sun wuce duk wani tunanin mai wani ƙaramin mai tunani.
“Turƙashi! Wato ke nan idan na fahimta kai ne! Kai ne!!.”
Ramla ta kasa ƙari sa zancen tana ƙara girman idanunta a kan sa.
Ya saki murmushi tare da ƙari sa ma ta da faɗin.
“E ni ne na kashe commissioner! Ko dai bai cancanci mutuwa ba ne?.”
Bata kai ga basa amsa ba suka tsinkayi Muryar Aunty tana faɗin.
”Tabbas Samra wato Lulu ita da ‘yar uwarta Samara ƴaƴana ne kuma ba kowa ba ne mahaifin su fa ce Mr Aabdar Dawlah!.”
Gaba ɗaya da wani firgici da tsananin tsoro game da tashin hankali suka dubeta especially ma Irshad, yayin da shi kuwa Mahbub ya kuma sakin lafiyayyen murmushi domin dama ya riga da yasan komai.
“Mr Aabdar Dawlah shi ne mutumin da ya ƙeta alfarmata sanadin hakan kuma na haifa yarana ƴan biyu na saka musu suna Samra da Samara sai dai duk da hakan bai kyaleni ba sai da ya bini har Kaduna da na gudu nake zaune a can saboda nasan koda na koma gida ba za'a karɓe ni da yaran dana samu a sanadin fyaɗe da a kayi min ba, a lokacin nayi matuƙar jin tsoro domin Mr Aabdar so yake ya kashe yaran nawa shi ya sa ni kuma domin tseratar da Rayuwar su nayi sadaukarwar da nake ganin shi ne daidai a wancan lokacin ta hanyar kaisu gidan marayu dake can Katsina, kuma tun daga wancan lokacin ban sake bibiyar su ba, domin a ganina idan na manta da su na kuma haƙura dasu ne kawai Rayuwarsu zasu tsira daga son kashesu da Mr Aabdar keyi.”
Babar Magana! Gaba ɗayansu jinjina girman al'amarin kawai suke. Nan shima Irshad ya basu labarin farkon haɗuwarsa da su Samra har zuwa yau.
“Am ina da tambaya! Shin Barrister Mahbub zamu iya sanin a'ina ka samo Samara?.”
Cewar Maiji. Mahbub ya ɗan juya tare da kallon Samara da har lokacin sharar baccin ta take hankali kwance sannan ya sake juyowa ya dube su kana ya ce.
“Tun bayan lokacin da Jaish ya kaɗe ta sannan Lulu ta kai ta asibiti a ka ƙi karɓar ta har ta dena numfashi wanda ita kuma Lulu ta ɗauka ta mutu ne, har hakan ya yi sanadiyar da ta suma batasan inda kanta yake ba sai farkawar da ta yi ta tsince ta hannun masu fataucin mutane har ta haɗu dake, a lokacin mutane daban daban ne suka ɗauke su wasu suka ɗauki Samara yayin da suka siyarwa da masu fataucin mutane Lulu, suka tafi da Samara wurin iyayen gidan su wato Alhaji Haashir da Alhaji Umair sai kuma Mr Aabdar suka ce musu ɗayar ta mutu shi ya sa suka ƴar da ita, a hannun waɗan nan mutanen uku Samara ta yi doguwar jinyar da har ta manta gaba ɗaya tunanin ta bayan ɗaukar dogon lokaci tana jinya sannan ta farfaɗo su kuma suka sakata cikin ƙungiyar su ta Zwandun Monster's kasancewar idan mutum ya rasa tunanin sa kuma ya kasance yana da wata baiwa tofa wannan baiwar baya rabuwa da ita, to hakan ce ta kasance ga Samara ta fara aiki da ƙungiyar Zwandun Monster's tana taimaka musu ta fannoni da dama sai dai tafi bada gudunmawa ta hanyar ɗauke tunanin mutane ko kuma jami'ai a kan wannan ƙungiyar da hakan ya bada gudunmawa babba ta hanyar tuna ma ta wasu abubuwa na memory nata da ta manta suka fara dawo ma ta, ta shiga cikin firgici sosai sai dai bata faɗa wa kowa ba, har zuwa lokacin da ta tuna Asalin wacece ita, ni kuma da nake bibiyar ta a lokacin ne na haɗu da ita har na samu na shawo kanta ta yarda dani na bata labarina sannan muka fara tsara yadda zamu rusa gaba ɗaya ƙungiyar ta Zwandun Monster's tabbas Samara tasan ‘yar uwanta Samra tana raye kuma har gidan da suke zaune na kaita ta hangeta kuma tana yawan zuwa unguwar kawai don taga Lulu ɗin sai dai taƙi bari su haɗu domin tafi so har sai mun gama da ƙungiyar sannan ta bayyana ga ‘yar uwan nata haka lokaci ya ci gaba da tafiya har muka tsara kuma kuma gabatar da abin da muka shirya ta hanyar kawar da commissioner da hakan ya zama matakin farko da muka bi wurin tarwatsa Jaish da tsarin sa domin mutuwar commissioner ɗin ta yi matuƙar taɓa sa har hakan ya sa shi fara yin abin da ba ɗabi'arsa ba cikin hakan har ya naɗa Samara da take amsa sunan Sanam matsayin shugaba ta biyu a ƙungiyar Zwandun Monster's wanda hakan ya janyo hatsaniya cikin ƙungiyar kuma ta gefe guda har waɗan nan mugaye uku shirya su kashe Sanam wato Samara to dama da shirin mu muke ni da ita, sun shirya haɗuwa da ita a wani gidan gona na Mr Aabdar dake nan a Abuja a yau domin su kasheta har suka yi nasarar buga masa kwalba a kai domin ta yi musu gardama lokacin da suka buƙaci ta sha Juice dake ɗauke da poison mai matuƙar hatsari ita kuma taƙi shi ne abin da ya fusata su har Mr Aabdar ya buga ma ta kwalba a lokacin ne kuma na fito daga maɓoyata ganin zasu kashe ta dama tare da ita mukaje nayi musu barazana da bindiga har na samu na fito da ita, sanadiyar buga ma ta kwalbar da a ka yi ne ta suma kuma har yanzu bata farfaɗo ba sai dai zata farfaɗo ɗin.”
Mahbub ya yi shiru lokacin da kai ƙarshen maganar.
Cikin jinjina kai tare da ta'ajjabi na wannan lamarin Maiji ta ce.
“Dama na sa ni Jaish shi ne shugaba na ɗaya kuma creator na ƙungiyar Zwandun Monster's wanda sanadin sanin wannan gaskiyar da Yayata wato matarsa ta farko, ta yi shi ya sa ya kashe ta ya kuma kashe iyayen ta wato Uncle ɗina da matarsa bayan haɗa hannu da ɗayan Uncle ɗin nawa Alhaji Umair da suka yi.”
“Wai kina nufin ba mahaifin ku ɗaya da Fanan tsohuwar matar Jaish ba?.”
Mahbub ya ma ta tambayar.
Girgiza kai ta yi ta ce.
“A'a amma dai shi ne ya riƙe ni tun ina ƙaramata, kafin mahaifiyata da ta kasance balarabiya ce ya haife ni mahaifina ya rasu sanadiyar hatsarin mota ita kuma mahaifiyata koda ta haifeni ko yaye ni batayi ba ta gudu ƙasar su a cewar ta bazata iya jure zama ba tare da mahaifina shi ya sa ta tafi ta bar ma danginsa ni, a hannun matar Uncle Sahir wato mahaifin Fanan na taso kuma na ɗaukesu matsayin iyaye har zuwa lokacin da wannan mummunan ƙaddarar ta afka mana na auren Jaish da Fanan ta yi dama ita ke son sa shi bai damu da ita ba, kuma bata damu ba a cewarta tausayin sa takeji domin ce ma ta ya yi shi maraya ne shi ya sa zata auresa gashi sanadin hakan ga abin da ya haifar ya saka ma ta da kasheta da kuma kashe iyayen ta nima Allah ne kawai ya tseratar dani daga sharrin sa.”
Shiru suka yi gaba ɗaya su na kuma jinjina girman wannan al'amarin lallai in baka mutu ba ka sha kallo.
Wucewar wasu sakanni....
“Rayuwar Lulu ta na a tsari zaman ta a hannun D.S.S ba zai zama kariya daga gare ta ba, domin cikin jami'an nasu ma akwai ɓata gari ya kamata Lulu ta fito.”
Cewar Mahbub, gaba ɗaya jinjina kai suka yi lokaci guda kowannen su ya shiga motar da ya zo suka bar asibitin domin zuwa DSS headquarter.
*Wato dai ta tabbata Jaish shi ne jezim inkiyar sa Shaytaan 🌚 Babbar magana.!*
Wato ana ta labari baku ce ina Hamraz yake ba ko?.
To mu haɗu a next page domin jin wani hali Hamraz yake ciki tare da sanin mene ne zai faru gaba!!🤦🔥🔥
*Labari fa yazo gangara saura ƙirisss 👌*
*RANAR BIYAN BUƘATA*
_Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba.!_
BY Nainarh KD Nkd's.✍️
_
E. 32 Final Episode.👏
A hankali yatsun ta na hannu suka fara motsi kaɗan kaɗan, yayin da jikinta ya fara kakkarwa kamar wacce a ka jona da wutar lantarki ba ma iya jikinta ba hatta gadon da take kwance shima Shaking yake.
Tana a tsaka da wannan hali Hamraz ya turo ƙofar ya shigo bakinsa ɗauke da sallama hannunsa kamar ko yaushe riƙe da wani ɗan littafi idanunsa sanye da farin Glass.
Da sauri kuma a hanzarce ya ƙari sa gare ta, bayan ya yi wurgi da littafin dake hannunsa.
Rasa mai ma zai ma ta ya yi domin kuwa jijjigan da take yi a yanzu ya mafi na ɗazu a lokacin da ya shigo ya sameta, sai can dabara ta faɗo masa, da sauri ya tallafo ta a ƙirjinsa yana faman bubbuga bayanta, tsawon mintoci zuwa yanzu ta dena jijjigar sai faman ajiyar zuciya da ta ke saukewa a kai a kai, sai can kuma kamar wacca a ka tsikara ta fara ƙoƙarin kwace jikinta daga garesa tana faman sumbatu faɗi take.
“Ni kakyaleni wayyo Neina ki taimake ni karya kasheni!!.”
Tana sumbatun ya ɗa gota daga ƙirjinta tare da girgiza ƙafaɗun ta yana karanto ma ta addu'o'i dan a yadda take sumbatun jikinta na rawa ya yi zaton aljanu ne duk da dama Dr Hadiza ta faɗa masa zata iya tashi ba'a hayyacinta ba.
Tunawa da hakan da ya yi ne ya sa ya fara ƙoƙarin ɗaukar ta kacokan domin kaita asibitin da Dr Hadiza ɗin take aiki don ta duba ta dan kuwa baya tunanin zai iya jira har sai ya kira ta a waya sannan tazo gwara ya je ya sameta.
*DSS Headquarter Mai Tama Avenue Abuja*
*OFFICER UMNIA POV.*
Ta ƙari sa shiga Interrogation ɗin tare da jan kujera kamar zata zauna, sai kuma ta fasa ta ɗaura ƙafa ɗaya saman kujerar, ta ɗan rangwafa tana duban Lulu dake zaune saman kujera cikin Interrogation cikin tsimewa da kuma nazari kamar ba zata yi magana ba, sai kuma ta fara.
“Mu ba. Jami'ai mu kan iya kauda ido daga kan mai laifi, mu kan iya bawa mai laifi dama, muyi masa ɗaurin talala kamar bamu san me yake ba.! Now tell me ya sa kika kashe commissioner sannan kuma kika kashe Prof Bakori?, Bana so firan namu yaja lokaci ki bani amsoshi kawai.”
Ta ƙari sa faɗa tana zuba ma ta rikitattun idanunta.
Ɗan taɓe baki Lulu ta yi ganin da irin salon da Officer ta zo da shi, ta ɗan yi baya tare da harɗe hannu a ƙirji tana duban ta da nata kausasan idanun ta ce.
“Yanzu me kike da buƙatar na faɗa miki ne Officer? irin kisar da nayi ma commissioner ko kuwa irin wanda nayi ma Prof Bakori ko kuwa dai na faɗa miki ainihin true color na kowannen su wanda Asalin kwarewar ki a bincike bai saka kin gano ba?.”
A fusace Officer Umnia ta miƙe daga rankwafawar da ta yi tana daka ma ta tsawa dan ranta ya fara ɓaci ta tsani rainin hankali ƙiri ƙiri hujjoji sun bayyana amma wannan ficiciyar yarinyar zata tsaya tana ɓata ma ta lokaci.
“Oh common Officer just relax mana, to mene ne na ɓacin rai? Ai bake ya kamata ran ki ya ɓaci ba, let me tell something da ke baki sani ba, commissioner da kuma Prof Bakori ba mutanen kirki ba ne al'ummar ƙasa gaba ɗaya farin ciki suke da mutuwarsu na sani sanadin mutuwarsu mutane da dama musamman ma ‘yan mata zasu tsira daga fyaɗe da a ke musu duk kwanan Duniya, wai kuwa kin san a kullum ana tashi ne da report na ɓatan yara ƙanana da kuma ‘yan mata kuma ba'a taɓa ganin su?, Kin san su waye ainihin commissioner da kuma Prof Bakori? Duka baki sa ni ba, hummp ina tunanin baki cancanci zama Officer ba Madam, tun da baki san meke faruwa a ƙasar ki da kikayi alƙawari zaki bada Rayuwarki wurin kula da al'ummar ta musamman talakawa da koda yaushe Rayuwarsu take mara ‘yanci, Officer ki sani bana taɓa dana sani a kan abin da na aikata ko kuma wanda zan aikata nan gaba dan kuwa yanzu wasan ya fara ba'ayi komai ba ma, don ba zan dakata ba har Ranar da adalci ya wanzu ga kowa koda hakan zai yi sanadiyar rayuwata naji na aminta. Saboda haka bazakiji komai ba daga bakina kije kwarewar ki da jajircewa ya saki ki binciko gaskiya.”
Ta ƙari sa zancen tana rage girman idanunta sannan ta sakar ma ta murmushi tana jijjiga ƙafa.
Garam kakeji lokacin da Officer ta fita ta bugo ƙofar Interrogation ɗin da ƙarfi, taɓe baki Lulu ta yi irin dai abin bai shalleta ba.
Da ƙarfi Officer tasa hannu tare da watsar da karikitan da ke saman desk ɗin office ɗin ta tana fitar da zazzafan huci na ɓacin rai, ɗan dakata wa ta yi tare da ciro bindigarta gadan-gadan ta nufa ƙofar zata fita, a ka yi Sa'a dai-dai lokacin Kiara ta shigo. Da mugun sauri Kiara ta ƙari sa tare da kwace bindigar tana faɗin.
“Kin rasa tunanin ki ne Officer mene ne kike shirin yi kasheta zakije kiyi?”
A fusace Officer ta bata amsa da faɗin.
“To mene ne amfanin Rayuwar nata bayan ita ɗin Murder ce she's killer sannan ko ban kasheta ba, a gobe za'a zartar mata da hukunci domin na riga dana shigar da ƙarar a kotu kuma gobe za'ayi zama na farko da ƙarshe don kuwa Akwai hujjoji a tare dani.”
Officer Umnia ta ƙari sa maganar tana jinjina ma ta kai alamar tabbatar wa. Yayin da Kiara ta fara yin baya baya cike da tashin hankali take duban Umnia sai kuma ta ce.
“Amma kuwa kin tafka babban kuskure Umnia wanda gyara sa ba zai zama abu mai sauƙi a wurin ki ba, yanzu a kan mutuwar wancan mugun kafirin wanda ya daɗe da fita daga musulunci saboda munanan ayyuka da yake yi, shi ne kika shigar da ‘yar ki ƙara kotu, ɗiyar ‘yar uwanki, amma gaskiya Umnia bakiyi ba, lemme tell you something su dai commissioner da Prof ɗin da kike waɗan nan abubuwan a kan mutuwarsu, to ba mutanen kirki ba ne manyan tantirai ne waɗan da tantirancin su ya wuce duk yadda kike tunani...”
Ganin yadda Officer Umnia take bin ta da kallon rashin fahimta ne yasa Kiara ta kamo hannunta tare da fito da ita waje tana faɗin bari na nuna miki wani abu da baki sani ba.
Wani irin dogon birki Officer Umnia taja tana duban Yarinyar da ta bari a Interrogation amma yanzu gata a waje kuma ƙarin abin ɗaure kan shi ne ba ita ɗaya ba ce tare take da wata Budurwar mai matuƙar kamanni da ita sak. Bama wannnan ne ya sa Umnia a ruɗani ba sai ganin Safiyya Aunty da ta yi tare da Irshad da kuma wasu mutanen da ruɗanin da take ciki bai bari ta gane su ba sai dai ta gane Mannah ɗiyar commissioner wacca take tsaye daga gefe.
A hankali ta fara taka wa domin ƙari sawa wurin ‘yar uwanta Safiyya Aunty bakinta na rawa ta ce.
“Ah'aa Aunty meme nene kike a nan?.”
Ta yi ma ta tambayar tana duban yadda Safiyya Aunty ta riƙe hannun ‘yan matan biyu masu kamanni da juna dukkannin su hawaye suke.
Sha re hawaye Aunty ta yi tare da duban yaran nata sannan ta duba ‘yar uwan nata tana jinjina mata kai.
*BAYAN SHUD'EWAR WASU DAK'IK'U!.*
“To fa kinji ainihin abin da yake faruwa.”
Aunty ta ƙari sa maganar tana duban ‘yar uwan nata Officer Umnia bayan ta gama faɗa ma ta ainihin abin da ke faruwa. ta sanar da ita cewar Lulu da Samara ƴaƴanta ne kuma ba kowa ne mahaifin su ba fa ce Mr Aabdar Dawlah.
Ainihin abin da ya faru shi ne a lokacin da suka iso DSS Headquarter ɗin da Kiara suka fara cin karo a gaggauce Aunty ta faɗa ma ta abin da yake faruwa, ita kuma Kiara da jin hakan shi ne kawai taje ta buɗe Lulu sannan suka iso inda su Auntyn suke dama zuwa lokacin Sanam (Samara) ta farka kuma da ita suka shigo Department ɗin, nan fa a ka tsaya kallon kallo tsakanin Lulu da mutanen especially ma Samara da kuma Aunty, kafin daga bisani ta ƙari sa da gudu ta rungume Auntyn tare da Samara domin kuwa ko zata mutu ta tashi ba zata taɓa manta kamannin Aunty kona Samara ba, a wannan taƙin ne kuma Kiara ta shiga office ɗin Umnia domin sanar da ita abin da ke faruwa, sannan kafin fitowar ta ne Aunty dama Samara suka feɗe ma Lulu ainihin abin da ya yake faruwa, a daidai lokacin da Umnia da Kiara suka fito ita kuma Tamannah ta shigo wurin shi ne ta tsaya ganin wani abin da yake faruwa.
*WANNAN KE NAN!.*
“Allahu mai iko Annabi mai dubun daraja, yanzu wannan rikitaccen lamarin da ko'a hasashe ba'ayi tunanin afkuwarsa ba gashi ya kasance ya faru mene ne mafita, ƙarin ruɗanin kuma shi ne Mr Aabdar Dawlah shi ne mahaifin Samra da Samara.”
Officer Umnia ita ke wannan maganar cikin taraddadi.
Taɓe baki Samara ta yi tare da faɗin.
”Tsoro kike kar muji babu daɗi a kan nan bada daɗe wa ba zai girba abin da ya daɗe yana shuka wa ko? Ai karma ki damu kanki a kan mu domin mutuwarsa ba zai ƙara mana ko rage mana komai ba da can ma ai da Bamu san uban mu yana raye ba muna nan daram balle kuma yanzu da gaskiyar Komai ta bayyana.”
Gaba ɗaya duban Samara suke yi da jin abin da take faɗa kuma da alamu tun daga ƙasar zuciyarta maganganun suke fitowa.
Ƙarar saƙon da ya shigo wayar Mahbub ne ya ja hankalinsu gaba ɗaya.
Ya saki wani killer smile bayan ya gama karantawa tare da duban Samara ya ce.
“Everything is done, ƙarshen azzalumai yazo.”
Ta saki kyakkyawar murmushi tare da jinjina masa kai tana faɗin.
“Good job Oga.”
Sannan ta dubesu gaba ɗaya tana faɗin.
“Ina ga fa komai ya ƙare domin Babban kifin tare da muƙarraman sa sun shiga hannu.”
“Kamar ya ya ban gane ba me kuke nufi?.”
Cewar Lulu cikin rashin fahimta.
Mahbub ya ce.
“Bari nayi muku bayani, tawagar bincike ta musamman na turawa address na waɗan nan mutane uku Alhaji Haashir Mr Aabdar Dawlah da kuma Alhaji Umair Ubaydullah kuma duka sun shiga hannu sannan shima shugaban nasu ma'ana mai jan ragamar nasu wato Jaish Jezim Inkiya Shaytaan an kama sa sannan a halin yanzu Zwandun Monster's ya zama labari domin kuwa fusatattun Jami'an sun