x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 9 - NISAN KIWO

  • 24001 words
  • 25414 words
  • Out of 25414 words

Category: Love Stories

Views 60

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
dan har da ɗinki, musamman ma Aman da yafi Khair jin ciwo,

Tunda ta shigo cikin asibitin take ta Safa da marwa hankalinta ya matuƙar tashi, babbar damuwarta kar su mutu dan bata burin hakan ko a mafarki,

Fitowar Amer yasata isowa gurinsa da gudu tare da riƙe hannunsa tace "bro ya jikin nasu?"

"Akwai alamun sauƙi ƙanwata ki kwantar da hankalinki dole suna buƙatar kulawa ta musamman gaskiya a yau kaɗai bazasu farfaɗo ba, zuwa gobe ma bamu da tabbas amma muna bukatarki a office"

Ƙirjinta ne ya bada dum dan ko wace irin tambaya sukayi mata bata da amsar da zata basu.

Sbda kar ya zargi wani abun yasa tai saurin binsa office ɗin, umarnin mazauni yayi mata kana ya cire farin gilashin dake manne a idonsa, kafin yace "akwai wasu tambayoyi da suka zamo dole ayi miki su"

Yai maganar yana kafeta da ido.

Sunkuyar da kanta tayi, kafin ta fara kuka, sai kuma ta tsayar da kukan tace "doctor dukkansu yayuna ne, farin shine wanda zan aura ɗayan kuma abokinsa ne, sun haɗu da ƴan fashi shine suka yi musu illah haka mu kanmu bamu san inda suka shiga ba kwana biyu, daga baya aka zubasu a ƙofar gidanmu, nazo fitowa naci karo dasu gashi mahaifiyarmu bata nan shine na sakasu a mota na taho dasu ai nayiwa Papa bayanin komai"

Cikin gamsuwa doctor yace "okay Babu damuwa Allah ya daɗa karewa"

Ta amsa da cewa "Amin"



Sai a lokacin ta samu damar yin ajiyar zuciya mai cike da nuna ta tsira.

Ƙarfe 6:pm Papa ya fito yana sanye da kaya na gida, Anan na ganinsa taje da gudu ta rungume shi tana cewa i miss You my Papa" wani irin so da ƙaunarta ne ke ratsa ko ina na jikinsa, yana shafa kanta yace "miss You too my lovely daughter daga tafiya ziyara shikenan, bani labari"

Rausayar da kanta tayi tare da cewa "Papa a kula da marasa lafiyar da na kawo zanyi maka bayani soon ta shiga mota tabar gurin.

Girgiza kai yayi yana murmushi har motar ta ɓace ma ganinsa, kafin ya koma cikin asibitin.

NIGERIA.

wani irin murɗawa cikinta keyi mata, yayinda wasu ƴan matan likitoci ke kanta, yarinya ce wanda a ƙalla bazata wuce 18yrs ba, "Maryam kiyi Nishi insha Allah zaki aihu lafiya sannan ki riƙe ƙafar gadonnan da kyau"

Sosai wacce suka kira da Maryam ɗin ta haɗa zufa, duk da ƴar madai-daiciyar Fanka dake bada iska daga sama, cikin ikon Allah tayi Nishi mai ƙarfi tare da ambaton sunan Allah, sai ga yaro nan ya fito, bayan nan mahaifa, Mama na gefe a zaune ta rafka tagumi tana ta kallon hidimar da likitocin keyi, jin muryar Amanda mai kaya yasa mama miƙewa zumbur tare da rungumeta, sosai sukayi murna da ganin juna sai washe wa juna baki sukeyi, jiyo kukan jariri yasa Amanda cewa "a ina kika sami yaro kamar ma sabon aihuwa" mama ta kawar da kanta gefe tare da cewa ƴarki ce ta aihu" Amanda ta fatalar da jakar dake rataye a kafaɗarta kafin ta kutsa kai ciki, lokacin har sun gyara boy ɗin an juye ruwan wanka anyi masa, abin mamaki da takaici a towel aka naɗeshi bai samu arziƙin kayan sawa ba, bayan sun gama aikinsu suka miƙawa mama dake zaune ita da Amanda, sannan suka umarci Maryam da ta tashi ta gyara jikinta tunda ta huta, da taimakonsu taje toilet suka gyarata sannan ta fito zuciyarta nayi mata zafi, suma kansu sunyi mamakin rashin kulasu da maman barayi ba, bayan sun kammala mama tace "nawa ne kudin ku?" Sukace 10k, ta ƙirgo ta miƙa musu suka fice suna godiya, ko kallon jaririn mama bata wani yi ba, ta miƙawa Amanda bayan Amanda ta karɓa mama tace "wannan jaririn da kike ganinsa na mallaka miki shi halaka malak gobe insha Allah zamuje ayi masa takardar yarjejeniya tabbas ya zamo naki na cika alƙawari".

Jin haka yasa Maryam waro idanu cikin galabaitacciyar murya tace "haba mama ya zakiyi min haka, ke da kanki kikace babu uwar da zata haifi ɗa ta gujeshi shin kina ganin kinyi dai-dai kenan, Anty Amanda fa ba musulma bace akan me zaki bata yarona?"

"Kin gama? nace kin gama? bazan san nasiha kikeyi min ba sai kinzo daidai saitin fuskata kin wankamin mari tukunna, Amanda ki kwantar da hankalinki babu wani abu dazai rabaki da yaronnan ki saka masa duk sunan da yai dai-dai da zuciyarki idan har kin amince yanzu ma sai mu wuce ayi takardar"

Jikinta na rawa ta janyo hand bag ɗinta tare da ciro kuɗi bandir na dubu ɗai ɗai har biyar ta ajiye a gaban Maryam kana suka fice tana rungume da jaririn, jakarta na kafaɗarta.

Tsabar takaici da baƙinciki ko kallon kuɗin Maryam batayi ba, dama jiri take gani a halin yanzu komai ya koma mata sabo, ciwon kai ya dawo tsananin jiri wanda yasa ko gabanta bata kallo duk ya dawo mata, har ta mike tsaye taji sam bazata iya tafiya ba ta durƙushe a gurin idanunta na zubar da zafafan hawaye.

Suna tafe a mota Amanda tana rungume da jaririn tana driving wani irin nishaɗi takeji a zuciyarta kuwa tana hasaso inda zata tafiyar da jaririn da take tunanin sunan da zata kaisa coci a sanya masa...

Zazzafar cakwakiya biki bidiri anan na kawo ƙarshen Free pages idan kinason ci gaba ga hanyoyin biya nan



Littafin NISAN KIWO na kuɗi ne 500 normal group posting sau ɗaya a rana.



1k posting sau biyu a rana har weekend.



Account number 3175689751 Zainab habibu first bank shaidar biya tanan👉08141799224 zanyi adding ɗinki a paid group



Karku manta Book1&2



Ƴan Niger katin Airtel zaku tura ku ɗauki hotonsa ku turomin ta wannan number 08141799224



Wanda basa da account katin Mtn zaku tura screen shot ki turomin ta numberta 08141799224 Please banda vtu


Masu tambayar document ɗinsa suyi haƙuri dan bazanyi document ba idan kinaso ki biya ki karanta👏


Sai mun haɗu a paid group ko a arewabook

Karfa ki bari ayi tafiyar

babu keee💃



Mutanena na facebook da Whatsapp ina miƙo saƙon gaisuwa.


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels
End Ads