ta tana mai fadin kiyi hakuri Lelatu komai Jauro zai maki shi dan gida ne ,kuma cin arxiki kikeyi gidan da bana mahaifinki ba...
Madafi ta nufa tana dafa nonon da suka samu ,kamin safe ta nufi da shi kasuwan rugar.
Tun daga wannan rana Lela komai jauro zai mata ta daina fada mawa kowa ,sai dai tasa masa kuka ,haka zai ta lallagwideta tana tsoron fada mawa Oumman ta da kuma Oumma Rabe .
A duk fadin garken nan babu wanda takejin dadin mu'amala dashi sai Abba lamido mutum mai fahimta da nuna mata soyayya bai damu da bala'in Oumma rabe ba ,kullum idan ya fita ya dawo ko wajen gari yaje sai ya taho mata da tsaraban ta nadabam ,wanda wannan yasa mata soyayyar Abban nata .
A wata rana ne Oumma 6ingel tasa Lela kaman kullum fita kiwo da shanayen ta ,wanda anan ne Komai na kadarar rayuwar ta yafara. Kaidar lela ita bata kiwo kusa da Rugar su sai taga ta fita tayi nisa da mutane ,hakan yasata shiga cikin daji sosai , wanda ko fulanin sai mai tsaurin zuciya yake iya shiga irin wannan daji da sunan kiwo .
Abunka ga mugun ka duk inda kake yana tare da kai ,ashe duk wannan tafiyar da takeyi Jauro na bayanta ya kudurci mugun nufi akanta .
Tsayawa tayi da shanayen ta a bakin wani ruwa suna sha kamin tayi gyefe can tana kallon yanda suke cin ciyawan su cikkin kwanciyar hankali murmushi tayi cike da yarinta da kurin cika baki take cewa " aradu na iya kiwo ,shiyasa duk rugar mu babu mai shabaye kaman nawa .
Maganan nata ya sauka a kunnen Abdul da Captain Sadeeq wanda suke kyeta dajin babu tsoro abunka matasan sojoji ,dukkanin su da kakin Su ta sojoji . Cak Captain Abdulrahman yajah ya tsaya yana dakatar da Captain Sadeeq hadi da saito bindigan su ga Yar fulanin da suke hange . A tunanin su wasu muyagun ne suka shirya masu fatsa da wannan kekykyawar yarinya . Tsayawa sukayi gyefen wasu bishiyoyi suna bin ta da kallo hadi da fahimtan ita din wacece ?? Ba tare da dogon lokaci ba suka fahimci yar fulani ce .
Basu bi takanta ba suka cigaba da nusan dajin suna tahowa inda Lela take ,wanda sam bata lura da tahowan su ba ,sai dai ganin su da tayi a gaban ta. Wani irin ihu ta saki hadi da walwali da sandar hannun ta tana jah baya da son kare kanta .
Bin ta da kallo sukayi suna ganin tsantsan firgici a kwayar idon ta .
Haba yar fulani ba cutar dake zamuyi ba ,muna sonne musan hanyar da xamu fasa mu fita cikin gari . Da ido Lela take binsu da kallo tsawon mintoci kamin ta aje sandar hannun ta kasa ,wanda wannan yasa su fahimtar cewa ta yarda da maganan tasu .
Can hanyan xaku bi ku shiga tacan dajin kuna tafiya kadan xaku fito rugar mu rugar SURBAJO wato rugar ya tara yammata ne cike shiyasa akayi masa lakabi da hakan .
Ohk mun gode !!
Suna fadin haka suka cigaba da tafiya cike da takon su wanda daka gani kasan da akwai jarumta da mazantaka .
Ido take binsu da shi har suka kule mawa ganin ta.
Shikam jauro ganin wa'annan sojoji bakaramun daga hankalin sa yayi ba ,wanda bai natsu ba sai da yaga wucewar su . Hakan yasa shi nufar inda Lela take gadan_gadon.
Tun kan ya karaso ta ganshi ,wanda mmki sosai ya kamata ganin jauron ne fah dai.
Jauro!! Jauro me kazoyi mun anan kuma ?. Tayi mgnan cike da tsoron ganin jauro a wurin .
Murmushi Jauro yayi yana mai cewa" nace ina sonki kin ce aa ,na biyoki nan ne na rabaki da mutumcin ki don dama dashi kadai kuke fahari da tunkaho .yau naga mai kwatan ki sai na kyeta maki budurcin naki kinga in yaso abani ke a sadaka.
Wayyo Ounma na jauro...kamin ta karake mgnan ne ya fixgota yana saka hannu yana Rufa mata baki hadi da kicin_kicin din kwance mata zanin jikkn ta .
Sukam su Captain Abdul tafiya sukeyi babu wanda ya kuma ce mawa dan uwansa kanzil har sai da sukayi nisa ,sannan Abdul yace" kai wai Sadeeq yaushe xaka daina shan giya ne?? Jubi fah duk takan shi kataso mu kasamu muyi wannan tafiyar . Babu raba Abdul ,kar fa kamanta tun ina sec sch nake shan giya da kwaya ,kaga ko babu yanda xa'ayi lokaci daya wai na daina sha .
Kwaya kuma ?!! Dama kana afa kwaya ne ban sani ba ?. Dariyar shikiyanci Sadeeq yayi mawa Abdul din kamin yace" ai na daina tun da dadewa saboda wata Yarinya da mukayi class daya da ita . Sam ba so ,nikuma a wannan lokacin nafi kowa tsanan ta sosai nake takura mata a schl dinnan ,tom ni saboda ita na daina sha ,don idan nasha kwaya nazo zatafa cemun dan kwaya gata da tsoro da tsiwa . Wannan dalilin yasaka na daina shaye_shaye ma a makaranta duka .
Dariya Abdul yayi yana fadin kai wannan yarinya Allah yy mata albarka ,kaga ka daina badon Allah ba donn ita kadai. Don ita wace??? Hmmm kai bar mgnan nan kawai ,amma wai Abdul bakaga wani yaro na la6en yar fulanin nan ba ? Captain sadeeq yayi mgnan yana barin wancan mgnan.Ni ma banyarda da shi ba , Abdul yace yana cigaba da tafiyan sa .
Dakata !! Sadeeq ne yayi mgnan yana kama hannun Abdul suna juyawa a tare .
Kafasa zuwa neman...kamin Abdul ya karake ne Sadeeq yace don Allah muje kai fa alokacin da ake serious mgn sai ka rinka yin unserious .
Bai kuma tanka sa ba suka cigaba da tafiya.... Koda suka baro inda sukaga jauro bashi a wurin ,hakan yasa su saurin tafiya cike da 44t suna kutsa kai cikin dajin .
Tun daga nesa suka hango jauro saman lela da batasan halin da take ciki ba ,don numfashin ta ma baya fita . Shikam sai gotso yake buga mawa yarinya karama hadi da ihu yanayi yana karawa . Innalillhi wainna ialihir rajiun. Kalmar da Sadeeq ke nanatawa kenan . Wanda da harda gudu suka isa ga Jauro ,wanda ce masa sukayi cikin tsawa daga ta dan ubanka!!!
Aaa wlh baxan daga ta nakidin. Abun da jauro yake cewa kenan cikin ficewar hayyaci ,wani irin duka Abdul yakai masa a fuska ,wanda nan take fuskan baayi sakanni ba ya haye sumtum hancin shi da bakin shi na fitar da jinin wahala. Wayyoooo!!! Abun da jauro yace kenan cikin dawowar hayyaci... Dagoshi Abdul yayi yyn da Sadeeq ya amshe shi yana masa dukan sojoji bai ki ya rayu ko ya mutu ba.....
Shikam Abdul nufan lela yayi yana dagota hadi da girgixata ko xata bude idanun ta amma ina yarinya tom teenage age . Sa6a ta yayi wanda cikin sauri ya fara kyeto dajin hadi da kokarin fitowa .shima nan Sadeeq ya dago jauro yana jansa a kasa kiyashi da mugun kwari na cixon shi baidamu ba ko maciji ne ya sareshi ya na biyo bayan Abdul .
Hadi da cigaba da taka jauro . Wanda shikan shina halin yanxu baisan duniyar da yake ba. Haka da aka zo wurin duwatsu yake janshi kurrrr duk jikin shi ya farfashe .
Cikin ikon Allah da kuma rashin sani suka shigo rugar surbajo.
Kawayen Lela ne suka ganta a hannun Wannn sojoji aiko nan suka hau ihu suna nufar gidajen su hadi da fara shaidawa cewa Lela a hannun sojoji da jauro . Wasu kuma suna lela ta mutu .
Ai tuni gaddawan fulanin nan masu son Lela suka fara fitowa da makaman su wai acewan su zasu yaki wannan sojoji biyun .
Liman ne ya tare su Abdul hadi da masu jagora zuwa karkashin wata rumfahn Jinka . Zaman su ke da wuya saiga Abba lamido .
Zama yayi yana salati hadi da fashewa da wani irin kuka yana kallon su Abdul da cewa" yarannan mai yasamu da ita me yasamu lela amana ta!!?
Ya isa malam lamido ,mu natsu inshaallh komai xaixo mana da sauki . Yara munajin ku mai yafaru .
Abdul bai iya basu mgn ba ,sai Sadeeq ne ya kwashe masu komai ya fadi masu ....mutane n dake bayan sune fulanin gari mata da maza suka dau salati . Wasu na fadin lallai Jauro yaci amanan marainiyar Allah . Sun zalinci yar mutane .
Kuka baba Lamido yakeyi sosai hadi da dabasani . Oumma rabe ne ke da baya tayi karaf wurin cewa karya kukeyi aradu sharri xakuyi ma jauro . Kune kuka yi mawa lela fyede xaku fake da jauro saboda sharri.
Wani irin tsawa Abba lamido ya sakin mata ,wanda yasata shiru badon ta shirya ba ,kawai sai cewa yake jauro Abunda kayimun Allah yy maka ban yafe ba jauro ,ka xalincimun amana .
Yara mun gode ,kuje ku kashe shi ni yafeshi a dana .
Kayya aaa malam lamido abun da Liman ke cewa kenan . Wanda oumma 6ingel ta gaza cewa komai sai hawaye .
Iyayen matan fulanin duk sun rufa mata suna rarrashi daga masu kuka sai masu jimami .
A fusace Abba ya mike yana daukar lela hadi da kutsa dunjimun mutanen yana barin jinkan .
Dattawan iyaye mata ne suka rufa masa baya suna bin shi don amsan lela suga lfyar ta ,damasu maganin Gargajiyar rugar .
Liman kam godiya sukayi mawa Su Abdul wanda ranshi yagama baci ,tausayin yarinyar ne ya tsirga masa sosai .
Liman ne da mai hukuncin rugar suka saka aka dauki jauro hadi da nufa dashi gidan jinya daga can kuma a wuce dashi gidan horo ga duk wanda aka kama shi yy irin wannan aiki .
Haka rayuwa ta cigaba tun daga nan Ouma 6ingel ta sauya takoma a dduar a kullum allah ya fito mawa da Lela miji tabar Garken nasu hankalin ta zaifi kwanciya .
Sosai aka hora Jauro kusan wata daya ,lela bata fita konan da can .
Tausayin abun da ya faru da ita ne yasaka mutane da yawa fitowa acewan su suna son lela ta zamto mata garesu. Shima nan jauro ya fito .sosaj hankalin Lela ya tashi a wannan lokaci . Cigaba da fita kiwo tayi wanda anan ne takuma haduwa da Su Abdulrahman .
Tun daga nan shakuwa ta shiga tsakanin su sosai,wanda Abdul shi tausayin ta yake matukar ji ,da tunanin idan mazan xananin suka aure lela sam basu san kaddaraba . Sosai zasu azabtar da ita ,hakan yasa shi tausaya mata matuka .
A wata rana ne tana zaune ta rafka ta gumi ,ya zo har inda take bata sani ba.
Laila!! Lailah!!! Sai da ya kira sunan ta sau uku sannan tayi gigif tana kallon sa. Meke damunki ?? Tunani me kkyi? Tambyar da yake mata kenan hadi da kafeta da lulun idon shi . Wanda yasata saurin sadda kai kasa ,tana wasa da ya tsunta hadi da fara tsiyayar da hawaye .
Plz laila fadamu meke damunki ko jauro ne??!.
Daga kanta tayi alamun eh kamin ta kwashe masa komai dake shirin faruwa da ita ,da kowa da ya fito ciki harda jauro .kuma Oum rabe tace jauro xaa bata ,tunda dai shi ya lalatata .
Kurr yayi mat da ido ,har taga maganan tana dago idon ta hadi da sauke shi busa kansa ,tana fadin Don Allah Audul ka Aureni kavar dani rugar mu banason Jauro kashe ni zaiyi...
Tausayin Lailan ne ya kamasa sosai kamin daga bisani yakai hannun shi yana rungumeta hadi da mannata da kirjin shi .
Laila kina sona!! Yayi mgnan yana dago fuskan ta hadi da kallon ta ido cikin ido.
Daga masa kai tayi hadi da cewa eh Audul.
Murmushi yayi kamin yace nima inason ki Laila kuma zan aureki .
Abunka ga yarint auren ma vatasan shi ba nan tahau murna atakaice dai da farin ciki tabar dajin.
Shikam Abdul garin adamawa yakoma hadi da sanar maawa mahaifin shi ,wanda a satin iyayen nashi suka isa rugar su lela hadi da samun Abba lamido ,wanda babu musu ya amince masu .hakan kam sosai yy masu dadi ,nan take aka tsaida komai hadi da saka rana ... Liman kam yy farin ciki haka Abba.
Wanda tunda Oumma rabe tajiyo wannan lbrn tafara masifa da balai ,sosai take bakin ciki da jin hakan .
Wanda ita kam Lela batasaniba ,don tasan dai Abdul ya koma gida . Hakan yasata kullum taba cikin kyewa .
Batasan da mgnan Aureb ta da Abdul ba sai ana saura kwana uku daurin Auren su ,sannan Oumma 6ingel ta cire kunya ta fadi mata . Tayi murna batayi murna ba ,don batason rabuwa da Oumman nata .
Tun daga wannan lokaci lela bata kara ganin Abdul ba har ranan daurin Aure . Tun ana saura kwanaki ukunne ake mata adon fulani hadi da kimtsata da gyaran lalle ...gashin nta kam yasha gyara anxuba man shanu.
Aranan Daurin Aure ne lela tasan ita wacece da salin ta ,kuma anan takejin suma dangin Abdul din sun san komai .
Mahaifiyar Abdul ce tace batason komaj na dangin Amarya itace uwar amarya ,ita su zasuyi mata komai na daki . Don sosai tayi murna da wannan Auren duk da yan tsegumi da masu son Abdul din yayan Aminan ta ,suna dariyar ya auri bagidajiyar bafullatana. Ciki kam harda Nabila wacce ta dauki aniyar ganin bayan Lela a gidan Abdul.
Sadeeq,Areef sune angwaye don sunfi angon dauki ,tunda shine yafara aure a cikin su .
Shigar fulani akayi mata na bakakken sak'i wanda da yammaci motoci suka taho don daukar Amarya . Kai munga duniya abun da ba'a ta6a ba ,don harda Mahaifiyar Abdul wato Hajiya Sa'a aka zo daukar amarya .
Sosai Lela tayi kuka na rabuwan ta da Oumma 6ingel wanda koda Suka isa garin Adamawa gidan Mom sa'adah aka wuce da ita.
Anan ne tasa aka fara yi mata gyara na musamman masu gyaran jiki dana Amarya .wanda lokaci daya laila ta koma kaman wata wayayyiya wacce bata san ma ya rayuwar Rugar take ba.
Abunka ga fillo da iya daukar wanka da ado idan an masu iyawane fa da sauki kam.
Riga da skirt aaka bata tasa na lace mai launin pink da cyan colour .
Makeup kadan akayi mata irin ta amare hadi da bata takalmi mmai tudu kadan da mayafi aka yafa mata.
Yan uwa da kawayen Mom sa'ada da aka zuba ido aga amarya akoma ayi gulma da dariya ,ganin Laila yasa su duka tsuke baki wasu suna kus_kus din cewa dama ashe ba yar kauyen rugar bace .
Kila dangun ta ne acan ,haka dai sukayi ta gulman su duk suka darara. Wanda tun kan a fita da laila nabila ta rike hannun ta gam tana manne mata tare suka nufi moton da zaa kaita gidan Ta.
Mom sa'adah ce gyefen ta ta sanya ta moton ,hadi da rufowa...ita dai idon lela a rufe yake har motocin suka fara barin gidan Hajiya Sa'a.
Ji tayi an riko yatsun hannun ta hadi da matsasu a hankali kamshi mai dadi ya mamaye cikin motom .
A hankali ta bude idon ta hadi da kallon mazaunin drivern Areef tagani yana driving cikin shigar sa ta manyan kaya kaman shinr angon ,sai gyefe guda Sadeeq adayan barayin .
Juyawa tayi ga gyrfen ta mazaunin bayan ta anan ne taga Gogan nata yana sakin mata kayataccen murmushi wanda yake narkar mata da zuciya .
Wanj irin kunyar sa ce ta kamata ,wanda yasata saurin sada kai kasa .
Murmushi yayi don sanin halin kunya irin na Laila yana mai kai Fuskan shi samn gyrfen wuyan ta hadi da shakan kamshin jikin ta da tasha gyara gurin Mom sa'ah .
Wani irin kissing yake binta dashi a hankali da babu mai jiyowa yana bin ta da lips din shi yana wani irin sauka daga kasan wuyan ta da sanyayyar kiss.
Kokarin matsawa take don mamaki ne ya kamata lokaci guda tom wannan meye kuma?? Meye abdul keyi matane?? Tambyar da take mawa kanta kenan hadi da jah baya . Tana dan tureshi a hankali kar su Areef su gani.
Muryar Areef suka tsinkaya yana cewa" kai oga sir kabari ku isa gidab ku mana ,wannan abu da mai yayi kama . Kabar yar mutane ta sauke gajiya mana!!
Dariya Sadeeq yayi kamin ya amshe da cewa" anya xaka rinka barin Laila tana hutawa kuwa ,vaxaka dameta da jaraba ba?...
*SIYAASA TA! na kudi ne banyarda ki karantamun baki biya ba ,idan kk karanta baki biya keda Allah"*
Maman teddy🧸
0808120293248_49
Murmushi su duka sukayi kana yace" ku kam dai da saka ido kuke ...tom ai dole masa ko wannan rawar kafan da kakeyi ka jawo hankalin mu ...Sadeeq ne mai mgnan don yafi Areef iya tsokana . Kaji rabu dashi Muma dai zamuyi auren nan muji mai sukeji ne da tun a moto kamin akai Amarya yake ta wannan rawar kafa.
Dariya duka suka saka banda Lela da tayi shiru tana tunanin Abubuwa barkatai game da rayuwa . Nisawa lela tayi tana sakin murmushin da batasan zata iya yin shiba a wannan lokaci .
Allah sarki Abdul mijina abokin rayuwa ta ban kyauta mawa kaina ba ,na cuce kaina dana rasa Abdul a rayuwa ta . Mgnan take lokaci guda hawaye ya tsanan ta da tsiyaya a kwarmin idon ta. Tuno da yanda Nabila ta ribace ta ta sanyata a hanyar madigo da mutumcin ta na Aure yasata fara doka mawa nabila allah ya isa . Tana cigaba da shar6an kukan ta harda kyekyatawa.
Abdul yasan komai na vaira6a wulakantani a rayuwa ba .ya maisheni tamkar Wacce tayi rayuwar wata kaasa bama nageria ba ,bare kuma har a kalleni ace wai na taso ne a cikin karkara ,tabbas indaba don nina fada ba ,kowa wani yaje ya fadamasa cewan ga Asali na babu mai yarda .
Ganin yanda Abdul ya gogar dani harda masu kula dani wurun shirya komai na yasa na zama cikakkiyar Matar Alhaji masuji da tashe matasa masu rumbin dukiya . Irin Arxikin abdulrahman yasa na jefa kaina cikin wannan mawuyacin dabia ,na koma mara kirki sam . Kai wayyo ni Laila nayi nadama ,alokacin da bashi da amfani gareni. A wannan dare kam laila kwanan zaune tayi tana kuka .wanda har duhu dubu take gani saboda tsaban kuka idon ta ya kumbura jijiyoyin idon ta sun rirrike mata .
Bangaren Ko Areef rasa abunyi yasa shi ba tare da 6oye mawa mahaifin shi ba yasanar masa komai game da mgnan da sukayi da honorable .