x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - RANAR BIYAN BUƘATA Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 59040 words

Category: Love Stories

Views 281

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
Down jikinta a sanyaye.

Maiji ta fara knocking ƙofar tare da kiran sunan ta. “Lulu.”


_
*- 100, Lake Chad Crescent, Maitama, Abuja, Nigeria*


“Baki dawo da wuri ba. Yau kam kin makara.”

Ya faɗa yana ƙari sa saukowa Downstairs ɗin tare da ƙari sawa Dining Area ya riƙe kujerar Dining ɗin ba tare da ya zauna ba yana mayar da idanunsa kan ta.


Ya mutsa fuska ta yi alamar gajiya tare da zama saman luxury sofa na palon ta fara kwance igiyoyin takalmin ƙafarta sannan ta ce.


“Lamari ne na kisan kai kuma commissioner na ƙasar baki ɗaya aka kashe sannan binciken a hannuna D.G ya ɗaura gaba ɗaya so i need to be very very careful a kai that's why har lokaci ya ƙure ban dawo ba.”



“Wai.! Kisan kai kuma commissioner aka kashe nicely kice wani sabon kwaron yana daf da bayyana ke nan tun da ya fara da kawar da Babban kwaron.”


Ya yi maganar silently da Muryarsa nutsatsitsya yana zama a kan kujerar Dining ɗin tare da kai Cup of jitter juice bakinsa ya fara sipping cikin nutsuwa. Ya ci gaba da faɗin. “Ai kuwa tun yau ga alamun zaki iya da case ɗin ma tun da har kin manta kin shigo palo da takalmi duka a cikin gajiya.”



“Hamraz..”!


Ta kira sunansa da ɗan ƙarfi ba tare da kallesa ba tana mirza hannunta na dama da alama hakan ɗabi'arta ne.

“Yeah Sunan na ne.”


“Ba zaka kiyaye ni ba ko?.”


“Me kuma nayi?.”


Ya tambaya yana Murmushi.


“Ka faɗa Alkhairi ko kayi shiru.”


“Wani abu mummana na faɗa just Babban kwaro fa nace.”


Ya faɗa yana ɗage kafa ɗa tare da sakin Murmushi kamar yadda ya saba idan yana so ya ƙullar da ita. Ai kuwa ta ƙulu. A fusace ta miƙe ta nufesa niyyar ta ta kifa masa naushi a wanann kyakyawar fuskar tasa ta ɓatar da wannan dimple ɗin da idan ya yi Dariya yake ƙara ƙullar da ita. Da sauri ya miƙe tsaye bayan ya a je Cup dake hannunsa.


“Wato kinje kin kwaso zafin kai wurin aiki shi ne zaki sauke a kaina innocent dani ko?.”


Ya faɗa yana kuma ma ta murmushi tare da ɗage kafa ɗa. Ganin ta nufesa gadan gadan ya sa da sauri ya nufa wani ɗan corridor dake can gefe a palon ya danna wasu lambobi tare da shige wa Room da ke wurin.


“Ka dakata mana kanaji ko wai ina Bittu ita fa zan tambaye ka.”


Ajiyar zuciya ta sauke tana Murmushi ganin ya shige Room ɗin, wato dai ganin ta dawo da alama kuma bata cikin walwala, sai da yasan yadda ya yi ya saka ta yi Murmushi.


Up ta haye direct ta nufa wani Bedroom ta shiga ta a je agogon ta da sauran tarkacen ta saman dressing mirror sannan direct bathroom ta shiga ta yi wanka bayan ta fito ta shirya cikin wata doguwar riga shirtwaist tare da saka ribbon ta tufke gashin kanta sannan ta zura dogon Hijab ta fito bayan ta gama abin da zatayi direct Downstairs ta sauko ta nufa corridor da Hamraz yabi ɗazu ta danna lambobi tare da shiga cikin Room ɗin da sallama ɗauke a bakinta.


“Assalamu Alaikum.”


Juyowa Hamraz dake zaune saman wata folding chair ya yi yana kallon ta tare da amsa ma ta sallamar ta ƙari sa, ba tare da ta zauna ba ta tsaya jikin gadon marasa lafiya dake Room ɗin wata matashiyar budurwa kwance akai an saka ma ta oxygen.


“Ya jikin nata Malam Likita?.”


Ta tambaya tana kallon sa yayin da shi kuma idanunsa yake a kan Budurwar dake kwance bata ma san Duniyar da take ba.


“Gashi nan fa Alhamdulillah zuwa yanzu kam.”


“Ma sha Allah Dr Hadiza tazo ne?.”


“E ita ce ma take tabbatar min da cewa in sha Allah Yarinyar tana dab da farfaɗo wa daga doguwar suma da ta faɗa.”


Cikin gamsuwa da bayanin nasa ta jinjina kai tare da faɗin.

“Alla ya sa.”

“Kar ki damu da Bittu tabi Dr ɗazu ta ce a can zata kwana.”


Ya faɗa tunawa da tambayar sa Bittu da ta yi a ɗazu.

___

*-25, Aminu Kano Crescent, Wuse, Abuja, Nigeria*


“Lulu wai mene ne gaba ɗaya kinbi kin sauya daga jin labarin mutuwar commissioner?. A tunanina farin ciki ya kamata kiyi na mutuwar wannan mugun mutumin bawai ki hana kanki sukuni ba.”


Lulu ta juyo a kai kaice tana kallon Maiji da ta yi maganar Sannan ta ce.


“Ban so ace ya mutu ba'a hannuna ba. Maiji naso ace tsananin azabar da zan yi ma wannan mugun da bai san Allah ba shi ne zai yi sanadiyar mutuwarsa. Wanene wannan mutumin da ya riga mu ganin bayan commissioner waye shi , shi ne abin da nakeson sa ni kawai a halin yanzu.”


Maiji ta zaro ido ganin yadda Lulu take maganar jikinta gaba ɗaya mugun rawa yake yi kai da gani kasan ranta a mugun ɓace yake bakinta kuwa har jini ya fara fitowa daga ciki, wani irin baƙin jini haka ma hancinta, idanunta sun kaɗa sun yi jajur da ɓacin rai.


Da sauri ta yagi tissue tare da miƙa ma ta. “Kiyi haƙuri ki manta da wannan tun da shi Commissioner ya mutu mu yi tunani a kan next target na mu kawai na tabbatar Miki zamu gano wanene ya kashe shi da kuma dalilin sa.”


Karɓan tissue ɗin ta yi, sannan ta fara goge bakinta wuraren da jini ya ɓata ba tare da ta ce ma Maiji komai ba.


Idanunta a kan mirror da take tsaye gabansa ta ce. “Ina Ramla?.”



“Mun yi waya da ita ɗazu ta fita ne amma ta kusa dawowa.”


“Okay..” Ta faɗa wani abu dake fuskarta yana jan hankalin ta. Hannu ta kai ta shafa wurin, bille ne guda biyu a wurin da suka haɗe suka bada alamar X. Shiru ta yi tana ƙoƙarin tariyo ainihin mussabbabin zaman wurin a hakan.


*Flash Back....*


Da gudu Yarinyar da ba za ta haure shekaru Biyar ba a Duniya ta shiga Ɗakin tana faman kiran sunan Aunty Aunty.


Matar dake ta can wurin wardrobe tsaye ta juyo tare da kallon ta fuskarta ɗauke da murmushi ta ce. “Samara mene ne kike kirana haka?.”


Yarinyar tana faman sauke haki na gudun da ta yi cikin maganar ta da bata fita sosai take faman faɗin. “Aunty kizo ga Samra can ta yanka fuskarta da reza yana fitar da jini.”
Ta yi maganar tana ma ta nuni da waje. Cikin sauri ba tare da ta jira Samara ta ƙari sa maganar ba. Aunty ta nufa ƙofa hankali tashe ta fito daga Bedroom ɗin ta ƙasa wurin Samra dake zaune a tsakiyar palon tana ƙarewa kanta kallo a madubin dake hannunta.


“Samra! Samra!! Mene ne haka kika yi jini ne fa yake zuba a fuskarki.”


Aunty ta yi maganar hankali tashe tana riƙe hannun Ɗiyar nata. Murmushi Samra ta yi cikin Muryarta mai daɗi ta ce. “Bille fa nayi Aunty. Gani nayi wanda aka yi min bai fito cocai ba shi ne fa nace zan ƙarayi domin ya fito cocai, cai gaji nayi ba daidai ba.”


Shiru Aunty ta yi cike da mamaki take bin Ɗiyar nata Samra da bata wuce shekaru biyar ba a Duniya da kallon tsaban al'ajabi tare da mamakin Yarinyar, kasa magana ma ta yi.....


_

“Lulu! Lulu!! Lafiya kuwa tunanin mai kikeyi?.”


Maiji ta tambaya ganin yadda Lulu ta zuba wa wuri guda ido tana kallo.


Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Maiji ɗin, ta bata amsa da faɗin. “Nothing, forget it kawai.”

___________

*WANENE MAKASHIN COMMISSIONER, MENE NE DALILIN SA⁉️*

*HAMRAZ DA OFFICER UMNIA, SU WAYE MENE NE ALAƘAR DAKE TSAKANIN SU, WACECE BUDURWA DA SUKE JINYARTA A SIRRAN CE CIKIN GIDAN SU⁉️*

*LULU, MAIJI, FATIYYA, MENE NE A ZUCIYAR SU DANGANE DA MUTUWAR COMMISSIONER ⁉️*

*SHIN WANENE MA SHI COMMISSIONER ƊIN SHI KANSHI⁉️*


*KUNA SON SANIN DUKKANIN AMSOSHIN WAƊAN NAN TAMBAYOYIN ⁉️*

*KU BIYO NI CIKIN WANNAN TAFIYAR KAWAI. KUN DAI JI KAƊAN DAGA CIKIN SALON...!💔🔥*



_____
*🌹 Perfectly Pen's ✍️✊*


*Our Ongoing Book's...✍️*


*1_ƘADDARA CE!.*

*BY: C Candy.*

*2_SHIRYAYYIYAR ƘADDARA.*

*BY: Queen Kainaat.*


*3_RANAR BIYAN BUƘATA.*

*BY: Nainarh KD Nkd's.*


*4_DESTINY LOVE.*

*BY: Oum Yasmeen.*



*Mun Shirya tsaf domin kawo muku daɗaɗan littattafan mu masu cike da ilmantar wa faɗakarwa tunatar wa wa'azantar wa har ma da Nishaɗantar wa.💝*



*🔥Kada ki bari wannan tafiyar ya kasance ba tare dake ba. Don't Miss It Dearest sisters 🔥*.



_____

*Masu Buƙatar a haɗa musu Book Cover ko banner, poster, birthday flyer, flyer, logo e.t.c dai duka Muna yi cikin farashi mai rahusa ku tuntuɓe wannan lambar (0708 521 2808.)*


𝑃𝑒𝑟𝑓𝑒𝑐𝑡𝑙𝑦 𝑝𝑒𝑛'𝑠..... ✍💫


*💫...RANAR BIYAN BUƘATA...💫*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_

*© Nainarh KD Nkd's... ✍️*


*Wattpad: @Nainarhkd3.*

_Dedicated To Oum Yasmeen.💖_

*Ep_5-6*



*Freetown Street, Aminu Kano Crescent, Wuse, Abuja, Nigeria.*


Ta ƙara riƙe steering da kyau ta tattara gaba ɗaya hankalinta a kan wayar da take, cikin shagwaɓa ta ci gaba da cewa.


“Allah da gaske nake Neina na ƙosa ki dawo gaba ɗaya gidan duk babu daɗi sam, Fatiyya har kuka take na rashin ki a kusa three days ke nan fa.”


Shiru ta ɗan yi tana sauraren abin da a ke faɗa ta wayar. Dariya ta yi daidai lokacin da taji ta bugi wani abu da motar nata, saurin ɗa go kanta ta yi tana kallon titin domin son hango wanda ta bige.
“Neina zan kiraki ina ga nayi karɓa fa.”
Ta faɗa hakan ba tare da jiran amsar Neina ɗin ba ta katse kiran sauri sauri ta fito daga motar hankali a ɗan tashe.


“Sannu fa bakaji ciwo ba kayi haƙuri ban lura ba ne.”


Ta faɗa daidai lokacin da ta ƙari sa wurin ta ɗan durƙusa kamar yadda shima mutumin wanda da alama a ƙafa ya bugu yake a durƙushe.

Miƙewa tsaye ya yi ba tare da ya ce ma ta bakomai yana ɗan karkaɗe jikinsa. Ita ma miƙewan ta yi. “Kayi haƙuri fa.”

Sai a lokacin ya ɗan kalleta kaɗan tare da buɗe a cikin nutsatsitsyar kamilalliyar muryarsa ya ce.

“Kar ki damu fa babu komai laifi na ne ma dana hau titi ba tare dana duba hanya ba.”

Ɗa go da idanunta ta yi ta kallesa jin yadda daddaɗar muryarsa ta karaɗe majiyar sautin ta tare da haifar ma ta da mummanar bugu a ƙirji da bata san dalilin ba.

Dogo ne shi fari sanye da khaki trouser sai kuma riga hoodie da ya rufe kusan rabin fuskarsa da hular rigar yana sanye da takalma sneakers. Kamilalliyar kyakyawar fuskarsa da take kusan rufe ya mutse da alama ta ɗan bigen shi. Abin da ta iya lura daga garesa a ɗan ɗagowar da ta yi shi ne alama ba irin mutanen nan masu yawan surutu ko hayaniya ba ne, saboda haka ta sauke ajiyar zuciya tare faɗin.

“Tohm, duk da hakan dai ina baka haƙuri. Allah ya tsare gaba.”

Ta faɗa tare da juyawa zata koma motarta. “Am nace bakiji ba.”

“Na'am.”

Ta juyo tana amsawa.


“Ki dena waya a lokacin da kike tuƙi akwai kasada, ya fiye miki ki sama gefan hanya ki faka motar sannan kiyi wayar ki, ke kanki zakifi samun nutsuwa.”

Jinjina kai ta yi alamar gamsuwa sam bataji haushin maganar ba.

“Na gode da shawara and sunana Ramla pleasure to meet Yallaɓai.”


Ta faɗa abin ta ba tare da jiran amsar sa ba, ta shiga motar tare da ja ta ɗauki hanya. Yayin da shi kuma ya harɗe hannu bibbiyu tare da bin ta da kallon nazari ya ɗan taɓe baki yana ɗan murmushi. “Nice girl.” Ya faɗa a taƙaice tare da nufar wata mota ƙirar Maruti Suzuki swift ya shiga mazaunin Driver sannan ya ja motar shima ya ɗauki wani hanyar.....



___
(★†★)
___
*-100, Lake Chad Crescent, Maitama, Abuja, Nigeria*

*7:50 Na safe.*



Da sallama ɗauke a bakinta ta tura ƙofar tare da shiga ciki. Hamraz dake zaune kamar koda yaushe saman folding chair hannunsa ɗauke da wani Book yana dubawa, ya ɗa go tare da kallon ta yana amsa sallamar.


Ƙari sawa Umnia ta yi taja kujera ta zauna idanunta a kan gadon da Budurwar ke zaune.

“Kardai kace anan ka kwana?.”

Ta faɗa ba tare da ta kallesa ba. Murmushi ya yi kaɗan yana shafa askin stubble medium dake fuskarsa ya ce.


“Yana iya kam ita ɗin jin ta nake canca ƙoluwa, that's why nakeji bazan iya bari ta kwana ita kaɗai ba, gashi kuma Dr ta ce za ta iya farfaɗo wa a ko wani lokaci.”


Jinjina kai Umnia ta yi bata sauke idanunta daga kallon farar fuskar Budurwar ba, da ta yi fayau da ita tana tuna wasu watanni baya da suka tsinceta cikin hali na neman taimako kuma motar su bisa aka si ta bugeta kuma har zuwa yau bata farfaɗo ba balle su san wacece ita ko sunanta da kuma dalilin shigarta wannan mummanar halin duk da cewa cikin jini suka tsinceta a lokacin sai dai Dr Hadiza ta tabbatar musu da babu alamar keta haddi a tare da ita, balle su yi tunanin ko ɓata gari ne suka yi raping nata suka barta a tsakiyar titi. Su bada lokaci kawai akwai abun da ya yi matuƙar firgita ta shi ne dalilin faɗa warta doguwar suma.


“Ina ga fa kina makara Officer.”


Ta juyo tana kallon Hamraz ba tare da ta ce komai ba ta miƙe tare da ɗan rangwafa wa ta sumbaci goshin Budurwar.


“Ina yi ma ta fatan farfaɗo wa cikin aminci da samun lafiya nagartacciya... Zaka ɗauko Bittu ɗin ne zuwa yamma ko kuwa idan na tashi na wuce can mu taho tare?.”

Wannan karon Umnia ta yi maganar bayan ta mayar da kallon ta garesa.


“Not really dai amma zuwa yamman ina sa ran fita wani wuri ina ga zan biya na ɗauko ta.”


Jinjina kai Umnia ta kuma yi. “Tohm shikenan Malam Likita nayi ciki take care of yourself for us.”


“Wato dai ƙarfi da yaji kin mayar dani Likita ko?. Wai! Wa yaga Hamraz da tsira allura ina ga ta kanki zan fara.”


Ya faɗa hakan yana dariya sanin cewa da ya yi a Duniya idan Akwai abin da yake gigita Umnia to bayan allura ne, sam ta tsani allura kamar ba jami'a jajirtacciya mai kamar maza ba.


“Kaji dashi dai, ai dole ma na kiraka da Likita kai ne koda yaushe riƙe da litattafai kala kala na Likitoci kana dubawa saboda pertinent ɗin ka ta warke gashi ko Sunanta baka sa ni ba... Af na manta ma Amelia fa ta ce na gaisheka sannan nayi maka Sannu da jiki and ta ce ta nan zuwa duba ka ma.”🥱


Ya mutsa fuska ya yi da jin abin da ta faɗa shi kuwa a'ina zai saka wannan natacciyar Amelia ɗin ya huta ne?.


“Kice ma ta naji sauƙi ba sai tazo ba please.”

“Ai kam babu ruwana ina ga kanada lambarta ai kun fi kusa.”


“Hmm! ai kuwa da Dr Hadiza zan haɗa su idan tazo babu ruwana.”

Ya faɗa yana dariya. “Dole kayi dariya na lura so kake tsaban kishi a ƙona Gidan a Ranar da za su haɗu wuri guda.”


Dariya kawai ya yi wai kuma duk a kansa lallai kam sun ji jiki. “Kedai ki tafi wurin binciken ki kar ki saka muga D.G Bilal Y.B anan da kansa.”


“Kai kam Allah ya shirya ka. Ba zan biye maka ka makarar dani ba.”

Ta faɗa tana fita daga Room ɗin tana jiyo dariyarsa. Murmushi Kawai ta yi a fili ta ce. “Silly Boy.”

Haka suke Rayuwarsu su kaɗai cikin farin ciki da fahimtar juna idan kaga yadda Officer Umnia take wasa da dariya a tare da Hamraz abin zai matuƙar baka mamaki. Matar da idan ta saka kayan aiki Murmushi ma batasan shi ba.....





*-25, Aminu Kano Crescent, Wuse, Abuja, Nigeria.*

*9:30 Na safe.*



Ta kasa kai lomar pancake da ta ɗauko baki tana kallon Maiji ido waje Ramla ta ce.


“Wai da gaske kike amma shi ne baki faɗa min ba tun jiya?. Kai amma nayi farin ciki da hakan kice wani sabon kwaro yana daf da bayyana a Abuja commissioner guda sukutum aka kashe kuma kisa irin na tozarci amma da zan haɗu da wannan makashin tabbas sai nayi masa Babbar kyauta coz ya yi abin ya dace?.”


Ajiyar zuciya Maiji ta sauke tana gyara zamanta a kujerar Dining da take kai ta ce.
“Ni Bama wannan ba yadda Lulu ta ɗauki abin ne ya bani mamaki ita da ya kamata ta yi farin ciki da hakan.”


Ya mutsa fuska Ramla ta yi. “Kar ki damu fa kin manta shigar sauri aka yi ma na, sai da mu shirya komai sannan wani ya riga mu kawar da shi.”


Ɗan gyaran Murya wani kakkauran Mutum dake zaune a kujerar Dining dake fuskantar Ramla ɗin ya yi suka mayar da kallon su a garesa. “Wannan ba lokacin wannan firan ba ne ku bari zuwa wani lokacin.”
Ya yi maganar daidai lokacin da wata ‘yar siririyar mace fara kana ganinta kaga bafulatana mai kamanni da Fatiyya ta ƙari so wurin ta zauna kusa da shi tana mayar da kallon ta kan Fatiyya dake zaune gefan Maiji ta ce.


“Ke jiya me ya sa kika dawo gida babu sanarwa ne sai neman ki nayi na rasa?.”

Fatiyya tana ‘yar dariya ta ce. “Gajiya nayi Umma shi ya sa na dawo ban sanar dake ba.”

Ta ƙarishe maganar daidai lokacin da Lulu ta ƙariso Dining ɗin ta zauna gefanta.

“Assalamu Alaikum Ina kwanan mu firan mai ake yi a dawo baya.”


Ta faɗa tana ƙoƙarin serving kanta abincin Breakfast ɗin.


“Tabb kunji wai ku dawo baya.”


Ramla ta faɗa tana dariya. “Ai babu damuwa dama magana zamu fara a kan Neina kunsan kuwa gobe zata dawo?.”

Cewar Maiji. Gaba ɗaya suka kalleta da mamaki. Cike da farin cikin zancen ta Fatiyya ta ce. “Lah ai kuwa naji daɗi dama ta tafi duk ta barmu da kewa.”
“Allah ya dawo da ita lafiya. Ke Fatiyya sauri kammala mu wuce restaurant lokaci ya ƙure.” Cewar wannan kakkauran Mutumin. Fatiyya ta amsa da faɗin. “Tohm Bubba...” Tana kai lomar meat pie dake hannunta a baki....




*DSS Headquarter, Maitama Evenue, Abuja.*

*UMNIA POV.*


Ba tare da ta ɗa go ba ta bada izinin shigowa sakamakon Knocking da a ke yi. Jami'ar ta shigo cikin girmamawa ta isa wurin tare da a je files dake hannunta saman Desk dake gaban Umnia sannan ta ja kujera ta zauna tana faɗin.

“Barka da safiya Officer kin iso lafiya?.”

“Alhamdulillah. Ya kike Kiarra, ya kuma aikin yake gudana har yanzu ba'a sama wani ƙarin Information daga wurin forensic ɗin ba.”
Ta yi maganar tana ɗan baya kaɗan saman Desk Chair da take kai ta jingine bayanta tana sauraren ta.

Gyara zama Kiarra ta yi sannan ta fara magana kamar haka.

“E to ɗazu kam mun yi waya
End Ads