An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
𝑃𝑒𝑟𝑓𝑒𝑐𝑡𝑙𝑦 𝑝𝑒𝑛'𝑠..... ✍💫
*SHIMFIƊA*
Akwai lokacin da wahala da tsananin azaba na wasu mutane ke saka raunannu daga cikin mutane gaza jurewa su tashi tsaye domin nemawa kansu ‘yanci. Akwai k'addara, Akwai son zuciya. Akwai K'addda ta Fyad'e, dake faɗawa wasu matan. Akwai tsananin zalunci da cin amana. Duka da suke taruwa wurin tagayyara Rayuwa su saka tsananin shakku da ruɗani a wasu zukatan.....
_
*💫...RANAR BIYAN BUƘATA...💫*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_
*25, Idowu Martins Street, Off Adeola Odeku Street, Victoria Island, Lagos, Lagos State, Nigeria.*
*07:30, Na safe.*
Da sauri yaron da ba zai wuce shekaru goma a duniya ba, ya tashi a firgice daga saman kujerar Dining da yake kai yana ƙoƙarin fara karin kumallo. Jikinsa ne ya ɗauki rawa kamar mazari lokacin da ya jiyo sautin fashewar Gilashi daga kitchen da iyayensa ke ciki. Da kyar ya iya haɗiye yawu na tsoron abin da ke faruwa a ciki.
Saɗaf saɗaf ya fara taku a hankali, har ya ƙari sa ƙofar kitchen ɗin ya tsaya tsaye sannan ya leƙa kansa ciki kaɗan domin ganewa idanunsa abin da ke faruwa duk kuwa da yasan wannan abu da yake ƙoƙarin yi a yanzu ba abu ba ne mai kyau domin mahaifiyarsa ta taja masa kunne akan aikata wannan ɗabi'a ta laɓe musamman ga manya.
Juya masa baya tayi tana ci gaba da abin da take yi ba tare da ta kula shi ko sauraren magiya da yake ma ta, domin kuwa a halin yanzu bashi da wata kalma da zai kwace kansa a wurin ta har abada kuwa, da idanunta ta ganshi a wannan karon ba wai zargi da take yi ba, daurewa kawai take yi domin kuwa ji take kamar Zuciyarta zatayi bindiga ta fito waje kanta kamar zai tsage gida biyu tsaban tashin hankali da damuwa da take ciki da kuma kishi na ganin Mijinta da wata da ta yi a daren jiya da shi ne dalilin fushin nata a yanzu domin nuna masa kuskuren sa sai dai da alama ya yi nisa sam baya jin kira a harkar.....
“Haba mana Tawan kiyi haƙuri nayi alƙawari ba zan sake ba fa wannan ma aka si aka samu kinji.”
Shiru ta yi tana sauraren sa ba tare da ta tanka masa ba. Ganin taƙi magana kuma da alama har yanzu bata haƙura ba, ya yi Murmushi kaɗan irin na gefen baki sannan ya kai hannunsa ya zagayo da ita suna fuskantar juna kana ya fara magana.
“Na ranste ba zan sake ba, nayi Miki alƙawari ko dan wannan tilon Ɗan namu.”
Ya faɗa yana ma ta nuni da yaron nasu da zuwa lokacin yana tsaye jikin ƙofar kitchen ɗin.
Girgiza kai kawai ta yi ba wai don ta yarda da abin da ya ce gaba ɗaya ba domin ba yau farau ba.
Cikin sassanyar Muryarta mai cike da nutsuwa ta ce.
“Shikenan komai ya wuce a wurina na yafe maka.”
Murmushi ya yi cike da farin ciki ya kamo hannunta tare da kashe Gas da ta kunna ya nufa ƙofar fita daga kitchen ɗin.
“Ah ah Abu J ina ne kuma zaka kaini ina girka ne fa?.”
“Ke dai kiyi shiru kawai bazata ne.”
Ya faɗa daidai lokacin da suka fito daga kitchen ɗin ya kama hannun yaron nasa ya sumbata, bayan ya saki nata.
“J dama ba kace min kanason zuwa wurin wasa tare damu ba?.”
Ya tambaya yaron bayan ya rangwafa daidai tsayin sa.
Kallon Mamansa yaron ya yi. Ta yi Murmushi tare da kyaɗa masa kai sannan ya mayar da kallon sa ga Mahaifin nasa ya kyaɗa masa kai alamar e.
“Toh shikenan yau zan cika maka Burin ka zamuje duk Wurin da kake da buƙata a tare.”
Ya faɗa yana Miƙewa tsaye tare da kallon fuskar matar nasa da take baƙa wani abu yana tsaya masa a rai, amma ya daure tare da sakar ma ta murmushi kamar yadda ya saba a koda yaushe, ita ma ba tare da jinkiri ba ta mayar masa duk da tanaji gaban ta na tsananta buga wa ba tare da ta san dalilin ba...
_
*Fantasy Land Lagos*
*11:50 na safe.*
Yarda yaron ya saki jiki yana wasa da dariya da sauran yaran dake wurin ne ya bata mamaki domin tafi kowa sanin wanene J yaron ta. Akwai tazara sosai tsakanin su da shi domin shi yana kan lilo ne tare da wasu yaran yayin da ita da mijin nata suke can sama a wurin. Juyawa ta yi domin mayar da kallon ga mijinta, ta buɗe baki zatayi magana daidai lokacin da ta juyo garesa shi kuma ya sakar ma ta Kyakyawan Murmushi daman abin da yake jira ke nan. Hannu ya sa ya tura ta gaba ɗaya ai kuwa take ta yi ƙasa tun daga saman Benen ko shurawa batayi ba lokacin da ta faɗo ƙasa kanta ya fa she Sakamakon tsagewa na buguwan da ta yi, jini ne ya fara malala a wurin yayin da mutane suka zagaye ta. Murmushi ya kuma sakarwa tare da lumshe ido Finally ya kawar da ita burinsa ya cika saura kuma me ya rage⁉️
_____
*2024*
*Shekara ta dubu biyu da ashirin da huɗu.*
_Abuja, Nigeria_
*DSS Headquarter, Maitama Evenue, Abuja.*
“Wani abu ne da ya kasance sabo a gane mu gaba ɗaya sannan mai cike da ruɗani da kuma sarƙaƙiya mai ɗaure ciciyoyin kai lamari ne akan kisan babban jami'in ƙasar nan da aka yi wato Commissioner Of Police Mr Aashir Aasaal. An kashe shi ne a cikin Gidan sa na hutawa dake wajen gari. Nasan akwai tarin tambayoyi a tare daku game da wannan ruɗaɗɗen al'amarin na kisan kai mafi ɗaukar hankali da aka yi a ƙasar nan. Mai zaku ce game da hakan wani irin tunani kukeyi akan Wannan lamarin da binciken sa zai kasance a hannun ku?.”
The Director General of the state security service, Mr Bilal Yusuf Bilal ke nan da kansa cikin ɗakin tattaunawa na binciken mayan laifuka irin su Kisan kai Garkuwa Da mutane Fyaɗe da sauransu, yake kwararo wannan baya nan cikin kwarewa da sanin makamar aiki yake bayanin yana nuni da farin allon wanda hasken kwan wutan projector ya haskesa, mai ɗauke da hoto na gawar commissioner da aka kashe kuma zasu ɗaura ɗambar bincike akan case ɗin.
Ya kammala bayanin tare da mayar da kallon sa akan kwararrun jami'ai na musamman da yake ji da su ya kuma yarda da basirarsu tare da kaifin tunanin su da kwarewa a aiki. Wannan dalili ya sa ya haɗa su a team guda domin fara binciken....
“Sir a tunani da nazarina wannan kisan kai bai wuce ɓarayi ne kawai suka yi ba, wata ƙila sun shiga gidan domin neman wani abun shi kuma ya nema ya yi musu gardama a matsayin sa na jami'i wata ƙila shi ne ya sa suka kashe sa sannan suka gudu.”
D.G Bilal Y.B ya yi shiru yana sauraren abin da ɗaya daga cikin jami'an yake faɗa bayan ya miƙe.
Ba tare da ya ce komai ba ya kuma bawa ɗayar da take mace damar ita ma ta yi magana sannan ta fara kamar haka.
“Wannan bai yi kama da ace ɓarayi ne suka yi ba, a iya nazari na nafi danganta hakan da kisa ne da aka yi domin ɗaukar fansa.”
D.G ya yi Shiru kamar yadda sauran jami'an suka yi shiru tare da Nazarin abin da ɗaya daga cikin su ta faɗa.
Bayan shuɗewar wasu sakanni D.G ya Girgiza kai tare da kallon ta tun da aka fara tattaunawar bata kalla kowa ba haka zalika ba tace da kowa komai ba, sai ma ‘yar yatsar ta da take bubbuga wa akan Cup of coffee dake a je gefenta yayin da idanunta suke tar akan allon majigin tana nazarin hotunan gawar da suke maimaita kan su kasancewar da na'urar projector ake hasko hoton.
“Officer muna sauraren ki, shin kina da wani abun faɗa game da wannan case da zan damƙa a hannun ku domin binciken ko kuwa dai sai kin ƙara nazari akai?.”
Ya ma ta tambayar ba tare da saka ran samun amsa daga gare ta duba da sanin Wacece ita da ya yi.
Baya ta yi kaɗan tare da Miƙewa tsaye ta ɗan kurɓa coffee dake hannunta sannan ta a je Cup ɗin. Ta ƙari sa gaban farin allon tare da juyo da kallon ta gare su sannan ta fara magana cikin Muryarta mai cike da jarumta rashin tsoro fikira da basira tare da jajircewa.
“Wannan kisan kai sam bai yi kala da sheƙe kai ko na ɓarayi ba ko kuma domin wani ɗaukar fansa kamar yadda wasun ku suka yi tsammani”
Ta faɗa a gajarce tare da nuni zuwa ga hoton da mutumin da babu alamar rai a tare da shi yake zaune saman wata kujera da alama ta lantarki ce an ɗaɗɗaure masa jiki da wasu igiyoyi bakinsa ma a tamke da gum. Ko'ina na wajen a kewaye ne da doguwar igiya mai launin ruwan ɗorawa, da aka yi rubutu _Restricted Area_ a jiki.
“Da alamu kafin a kashe sa an yi matukar gana masa azaba da wutar lantarki sannan kuma ga dukkanin alamu bawai cikin zafin rai ko kuma don ɗaukar fansa aka yi masa wannan mummanar kisan ba. Ga dukkan alamu wani ake ma nuni da hakan ba shi ne ainihin wanda za'a ɗauki fansar akan sa ba. Cike da kwarewa da aiki da ilimi aka shirya komai sannan makashin ya gabatar da komai daidai. Wannan shiryayyiyen kisan kai ne da aka daɗe ana shirya sa sannan kuma makashin dole zai kasance mai matuƙar kaifin basira ne kuma ya san me yake yi, sai dai duk da hakan ba zai tsere daga gare mu ba zai shigo hannu cikin saiɓi very soon.”
Ta faɗa tana murza hannunta na dama... Gaba ɗayan su, su biyar ne a cikin madaidaicin ɗakin tattaunawa mata uku duk da ita sai Namiji ɗaya sannan sai Director General Bilal Y.B.
“Da kyau Officer Umnia na tabbatar kamar saura wannan binciken shima zaki gudanar da shi yadda ya kamata cikin fikira da basira ke da Tawagar ki na baku cikakken goyon baya akan wannan domin ba ƙaramin mutum aka kashe ba commissioner ne na ‘yan sandar ƙasar nan gaba ɗaya, so be very very careful akan wannan case ɗin.”
Jinjina masa kai ta yi cike da girmamawa a gare sa, ta amsa ma sa, sannan shi kuma ya fita su kuma su ci gaba da tattaunawa akan yadda lamarin binciken nasu zai kasance....
___
*A FARA DA WANNAN... Mu je zuwa....🔥*
# Khadeejarth Sabi'u Yahyah
# Nainarh KD Nkd's ✍️
________
*🌹 Perfectly Pen's ✍️✊*
*Our Ongoing Book's...✍️*
*1_ƘADDARA CE!.*
*BY: C Candy.*
*2_SHIRYAYYIYAR ƘADDARA.*
*BY: Queen Kainaat.*
*3_RANAR BIYAN BUƘATA.*
*BY: Nainarh KD Nkd's.*
*4_DESTINY LOVE.*
*BY: Oum Yasmeen.*
*Mun Shirya tsaf domin kawo muku daɗaɗan littattafan mu masu cike da ilmantar wa faɗakarwa tunatar wa wa'azantar wa har ma da Nishaɗantar wa.💝*
*🔥Kada ki bari wannan tafiyar ya kasance ba tare dake ba. Don't Miss It Dearest sisters 🔥*.
_____
*Masu Buƙatar a haɗa musu Book Cover ko banner, poster, birthday flyer, flyer, logo e.t.c dai duka Muna yi cikin farashi mai rahusa ku tuntuɓe wannan lambar (0708 521 2808..)*
𝑃𝑒𝑟𝑓𝑒𝑐𝑡𝑙𝑦 𝑝𝑒𝑛'𝑠..... ✍💫
*💫...RANAR BIYAN BUƘATA...💫*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_
_Dedicated To Fatahiyya Muhammad Yakasai.(Oum Yasmeen.)_
*Ep_3-4*
*-25, Aminu Kano Crescent, Wuse, Abuja, Nigeria.*
Kyakykywa ce sosai fara yanayin fatarta irin na asalin fulani. Bata bari mai Napep ɗin da ya kawo ta, ya tsaya da Napep ɗin ba, ta fito ta miƙa masa kuɗin sa, ba tare da ta jira canjin ba ta yi gaba, ta shige cikin Gidan ta ƙaramar ƙofar gate ɗin. Sauri sauri gudu gudu take tafiyar har ta ƙari sa ƙofar palon gidan ta danna wasu lambobin da suka daɗe da haddatuwa a kanta sannan ta shiga da sallama ba'a nutse ba, kai daga ganin yadda ta shiga Palon kasan bata cikin nutsuwa.
Babu kowa a palon saboda haka direct kitchen ta nufa tana kwala kiran. “Lulu.”
Tsayawa ta yi tana kallon wacca take a kitchen ɗin tare da ja baya zata koma wacca take a kitchen ɗin ce ta yi magana ta ce.
“Lafiya kuwa Fatiyya mene ne ya dawo dake a yanzu ko dai har kin tashi daga restaurant ɗin ne?.”
Ta yi maganar tana fitowa waje bayan ta wanke hannunta.
Ganin ta juya bata amsa ma ta ba sai nufar Staircase's da ta yi ne ya sa ta kuma cewa.
“Naji kina kiran Lulu lafiya dai ko?.”
Sai a lokacin ta kuma juyowa bayan ta ɗaura ƙafa ɗaya a kan cases ɗin ta kalle ta tare da bata amsa da. “Babu lafiya Anty Maiji.” Sannan ta yi gaba sauri sauri. Da jin hakan ita ma ta tsayen da ta kira da Maiji ta mara ma ta baya cike da tunanin abin da ke faruwa a ranta.
Cak... Fatiyya taja ta tsaya bakin ƙofar ɗakin ta sauke ajiyar zuciya kaɗan tana matsar da kanta ta leƙa ɗakin kaɗan idanunta suka hango ma ta wacca take da muradin gani daidai lokacin da ita ma Maiji da take bin bayanta ta ƙari so wurin gaba ɗaya suka zuba wa ƙofar ɗakin ido suna kallon yadda ‘yar uwar tasu take gudanar da kafcen Kung Fu cikin kwarewa da iyawa sanye take cikin riga da wando ta ɗaura wani igiya jikin rigar ita kaɗai ce cikin ɗakin amma yadda ta dake tana faɗan kung fu ɗin zaka rantse tare da wani ko wata take yi.
“Wai ba zaki faɗa min mene ne yake faruwa ba?.”
Maganar da Maiji ta yi ne ya sa ta cikin ɗakin dakatawa da abin da take yi sannan ta juyo da kallon ta gare su kafin ta fara takowa tana ƙari so wurin su.
“Tun yaushe kuke anan, ke kuma mene ne ya dawo dake yanzu?.”
Ta watso musu tambayar tana nufar cases domin sauka Down. Hannunta riƙe da gorar ruwa da ta buɗe tana sha.
Magana Fatiyya ta fara cikin inda inda ba wai kuma dan haka maganar nata yake ba. A'a fargaban yadda zasu ɗauki maganar da zata faɗa take yi.
“Am um dama dama commissioner ne ya mutu, au aka kashe shi, haka naji labarin.”!
Numfashin Maiji da take niyya magana yai kamar zai ɗauke sakamakon jin abin da Fatiyya ta faɗa da sauri ta mayar da kallon ta kan Fatiyya da ta yi maganar Sannan ta mayar kan ta domin gani da son gane yadda maganar Fatiyya ɗin yazo ma ta.
Ƙafa ɗaya da take yunƙurin ɗaurawa bisa cases ɗin ta dakatar kamar yadda ta dakatar da duk wani motsi nata na wasu ‘yan daƙiƙu yayin da duk suka yi shiru idanun su akan ta.
“Da ina restaurant na gani a labarai dama shi ne abin da ya dawo dani yanzu.”
Ta juyo da dara daran sable eye nata ta ɗaura su a kan Fatiyya tare da furzar da ruwan dake a bakinta haɗe da jefar da gorar ruwan ta nufa ƙofar wani Bedroom ta shige ciki tare da rufo ƙofar garam.
Juyowa Maiji ta yi da kallon ta kan Fatiyya da ita ma itan take kallo.
Dafa kafaɗarta ta yi. “Kar ki damu a bazata maganar taki tazo ma ta shi ya sa ta yi hakan kije palo ki zauna bari nayi magana da ita Kinji?.” Girgiza ma ta kai Fatiyya ta yi tare da nufar