa daga Gidan bayan shafe kwanaki suna gudu a daji sun samu sun fito cikin gari da kyar daga bisani suka samu wurin ɓuya makafa tsawon kwanaki suna garari da gararanba a garin Lagos domin nemawa kansu mafita da abin da za su ci, domin babu mai basu, silar hakan suka haɗu da Ramla cikin wani mummanar hali kuma suka taimaka ma ta suka ci gaba da Rayuwarsu su uku abin su kafin wani lokaci suka koma Abuja sanadiyyar hakan kuma a ranar da suka sauka Abuja BUBBA da Matarsa Umma suka shigo Rayuwarsu kafin Neina da take matsayin Yaya a wurin Bubba ita ma ta shigo Rayuwarsu sannan munanan abubuwa da dama suka biyo baya da suka ƙari sa tarwatsa farin cikin dake Rayuwar kowannen su kuma zuciyoyin su suka bushe babu abin da suke buƙatar samu sai ADALCI kuma kafin samun wannan sai ka zama Very Strong ka mayar da komai ba komai ba, sai kayi juriya matuƙa, a taƙaice wannan ke nan abin da ya faru da Samra (Lulu) har take matakin da take a yanzu....
_Wannan shi ne labarin Samra ita da ‘yar uwanta Samara da irin gwagwarmayar da suka sha a Rayuwar har ya yi silar rasa Rayuwar Samara.🩸😭💔_
1. Shin mene ne ainihin abin da ya faru har Samra ta tsinci kanta a Lagos?.
2. Wane ne Prof Bakori shi ne mutumin da yake matsayin next target nasu Samra, mene ne zasu yi masa?.
3. Ramla, Maiji Dukkanin su mabanbantan mutane ne kuma ko wacce tana da Labarin ta, shin ya ya Labarin su yake wani irin ƙalubale suka fuskanta a nasu Labarin?
4. Mene ne ainihin abin da ya faru da Mienal Ɗiyar Neina kuma tana a wani hali a halin yanzu shin tana raye ma?
5. Wane ne makashin commissioner mene ne dalilin sa me yasa su Samra suka so a ce su ne suka ga bayansa?
6. Wanene Jaish?
7. Wacece Annabella?
8. Ina Labarin Tamannah ?
9. Ina Labarin mutumin da Ramla ta haɗu da shi harta kusa kaɗesa?, shin Murmushin me ya yi a wancan lokacin?
10. Da gaske aljanu ne a tare da Samra (Lulu) har suke umartatar ta sha jini?
11. Mene ne Labarin Safiyya (Aunty)
12. Mene ne ya faru da Hamraz bayan rabuwar sa da su Umnia
13. Shin Umnia zata sama Nasarar damƙe makashin commissioner?
14. Su waye selfsame da Irshad yake magana a kai kuma zai tafi Katsina saboda su?.....
_Ba'a yi komai ba yanzu labarin ma ya fara with 🔥🔥_
*Mu tara a next page domin samun duka amsoshin tambayoyin ku.*
# RANAR BIYAN BUKATA 🔥
# NAINARH KD NKD'S
*💫..RANAR BIYAN BUƘATA...💫*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_
A hankali take saukowa daga benen hannunta na dama dafe da kanta dake ɗan sara ma ta sakamakon rashin wadataccen bacci da bata samu ta yi ba a daren jiya.
Daga ganin yanayin ta zaka san bata tare da walwala, koda dama ba abin mamaki bane ganinta cikin irin wannan yanayin domin su kansu mutanen gidan, sheda ne a kan kafin dai a ga dariyar Lulu tofa babban abu ne ya faru, ita kanta takan manta rabon da ta yi dariyar, a taƙaice dai idan kaga dariyar ta tofa sai dai idan wani abun na mugunta a kayi to ta yi nan take zagewa ta yi dariya kamar ba gobe.
Fatiyya da yau ta makara bata fita restaurant da wuri ba har su Umma sun tafi sun barta, tana daga Dining Area ita da Maiji suna karin kumallo, yayin da Neina take kitchen ita kuma Ramla tana zaune saman 1 sieter tana duba system tana jiran ƙari sowar Abrad da suka yi waya zai zo sannan su tafi School tare.
Fitowar Neina daga kitchen ke nan tana yarfe hannu ta dubi Lulu da ta ƙari sa saukowa ƙasa fuskarta ɗauke da murmushi take faɗin.
“Samra kin tashi ke nan dama ina shirin taso ki sai kuma gaki.”
Ƙari sawa Lulu ta yi tare da ɗan ma ta side hug ta ce. “Na tashi Neina Barka da safiya, mene ne ya faru kike nema na?.”
“Malam ne ya ƙari so jeki saka mayafi bari na shigo dashi.”
Cewar Neina bayan ta amsa ma ta tana nufar ƙofar fita daga Palon. Gaba ɗaya suka dubeta da mamaki Fatiyya ta ce.
“Malam kuma mai zai yi?.”
Neina tana riƙe da handle na ƙofar palon ta juya tana faɗin Malamin da zai duba ta ne, dama ai already mun yi maganar da Maiji ban sa ni ba kota faɗa ma ita Lulu ɗin.
Kama baki Maiji ta yi tana gimtse dariya dan kuwa bata faɗa wa Lulu ba, domin tasan koda ta faɗa ma ta ba zata yarda ba, shi ya sa taja bakinta ta tsuke.
“Okay! Kice ma kin san da maganar ke nan?.”
Ramla ta tambaya Lulu da take tsaye ba tare da zauna ba, tana nazarin kalaman Neina 'Malam zai zo' to ya yi ma ta uban me?.
Ɗan Murmushi ta yi tana zura ido domin ganin kalan Malamin na kirki ne ko a kasin hakan.
“Nima ban san da maganar ba sai yanzu amma kam babu damuwa ai ya ƙari so ina jira.”
Ta faɗa tana zama saman hannun kujerar.
“Kice yau akwai kallo.”
Fatiyya ta faɗa tana dariya. Ita kuwa Ramla duban Lulu Kawai take yi tasan wani muguntan ta shirya tun da ta ce ya zo kuma bayan bata ma san da maganar ba.
“Laifin ki ne da baki faɗa ma ta ba.”
Ramla ta faɗa tana duban Maiji. Dariya Kawai Maiji ta yi. “Naga koda na faɗa ma ta ba yarda zatayi ba domin ita bata yarda da wasu mutanen ɓoye a tare da ita ba, amma tun da ta amince shi Malamin ya shigo yanzu, mu dai mu zuba ido kawai.”
“Ai kuwa dai musha kallo ba.”
Cewar Fatiyya tana duban mutumin ta Abrad da ya shigo palon da sallama. Ramla ta amsa bata bari ma ya zauna ba ta ce. “Sannu da shanya ni gaba ɗaya na makara saboda jiran ka dana tsaya yi.”
Ta yi maganar tana bin sa da hararar wasa. Shi kuwa idanunsa a kan Lulu ya lura da yanayin da take saboda haka yasan koda ya yi magana Bama kulasa zatayi ba, ya dubi Ramla da ta rufe system dake gabanta tana miƙewa tsaye tare da faɗin.
“Ba dan banaso na kuma makara a kan wanda nayi ba, da sai na tsaya kallon abin da zai faru kuwa. Ko da yake babu damuwa ke Fatiyya idan na zo kya bani labari.”
“Ai kuwa ni kam ba zan tafi ba, ba tare dana saka wani abu a cikina ba, kuma mene ne zai faru da ba kya so kallo ya wuce ki?.”
Abrad ya yi maganar yana ƙari sawa Dining dasu Maiji suke zaune, ya kai hannu tare da buɗe ɗaya daga cikin kulolin dake wurin sai dai babu komai a ciki ya kuma buɗe wata yana zama ita kuma miyar taushe ce a ciki.
Hannu Fatiyya takai tare da buɗe kular dake gabanta ta ciro mulmulen tuwon shinkafa tana faɗin. “Tuwon shinkafa ne a wannan zakaji?.”
“Ah sosai ma kuwa kamar kin san favorite nawa ke nan sass....”
Sauran maganar nasa ne ya maƙale a maƙoshin sa sakamakon tura masa mulmulen tuwon shinkafan gaba ɗaya a bakinsa da Fatiyya ta yi tana Dariyar mugunta. Shi kuwa zare ido kawai yake cikin Azaba na zafin da tuwon shinkafan yake da dashi ya miƙe tsaye yana so ya yi ihu amma ya kasa da kyar ya iya kai hannu ya ciro, ai kuwa wani uban tiriri ne ya fito ta bakin nasa. Gaba ɗaya dubansa suke suna gimtse dariya, Fatiyya da Lulu kuwa tsaban mugunta a fili suke nasu Dariyar.
“Amma Fatiyya baki da kirki fa.”
Cewar Maiji yana saita kanta kar ya gane dariyar da take ɓoyewa.
“Rabu da ita kawai bashi taci kuma zan rama very soon.”😤
Cewar Abrad bayan ya sauke bottle na ruwa da yakai baki wai ko zai dena fitar da tiririn da yake domin zafin gaske mulmulen tuwon shinkafan yake da kuma tsaban ita Fatiyya ɗin ba ƙaunar ganinsa nan ƙalau take ba shi ne ta saka masa a baki.
“Amma kam kasha zafi wannan uban tiriri da ya biyo baya haka.”😃
Ramla ta faɗa tana dubansa tare da ɗan Murmushi. Bai kulata ba sai ma fakar idon Fatiyya da ya yi, ya ɗauki mulmulen tuwon da ya a je saman Plate a lokacin da ya fito da shi daga bakinsa, cusa ma ta a nata bakin ya yi tare da damƙe bakin da hannunsa a dole sai ta cinye. Sai da ya tabbatar ta haɗiye kuwa ganin yadda take zare ido sannan ya cire hannunsa daga saman bakin nata yana dariya.
“Amma dai ka Cuceni wallahi.”
Fatiyya ta faɗa tana raurau da ido bayan ta ɗan dawo hayyacinta domin kusan shaƙeta tuwon ya yi.
“Ba wani cuta one one mukayi ai ke kika fara.”
Ya bata amsa yana kai hannu saman Plate dake gabanta ya ɗauki Plantain rolls ya kai baki.
“Gobe kya kuma ma wani mugunta.”
Maiji ta faɗa tana mayar da dubanta zuwa ga ƙofar palon da Neina ta shigo da sallama. Ita kuwa Fatiyya da ta shaƙa batama kulata ba sai ma mayar da duban nata kan Neina ɗin da ta yi.
“Malamin yana can ɗakin baƙi fa, Samra kije can kamar zai fi.”
“Malami kuma wani Malamin ke nan?.”
Abrad ya tambaya da mamaki.
“Wai Malamin da zai duba Lulu ne ya zo.”
Cewar Fatiyya ba tare da ta dubesa ba domin haushin sa take ji abin da ya yi ma ta.
“Abin mamaki dama Lulu bata da lafiya ne?.”
“Ah lafiyar ta Qlau wannan fa daban ne.”
Ramla ta basa amsa a yanzu. Yayin da Neina ta ce. “Malami ne mai cire Aljanu.”
Wannan karon Miƙewa tsaye ya yi yana duban Lulu da ta yi kamar ma bata Palon tana zaune inda take saman hannun kujera.
“Sauri yake yi kin san irin waɗan nan Malaman na addini basu da lokacin kan su yanzu haka ma wani wurin zashi daga nan ma za ki saka mayafi kije.”
“Wai taje ina?.”
“Zuwa wurin sa domin ya duba ta mana.”
“Amma bai kamata taje ita ɗaya ba ko muje kawai.”
“Bar ni kawai bari naje a haka na.”
Ta faɗa tana Miƙewa tsaye ta nufa hanyar da zai sadata da palon baƙin. Da sauri Fatiyya ta miƙe tabi bayan ta shima Abrad bai ma tsaya sauraren abin da Neina take faɗi ba yabi bayansu.
Tsaye ta yi tana duban mutumin da yake a matsayin Malamin da ya ɗan juya baya bata ga fuskarsa ba. Hakan ya sa ta ɗan yi gyaran Murya kaɗan tare da ƙari sa shiga ciki ta zauna saman 1 sieter ba tare da ta dubesa ba, sai dai tana lura da yadda yake ƙare ma ta kallo domin sanye take da Doguwar rigar Bacci mai shara shara kuma mai gajeren Hannu ce, kanta kuma hula ne da bai gama rufe gashin kannata ba. Ita kanta tasan shigar jikinta bai yi ba, amma ta sha re, ganin bai ce komai ba sai wani gyaran Murya da yake ne ya sa ta ce.
“Gani fa.”
Ta faɗa tana duban wani sharɓeɓen Carbi dake hannunsa yana ja. Da sauri ya kau da kansa daga gare ta cikin inda inda na fitar magana ya ce.
“Ma sha Allah! Toh Toh sannu.”
“Ba sannu zakamin ba, koba dubani kazo ba.”
“E haka ne rankin shi daɗe.”
“Kamar na san ka..!”
Gaba ɗaya daga Malamin har ita suka juya suna duban Abrad da ya shigo Palon Fatiyya tana bin sa a baya.
“Kai Yaro baka sanni ba, sai dai idan mai kama da ni, waye kai ma.”
Malamin ya faɗa yana zare ido cikin rashin abin yi, yayin da Abrad yake bin sa da wani Shegen kallo ya ce.
“Ba kai ne Malam Hadi ba?.”
“E shi ne wani abu ne ya faru?.”
Cewar Neina da hankalinta ya kasa nutsuwa ta biyo bayansu.
“Neina wannan Malamin ba Malamin Allah da Annabi ba ne, ya bar gidan nan tun Kafin nayi masa rauni.”
Abrad ya faɗa yana ƙoƙarin ƙari sawa wurin Malamin da ya fara sharce gumi domin ya gane Abrad sarai. Dama an ce tabarmar kunya da hauka a kan naɗe ta. Tsoron kar ya tona masa asiri ko ya tozarta shi ya sa Malamin faɗin.
“Fisabilillah an san cin mutunci za'ayi ma mutum shi ne a ka kirasa domin ɓata masa lokaci da suna to shikenan na tafi ma.”
Ya faɗa yana nufar ƙofa fuuu ya fice har yana kusan tuntuɓe.
“Wai meke faru wa ne, a'ina kasan shi ne?.”
Neina ta kuma tambayar ganin yadda malamin ya fita ba'a nutse ba.
“Humph Maƙaryaci ne an taɓa kiransa gidan Uncle ɗina domin duba wata ɗiyar Uncle ɗin nawa da aljanu suka dameta, mutumi ne ya ce a rufe ɗaki daga shi sai ita, a she ba Malamin gaskiya ba ne, kawai ya ari malimtar ne domin cutar mutane.”
“Tofa Tohm Allah ya kyauta gaba.”
Neina ta faɗa tana jinjina lamarin. “Wai ya naga Malamin ya fita ne ko har an gama ruƙiyar?.”
Ramla da Maiji da suka shigo suka tambaya a tare. “Wani an gama ruƙiya ga wanda ya ɓata min budget nan ai tun shigowa ta na lura bana kirki bane naso na ɗan gyara mai saiti gashi wannan ya ɓatamin shiri.”
Cewar Lulu tana Murmushi domin ita kaɗai tasan abin da ta shirya ma Malamin gashi Abrad ya ɓata komai, sai dai ba komai idan halinsa ne zasu kuma haɗuwa, amma kam taso a ce ta ɗan saita masa zama kota sama nishaɗi Sanadin hakan domin yau da dare ne zasu gudanar da aikinsu a kan Prof Bakori Tohm tana buƙatar nishaɗi da walwala kafin lokacin.
“Kai kuwa ya zaka mana haka ai da mun ɗan kwashi nishaɗi domin nasan Lulu ba zata masa da sauƙi ba.”
Cewar Maiji, ita ma Ramla ta amsa da faɗin. “Ai kuwa dai amma ba komai idan halinsa ne ai zai ci gaba kuma zai haɗu da mai maganinsa koda ba Lulu ba.”
Ita dai Lulu Murmushi kawai take yi ta bar Palon domin babu abin