nuni da sarƙar dake hannunta a cikin wata leda da suka saka.
“Good hakan ya yi ku ƙara bincika wa ƙila a sama wani abun. Amma muga sarƙar.”
Umnia ta faɗa tana duban sarƙar da kyau yayin da gabanta yake ɗan faɗi. Ta zubawa sarƙar dake cikin ledar idanu, tana duba gani take kamar ta san sarƙar sai dai a'ina ke nan?, Shi ne abin da ta kasa tunawa. . .
____
*IRSHAD POV.*
Duk da cewa baya jin daɗi sosai kuma rashin jin daɗin nasa ya samo Asali ne sakamakon rasa selfsame nasa da ya yi sannan bai san a'ina zai same su ba shi ne dalilin damuwarsa har hakan yaso jan yo masa zazzafar zazzaɓi dan kuwa duk da bayaso amma haka nan sai da Dr yazo ya duba sa, sai dai hakan bai hanasa shirya wa a yau ya taho Mining Company ba.
*Ayi Manage da wannan, mu haɗu a next page domin jin yadda zata kaya.🥱*
_Mutane na facebook masu complain a kan rashin samun hanyar yimin magana ta account ɗina kuyi haƙuri ni kaina ban san dalilin hakan ba. Akwai sabon account ɗina Nainarh KD zan saka Link nasa ayi supporting ɗina ta hanyar sharing and following please mutanen Amana 😍 kuma mai son magana dani ta facebook zai iya samuna ta New account ɗin nawa 👏_
_Masoya ina ganin saƙon fatan Alkhairi ina matuƙar godiya da ƙaunar ku tare da fatan Alkhairin ku a gareni Ubangiji ya bar ƙauna tare da zumunci.🥳🤩👏_
A makare ta ƙari so Mining Company ɗin da ya kasance yau zata fara aiki matsayin malamar jinya.
Sauri sauri ta fito daga napep ɗin da ta zo ciki bayan ta biya mai napep ɗin kuɗin sa sannan ta fara tafiya ba tare da kallon gabanta ba sakamakon ƙoƙarin goya bagpack ɗin ta da kayan aikin ta suke ciki da take yi, taji ta yi karo da mutum da har hakan ya yi sanadiyar zubewar wayoyin dake hannunsa a ƙasa, a hanzarce ta ɗa go kanta domin bawa ko wanene haƙuri, ai kuwa idanunta suka shige cikin nasa idanun da suke a ɗan lumshe.
“Sorry Sir sam ban lura da kai ba.”
Ta faɗa tana duban sa tare da miƙa masa wayoyinsa da suka faɗi a ƙasa, sannan ta yi gaba bayan ya karɓa ba tare da ya ce ma ta komai ba. Shi kuwa Irshad dafe kansa dake ɗan sara masa ya yi ya yanke shawarar gwara ya koma gida kawai domin sosai baya jin daɗi.
A hankali ya buɗe idanunsa dake a lumshe da niyyar ya ƙari sa motarsa sai dai cikin rashin Sa'a idanun nasa suka hango masa ita, wato ita ba Abida matar mahaifinsa matar da duk Duniya babu wata mace da yaƙi jinin ya ganta kusa da shi sama da ita, a bazata ya ganta kuma inda yake take nufowa, haka kawai jikinsa ya fara rawa na ɓacin ran Ganinta ne ko shakkan ta? Shi kansa bai sa ni ba, abin da ya sa ni kawai shi ne ta saka masa tsoronta tun yana yaro sakamakon azabtar war da ta yi ta masa, wannan shi ne kaɗan daga cikin dalilan da suka saka ko hanya bayason haɗa wa da ita, ko'a gida ɓangaren ta daban shi ya sa ba sama haɗuwa balle wani abun ya biyo baya.
Baya ya yi domin guje ma ta, ai kuwa ya yi tuntuɓe da marmara na duwatsun dake wurin ya yi taga taga kamar zai faɗi sakamakon jikinsa da sam babu Gwari hakan ma ba ƙaramin ƙoƙari yake ba, Maiji da ta juyo sakamakon wayarta da ta haɗa masa da shi lokacin da take basa nashi, sai da ta yi gaba sannan ta gane hakan, ta juyo domin ta karɓa wayar nata, ta yi saurin tare sa tana zaro ido ganin mutum da lafiyarsa yana ƙoƙarin faɗi.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke a lokacin da Hajiya Abidar ta yi gaba tana amsa waya abin ta, mamakin sa bai wuce a kan mene ne ya kawo ta Mining Company ba.
“Kana lafiya kuwa?.”
Maiji ta tambaya bayan ta taimaka masa ya saita tsayuwar sa.
“Idanunka sun yi ja jikin ka da ɗumi da alama bakajin daɗi.”
Ta kuma faɗa ba tare da ta jira ya amsa ma ta tambayar da ta yi masa sa farko ba.
Bai iya magana ba, sai nuni da mota da ya yi ma ta sannan ya miƙa ma ta keys dake hannunsa. Jinjina kai ta yi tana duban motar tafiya kaɗan za'a ƙari sa wurin da take a fa ke, daurewa ta yi ta taimaka masa ya ƙari sa wurin motar ya shiga mazaunin driver ita kuma ta juya zata tafi, sai dai jin an riƙe hannunta yasa ta juya da sauri tana dubansa ita fa so take ta bar wurin ko ƙwaƙwalwarta ta sama damar tunani a kan kamannin da take hangowa a fuskarsa sak Nanay ɗin ta.
“Please karki tafi Please i need your help.”
Ya faɗa cikin wata kasalalliyar murya da ciwo yaji ƙarfin ta.
Zaro ido Maiji ta yi tana tunanin abin yi, yanzu ita ya zata yi ne da wannan mutumin mai kama da sak da Nanay ɗin ta gashi kamar bai da lafiya kuma taimakon ta yake nema.
Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da wayarsa ta yi ƙara sai a lokacin ta tuna bata ma amsa wayar nata dake tare da shi ba.
Gaba ɗaya suka zubawa wayar ido, alama ya yi ma ta da ta ɗa ga. Ta ɗan curo hannunta cikin motar sannan ta ɗauki wayar tare da picking ta saka speakern gaba ɗaya.
“Hello Pooh kanajina?.”
Abin da a ka faɗa ke nan bayan ta ɗa ga kiran. Dubansa ta yi, ya yi ma ta alama da ta yi magana. Sai da ta haɗiye wani abu mai kama da yawu sannan ta ce.
“Bashi ba ne Maiji ce bayajin daɗi ne.”
Ta faɗa tana jiran amsa.
“To! Maiji kuma? kuna ina ne haka?.”
Mai kiran da Maiji ta ga an yi saving da BFA (Best-Friend-Aunt) ta faɗa muryarta yana nuna ɗan tashin hankali da ta shiga.
“Ki kwantar da hankalin ki muna a Mining Company ne kiyi min kwatancen gidan sai na tuƙosa naga kamar ba zai iya tuƙi ba.”
Cewar Maiji. Kwantar da hankalin nata da ya fara tashi Aunty ta yi sannan ta yi ma Maiji kwatancen Anguwar da gidan, sannan Maiji ta kashe wayar ta shiga motar bayan ta samu ya koma gidan baya da kyar, mamaki fal ranta na wannan lamarin har ta ƙari sa can katafariyar unguwar.
★ . . .
*SADDIQA POV.*
Da gudu ta shiga palon tana jifa da figigin mayafi wanda da shi gwara babu dake kanta a saman luxury sofa dake palon.
“Mom! Mom!!.”
Shi ne kawai sunan da take kira hawaye shaɓe shaɓe a fuskarta kamar wata yarinya.
Ganin babu kowa a palon ne ya sa ta fara taka stairs ta nufa up bata dena kiran Mom ba.
Faɗa wa bedroom ɗin ta yi ba tare da ta yi sallama ba. Hajiya Abida dake waya ta yi saurin kashewa ta dubeta tana ɓoye ɓacin ran ta ta ce.
“Mene ne kuma?.”
Ta faɗa tana bubbuga bayan ta alamar rarrashi bayan ta rungumo ta.
Cikin Wata kalar shagwaɓaɓɓiyar murya na shagwaɓaɓɓun yara Saddiqa budurwar da ta haura shekaru Ashirin da uku ta ce.
“Mom ba Pooh ba ne, ganinsa fa nayi da wata yarinya ta kawo sa gidan nan ƙilama budurwar sa ce, Mom tsoro nakeji kar Pooh ya ƙara suɓu ce mana a wannan karon bayan ƙoƙarin da muka yi a kan sa mun rabasa da duk wata yarinya da ta shiga Rayuwarsa har waɗan nan marayun ƴan biyun da babu wanda ya san yana tare dasu saimu da muke bin sahun sa duk inda yasa ƙafa, kawai dan na mallakesa matsayin miji a gareni, muka saka masa tsanar mata da soyayyar gaba ɗaya sannan muka saka ya manta da lamarin waɗan nan ƴan biyun gashi yanzu sai da komai yazo gab yake ƙoƙarin suɓu ce mana gashi daɗi da ƙari ko kyakkyawan kallo ban taɓa samu daga garesa ba.”
Ta ƙari sa maganar tana mai matsar kwalla tare da yin shiru domin jin abin da uwar rainon nata wato Hajiya Abida Yayar mahaifiyar ta da ta rasu zata faɗa tana fata wannan salon da tazo da shi ya yi aiki, Hajiya Abida ta yi wani abun ko ta samu ta mallaki muradin ranta wato Irshad mutumin da ko kallon arziƙi bata taɓa samu daga gare sa ba, gashi kullum ƙara nitso take cikin kogin son sa. . .
A ɓangaren Hajiya Abida kuwa ta saki wani ɗan iskan murmushi tana saving record na Muryar Saddiqa da ta ɗauka lokacin da take zubo wannan maganganu na abin da suka aikata ma Irshad, tasan za'ayi hakan shi ya sa tun kafin Saddiqa ta shigo Ɗakin ita kuma ta yi sauri ta barbaɗa garin magani da bokan ta ya bata yace muddun Saddiqa ta taka da kanta zata faɗi duka abin da suka yi ma Irshad wanda ita kuma Hajiya Abidar hakan takeso domin wani tarkon daban zata ɗana wa Saddiqan da wannan record ɗin. Hauka take ta bari jinin ta ya haɗu da na Aabirah (wato mahaifiyar Irshad) matar da ta Aure ma ta mutumin da ta fi ƙauna a Duniya sama da kowa, ita kuma ta kasa haƙura sai da tasan yadda ta yi ta shiga ta fita wurin Malaman ta a wancan lokacin har sai da Alhaji Khalil I Khalil ya saki Aabirah sannan ita ya aure ta.
Ɗa go Saddiqan ta yi tana sha re ma ta hawayen dake kuma tun ta, ta ce.
“Ba dai Irshad ba ne? duk dan saboda shi ne kike zubar da hawayen ki ko? To nayi miki alƙawari daga yanzu ba zaki ƙara zubar da hawaye saboda shi ba, domin zaki mallakesa gaba ɗayansa sai abin da kikeson ya yi shi ne kawai zai aikata muddun ina nan.”
Ta ƙari sa maganar tana jinjina ma ta kai alamar da gaske take faɗar abin da ta faɗa.
Cike da farin ciki Saddiqa ta rungumo ta tana faɗin. “You are the best Mom ina son ki.”
Ta faɗa tana sakin dariya mara sauti ganin haƙan ta ya cimma Ruwa, ta lura wannan Hajiya Abidar idan ba ana haɗa ma ta da bariki ba, tofa ba zata taimaka mata wurin ganin ta mallaki muradin ranta ba.
Ɓangaren Hajiya Abida ita ma kyakkyawar murmushi ta saki tana bubbuga bayan Saddiqa. “Hhhh yaro bai san wuta ba sai ya taka. .!” Ta faɗa hakan a ranta.
Wannan abu shi a ke kira da, a rashin sani, bako ya sha ruwan wanka!. ( Tofa! Hajiya Abida da Saddiqa zamuga yadda zata kaya tsakanin ku...🤔)
★. . .
*-25, Aminu Kano Crescent, Wuse, Abuja, Nigeria.*
9:45 Na Dare.
“Yanzu ya za'ayi da recording ɗin nan ke nan?.”
Neina ta tambaya tana dubansu.
Bubba ya ce.
“Ina ga a bawa Jami'an tsaro domin zai taimaka musu a ganina.”
Ya faɗa a nasa shawarar.
“An ya kuwa ni a ganina ban ga amfanin basun ba tun da ya riga ya mutu basu ɗin babu wani amfani.”
Cewar Ramla.
“E haka ne amma kuma ai zai taimaka musu ne wurin gano bayanai a kan ƙungiyar Zwandun Monster's ɗin nake ga.”
Maiji ta amsa da faɗin hakan.
“Duka kuna da gaskiya sai dai ni kam ban goya bayan a bawa jami'ai ba, gwara kawai mu ya ɗa shi a social media kowa ya gani.”
Lulu ce mai wannan maganar a yanzu. Gaba ɗaya dubanta suke suna nazarin maganar ta.
“An ya kuwa babu hatsari a hakan?.”
Bubba ya tambaya.
“Babu saboda ta hakan ne kawai al'umma zasu ankara da halin da a ke ciki, su ƙara kula kuma suyi taka tsantsan fiye da baya, ko ya kuka ce?.”
Ta tambaya tana dubansu gaba ɗaya domin a counseling room suke komai nasu suna yi da taka tsantsan da kuma kula.
“Good idea ina bayan ki muyi haka ɗin kawai kun ga sai mu buɗe sabon account wanda zamu yaɗa da shi ko?.”
Gaba ɗaya duk suka amsa domin shawara ce mai kyau ta kawo.
“Yanzu an wuce babin recording tun da an sama solution, saura magana ta biyu, ita ce a kan cewar da Prof ya yi kafin ya mutu da ya ce Samara tana raye, mene ne tunanin ku a kan hakan?.”
Neina ta yi tambayar tana dubansu. Gaba ɗaya suka yi shiru suna nazarin maganar domin magana babba wacce hankali ba zai ɗauka ba.
“Ni dai bana tunanin ƙarya yake saboda yana gaɓar mutuwa ya faɗa haka ɗin.”
Cewar Maiji. Ramla ma ta jinjina kai tana faɗin.
“Tabbas kuwa mutuwa zai yi a lokacin, koda ya yi ƙarya ba amfanar sa zata yi ba.”
“Bincike shi ne zai bayyana Komai kawai.”
Bubba ya faɗa.
Yayin da Lulu ta ce.
“A barshi ma tana rayen, ɗayan biyu ne kodai tana hannun su ko kuma tana wani hannu daban, sai dai ni nafi tunanin tana wurin su saboda haka yanzu turbar Binciken mu zamu ɗaura a kan gano wanene ainihin shugaban ƙungiyar Zwandun Monster's shi ne kawai.”
Gaba ɗaya suka jinjina kai cike da gamsuwa, Neina ta ce.
“Sannan mutane ukun nan wato Alhaji Haashir da Alhaji Umair Ubaydullah sai kuma Mr Aabdar Dawlah idan muka bibiyesu zamu iya gano wasu bayanan game da ƙungiyar saboda gaba ɗayan manyan members ne cikin ƙungiyar Zwandun Monster's ɗin.”
“Haka ne sai dai fa bibiyar lamarin su is not easy fa saboda mutane ne masu matuƙar hatsari sun san me suke yi kuma a mabanbantan wurare suke rayuwa hasali ma basu nuna wa Duniya su ɗin duka ukun suna mu'amala da juna ba sai a ɓoye.”
Maiji ce take wannan bayanin.
Lulu ta amsa da faɗin.
“E duk da hakan ai ba su zamu bibiya ba, iyalansu zamu bibiya, shi wannan Mr Aabdar Dawlah ɗin ba ya aurar da ƴar sa mafi soyuwa a garesa cikin ƴaƴansa ba ga wani mutum daban, to shi wannan mutumin muke son fara sa ni domin dole yana da ɓoyayyiyar alaƙa da Mr Aabdar Dawlah ɗin shi ya sa har shi Mr Aabdar ɗin ya aura masa ƴar sa kuma auren sirri, sannan sai Alhaji Umair Ubaydullah shi kuma wannan ke Maiji kece kikafi mu saninsa, matsayin sa na ƙani wurin mahaifin ki sannan sai Alhaji Haashir . . .”
Lulu ta yi shiru tana duban Neina sanin cewa shi ɗin tsohon Mijin Neina ɗin ne.
“E Alhaji Haashir ba na san shi ko nace nasan wani abu kaɗan a tare da shi shima wannan bibiyar sa ba zai mana wahala ba.”
Cewar Neina tana dan ne abin da ke taso ma ta na ɓacin rai idan ta tuna har ‘ya ce tsakanin ita da wannan azzalumin mutumin gashi ta sanadiyyar sa ‘yar tasu ta ɓata bata san ina ne zata ganta ba.
Maiji ta ce.
“Shima Alhaji Umair Ubaydullah ɗin bibiyar sa ba zai yi mana wahala ba.”
“Yawwa mutane na ina jinjina muku in sha Allah duka ƙoƙarin mu ba zai tashi a banza ba waɗan nan azzaluman mutanen Sannu a hankali zasu girbi abin da suka daɗe suna shukawa.”
Cewar Bubba.
“Tabbas kuwa domin ɗaurin talala Ubangiji ya yi musu badan ya manta da lamarin su ba.”
Cewar Ramla.
Da haka dai meeting ɗin nasu ya tashi ko wacce ta koma bedroom nata. Bayan sun gama tattaunawa a kan neman mafita.
Cewar Lulu a yayin da take saukowa daga matattakalan benen sanye cikin blouse satin tank shirt blue color sai kuma Ladies khakis trouser ƙafafunta cikin wasu bondage boot baƙi mai gaurayen golden, idanunta maƙale da round glasses da ya yi matuƙar dacewa da fuskar nata ta yi kyau sosai abin ta. Long upsweep black hair nata ta kama bayan ta sauko down tare da ɗaurewa sannan ta saka after dress dake hannunta, kana ta yafa mayafi fari mai ratsin golden. Ta dubi Fatiyya da ta saki baki da hanci tana kallon ta from head to toe.
“Wannan kallon fa, ko dai nayi kyau ne?.”
Ta tambaya ta wani killer smile.
Fatiyya da bakinta ya kasa rufuwa ta yi saurin amsa ma ta da faɗin.
“Ai kyau na ƙarshe ma Wallahi. Aunty Lulu kin gan ki kuwa sai kace SARAUNIYAR KYAU.”
Dariya Lulu ta yi tana faɗin.
“Kice na zama Afeefah Mai Kyau kawai.”😍
“Ai kin ma fita.”
Fatiyya ta kuma faɗa tana washe baki.
“An ya kuwa Fatiyya?, Afeefah Mai Kyau fa ƙarshen zance ce Indai fannin kyau ne.”
Lulun ta kuma faɗa tana buɗe handbag dake hannunta.
“Wa nake gani haka, wannan kwalliyar fa kamar mai shirin zuwa Gasar sarauniyar kyau ta Duniya?.”
Neina da ta fito daga kitchen ta tambaya.
Fatiyya ta washe baki tana amsa ma ta da faɗin.
“Wallahi kuwa Neina dubamin kam Aunty Lulu ce.”
Neina tana murmushi tare da yaba kwalliyar ta ce. “Ma sha Allah amma fa kin yi kyau Amma ta na.”
Fatiyya ta amsa ma ta da faɗin.
“Da akwai ƴan canji da an baki.”😂
Gaba ɗaya suka yi dariya.
“Ku dai kuka sa ni, Neina ayi mana addu'a yau unin restaurant zan yi.”
Cewar Lulu.
“Ma sha Allah, ai gwara dai ki fita kiga gari kullum kina a gida, sai kun dawo ƴan mata na, Ubangiji ya tsare hanya,."
Gaba ɗaya suka amsa ma ta suna dariya sannan Lulu da Fatiyya suka fita a tare, Neina ta bisu da addu'ar a dawo lafiya.
*Alhamdullilah mu tara a next page domin sanin ya zata kasance...*
_Assalamu Alaikum al'ummar Musulmai maza da mata masu karatu dama marubutan fatan Alkhairi ga kowa, dama wata magana ce dani da ta daɗe tana cin raina nakeso nayi muku wani ƙarin haske, maganar ita ce a kan kallon marubuta da a ke yi matsayin masu gurɓata tarbiyya especially ma mu online writer's, yes a komai zaka samu akwai na gari akwai kuma na banza, to haka muma a cikin mu akwai masu ɓatawan akwai kuma waɗan da Burin su su gyara ba wai su ɓata ba, sai dai duk kallo guda a ke mana matsayin duk ba na gari ba ne, kuma wannan ba gaskiya ba ne sannan duk wata marubuciyar online ko marubuci muddun tsakani da Allah yake rubutun sa kuma ya tsaftace alƙalamin sa zaka samu wannan kallo da a ke mana