ya ƙari sa wani wuri cikin Ɗakin ya buɗe locker dake wurin sannan ya ciro takardun ya miƙa wa Mr Aabdar Dawlah.
“Gashi nan na baku ku taimaka ku kyale min matata yarinya ce bata da laifin komai kuma batasan komai ba.”
Mr Aabdar Dawlah ya karɓi takardun yana ma le baki ya dubi sauran abokin neman Duniyan nasa yana wata shegiyar dariya ya miƙa musu takardun ai kuwa take a wurin suka yayyaga ta gutsire gutsire gaba ɗaya suna sakin dariyar Nasara.
Yazan ya miƙe a daddafe domin ya ƙari sa wurin Matarsa. Daidai lokacin kuma ɗaya daga cikin masu kama da samu dawan nan da Mr Aabdar Dawlah ya yi ma alama da ido a lokacin da Yazan ya juya, mutumin ya saita bindigar sa ya ɗana tare da sakin ta saitin goshin Yazan...
Tass...!
Kakeji gaba ɗaya Ɗakin lokaci guda ya amsa da ƙarar harbin. Yayin da Yazan ya zube ƙasa ko shurawa bai yi ba, idanunsa a buɗe suna zubar da kwalla kuma suna duban Ramla. Da jikinta ya ƙame ƙam fuskarta sharkar da jinin Yazan da ya fallasa a saman fuskar nata, idanunta a zazzare cikin maƙurar tashin hankali da kiɗima tun lokacin da jinin nasa ya fallatsa a fuskarta bayan an harbesa ta saki ihu tare da ƙamewa a wurin alamar ta suma a tsayen....😭😭
Gaba ɗaya suka sheƙe da dariya yayin da Mr Aabdar Dawlah yake bin Ramla da wani shegen lalataccen kallo. Bottle water da ɗaya daga cikin yaran nasu ya miƙa masa ya buɗe tare da watsa ma ta saman fuskarta sai dai ko gezau, ganin hakan ya sa ya watsa ma ta gaba ɗaya ruwan gorar mai sanyin gaske, ai kuwa ta ja dogon numfashi tare da zubewa a ƙasa badan ta kuma suma ba.
Girgiza kai kawai take yi tana duban yadda mutumin wato Mr Aabdar Dawlah yake tunkaro ta yana kuma yunƙurin cire kayan dake jikinsa amma duk da girgiza masa kan da take yi bai dena abin da yake yi ba, ganin haka ya sa ta daddage iya kar ƙarfin ta ta tashi tsaye da kyar sai dai tun kafin ta gama tsayuwar wani irin azababben zafi ya ziyarci kanta sakamakon kan bindiga da ɗaya daga cikin mazan ya buga mata. Faɗi ƙasa ta yi idanunta suna juyawa yayin da take fita a hayyacinta saboda tsananin azaba. Ta suma yafi a ƙirga tana tashi dan kanta kuma duk da hakan bai sa waɗan nan azzaluman mutane sun fasa daga abin da suka yi niyyar yi a gareta ba, tanaji tana gani bata da kataɓus ko wani dabara da zata kwaci kanta daga hannun waɗan nan azzalumai tun tana gane Duniyar da take har jinta da ganinta gaba ɗaya ya ɗauke. . . Sai farkawa ta yi ta tsinci kanta a gadon asibiti cikin matsananciyar jinya nan ne bayan ɗaukar dogon lokaci tana jinyar da har sai da mental problem ya kusa taɓa ƙwaƙwalwarta sannan cikin nufar Ubangiji ta dawo hayyacinta har take samun labari wurin wasu ‘yan mata su biyu da suka ce sun tsinceta bayan an ‘yar da ita a can wani kango shi ne suka kawo ta asibiti nan a ke sanar dasu cewar mummunan fyaɗe a ka ma ta kuma a ka watsar da ita a kango. . . Bayan sun kaita asibitin ma sai da ta kwashe watanni biyu sannan ta farfaɗo. . . Ta yi kuka sosai da tsanar Rayuwarta lokacin da suke bata wanann labarin. . . Anan ne take basu ainihin labarin ta suka tausaya ma ta sosai kuma suma suka bata nasu labarin. . . Sunayensu shi ne Samra da Mai Jiddarh ta yi matuƙar tausaya musu sosai a lokacin da taji LABARIN SU (BY Salma Ahmad Isah 🍬😍). . .
Wait! Ma tukunna wannan Alhaji Haashir ba shi ne mijin Neina ba 🤔 turƙashi! Akwai chakwakiya fa 🤨 mu haɗu a next page kawai inda zamu ɗaura da ci gaban labari. . . 🔥
_Nanameera (Queen Of Squad) And Fatahiyya Muhammad Yakasai (Oum Yasmeen) wannan feji kyauta ne a gare ku mutanen amana Allah ya bar zumunci.👏😘❤️_
_
E . 27.
*-25, Aminu Kano Crescent, Wuse, Abuja, Nigeria.*
7:45. Na safe.
“Barka da safiya.”
Maiji ta faɗa lokacin da ta shiga bedroom ɗin Lulu ta hangeta can bakin window tana tsaye hannunta riƙe da mug tana sipping yayin da idanunta ke kallon wuri guda da alama dai ta yi nisa a duniyar tunani.
Ganin da alama bata ji ta ba, ya sa Maiji ta ƙari sa wurin tare da dafa kafaɗarta tana kiran sunanta.
“Lulu! Lafiya kuwa?, tunanin mai kikeyi haka ina ta sallama baki ji ba?.”
Lulu ta ɗa go idanunta da suka yi ja alamar bata sama bacci ba a daren jiya, ta dubi Maiji sannan ta ɗan girgiza kai tana kawar da idanunta.
“Nima kaina ban san mene ne yake damuwa ba, abin da na sa ni kawai shi ne akwai aiki Babba a gabana, na kasa yarda da maganar Prof Bakori na cewa Samara bata mutu ba, nafi tunanin domin ya caza min ƙwaƙwalwata kawai ya faɗa, amma me ya sa zuciyata takeson aminta da zancen nasa?. Marh Ji (Da yake haka take kiran Maiji sometimes.) Ina buƙatar nasan gaskiya yanzu, ina nufin a wannan gaɓar, ji nake lokaci ya yi, a jikina nakejin wani abu yana daf da faruwa sai dai ban san ko mene ne ba.!”
Tun da ta fara maganar Maiji ta nutsu tana sauraren ta, ba kuma tare da ta dakatar da ita ba, har sai da ta kai aya, sannan Maiji ta sauke ajiyar zuciya nannauya tare da kamo Lulu ɗin ta zaunar da ita gefen Gado sannan ita ma ta zauna tana dubanta a nazarce kana ta fara magana cikin nutsuwa.
“Tabbas na iya fahimtar irin yanayin da kike ciki a yanzu, especially ma a kan maganar cewa Samara tana raye, bana ce komai ba a kai a halin yanzu, sai dai bana tunanin ƙarya yake yi kawai domin caza ƙwaƙwalwarki, ki tuna fa yana daf da mutuwa ne ya faɗa hakan, saboda haka bana tunanin ƙarya ya faɗa, bincike shi ne kawai zai bayyana dukkanin gaskiyar lamarin, Saboda haka ki kwantar da hankalin ki in sha Allah Samara tana raye kuma cikin kwanciyar hankali a kuma hannu mai kyau.”
Maiji ta ƙari sa maganar tana ɗan damƙe hannun Lulu dake cikin nata tare da ɗa ga mata kai alamar tabbatar da kalaman ta.
Lulu ta dubeta fuskarta babu wadataccen walwala ta ce.
“Na gode Marh Ji na gode miki da dukkanin kulawarki a gareni tabbas ke ɗin ta dabance kuma mai kyakkyawar zuciya ina fata Ubangiji ya bar mu tare har zuwa Ranar da zamuga ƙarshen waɗan nan azzaluman mutanen su girba abin da suka daɗe suna shukawa.”
Murmushi Maiji ta yi tana amsa wa da “Ameen. .!”
Haka take baka taɓa ganin fushin ta indai Maiji ce koda yaushe kyakkyawar fuskarta ɗauke take da murmushi ga kowa.
Ita ma Ramla dake tsaye bakin ƙofar bedroom ɗin da basu san lokacin da ta shigo ba, murmushi ta yi at the same time tana sha re hawayen da ya gangaro ma ta, sannan ta ƙari sa garesu tare da rungumo su gaba ɗaya tana sakin kuka.🥲
“Kin ganni kukan kuma na mene ne haka? Yanzu zaki saka muma mu fara.”
Cewar Lulu tana dubanta tare da sha re ma ta hawayen.
Maiji ta ce.
“Kai an ya kuwa Queen Lulu da Kuka abin ai zai yi banbara kwai fa, dama dai irin ne mu ne, mu ne kuka ya da ce damu, koba haka ba sister?.”
Ta faɗa tana duban Ramla.
“Tabbas kin faɗa daidai.”
Cewar Ramla ita ma tana dariya. Duka Lulu ta kai musu tana faɗin.
“Lallai ma wato saboda ni ba mace bace kun mayar dani wani abun daban, shi ya sa zaku ce bana kuka ko, ai naga kukan Rahama ne.”
Kauce wa suka yi Ramla tana bata amsa da cewa.
“E haka ne kuka rahama ne amma ai ke ɗin ta dabance bai dace dake ba dan kuwa na tabbatar shagwaɓa ma baki iya ba, kin dage sai kin mayar da kanki mai kamar maza.”😂
A fusace Lulu ta kuma kai ma ta bugun wasa, ai da sauri Ramla ta kauce tana dariya.
“Lallai Ramla na lura kin ga gadon bacci na da yawa, wato ni ce ban iya shagwaɓar ba ko, bakomai ai.”
Lulu ta faɗa kamar da gaske idan ance ta yi shagwaɓar zata iya.🙄
“A'a magana ta gaskiya fa a ke yi, mun ji cewa kin iya shagwaɓar to kiyi mana yanzu muji.”
Cewar Maiji.
“E kiyi mana muna sauraren ki Indai da gaske ne kin iya.”
Cewar Ramla ita ma dariyar take yi cike da nishaɗi da suka daɗe basu sama kansu ba a ciki.
Shiru Lulu ta yi taga alama sister's for love ɗin nata so suke su ƙureta wato saboda yau bata ɗaure fuska ba ko?.🙂
“Wato saboda kun mayar dani Laluh ba Lulu ba shi ya sa kuke son ƙureni ko to ba za a yi shagwaɓar ba na bita da gudu tumɓur.”
Kwashe wa da dariya suka yi har da tafawa. Ramla na faɗin.
“Ke dai kawai Malama ki yarda cewa baki iya shagwaɓa ba.”
“Haka dai kika ce.”
Cewar Lulu tana zazzare ido wai ita a dole an ce bata iya shagwaɓa ba.
“By the way sister's for love mene ne plan naku ne a gaba?.”
“Kamar ya ya ke nan?.”
Lulu ta tambaya jin abin da Maiji ta ce.
“Ai kam tambaya mana dai.”
Cewar Ramla.
Murmushi Maiji ta yi ta ce.
“I mean bayan komai ya ƙare, buƙatar mu ta biya an yi mana adalci a kan abin da azzalumai suka yi komai ya wuce, a lokacin mene ne kuka tsara ma Rayuwar ku?.”
Ta tambaya tana murmushi cike da zumuɗi tana dubansu gaba ɗaya.
“Tofah! Wata sabuwa in ji ƴan caca! Ni kam babu wani abu da nayi plan a halin yanzu.”
Cewar Ramla iya kar gaskiyarta.
“A'a dai ki dai yi tunani dole baza'a rasa wani abun ba.”
Maiji ta faɗa tana dubanta.
Ɗan shiru Ramla ta yi kamar mai tunani sai kuma can ta ce.
“E to kaɗan ne dai kuma shi ne bayan Komai ya wuce zan koma can Kaduna state wurin Dangina na zauna da su domin alƙawari nayi muddun ban sama adalci na zalunci da a ka mana ba. Ni da Yayana kuma mijina Yazan Allah ya yi masa rahama, tofa ba zan taɓa komawa gare su ba sai dai nayi matuƙar kewarsu sosai especially ma Zahra yarinyar kirki babu ruwanta.”
Gaba ɗaya dubanta suke cike da tausaya wa. Ajiyar zuciya Maiji ta sauke tana girgiza kai ta ce.
“Shikenan ko akwai wani abun?.”
“E to Akwai amma ba shi da wani muhimmanci sosai fa.”
Ta dubesu cikin rashin fahimta ganin yadda suka haɗa baki wurin tambayar. Ai kuwa suka kwashe da dariya.
“Mene ne kuma na dariyar?”
Ta tambaya da mamaki.
“Ah bakomai muna sauraren ki...”
Cewar Lulu tana ɓoye dariya.
“Na ma fasa faɗa baku da kirki yaran nan.”
Ramla ta faɗa tana ya mutsa fuska, dama maganar Mahbub taso ta yi musu amma ta fahimci cewa wani fahimta daban suka ma zancen shi ya sa ta fasa faɗa.
“Hhh koma wanene wannan wanin idan ta yi wari ma ji. Yawwa Lulu saura ke wani plan kika shirya ma Rayuwar ki a nan gaba kaɗan bayan komai ya lafa?.”
Cewar Maiji tana mayar da dubanta kan Lulu ɗin.
Shiru Lulu ta yi tana tunanin abin faɗa to mai ma zata ce ne?.
“Abin da na sa ni shi ne bayan faruwar komai kuma ta tabbata Samara tana raye bata mutu ba, zan yi iyakar bakin ƙoƙarina wurin ganin na nemo mahaifiyar mu domin a jikina nakejin tana raye bata mutu ba, zan tambaye ta wanene ainihin Mahaifin mu da kuma dalilin da ya sa ta kai mu gidan marayu bata ƙara neman mu ba, baya da waɗan nan akwai tarin tambayoyi da nake so nayi ma ta idan Ubangiji ya ƙaddara haɗuwar mu, sannan kuma sai shi, shima ina so na nemo sa, sannan nayi masa godiya na halarcin da ya yi mana a Rayuwa, nasan duk inda yake a yanzu hankalin sa baya a kwance na rashin ganin mu shekaru huɗu ke nan, wannan shi ne abin da yake zuciyata a kullum.”
Lulu ta yi maganar tana dubansu, ganin yadda duk jikinsu ya yi sanyi, ya sa ta yi murmushi tare da miƙewa tsaye tana faɗin.
“Mene ne kuma sister's Rayuwa ce fa mai cike da buri ka, ya naga jikin ku ya yi sanyi ne, karku damu wata ƙila ma Samara ɗin bata raye haka zalika shima Dimple Perfect gajiya ya yi da hidima damu shi ya sa ya bai nememu ba, sannan zata iya kasancewa ita ma takurawa rayuwar ta muke shi ya sa ta zaɓa ta kai ku gidan marayu ta yi nesa damu. . . Maiji ina ga ya kamata ki tashi ki tafi wurin aiki ko kin manta yau ne Ranar ki ta farko ki tafi kar ki makara kinji?.”
Lulu ta canza maganar da take yi tana duban Maiji.
Miƙe wa Maiji ta yi ta ce.
“To Lulu abin da kika ce shi za'ayi.”
“Yawwa ko ke fa Allah ya tallafa.”
“Yau kam me ke damun Lulu? Koma mene ne Allah ya shiga lamurran ki Lulu ta.”
Ramla ta faɗa a ranta. Yayin da ita kuwa Maiji a zuciyarta ƙudirtawa ta yi zata taya Lulu da addu'a kuma zata dage wajen ganin Lulun ta haɗu da waɗan nan mutane uku masu muhimmanci a Rayuwarta. Mahaifiyarta, Ƴar uwanta. Da kuma Dimple Perfect nata koda haka zai yi sanadiyar da ita zata rasa ta ta Rayuwar ne koda dama Rayuwar nata bata da wani muhimmanci tun da bata da wasu sauran Dangi da zata gani taji farin ciki, shi ɗin ya kashe ma ta kowa saboda bak'ar zuciya da neman Duniya ya kashe mata mahaifinta, mahaifiyar ta, da kuma Antyn ta mai ƙaunar ta Fiye da kowa. Bata tunanin mutane biyun nan zata taɓa yafe musu wato Tsohon Mijin Antyn ta da kuma Ƙanin Mahaifinta wato Alhaji Umair Ubaydullah sanadin su ta rasa kowa nata kuma duk wani farin ciki dake cikin Rayuwarta ya tarwatse. (Allah Sarki Maiji 😪🥲)
___
*UMNIA POV.*
“Good Morning Madam.”
Ɗan sandan ya faɗa yana sara ma ta.
“Morning yaka ke?.”
“Lafiya Lau Madam nan hanyar zamu bi.”
Ya faɗa yana ma ta nuni da palon da ake binciken wanda komai ya faru a ciki na mutuwar Professor da a ka waye gari da shi kuma D.G ya turo ta domin bincikar lamarin duk da cewa bata gama da case dake hannunta ba.
“Good.”
Ta faɗa sannan suka ƙari sa shiga ciki. Cikin nutsuwa tare da nazari take bin ko'ina da kallo bayan ta cire Glass dake idanunta.
“Mene ne ainihin abin da ya faru sannan ina iyalan Mamancin suke?.”
Ta tambaya Ɗan sandan dake kusa da ita.
“Gasu can ta can Madam sannan abin da muka gane a binciken da muka fara shi ne ya mutu ne sanadin bomp da ya tashi a saitin zuciyarsa Irin wannan na'urar ne da ƴan ta'adda suka fi amfani da ita.”
Duban jami'an da suke cike da palon ta yi tun daga kan forensic da suke baje sai faman tattara hujjoji suke da ma sauran jami'an dake wurin sannan ta mayar da kallon ta kan Iyalan Prof ɗin da suke wuri guda kamar dai a firgice suke daga ƙarshe ta sauke idanunta a kan saurayin da yake Babban ɗan Prof kuma a gaban sa komai ya faru, tafiya ta fara yi har ta ƙari sa wurin da yake tsaye daga gefe ya harɗe hannu a ƙirji kamar mai tunanin wani abun daban.
“Madam sunan sa Aminullah shi ne Babban yaron prof kuma yana nan a daren jiya lokacin da abin ya faru.”
Ɗan sandan wanda da alama aikinsa ke nan bata bayanai ya faɗa hakan.
Jinjina kai ta yi tana mirza hannunta sannan ta ce.
“Malam Aminullah jiya da dare an ce a gaban ka komai ya faru, shin zaka iya mana bayani dalla dalla na abin da ya faru?.”
Ta tambaya tana dubansa.
Sai a lokacin ya kalle ta tare da sauke ajiyar zuciya yana tunanin ta inda zai fara to mai ma zai ce musu bayan sanin komai da ya yi a yanzu, ya faɗa musu gaskiya sunan mahaifinsu da ya riga ya mutu ya ɓaci a kan abubuwan da ya aikata ko kuwa ya musu bayani a kan mutanen da suka ja faruwar hakan duk da cewa adalci suke nema na abin da mahaifin nasa ya yi musu.
“Bazan iya tuna komai da ya faru ba saboda su mutanen da suka zo sun rufe fuskokinsu kuma na nema nayi musu gardama wannan dalilin ya sa suka buga min wani abu a kai da hakan ya yi sanadin da har na suma saboda haka bazan iya tuna komai ba.”
Ya faɗa hakan yana musu nuni da iya kar abin da ya sa ni ke nan. Ya nema ya ɓoye ainihin abin da ya faru ne saboda kimar ahalinsa a idon duniya sannan kuma bazai so ya bada gudunmawa da har Rayuwarta zai shiga hatsari ba ita ɗin da ya ga kyakkyawar fuskarta kuma ta tafi da shi wani abu da ake kira da Love at first sight ya faru da shi a lokacin da ya fara ganin iyakar fuskarta kawai. (Lallai Aminullah ka ɗauka dala ba gammo 😳🧐)
Shiru Umnia ta yi tana dubansa tare da nazarin sa da kalaman sa, ta yarda ba gaskiya yake faɗa ba, dole dai Akwai abin da yake ɓoyewa, sai dai koma mene ne zata lalubo.
“Shin zaka iya tuna ko su nawa ne?.”
Ta kuma masa tambayar.
“E su biyar ne, kuma maza da mata ne bazan iya banbance su ba.”
Ya bata amsa. Zata kuma magana sai dai ƙari so wurin da wata daga cikin forensic ɗin ta yi shi ne ya hanata faɗar abin da ta yi niyya.
“Kun sama wani abun ne?.”
Ta tambaya.
“E Madam wannan sarƙar ne kuma akwai zanen yatsu a jiki ina ga zamu iya gane ko wanene ta hanyar zanen yatsun.”