x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 16 - RANAR BIYAN BUƘATA Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba

  • 45001 words
  • 48000 words
  • Out of 59040 words

Category: Love Stories

Views 289

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
game da zagi, baya jin daɗin sa, shi ya sa nayi amfani da wannan damar wurin sanar daku cewa ba duka ne a ka taru a ka zama ɗaya ba, Dan Allah masu zagin marubuta especially ma na online ku taimaka ku dena haɗa wa gaba ɗaya domin ba duka ne a ka zama ɗayan ba dole dai Akwai na gari a ciki Allah ya sa mu dace, ina fata zaku fahimta domin Wallahi banajin daɗin zagin marubuta da a ke yi.🥺👏❤️_





. . . Perfectly Pen's🖊️. . .

*🔥 RANAR BIYAN BUƘATA 🔥*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_

. . Nainarh KD Nkd's . . . ✍️
07067953066.




_Meerat Umar And A'ishah Muhammad Bashir (A'ishah MB) Ban zan manta daku ba mutanen Amana ta 🤩 fejin kyauta ne a gare ku._👏


https://www.facebook.com/profile.php?id=61559956525673&mibextid=kFxxJD


_Don't Forget To Follow My Facebook Profile 👏_
_
E . 29.


A mota kuwa suna zaune ne a gidan baya driver ya ja suka nufa restaurant ɗin, Lulu tana ɗan jan Fatiyya da fira sama sama, ita dai Fatiyya abin wani banbara kwai ya kasance ma ta domin kamar a mafarki take gani wai yau Lulu ce ta saki jiki take fira har da dariya ga wannan make-up da gayu da ta sha, Lallai akwai wani abun a ƙasa, haka kawai Fatiyya take ayyana wa har suka ƙari sa restaurant ɗin da yake ba nisa ne sosai ba, fitowa suka yi suka shiga ciki, Lulu ta sama wuri ta zauna tana danna waya yayin da Fatiyya ta shiga ciki domin sauya kaya zuwa restaurant da kuma kawo ma ta kayan maƙulashe.


“Lale lale marhaban yau kuma Samra ce a restaurant ɗin namu.”


A hankali Lulu ta ɗa go kanta daga latsa waya da take yi ta dubi Umma da ta yi maganar lokacin da ta ƙari so wurin fuskarta ɗauke da murmushi tare da farin ciki na ganin Lulun.

“Ai kuwa dai yau nayi abin kai, fatan na sameku lafiya.”


Lulu ta faɗa tana ɗan murmushi tare da duban Umman.

“Ai kuwa ba ƙarami ba ma kuwa kin bawa Kowa mamaki sai dai mun yi farin ciki ai.”

Umman ta faɗa tana duban Fatiyya da ta ƙari so wurin sanye cikin kaya irin na ma'aikatan wurin, ta a je serving tray mai ɗauke da Chicken fried stick da Apple Pie a mabanbantan plate sannan sai Apple Juice a glass cup ta dure serving tray ɗin a saman table da Lulu ke zaune tana faɗin.

“Yawwa Aunty Lulu ta duka wannan naki gaba ɗaya. har da favorite naki na haɗo Apple Juice.”


Ta faɗa tana tura ma Lulu serving tray ɗin gabanta.

Dubanta Lulu ta yi sannan ta dubi serving tray ɗin da abubuwan da ke ciki ta kuma duban Umma ta ce.

“Umma da alama wannan ƴar taki so take na kasa tashi a nan wurin ba?.”

“A'a fa ai wannan ma ya yi kaɗan bari ki gani na ƙaro miki.”

Umma ta faɗa tana dariya sannan ta yi gaba domin ta ƙaro ma tan.

“Please Umma barshi haka nan ma na gode na lura so kuke nayi ƙiba.”


“Uhump ke kuma bakyaso kiyi ke nan?.”

Fatiyya ta faɗa tana dariya.

“Oho dai jeki ki sallama costumer's suna jiran ki.”

Lulu ta faɗa dan ta san Indai zata biyewa surutun Fatiyya tofa Fatiyya ɗin ba tashi zatayi ba.

Tafiyar Fatiyya ta yi yayin da Lulu ta bisu da ido Fatiyya da Umma yadda suka dage suna kula da costumer's nasu gunin burgewa, murmushi ta tsinci kanta da yi, miƙewa ta yi tana amsa kiran da ya shigo wayarta, ta ɗan juya baya ba tare da ta bar wurin ba, har sai da ta gama wayar sannan ta zauna ta ɗan taɓa kaɗan daga abin da Fatiyya ta kawo ma ta sannan ta ci gaba da danna waya tana jiran mutumin da za su haɗu a wurin ya ƙari so.


“Sannu Aunty Lulu mun barki ke ɗaya ko?.”

Fatiyya da ta ƙari so wurin ta faɗa.


“Ba komai wai ina Bubba yake ne?.”

Lulu ta amsa tare da jefo ma ta wannan tambayar.

“E to tun ɗazu ya ce dai zai ce ya dawo haka Umma ta faɗa dana tambaye ta, amma bai dawo ba.”

Fatiyya ta faɗa tana jan kujera ta zauna. Ɗan waigawa Lulu ta yi tana duban mutanen dake wurin ta buɗe baki zata yi magana sai dai me, ta tsinci kanta da kasa furta komai sakamakon ido huɗu da suka yi ita da shi.

Kamar a mafarki da ta saba a kullum sai kuma abin ya kasance kamar almara kai kamar ma dai gizo take gani ba shi ɗin ba ne, wanda hakan ne ya sa ta miƙe tsaye tana mirza ido don tabbatar wa kuma a daidai lokacin da ta miƙe ɗin shima da alama ya shiga makamancin halin da ta shiga na kokwanto ya miƙe haka ma Budurwar mai sanye da fafaren kaya na malaman jinya ta miƙa tana duban wurin da yake duba.

“Mamm... Maiji! Me kike yi anan kin san wannan ne?.”


Lulu ta tambaya cikin rarrabe war murya tana duban Maiji dake tsaye kusa da Irshad da zuwa lokacin da Lulu ta yi maganar ya fara taka wa domin ƙari sawa gareta.

“Lulu kin san shi ne kema?.”

Ita ma Maiji ta kuma dawo wa da Lulu tambayar cikin rashin fahimta domin kanta ya kulle ganin irin kallon da suke ma juna ita da Irshad kamar dai kallo ne na sanayya tare da wani abun kuma daban ta yiwu bazata haɗuwar tasu ta kasance a yanzu.

“Sassam Samra!...”

Irshad ya faɗa lokacin da ya ƙari sa dab da ita kuma ya tabbatar da cewa ba gizo take masa ba tabbas wannan Samra ce domin ko'a bacci ya tashi ba zai kasa gane ta ba duk da cewa an ɗauki shekaru rabon da su haɗu da juna.

Jinjina kai ta yi tare da girgiza wa lokaci guda tana ja da baya ganin haka shima ya fara taka wa yana isa gareta. Da wani irin zafin nama ta juya tare da ficewa daga restaurant ɗin gaba ɗaya.

“Yallaɓai! Yallaɓai l! Wai mene ne ke faruwa ne ka santa ne, ina kuma zataje?.”


Maiji ta tambaya cikin ruɗu tana dubansa, dakata wa daga yunƙurin bin bayan Lulu da yake yi, ya yi, tare da duban Maiji.

“Kodai kaine Dimple Perfect ɗin nata?.”


Ta kuma jefo masa tambayar.

A halin da yake ciki ba zai iya magana ba hakan ya sa ya jinjina ma ta kai yana shafa kan tare da furzar da iska mai zafi, wai meke damunsa ne? Me yasa tsayin shekarun nan bai tuna da su ba sai yanzu? Wai ma ina Samara ɗin take, Samra ya gani yanzu ita Samara ɗin fa.


“Yallaɓai karka bita ka kyale ta kawai nasan ba zata cutar da kanta ba.”


Maiji da tsananin mamaki ya cika ta, ta tsinci kanta da faɗin hakan tana tuna ainihin dalilin zuwan su restaurant ɗin shi ya buƙaci hakan, ita kuma ganin da ta yi bayajin daɗi a jiya kuma gashi yau ya dawo Mining Company da kuma sanin Matsayin sa a wurin, ya sa ta rakosa nan ga kuma abin da ya biyo baya.


“Maiji mene ne ke faruwa ne ina kuma Lulun ta tafi naga ta fita da gudu?.”

Umma da ta ƙari so wurin hankali tashe ta tambaya tana dubansu gaba ɗaya.


Ajiyar zuciya kawai ta sauke cike da taraddadi ta ce.

“Umma Labarin da yawa saboda wannan mutumin Lulun fita.”


Ta faɗa tana ma ta nuni da Irshad da ya zauna zuwa lokacin yana dafe kansa dake mugun sara masa jin sa yake kamar ba shi ba. Wani abu dai haka yana taso masa kamar dai wanda ya farka daga bacci daɗaɗɗe.


“Ban gane saboda shi ba to mai ya ma ta ne, kiyimin bayani yadda zan gane mana Maiji!.”

Umma ta kuma faɗa fuskarta na nuni da tashin hankali da ruɗa ni.

“Shi ne mutumin da ya taimaki rayuwar Lulu ita da ƴar uwarta a shekarun baya.”


Maiji ta bata da amsa tana kuma ma ta nuni da Irshad ɗin. Da sauri Umma ta dubesa fuskarta ɗauke da wani kalan yanayi ta kasa faɗin komai daidai lokacin kuma Bubba ya shigo restaurant ɗin...


*LULU POV.*



Tun lokacin da ta fita daga restaurant ɗin ita kanta ba ta ce ga inda take jefa ƙafafuwan ta ba, da fari tafiya take yi amma daga bisani da ta fahimci tafiyar bai wa dace ta ba, sai ta fara gudu, gudun take babu sassauta wa bata san inda take jefa ƙafafun ta ba, har sai da ta yi gudu sosai ta tabbatar da ta gajiyar da jikinta sannan ta dakata ta fara tafiya a gefen titin da babu kowa tsit, jefi jefi motoci ke wucewa.

Wata baƙar mota ce Rangerover ta taho a 360 tana falfala gudu a titin. Har motar ta wuce Lulu bata dubeta ba kuma bata dena tafiyar da take yi ba da zuwa lokacin ta koma gefen titin tana tafiya riƙe da takalman ta bondage boot a hannunta, idanunta na duban ƙasa, jin alamun tsayawar mota a kusa da ita da ta yi hakan bai sa ta dena tafiyar da take ba, suma na cikin motar basu dena bin ta ba, ganin ba zata tsaya ba ne, yasa suka sha gabanta da motar. Wanda hakan ya sa dole ta dakata ta ɗa go domin ganin wani mai ƙarar kwanan ne zai fito daga motar.

Wasu matasan Samari ne su uku suka fito daga cikin motar kowanne su da ka gansa kaga tacaccen mara kunya mai ji da ƙuruciya da kuma dukiya, wani irin aski ne na rashin mutunci a kan kowanensu, duba da yadda suka fito suna rangaji ta iya yiwuwa a buge suke kuma suke tuƙi. Ɗaya ma sigari ce a bakinsa, Wani ne daga cikin su ya fara magana cikin wata bugaggiyar Murya.

“Kai mun kuma yin babbar kamu fa ‘yar shila ce da alama tafi wancan ta motar, gata nan kuma tsuntu daga sama gasashe yau akwai ƙarin kodimo.”


Ya faɗa yana wani tafiyar banƙarau haɗe da shafa ƙeya shiga tatacce.

Ɗayan ya amsa da faɗin. “Kai Babah da alama fa zazzafa ce kuma zatafi wancan ta motar bari dai muji.”

Ya faɗa lokacin da ya ƙari sa wurin ta tare da kai hannu da niyyar taɓo ta. Baya ta yi tana dubansu gaba ɗaya. Tare da nazarin abin da ta ji suna faɗa duk da muryoyin nasu a ɗan disashe suke maganar sakamakon tatul da suka yi. Sai dai fa Kamar wata taji suke faɗa?. Ke nan wata yarinyar ce a motar nasu, to mai suka ma ta?.


Kamar zai afka ma ta Saboda yanayin tafiyar rangaji da yake yi ya kuma bin ta tare da kai hannu zai cakumo ta.

Ai kuwa ta damƙe hannun tare da murɗa hannun iya ƙarfin ta, hannun ya bada wani kalan ƙara, ƙarass! Alamun dai an ƙarya.

Wani irin firgitaccen ihun azaba ya saki yana duban hannun nasa dake lilo alamun dai an ƙarya ƙashi.


Ɗaukar sigarin bakinsa da ta faɗi ƙasa ta yi tare da jefa masa a fuska, ai kuwa ta ƙona masa fuskar.

Ganin haka ya sa a fusace ɗayan ya dumfaro ta, ai kuwa yana ƙari sowa ya kai hannu da niyyar taɓa ta, ta yi ƙasa tare da zuba masa kyakkyawan zazzafar naushi a ciki, ai kuwa take a wurin ya amayo abin da ya sha har ya saka sa maye.

Ganin abin da a ka yi ma ƴan uwansa ya saka ɗayan ya yi ƙoƙarin kwasa a tammanin zai fece. Ai kuwa Lulu ta mara masa baya. Sai ji ya yi an yo baya da shi tare da buga kansa da motar, ya zube a ƙasa yana fitar da numfashi.

Buɗe motar ta yi domin ganin yarinyar da suke magana a kai, da sauri ta yi baya tana kau da kai hankali a tashe ta kuma dubansu zuwa lokacin ta kawo iya wuya domin ganin irin halin da yarinyar ke ciki ya tabbatar ma ta da cewa raping ɗin ta suka yi, musamman ma ganin jini a jikin rigar ɗaya daga cikin su da ta yi.

Juya wa ta yi ga na farkon da ta ƙarya ma hannu, kuma ta ƙona masa fuska, yana durkushe a ƙasa, ɗa go sa ta yi tare da fara zuba masa naushi a fuska kamar Allah ya aiko ta, bata kyale sa ba sai da taga ya dena numfashi alamun ya suma, sannan ta ƙari sa wurin na biyun da ya fara ja da baya amma ya kasa gudu, sai lokacin ma ta tuna da bindiga a tare da ita, ai kuwa babu imani ta ciro ta harbe sa a gabansa domin shi ne wanda rigar sa ke jiƙe da jinin.

Kasa ihu ya yi sai zufa da yake yi na tsananin azaba. Daga inda take tsaye ta kalla na ukun nasu dage kwance magashiyan tun lokacin da ta buga kansa da mota, saita saitin ƙafafuwan sa ta yi tare da sakin masa alburusai a duka ƙafafun.

Sannan ta mayar da bindigar a trouser pocket nata, sai a lokacin hankalin ta ya fara dawowa kanta, waya ta ciro tare da kiran layin taimako. Ba'a ɗauki dogon lokaci ba Ambulance ta ƙari so wurin ta ɗauki yarinyar a ka tafi da ita zuwa asibiti, suma waɗan nan Samari da Lulu ta caccasa a ka kwashe su domin kaisu asibitin a basu kulawa da gaggawa domin ba ƙaramin rauni ta yi musu ba gaba ɗaya.



*TAMANNAH POV.*



Kanta na wani irin juyawa tsaban tension da ya yi ma ta yawa, cike da tashin hankali ta kuma duban likitan jin bayanin da yake ma ta, da kyar ta iya buɗe bakinta dake rawa ta ce.


“Yanzu Doctor ba wani taimako da zaku iya bawa Mommyn mu kake nufi? ina sanin ka ta fannin yake?, har yanzu fa bata dena zubar da jini ba.”


Ta yi maganar tana zubar da hawaye domin zuwa yanzu ta sadaƙar zasu rasa Mommyn su ne domin tun jiya a ke abu ɗaya sauƙi yaƙi samuwa kuma har yanzu bata dena zubar da jini ba sai kace mai haihuwa abin ya ɗaure wa kowa kai.


Girgiza kai Likitan ya yi yana tausaya ma ta domin ya fahimci halin da suke ciki musamman yanzu da ya sama Labarin komai a kan su.

“Kiyi haƙuri Madam domin kuwa babu wani taimako da zamu iya bata a anan ciwon nata domin bana asibiti ba ne, amma jira bani minti kaɗan ina zuwa.”

Ya faɗa yana ɗaukar wayar tarho dake saman desk sannan ya danna wasu lambobi bada daɗe wa ba, a ka ɗa ga, ya fara magana cikin harshen turanci. Yayin da Tamannah take zaune gefe tana matsar kwalla na tausayin kansu ta bisa da ido.

“Am nace ba ki dena kukan haka in sha Allah babu abin da zai sameta.”

Ya faɗa bayan ya gama wayar yana dubanta. Girgiza kai ta yi kuma hawayen bai dena zuba ma ta ba.

“Bani da ikon dakatar da hawayena muddun wani mummunan abu ya faru da mahaifiyata.”

Ta faɗa cikin Muryar kuka tana kau da kai.

“Na sani amma babu ma abin da zai sameta ungo wannan share hawayen.”

Ya faɗa yana miƙa ma ta tissue. Karɓa ta yi daidai lokacin kuma a ka tura ƙofar office ɗin tare da shigowa da sallama.

Amsa wa Likitan ya yi sannan ya miƙe tsaye suka yi misahaba da wanda ya shigo ɗin, bayan sun zauna ne likitan da ya shigo ɗin ya dubi Likitan tare da faɗin.


“Dr Abdallah gani lafiya dai kake nema na ina shirin tafiya gida?.”

Ya tambaya yana dubansa. Girgiza kai Dr Abdallah ya yi ya amsa masa da faɗin.

“Lafiya ba lafiya ba, Dr Jamil amma komai ya zo da sauƙi tun da gida ma zakaje nasan dai Malam yana a gari ko?.” (Wato mahaifin Dr Jamil ɗin.)

Amsa masa Dr Jamil ya yi da faɗin. “Yana nan kuwa jiya ya dawo daga ƙauye ai fushi ma yake da kai sam Dr Abdallah baka son zumunci.”


Shafa kansa Dr Abdallah ya yi yana jingina bayansa da kujerar da yake kai ya ce.

“To ya za'ayi abubuwan ne sun sha kai ba lokaci.”

“Kai kam kaji jiki kullum a hakan kake ai. By the way mene ne dalilin nema na da a ke ne?.”

Ya tambaya yana ɗan duban Mannah da ta kauda ido sama sama takejin firan da suka fara da alama an manta da ita ma.


“Lamari ne a kan wata patient tawa to matsalar nata na lura ba na nan asibiti ba ne, shi ya sa nakeson sanin ko Malam yana nan kaga sai a kaita can wurinsa domin tanajin jiki fa. Kaga tun da yanzu gidan zakaje shikenan ma tafi tare kawai.”


“Ayya! To hakan ma ya yi ba damuwa, sai nayi masa waya domin ya shirya zuwan naku. Nima jikina yau a mace yake gaba ɗaya shi ya sa zan tafi gida yanzu.”

Dr Jamil ya faɗa yana miƙewa tsaye.

“To! Wani abu ne ya faru kuma ko bakajin daɗi ne?.”

Cewar Dr Abdallah. Girgiza kai Dr Jamil ya yi yana basa amsa da faɗin.

“Ko ɗaya Wallahi wata Baiwar Allah a ka kawo maza har uku suka yi raping nata kuma da alama sai da suka bata kayan maye, common 18 years da wuya yarinyar ta kai, abin dai gunin ban tausayi shi ne dalilin sanyin jikin nawa.”


Tamannah ta dubesa a karo na farko tun da ya shigo office ɗin jin abin da ya faɗa. Yayin da shi kuwa Dr Abdallah girgiza kai kurum ya yi, duk da cewa su likitoci ne suna ganin fiye da hakan ma amma sun kasa saba wa especially ma yanzu da lamura na fyaɗe ya yi yawa kamar babu hukuma.🤧

“But.. Nayi farin ciki ta wani ɓangaren ganin irin hukunci da su masu fyaɗen suka samu daidai da abin da suka aikata.”

Dr Abdallah ya dubesa yana faɗin. “Ƴan sanda ne suka hukunta su?.”

Sai da ya zura hannu a trouser pocket sannan ya ce. “Ko ɗaya wata ce dai mace mai kamar maza a yadda na sama labari daga bakin waɗan da abin ya faru da su, zan so kaga irin hukuncin da ta yi musu, ta yi daidai sai dai ina jiye ma ta abin da zai je ya dawo kasan yadda ƙasar tamu take gasu kuma ƴaƴan manya ne har da Yaron Mr Aabdar Dawlah fa.”


“Allah ya sa mu dace kawai.”


Cewar Dr Abdallah domin idan suka tsaya bin ta zancen sai su kwana sai dai fatan shiriya ga ɓata garin kawai. Daga haka suka rufe babin zancen, gaba
End Ads