ta yi a gaban zanen tana kallon fuskar budurwar da a ka zana.
Nan da nan ta tara jami'ai kwararru a ka shiga bincike a kan inda za'a gane ina ita wannan budurwar da a ka zana take. Da yake jami'an nata sun horu ta fannin aikinsu kuma kwararrun masana na'ura ne su ɗin shi ya sa ba'a ɗauki dogon lokaci ba suka gano ainihin wacece wannan budurwar ta na'urorinsu masu ƙwaƙwalwa da kuma bayani a kan ta duk da ba yadda suke so suka samu ba sannan a lokacin da suka gano ainihin daidai wurin da take a wannan taƙin ne officer Umnia ta ɗiba jami'an ta domin case yazo ƙarshe nan suka dumfami address ɗin wurin da take ta hanyar amfani da map har suka cimma ta daga nan komai da ya faru ya biyo baya...
*Present Day. . .*
Suna nan tsaye curko curko cikin rashin madogara sai ga wata mota maroon color ƙirar companyn Kia ta shigo hospital ɗin kai da ganin yadda mai motar ya shigo a sukwane kasan ba lafiya ba. Fitowa Mahbub ya yi da saurin sa ya ƙari sa wurin da suke tsaye curko curko. Ramla da ganin sa ya bata mamaki domin ta tuna sa ta sha re hawaye lokacin da ya ƙari so yana faɗin.
“Allah ya sa ban makara ba ina Lulu take?.”
Cike da tsananin mamaki gaba ɗaya suke dubansa jin abin da ya ce.
“Kamar ya ya Allah ya sa baka makara ba, sannan kasan Lulu ne a'ina kuma waye kai?.”
Maiji da take iya wuya ta jero masa tambayoyin tana dubansa.
Shafa kai ya yi yana lumshe ido sannan ya buɗe alamu dai sun tabbatar ya makara ke nan, sam bai so hakan ba, da ƙarfi ya kai ma iska naushi idanunsa sun yi jajur. “Me ya sa hakan take faruwa?.”
Ya yi tambayar a fili kuma da ƙarfi kai daga jin muryarsa kasan a fusace yake daidai wannan gaɓar.
“Bawan Allah ko zamu iya sanin wanene kai da dalilin da yasa kake neman Samra.”
Neina ta yi masa tambayar cikin sanyin murya tana dubansa. Yayin da ya ɗa go ya kalle ta at the first time ya gane matar ita ce tsohuwar matar abin harinsa wato dai Alhaji Haashir, duk da cewa bai taɓa ganinta a zahiri ba sai a hoto amma ya gane ta. A hankali ya furta.
“Labarin mai tsawo ne.”
Daidai lokacin kuma motar Irshad da ta shigo hospital ɗin ya ƙari sa wurin tsaye curko curko, tare da parking a gefe, sannan ya fito shi da wata mata da basu san ta ba, abin da yake a zahiri shi ne, Maiji tana da lambar Irshad jiya ta karɓa to ɗazu ya kirata bayan da jami'an nan suka tafi da Lulu sai take faɗa masa abin da yake faruwa.
“Ina take?.”
Irshad da ya ƙari so wurin a sukwane ya tambaya yana dubansu.
“Jami'ai sun tafi da ita zuwa headquarter nasu.”
Maiji ta basa amsa don kuwa yanzu ba wani ɓoye ɓoye komai ya caɓe.
“Pooh wai mene ne yake faruwa ne wacece kake nema?.”
Aunty dake tsaye gefansa ta tambaya tana cikin ruɗi dan ta kasa gane komai ita da ya tuƙo ta domin zuwa wurin Umnia don akwai Magana mai muhimmanci da suka fara jiya ta waya basu ƙari sa ba shi ne ita kuma ta kasa jure har sai Umnia ta tashi daga wurin aiki sannan ta je su ƙari she maganar, to shi ne fa Auntyn ta nema Irshad da ya yi driving nata zuwa D.s.s headquarter ɗin suna a hanya ne bayan ya kira Maiji take faɗa masa abin yake faruwa shi ne fa kai tsaye ya yo hospital ɗin da ita.
“Zan yi miki bayani daga baya Aunty Labarin da tsayi, babu lokaci a yanzu.”
Ya faɗa yana ƙoƙarin kiran lambar Umnia bayan ya ciro wayarsa a trouser pocket nasa.
“Me kake ƙoƙarin yi ne Irshad ka barta kawai domin a halin yanzu Rayuwarta yana cikin hatsari zaman ta a can shi ne tsirarta zuwa nan da wani ɗan lokaci.”
Galala Irshad ya yi yana duban Mahbub da ya yi maganar sai kuma ya daure cikin muryarsa da a yanzu in'inar ta ragu da kaso 75% cikin 100% ya ce.
“Saboda me kace Rayuwarta tana a hatsari?. Wai menene yake faruwa ne can you All explain to me, what is really happening?.”
Ya yi musu tambayar da ƙarfi cikin wata iriyar murya da batayi ko kama da tasa ba, yana kuma dubansu gaba ɗaya.
“Su kan su yanzu basa cikin nutsuwar da zasu yi maka bayani domin suma ba komai suka sani ba ko nace suke ganewa ba a yanzu domin suna cikin ruɗani a kan ta yadda jami'ai suka sama information har suka kama ɗaya daga cikin tawagar su wato Lulu, amma bari nayi maka bayani.”
Mahbub ya kuma faɗa yayin da gaba ɗaya suke dubansa da tsananin mamaki an ma rasa mai tanka masa har ya fara magana kamar haka.
“Dalilin da ya sa nace Rayuwar ita Lulu yana a hatsari shi ne samarin da ta yi ma duka har da rauni a jiya cikinsu akwai yaron Mr Aabdar Dawlah ina tunanin kunsan shi domin ba ɓoyayyen Mutum ba ne a ƙasar nan baki ɗaya. Ta yi ma yaron nasa mai suna David babbar illa a gabansa wannan dalilin ya sa Mr Aabdar Dawlah ya fusata har yake ƙoƙarin aikata wani abu da ka iya zama nadama nan gaba a garesa bayan gaskiya ta bayyana, ya saka an fara farautar Rayuwarta a yanzu haka, sai a ka yi katari jami'ai sun tafi da ita shi ya sa nake tunanin wata ƙila zata fi samun tsaro a hannunsu.”
Gaba ɗaya kansu ya kulle da jin bayanan sa maimakon fahimtar sa sai ma ƙara shiga ruɗani da wasunsu suka yi. Ita kuwa Aunty daga jin sunan da ya ambata, nan take cikinta ya yi wani irin hautsinewa gabanta ya yi mummunar bugawa da ƙarfin da ya sa sai da ta kusa kifawa ƙasa cikin tsananin firgici da tashin hankali.
Da bala'in sauri Neina dake tsaye dab da ita, ta tarota tana ma ta sannu.
Yayin da ita kuwa Aunty babu sunan da ke maimaita kansa a ƙwaƙwalwarta sai sunan Mr Aabdar Dawlah, to ta ya ma zata manta da wannan mugun mutumin?, da ya lalata ma ta Rayuwa bayan hakan ma bai kyale ta ba, har sai da yaso ganin bayan yaran da ta haifa sanadiyar rabata da mutuncinta da ya yi.!
“Mr Aabdar Dawlah nasan sa mugun mutumi zai iya aikata komai muddun zai sama biyan buƙata na daga ƙudirin sa ko wani kala ne, sai dai mene ne dalilin da ya sa ita yarinyar ta yi ma samarin da kake mana abin da ta yi?.”
Aunty ta jero masa tambayoyin da ta fizgo da kyar tana dubansa domin haka kawai zuciyarta ke son sanin ainihin lamarin.
Mahbub ya dubeta sannan ya saki murmushi kaɗan ya ce.
“Koda nayi miki bayani a yanzu ba zaki gane ba, amma dai duba nan kiga.”
Ya yi maganar yana ƙari sawa wurin motarsa sannan ya buɗe gidan baya yana ma ta nuni da ta ƙari so ta duba abin da ke ciki.
Ba iya Aunty kaɗai ba gaba ɗayan su ne suka ƙari sa domin ganin menene a ciki. Sai dai abin da suka gani ya yi matuƙar gigitasu da kuma sake rikita tunanin su ganin wacca ke kwance mai matuƙar kamanni da Lulu kanta ɗaure da bandage jikinta ma kayan marasa lafiya na asibiti ne da alama ma baccin wahala take yi.
“Lulu! Wannnan ai Lulu ce Neina duba mana Lulu ce mene ne ya faru da ita.”
Ramla ta yi maganar da ƙarfi tana nuni da budurwar mai matuƙar kamanni da Lulu dake kwance cikin motar tamkar babu rai a tare da ita.
“Wannan ba Lulu ba ce, to amma wacece kardai a ce ita ce! Ita ce!.”
Maiji ta kasa ƙari sa Maganar bakinta na rawa ta kalla Mahbub ta kasa furta komai ma sai bakinta dake rawa tana kuma nuna budurwar dake kwance.
Jinjina ma ta kai ya yi sannan ya ce.
“Ba Samra Lulu ba ce wannan ‘yar uwanta ce Samara da kuke tunanin ta mutu a shekaru huɗu baya.”
Ya yi maganar yana duban Aunty domin ganin reaction nata. Yayin da Irshad ya yi wani irin zaro ido yana kuma duban budurwar dake kwance tamkar dai babu rai a tare da ita. Tsugunawa ya yi a wurin tare da kai hannu zai taɓa ta, sai gani ya yi wani hannun daban ya rigasa taɓa ta.
Wani irin luguden bugu ƙirjin Aunty yake tun lokacin da taga wannan budurwa bata gama tantance wani hali take ba, ta kuma jin abin da Mahbub yake faɗa da suke sauka a kunnuwanta tamkar saukar aradu.
Bakinta na wani irin rawa kamar mazari ta kuma duban Mahbub lokacin da ta kai hannu ta taɓa Budurwar zuciyarta ta yi wani irin tsinkewa, tabbas jini ba wasa ba ne, wannan budurwar dake kwance jinin ta ce.
Jinjina ma ta kai kurum Mahbub ya yi domin ya fahimci tambayar da takeson ta yi masa.
“Nasan a yanzu gaba ɗaya kuna cikin ruɗani kuma kunason sanin ainihin abin da yake faruwa zan faɗa muku amma kafin nan zaku fara sanin ainihin wanene ni.
Sunana Mahbubullah Muhammad Sani haifaffen garin Katsina ne ni anan gaba ɗaya dangin mu suke kuma anan na taso nayi karatu tun daga primary har zuwa matakin secondary daga nan na fita Abroad na ɗauki shekaru ina karatu ɓangaren Shari'a bayan na kammala na dawo Nijeriya kuma a lokacin a ka ɗaura auren mu da Rahama ɗiyar ƙanwar mahaifina tun muna ƙanana a kasan alaƙar dake tsakanin mu shi ya sa koda na kammala karatu ba'a ɗauki dogon lokaci ba a ka ɗaura mana aure, sannan a lokacin ne wani irin rikitaccen case yazo hannuna a kan wasu ɓoyayyun miyagun Laifuka da late commissioner na ƙasar nan yake aikatawa har wani daga cikin jami'an sa ya gane gaskiya, gudun kar ya tona masa asiri ne ya saka commissioner ya kashe sa har lahira, sai dai bai sama hujjojin da suke a tare da wannan jami'in ba, ashe kafin jami'in ya mutu ya bawa Matarsa wannan baya nan, shi ne ita kuma bayan mutuwarsa ta shigar da ƙarar commissioner a kan zargin shi ne ya kashe ma ta miji, lamarin dai duk yadda a ka so kashe sa bai mutu ba har sai da ya kai ga an shiga kotu ni ne nake matsayin lauyan wannan matar kuma ta bani waɗan nan hujjoji da mijinta ya bar ma ta, waɗan da su kaɗai sun isa hujjar da commissioner zai ƙare rayuwarsa a gidan kaso, sai dai ashe shiga wannan lamarin da nayi har na amsa hujjojin nan ba ƙaramin kuskure na aikata ba. Matata Rahama Mai tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe suka kashemin a dalilin shiga lamarin da nayi...”
Mahbub ya ɗan yi shiru yana sauke ajiyar zuciya, sannan ya ci gaba da faɗin.
Jaish Jezim shi ne cikakken sunansa ya taso ne cikin wata kalar Rayuwa da ta banban ta dana sauran ƴaƴa, yana da shekaru goma a duniya Mahaifinsa ya kashe masa mahaifiya a gaban idanunsa, daga nan ba'a ɗauki dogon lokaci ba, shi mahaifin Jaish ɗin ya aura wata baturiya mai suna Clara wacca a dalilin ta ya kashe matar tasa wato mahaifiyar Jaish saboda ta taɓa kamasu a tare suna abin da bai dace ba. Saboda dalilai biyu zuwa uku kwarara mahaifin Jaish ya kashe matar sa maman Jaish, na farko dama can ya aure ta ne saboda dukiyarta bashi da komai ta auresa duk wata daula da suke ciki nata ne, na biyu kuma shi ne ita mahaifiyar Jaish mai suna Falisha bata kasance cikin kyawawan mata ba, tana da wata kalar fata ne mara kyan gani wacca babu likitan fata da basu haɗu da shi ba a kan matsalar amma abu ya cutura domin da hakan a ka haife ta babu wani abu da zai canza kalar fatar nata shi ya sa ma ta rasa mai aurenta, duk da masifar dukiyar da take da, wannan dalilin ya sa lokacin da baban Jaish wato Jezim ya nema ya aure ta bata ƙi ba, anan suka yi Aure kuma ta damƙa masa ragamar dukiyarta gaba ɗaya shekara guda da aure ta haifa ɗan Namiji suka saka masa suna Jaish suke kiran sa da J.
Abin da Falisha bata sa ni ba shi ne Jezim ba don yana son ta ya aure ta ba sai dan dukiyarta kuma sannan shi yana da wacca suka daɗe tare kuma suke da muradin auren juna wato Clara sai dai ita Falisha bata san da hakan ba har zuwa wata rana da dubunsu ta cika ta kamasu a tare, a lokacin ta yi matuƙar ɗaukan zafi da shi, sai dai da yake mugun makiri ne sai da ya san yadda ya lallaɓa ta har suka fita wurin shaƙatawa tare anan ne kuma ya yi amfani da damar sa ta hanyar jefata ƙasa tun daga saman bene, sai dai wani kuskure da ya yi shi ne a gaban idon Yaron sa Jaish ya jefa matarsa Falisha ƙasa da haka ya yi sanadiyar mutuwar ta, dama hakan ya tsara shi da Clara domin ta hakan ne ba za'a zarge sa ba, domin abin ya kasance ne tamkar bisa tsautsayi ya faru.
Ba'a ɗauki lokaci ba ya auri Clara kuma suka ci gaba da zama anan gidan da suke da Falisha.
Jaish a sakamakon abin da ya faru na kashe mahaifiyarsa da Mahaifin sa ya yi a gabansa hakan ya haifar masa da firgici mai cutarwa har hakan yaso ya taɓa ƙwaƙwalwarsa kuma abin ya ci gaba da girmama ne sakamakon abubuwa da basu kamata ba da Babansa da matar baban nasa Clara suke yi a gabansa domin su sumbaci juna a gabansa ba wani abu ne ba a wurin su, har ta kai ta kawo suna iya kusan saduwa da junansu a gabansa, baya da haka Clara tana matuƙar masa horo na azabtar wa sosai ta hanyar tsare sa da wuƙa ta ce sai ya kira da Mama ko kuma ta kashesa, irin waɗan nan abubuwan sune suka ci gaba da faruwa da Jaish tsayin shekaru Biyar zuwa lokacin kuma zuciyarsa ta yi wani irin ƙeƙashewa da lamarin Duniya wani irin mugun tunani ƙwaƙwalwarsa ke basa tana bashi tabbacin komai nene ya yi ba laifi ba ne, a wani lokaci ne kuma wannan tunanin nasa ya kaisa ga aikata wani Babban laifi da ya zama ƙofa na buɗe war miyagun abubuwan da ya ci gaba da aikawa. A wani yammaci Jaish ya yi amfani da bindigar da ya samu wurin wani abokinsa ya yi ma Mahaifinsa da Clara wani irin mummunar kisa wanda ko a tarihin miyagun Laifuka na kisa ya sha banban da saura, bayan faruwar hakan ne Uncle ɗin sa Aashir Aasaal wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya da mahaifin Jaish.
Ya ɗauki Jaish ɗin ya ci gaba da rayuwa a tare da shi, sai dai bai saka sa cikin iyalansa ba, ya ci gaba da koya masa miyagun Laifuka kuma sauke yi tare da fari ya fara da koya masa dallanci na miyagun kwayoyi da yadda a ke siyarwa da su, daga baya harkar tasu ta faɗa ɗa suka koma harda safaran makamai, to dama ance makoyi mafiyi, Jaish ya taso wani irin murɗaɗɗen mutum ne shi mai wata kalar baƙar zuciyar da babu ko ɗigon tausayi cikinta kuma sannan ya tsani ma ta wannan dalilin ya sa a lokacin da case ɗin Uncle ɗin nasa commissioner yake a hannuna ganin alamun zasu yi rashin nasara zasu faɗi shi ne dalilin da ya sa shi ya sace matata Rahama Mai tsohon ciki bai duba wannan ba, a lokacin da ya sace ta a garin Katsina yana gudu da motar ne har ya yi sanadiyar da ya kaɗe Samara kuma bai dakata ba daga bisani kuma cikin rashin imani da tausayi ya kashe ta har lahira, ni kuma suka saka yaransu suka sace ni a hanyata na zuwa court suka min shegen duka da tunanin na mutu domin duka da sara suka haɗa min suka watsar dani a daji suka yi gaba, daga nan wasu mazauna nan daji ne suka tsince ni kuma suke kula dani tsawon shekaru biyu da wani abu ina jinya domin har manta gaba ɗaya tunani na nayi sai daga baya na sama sauƙi kuma na taso domin wata kalar muradi na ɗaukar fansa bisa abin da suka yi min, nabi duk wata hanya domin ganin na ɗauki fansa, a nan ne na ƙara sanin cewa Aashir Aasaal Uncle ɗin Jaish da yake matsayin commissioner tantirancin sa ya wuce tunani duk wani ƙaramin mahaluki, kafin na fara wani yunƙuri na ɗaukar fansa sai da na fara bincika Asalin wane ne commissioner nan ne na gano Jaish sanadin binciken da nayi kuma ban tsaya iya nan ba sai da na fara binciken ko akwai wasu masu buri Irin nawa na son ɗaukar fansa a kan su, nan ne na gano tawagar su Lulu duk da cewa sun tabbatar wa kansu domin adalci suke abin da suke bawai na fansa bisa abin da a kayi musu ba, a lokacin ne na bincika Asalin Labarin kowaccensu tun daga kan Ramla da a ka kashewa miji da Lulu wato Samra har Maiji wacca ‘yar uwanta ta taɓa auren Jaish har ya kashe ta saboda ta gano asalin wanene shi kuma ya haɗa hannu da Uncle ɗin ta da yake member na wata hatsabibiyar ƙungiyar da Jaish ya kafa ta shi da Uncle ɗin sa commissioner, Uncle ɗin Maiji wato Alhaji Umair Ubaydullah shi ne suka haɗa hannu da Jaish suka kashe iyayen Maiji gudun kar su gane ainihin abin da ya faru har ya yi silar mutuwar Fanan a lokacin ƙudirar Allah ne kawai ya tseratar da Maiji basu sama nasarar kasheta ba har ta faɗa hannun masu fataucin mutane da hakan ya zama sanadiyar haɗu warta da Lulu...”
Mahbub ya kai ƙarshen maganar yana harɗe hannu a ƙirji tare da jingina da motarsa.
Yayin da gaba ɗaya jikinsu ya yi wani irin sanyi tare da cika da tsanani mamaki da jin wannan labari da ya bada wai dan ma a hakan ma a gurguje ya basu domin Jaish da commissioner