da su an tabbatar da silin gashin da aka samu a wurin da abin ya faru bana commissioner ɗin ne hasalima gashin dogo ne kuma baƙi a taƙaice dai gashin mace ce.”
Umnia ta ɗan ƙara girman idanunta tana gyara zamanta a ɗan rarrabe ta ce. “Mace kuma what kind of mace kina nufin mace ita ce za'a ce ta yi kisan ke nan?. Impossible!.”
“Ban tabbatar ba kam amma bincike shi ne zai tabbatar da Komai.”
Cewar Kiarra tana Miƙewa tsaye. “Bari na koma office Akwai ayyukan da zan ɗan gabatar.”
Amsa ma ta Umnia ta yi tana janyo files ɗin da Kiarra ta shigo da su ta fara dubawa yayin da ita Kiarra ta yi waje....
______
*WAI SHIN KUN YARDA MACE CE TA KASHE COMMISSIONER KO KUWA ZARGI NE KAWAI ⁉️*
*WACECE NEINA MENE NE ALAƘAR TA DASU LULU ⁉️*
*WAI ME YA SA SU MAIJI SUKA DAMU NE A KAN MUTUWAR COMMISSIONER ⁉️*
_____
*🌹 Perfectly Pen's ✍️✊*
*Our Ongoing Book's...✍️*
*1_ƘADDARA CE!.*
*BY: C Candy.*
*2_SHIRYAYYIYAR ƘADDARA.*
*BY: Queen Kainaat.*
*3_RANAR BIYAN BUƘATA.*
*BY: Nainarh KD Nkd's.*
*4_DESTINY LOVE.*
*BY: Oum Yasmeen.*
*Mun Shirya tsaf domin kawo muku daɗaɗan littattafan mu masu cike da ilmantar wa faɗakarwa tunatar wa wa'azantar wa har ma da Nishaɗantar wa.💝*
*🔥Kada ki bari wannan tafiyar ya kasance ba tare dake ba. Don't Miss It Dearest sisters 🔥*.
_____
*Masu Buƙatar a haɗa musu Book Cover ko banner, poster, birthday flyer, flyer, logo e.t.c dai duka Muna yi cikin farashi mai rahusa ku tuntuɓe wannan lambar (0708 521 2808.)*
𝑃𝑒𝑟𝑓𝑒𝑐𝑡𝑙𝑦 𝑝𝑒𝑛'𝑠..... ✍💫
*💫..RANAR BIYAN BUƘATA...💫*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_
*_🪄MARYAM NASEER A.k.a Real Mirah A.k.a Ammiey laylerh.✍️. Sako ne daga gare ta. Ta ce. Tana bawa masoyanta haƙuri na jinta shiru kwana biyu da aka yi wata ‘yar matsala ce sanadi, sannan in sha Allah komai ya daidaita, tana muku albishir da cewa tana nan dawo very soon ku zuba ido kawai, sannan ta ce ta yi kewarku sosai. AMMIE LAYLERH taku ta Amana. Saƙo daga gare ta.✍️✊🪄_*
_____
*Ep_7-8*
*- 100, Herbert Macaulay Way, Garki, Abuja, Nigeria*
Kamar da wasa Aunty dake ta can ɓangaren Dining Area tana serving mijinta abinci yayin da yara suke daga can gefe guda cikin katafaren palon suna shirin school. Ta ɗa go kanta domin son tabbatar wa da kanta ƙamshin da take ji kuma ta tabbatar Mutum ɗaya keda irin wannan ƙamshi kaf cikin zuri'ar gidan, sanin da ta yi kuma baya ƙasar ma gaba ɗaya shi ne dalilin ta na son tabbatar wa. Kasa koda motsi ta yi, ta ƙame cike da mamaki take ƙara waro idanunta tana ƙure Mutumin dake tsaye tsakiyar palon da kallo, yayin da shi kuma yake sakar ma ta Kyakyawan Murmushi da ya bayyana point na gefan fuskarsa. Da kyar ta sama zarafin buɗe bakinta dake ɗan rawa na mamakin ganinsa a lokacin, ta kira cikakken sunansa tare da sunan da ita ɗaya ke kiransa da shi, ko da ace ma wani a cikin yaran Gidan yana kiransa da sunan badai a gaban sa ba sai dai a bayan idonsa. Maganar da ta yi ya saka mijinta da bai lura da abin da take gani ko yanayin da take ciki da fari ba, ya ɗa go da saurin sa.....
“Irshad. Pooh! Yarona...”
Gaba ɗaya kyawawan yaran su uku da alama Triples ne mata biyu Namiji da ba za ta su haura shekaru tara a Duniya ba, duk suka dakata da abin da suke yi jin sunan da Auntyn tasu ta kira. Da gudu suka baro wurin da suke suka ƙari sa wurin sa fuskokinsu ɗauke da farin ciki na ganinsa domin kuwa ba ƙaramin kewarsa suka yi ba, sai dai koda suka ƙari sa garesa sun kasa tunkarar sa, tsaya wa suka yi suna kallon sa....
“Abbana Saukar yaushe haka babu sanarwa sai dai kayi mana Dawowar bazata?.”
Sai a lokacin ya ɗauke kallon sa daga kan Aunty ya mayar kan Triples ɗin tare da ɗan rage tsayi kaɗan, ya kamo su zuwa jikinsa tare da rungumo su ya lumshe kyawawan idanunsa masu cike da gajiya da kuma ‘yar ɓoyayyiyar damuwa. Idanunsa a rufe ya ce...
“Jiya da dare na dawo, daddama Sissurprising naku nakesso nayi, gashi kuma nayin...”
Da in'ina ya yi maganar kuma a rarrabe, wani abu ke nan da ya zama nashi ƙadararar.! Duk da cewa bada hakan a ka haife sa ba, sanadin ta ya sama wannan in'ina...
Ita kuma ta gujeshi Sanadin hakan, yayin da su kuma suka ƙaunace shi a dalilin hakan. Dukkanin su wasu mutane ne da kowannen su yake da wani gurbi a Zuciyarsa da rayuwarsa.
Ya buɗe Frisco eye nasa ya watsa su saman fuskar mahaifin nasa Mutumin da ya kasance masa wani ɓangare a rayuwa shi ne komai nasa, farin ciki, kwanciyar hankali, murmushin sa, ya so sa kuma ya kula da shi a lokacin da mahaifiyarsa da ta haifesa ta watsar da lamarin sa, ta tafi ta barsa bisa son zuciyarta...
Miƙewa tsaye ya yi tare da janyo hannun yaran ya ƙari sa da su Dining Area ɗin suka tsaya gaban Aunty da tun lokacin da ta kira sunansa bata kuma magana ba sai harɗe hannu da ta yi a chest nata tana bin sa da kallon da ya san dalilin sa...
“I really miss you Momma Aunty, please forgive me for the abandoned naki da nayi na tsawon lokaci.”
Kamar koda yaushe a rarrabe ya yi maganar Sannan kuma da kyar ya ƙari sa a hakan ma ya yi Namijin ƙoƙari.
Ƙoƙarin rungumota ya yi tare da yaran a hannunsa don zuwa lokacin ya ɗauki mace ɗaya ya riƙe ta. Da sauri ta yi baya tana kuma tamke fuska. Murmushi ya yi domin ya san fushi take da shi, shi kan sa yasan ya cancanci hakan sai dai ba laifin sa ba ne wurin da ya tafi ne Cibiyar sadarwa gaba ɗaya baya aiki a wurin.
Kallon Mahaifin sa Alhaji Khalil I Khalil sanannen attajirin mai Dukiya a ƙasar Nijeriya dama wajen ta kuma mai Company na Haƙan ma'adinai, Irshad ya yi tare da faɗin.
“Daddy Please! ka saka baki domin ba zan iya jure wannan fushin na Momma Aunty ba sam.”
Dariya Daddy ya yi yana ɗa ga hannu alamar babu Ruwansa sannan ya ce.
“A'a fa ina ga kun fi kusa babu ruwana a wannan zancen.”
Ya faɗa yana ci gaba da kai loma na haɗaɗɗen girkin kwararriyar matar tasa da baya gajiya da ci a koda yaushe.
Irshad ya buɗe baki domin sake magana duk da bai fiye son yin ba, sai dai wani irin ƙarar da ya bada sautin... “Fiiiooo.”!
Alamar dai fi to ne a ka shigo Palon ana yi, shi ne abin da ya hana shi faɗar maganar da ya yi niyya. Ya juya domin ganin mahalukin da ya yi wannan aiki.
Wani irin wawan birki kyakyawan matashin Saurayin da ya shigo palon da fi ton yana shirin magana ya yi, sakamakon ido huɗu da suka yi da Dodo acewarsu, wani irin hautsinewa ‘ya‘yan cikinsa suka yi suka bada sautin ƙulu lu lu...! Lokaci guda yaji gudawa nason kwace masa ta fito a 360. Da kyar ya iya ƙarfin halin juyawa cikin sakanni da ba za su haure biyu ba, fit.... Ya ɓace daga palon kamar walƙiya. Hakan da ya yi, ba ƙaramin bawa yaran dariya ya yi ba, shi kuwa Ogan fuskar nan a ɗaure tamau ya fara taku domin bin bayan sa, sai dai kiran sunan sa da Aunty ta yi, shi ne abin da ya dakatar da shi.
Wata wawiyar ajiyar zuciya Abdallah ya sauke lokacin da ya tsinci kansa a waje, sharce gumi ya yi yana zare ido, ya ciro wayarsa dake ruri a trouser pocket nasa ko duba sunan mai kiran bai yi ba, ya kara wayar a kunne domin ya riga da ya gane ko wanene don ringtone na musamman ya saka masa.
Bai bari wanda ya kira san ya fara magana ba. Shi ya fara da faɗin...
“Jar uba yau na tsallake rijiya ido rufe.”
Shi ne abin da ya fara faɗa maimakon sallamar sannan ya ci gaba da cewa.
“Abrad! Kana ina ne?. Da alama baka sama labarin dawowar Boss ba, domin naji alamar tuƙi kake.”
Daga ɓangaren Abrad ya ƙara riƙe steering da kyau, idanunsa na kallon kwalta, ya yi dariya yana faɗin.
“Wanene kuma haka ya saka kake faɗin ka tsallake rijiya ido rufe?.”
Abdallah bai yi magana ba, har sai da ya sama wuri a garden da ya ƙari sa ya zauna sannan ya ce.
“Pooh nake maka magana shi ne ya dawo.”
Wannan karon dariyar rainin wayo Abrad ya yi kuma har lokacin bai wani fahimta ba, ya ce.
“Wai wani Pooh kake magana ne?, ban fa fahimta ba har yanzu.”
A hasale kuma a ɗan fusace. Abdallah ya ce.
“Pooh Dodo..! Nake nufi Dalla.”
Wani irin juyi cikin Abrad ya yi ya murɗa tare da bada sauti, yayin da Maganar Abdallah ta daki kansa tamkar saukar aradu, fuskar Pooh ta bayyana a idanunsa tamkar bayyana kumurcin zaki yake bayyana a gaban namun daji. Ikon Allah ne kawai ya sa ka Abrad ya iya riƙe steering da kyau, amma da haƙiƙa sai ya daki motar gaban sa da hakan ta kasance kuma ba ƙaramin Accident za'a samu a titin ba, sai dai cikin kariyar Ubangiji babu abin da ya faru Sakamakon jajircewar da ya yi ya tattaro ƙarfin sa gaba ɗaya ya riƙe steering.
“Amma dai Allah ya isa na Abdallah, kana sane tuƙi nake yi shi ne ka faɗa min wannan mummanar labari.”
Gimtse dariya Abdallah ya yi yana basa amsa da faɗin.
“Sorry Bro so nayi ka fahimci yadda naji a lokacin da na gansa, kuma naga alama kaji fiye da hakan, yanzu dai koma mene ne kuma koma ina zaka ka dawo gida domin kasan motar da ka ɗauka bata fita ba ne And yanzu Pooh ya dawo hakan yana nufin duk wani iya shege a adana sa a gefe, a nutsu a ka sin hakan kuma.... Kasan sauran domin Pooh baya shakkar dukan uban kowa ko a gaban ko uban waye.
“Pooh Dodo.! Yaya Irshad namu mai razana gwarazan Samari su shiga taitayin su dan uban su ko basu shirya ba.”
Abrad ya faɗa tare da ihu yana buga steering yana dariya.
“Kai ka sa ni dai.”
Abdallah ya faɗa tare da kashe wayar da, don har lokacin ƙarfin hali kawai yake na magana, amma shi kaɗai yasan yadda yaji lokacin da suka yi Four eyes da Irshad. Babu abin da yake tunani sai yadda haɗu warsu zata kasance.🔥
____
(★†★)
___
*-100, Lake Chad Crescent, Maitama, Abuja, Nigeria*
*UMNIA POV.*
“An ya kuwa zan tsaya cin abincin nan, na makara fa, ai ka barshi kawai.”
Ta faɗa tana kuma kallon agogon dake ɗaure a tsintsinyar hannunta. Sannan ta mayar da kallon ta kan Hamraz dake sanye da apron ta ce tsaye gabanta.
“Malam cooker zan tafi take care of yourself for us.”
Ta yi maganar da ta saba a garesa kamar kullum tana kallon sa kyakyawan saurayin ƙanin nata son ko wacca mace, shi ne Abokinta, farin cikin ta rayuwarta mai girkin ta komai nata duka a Rayuwa shi ne tana masa so irin sosai ɗin nan kuma bata fata wani abu ya raba su da shi da ita da kuma Safiyya wato twin's Sister nata da take Aure a garin Abujan suke zaune da mijinta.
Ta kawar da tunanin da ke son addabar ta a ‘yan kwanakin tare da yi sama sallama ta fi ce ya bita da a dawo lafiya. Bata daɗe da fita ba Driver ya shigo domin tafiya da Bittu Ɗiyar Hamraz ɗin da ta rasa Mahaifiyarta a wasu ‘yan shekaru marasa yawa baya, sakamakon aikin mahaifin nata da shi ne sanadin rushewar wasu al'amurran daga ciki har da kaso 45 na farin cikin wannan ƙaramin Ahalin....
____
*-25, Aminu Kano Crescent, Wuse, Abuja, Nigeria.*
*LULU POV.*
Jiya ne Abar ƙaunarsu gaba ɗaya wato Neina ta dawo daga tafiyar da ta yi zuwa wani local government dake Kaduna State garin iyayenta.
Kamar kullum Fatiyya da Umma sai kuma Bubba suna restaurant nasu kamar yadda suka saba domin Fatiyya ta kammala J.S.S 3 nata ne ta yi jarabawa na shiga S.S 1 ma lokaci kawai a ke jira ta ɗaura, shi ya sa kafin nan take bin Auntyn nata Umma da mijin Auntyn nata da suke kira da Bubba restaurant nasu domin tallafa musu da wani abun da ba'a rasa ba.
Ramla tana karatu ne anan wata Babbar University dake Abuja tana karantar Nazarin Ɗabi'a.... Yayin da ita kuma Maiji ta kammala karatun na Nursing yanzu haka kwana kaɗan ya rage ta fara zuwa gudanar da internship nata.
Ƙoƙari take sosai wurin ganin abin bai taso ma ta ba, tana iya kar bakin ƙoƙarin ta wurin ganin ta bijirewa umarnin da sheɗaniyar muryar dake ma ta amo a kunne take ba ta, kuma ba ƙaramin wahaltu wa da hakan take ba. Cikin Wata iriyar kiɗimammiyar ƙatuwar murya mai ban tsoro ake bata umarni da ta je ta sha jini ta yi kisa kona wanene kawai jini a ke so tasha a wannan daidai lokacin, yayin da ita kuma ta dage taƙi ta yi abin da ake umar tarta dashi.
Da ƙarfin gaske ta kuma damƙe zanin gadon da take kwance a kai yayin da gaba ɗaya jikinta ya fara Miƙewa daga kwancen da take tamkar ɗa ga ta a ke, baƙin gashin kanta ya rufe ma ta fuska gaba ɗaya, bata sare ba taƙi karɓar umarnin da alama kuma ta fara fusata su, da ƙarfin gaske suka sake ta ta koma saman gadon ta faɗa ta kwancen, kanta ya bugu da headboard na gadon, ta kurma wani gigitaccen ihu, bakinta yana fitar da wani irin baƙin jini haka ma gefan idanunta baƙin jinin yake fitarwa kamar ruwa, idanunta suka ragu daga girman da suka ƙara, jikinta ya dawo daidai daga lallan kwashewar da ya fara, gashin ta ya koma wuri guda tamkar ba shi ne yake a hargitse ba. Iyakar wahala kam ta sha shi.
Daidai lokacin kuma a ka turo ƙofar Bedroom ɗin a hauka ce Maiji da wata kyakyawar Dattijuwar mace suka shigo da alama ita ce Neina.
Da gudu Maiji ta ƙari sa tare da rungumo Lulu da ta fita a hayyacinta tana kuka sosai ta kalla Neina da ta durƙusa tana sharewa Lulu jinin da ya ɓata ma ta fuska da tissue, ta ce.
“Neina abin nan fa ya yi yawo Lulu tana cikin wani hali na tabbatar tana shan wahala sosai, gashi indai wannan abun zai motsa tana fitar da baƙin jini sosai, ya kamata muyi wani abu a kan hakan a nemo malamai na addini domin ina zargin akwai saka hannun mutanen ɓoye a wannan halin da Lulu take ciki.”
Neina ta yi shiru tana sauraren Maiji da nazarin Maganar ta, gaskiya ta faɗa. Shigowar da Ramla ta yi ne ya hana Neina faɗar abin da take shirin faɗa.
Da gudu ita ma Ramla ta ƙari sa tare da rungumo Maiji haɗe da Lulu ɗin tana kuka kuma ko basu faɗa ma ta ba, ƙarar da taji ya fahimtar da ita abin da ke faruwa. Ajiyar zuciya Neina ta sauke sannan ta ce.
“In sha Allah za'a bincika za'a nemo Malamin da ya dace wanda zai iya raba Samra da waɗan nan mutanen kuyi haƙuri ku dena kuka kunji in sha Allah zata sama lafiya.”
Jinjina kai Maiji ta yi dan batajin zata iya cewa komai a halin yanzu, sosai take masifar tausayin Lulu da halin da take ciki, ita kuwa Ramla mai arhan hawaye ban da hawayen babu abin da take yi domin ita ce mai rauni a cikin su, koda yake dole ta zama mai rauni duba da yadda Rayuwarta ta baya take. Maiji ita ce mai ɗan dama dama a cikin su kuma mai sanyin hali, Lulu kuma ita ce Jarumar cikin su.
“Amma tun da na tafi basu zo leƙo ba sai yau ko?.”
Neina ta tambaya.
Jinjina kai Maiji ta yi sannan ta ce.
“E basu zo ba sai yanzu.”
_____
*- 100, Herbert Macaulay Way, Garki, Abuja, Nigeria*
*IRSHAD POV.*
Ya yi Shiru kaɗan yana ƙoƙarin biyewa zuciyarsa da take tariyo masa wasu watannin baya da suka shuɗe a rayuwarsa kuma yake fata da kar ya ƙara tunasu a cikin Rayuwarsa domin sun wuce da wani sa rai da yake da shi a Rayuwa.
*Flash Back...*
Ya kuma Murmushi yana ƙara ƙasa da kansa domin son hango kyakyawar fuskar nata gaba ɗaya. Ita ma Murmushin take ta kallesa kaɗan tana mayar da Camera ɗin ta cikin backpack Sannan ta ce.
“Suna na Ariana. Suna mai daɗi ko?.”
Ya jinjina ma ta kai, ta kuma murmusa wa. “Haka Mutane suke yawan faɗa cewa na dace da sunana, idan na tambaye su Dalili sai suce saboda ni ɗin kyakyawa ce. Kai fa mene ne Sunan ka, kai ma kana cikin team namu na lens journey da zamuyi ke nan fatan Nasara tare da addu'a kar Ubangiji ya haɗa mu da namun dawa a tafiyar da zamuyi na ƙarin ilimi cikin wannan daji mai haɗari.”
Ta yi maganar ba tare da wannan ƙayataccen murmushi ya bar saman kyakyawar fuskarta ba, tana kuma miƙa masa hannu, alama dai take da su gaisa. Bai ce komai ba, kuma bai dena Murmushin ba, ya dai ƙura ma ta ido babu ko ƙiftawa tare da kallon hannun nata da take miƙa masa._
“Pooh! Kanaji kuwa?, lafiya dai, ya ya tafiyar taku ta kasance?.”
Aunty ta kuma magana da take ta faman maimaita masa da alama ya yi nisa duniyar tunani, hakan ya sa ta ɗan bubbuga hannunta a saitin fuskarsa.
Yaja wata ajiyar zuciya tare da kallon ta, ya sauke idanunsa da suka yi ja ƙasa, har yanzu gajiya bai sake sa ba kamar yadda zuciyarsa bata gama yarda da abin da ya riga ya faru ya shuɗe ba.
“Jiya bamu samu mun yi wata fira ba. Ina fata dai komai lafiya a tafiyar taka?.”
Jinjina ma ta kai ya yi sannan ya amsa ma ta da faɗin.
“In shsha Allah.”!
Ya faɗa da ‘yar in'ina ba tare da ya damu da kallon da take bin sa da shi ba.
“Daddy ya ce jibi zaka fara zuwa Mining Company As a supervisor, zaka iya kuwa ko sai ka ƙara huta wa sosai?.”