lura da yanayin Arshi ɗin ba, kan kace me tayi zigidir daga ita sai pant sai rawa take tana ihu tana cewa asosa a durje idan an gama asamin kaya, sai ihu take, daga ƙarshe tai saurin zuwa gurin Arshi tana shirin wanka mata Mari hannunta ya maƙale, dai dai lokacin Alhaji Kasim ya turo ƙofar parlo, hankali a tashe ya ƙaraso Anty Hadiza taje da gudu ta rungume shi, hhh ta kuwa shafa masa rabonsa, dan shima sai da yayi zigidir sai sama yake yana ƙasa, Arshi ta mike jiki a sanyaye dan abin ya fara sakinta ta ɗauki remote ta kunna musu waƙa kana ta barsu a gurin...!
[11/1, 9:28 PM] Mom Islam 🍹💋: *NISAN KIWO❄️*
Page 12
Mom Islam
Cikin zafin rai Anty Hadiza ta kalli Alhaji Kasim kafin ta kalli jikinta sannan tace "yaya banda zubar da girma a gaban ƴar cikinka kake rawa?"
Sai da ya harareta lokacin ƙaiƙayin ya ɗan sakeshi kafin yace "har na kaiki da kikayi zigidir a gabanta?"
Tsaki taja mtsew tare da barin parlon ta wuce hanyar bedroom ɗinta, anan ta samu Arshi a zaune ta takure ta rusa tagumi, "ke ƙaramar makira uban me ya kawoki nan?"
"Baki nunamin ɗakin da zan zauna ba kuma sanyi nakeji"
Arshi ta faɗa haƙoranta na kaɗawa.
Anty Hadiza tai fatali da ƙafarta tare da tura door na bedroom ɗinta, tasa ƙafa ɗaya zata sanya ta biyu kawai ta sule suuuu, ƙafarta ɗaya a gaba ɗaya a baya, ta kurma ihu tana cewa "Arshi kiramin yaya dan Allah zan mutu ƙila ma karyewa nayi"
Arshi na zaune a inda anty Hadiza ta barta tsabar kaɗuwa da jikinta keyi, sai samun guri tayi ta kwanta sai wani irin numfarfashi takeyi,
Alhaji Kasim ya taho da rigarsa a kafaɗa, sam bai lura da tana kwance a tsakankanin ƙofarsa da ta anty Hadiza ba, jin ƙafarsa ta dunguri abu yasa shi ja da baya, kafin ya ƙarewa Arshi kallo, sannan yace "ke mai ya kawoki nan?" ta kasa bashi amsa sai riƙe kanta da takeyi sbda zazzaɓi ya dirar mata tashi ɗaya, har zai tsuguna yaji ihun anty Hadiza tana cewa "yaya idan ma a gurin wannan yarinyar kake wlhi ka gaggauta kaucewa dan aljana ce ba mutum ba"
Alhaji Kasim ya zaro ido, ya fara tafiya da baya da baya har sai da ya fito parlo, da ƙyar anty Hadiza ta samu ta rarrafo zuwa bakin ƙofa, ga mamakinta sai taga kamar idanunta gizo sukeyi mata da abinda suka gane mata, tsantsar tsoro ya bayyana a zuciyarta da idanuwanta, da sauri ta cigaba da jan ɗuwawu ta koma ciki, anan cikin ma ƙarar wacce take kama da na guguwa ne ya kewayeta, cikin ɗaga murya take cewa "wa innahu sulaimanu wa innahu jafaru, sai maimaitawa takeyi tana sake ja da baya, ita dai Arshi tana mugun bata tsoro dan fuskarta ta fara gani, bayan Arshi ɗin na kwance a ƙofar ɗaki, tashi ɗaya taji abun kamar anyi ruwa an ɗauke, cikin sauri ta miƙe dan ƙafafun sunyi mata dama dama, ta tako a hankali gabanta na ci gaba da faɗuwa, a tsorace ta tsallake Arshi ta wuce, dan a cewarta ta daina kulata tunda ta zamo musu masifa, koda ta fito parlo babu Alhaji babu alamarsa, ɗan zanin da ta samu ta ɗaure ƙirjinta ta gyara kafin ta fito harabar gidan taga babu motar da yake fita da ita, cikin ɗaga murya tace "mai gadi Alhaji ya fita ne?"
"Eh ya fita yanzu ma kuwa?"
Tai ƙwafa tare da komawa ciki.
******
Yau kwananta uku da barin gida, bayan fitar mom daga gurinta bata sake shigowa ba, sai dai suna haɗuwa a kitchen suyi aiki sannan kuma tana zuwa gaishe ta duk safiya, alhamdulilah taji sauƙin ƙuncin da take ciki, babbar damuwarta ranar da suka gane halittarta ta fita daban da tasu, 6:am tana tsaye gaban mirror tana sake aske kewayen bakinta inda gashi ke fitowa, duk da yiwa ƙofar key da tayi, tsananin tsoro ya matuƙar baiyyana a zuciyarta, hankali a tashe take gyara gemun nata, bayan ta gama ta gyara gurin ta gogo sannan ta shiga toilet ta tara ruwa ta cire kayan jikinta kana ta fara shirin yin wanka, babban abin tsoron bai wuce mantawa da ɗankwalinta da tayi a parlo ba, gashi ta cire kaya.
Tana cikin tunani aka turo ƙofa tunda ta waje ma akwai extra key guda ɗaya, muryar Little Hajo ne ya bugi dodon kunnenta, ƴar aiki kizo inji anty Jumayma" bata bata amsa ba, taci gaba da wankanta, har ta kammala, tana tsugune aka turo ƙofar toilet da sauri ta matse ƙafafunta tare da runtse idanu cikin sigar lallashi tace "Hajo dan Allah ki rufeni zansa kaya" cikin ɗaga murya Hajo tace "mai kan maza" Anum ta mike da sauri tare da sanya hannu a baki alamar little Hajo tayi shiru, itako Hajo tayi ido biyu da gaban Anum ta zube a gurin sumammiya hankali a tashe Anum tayo parlo sai da ta zura doguwar rigar atamfa tare da ɗaura ƙaton ɗankwali kafin tazo gurin little Hajo dake kwance rai a hannun Allah, jin horn na motar dad yasa Anum jingina da bango tare da ƙaddarawa kanta kwananta ya riga da ya ƙare dan idan ya shigo ya samu Hajo a wannan halin tama gama yanke wa kanta hukuncin kasheta zaiyi.
THAILAND
A satinnan suke da niyar kammala duk wani shiri da ya shafi Leeela domin kuwa Monir ya samo musu mafita harma da shigar da ta dace suyi, yau kwanan Anan biyu kenan da zuwa gidansu Arya sun saba da granny sosai kai kace sun shekara, a ƴan kwanakin nan Arya sam bata cikin walwalah damuwarta da burinta shine ta ganta gata ga Khair,
Washe gari.
Ƙarfe 2:pm Monir yazo gidansu, dukkansu suka taru a parlo yana yi musu example na inda abin zai kasance, Anan ta ɗaga hannu sama tare da cewa "ya kamata kafin mu shigar masa mu sami wani na hannun damarsa ina ganin abin zai fi ko, amma shawara ce" Monir ya zuba mata idanu, kafin yace "komai cikin sirri ake yinsa Babu buƙatar wani sai yaji" yai maganar in seriously.
"Okay tom shikenan" Arya ta faɗa hannunta na riƙe da biro da wata ƙatuwar takarda, cikin nutsuwa ta fara zane wanda take yinsa cikin ilimi da ƙwarewa, "a shawarar da ka yanke kace ni zan fito a matsayin wawuya ko? ita kuma Anan a matsayin gurguwa" eh hakane ta hakane zaku samu duk wasu muhimman abubuwa, yai maganar yana miƙewa tsaye.
Jikin Granny a sanyaye tace "Ubangiji ya bada Sa'a nikam zuciyata ta mugun tsinkewa amma nasan da izinin Ubangiji akwai Sa'a a tare daku"
Monir ya mike tare da gyara zaman jakar hannunsa, kana yace "ni zan wuce kuyi ƙoƙari ku cimma nasara kunji"
Dunkansu suka gyaɗa kai alamar "toh"
Granny ta rakashi har parking space inda motarsa take sukayi sallama ya wuce.
Har Arya ta miƙe Anan ma ta miƙe tsaye kafin tace "zan ɗan fita zuwa out ko akwai abinda kike buƙata?"
Arya ta girgiza kai, kana takai biro bakinta, tana kallo Anan ta fice zuciyarta cike da waswasi.
Lokacin da Anan ta fito Granny ta koma ɗaki, dan haka ta samu damar ficewa kai tsaye.
Tana tafe tana waigen bayanta har ta iso bakin get, juyowar da zatayi suka haɗa ido da Arya, cikin zafin rai ta ƙarasa gurinta tare da kallon ƙwayar idanunta kafin tace "kodai akwai wata matsalar ne?"
Anan tai saurin girgiza kai tare da daburburcewa tace "inaa so..son.."
Arya tayi murmushi kafin ta sake matsowa inda take kana tace "karki damu sis ki faɗi abinda kikeson faɗa Kinga time ɗin la'asar yayi muje muyi sallah sai in rakaki ki siyo"
Ba haka taso ba gudun kar Arya ta fahimci wani abu yasa tace "toh muje"
Suna shigowa ana kiran sallahar la'asar Arya ta shiga tayi alwalah, tace Anan taje tayi alwalah, jiki a sanyaye ta nufi hanyar toilet tare da shigewa ta matsa jikin bango tare da jingina kanta, a zuciyarta tana cewa "itafa wannan sallahar da takeyi bazata iya aikin wahala ba, sai ta jiƙa fuska sannan tazo ta dungura goshi a ƙasa gaskiya aikin yayi yawa, "Anan lafiya kuwa na jiki shiru har yanzu baki fito ba?"
Arya ta faɗa lokacin da take ƙarasawa gaban mirror tana sake gyara fuskarta,
"Zan fito yanzu"
Anan ɗin tace tana tsaye dan ta ma mance inda Arya tayi alwalah har ta kwaikwaya tayi, cikin sauri ta ɗan dangwalo ruwa ta shafa a fuskarta kana ta shafa a ƙafarta da hannu, sannan ta fito tana ɗan gyara gashin kanta da suka zubo, Arya tana zaune gaban mirror ta hangota ta fito, cikin zolaya tace "Anan kodai kema cikinki ya rikice ne irin na Granny?" Anan tayi murmushi dan ita kaɗai tasan halin da take ciki, sbda a halin yanzu tunaninta taya zatayi sallah Arya tana zaune a gurin, tana ta tsaye har sai da Arya tace "ki ɗauki sallahya mana ga hijab nan a gurin" jiki a sanyaye ta isa gurin sallahyar tare da sanya hijab ɗin ta kalli yamma, sbda ta mance a yaya tayi jiya, daga cikin mirror Arya take kallonta "ba nan zaki kalla ba, a tunanina kin riga da kinsan gabas naga kinyi sallah shekaranjiya da jiya"
Anan ta dafe ƙirji zatayi magana Granny ta shigo, sai da ta ƙare musu kallo kafin tace "yanzu mukayi waya da Khair ammafa yana cikin mawuyacin hali dan muryarsa bata fita sosai anya tafiyar nan ba tare dani zakuyita ba" Arya ta harari Granny tare da ficewa a ɗakin, itama Granny bayanta tabi lokacin da granny ta iso ɗakinta har Arya ta shige ta ɗauki wayarta tana gwada number Khair, cikin Sa'a ta shiga yana ɗagawa ta fashe da kuka tare da cewa "khair kana cikin ƙoshin lafiya ko? karka damu zanzo in dawo dakai gida insha Allah kayi haƙuri kana raina"
"Arya bana cikin kwanciyar hankali rabonmu da abinci tun shekaranjiya tunda muka zo sau ɗaya aka bamu coffee sai ruwa da ake kawo mana koda yaushe, a gigice tace "Khair babu inda zakayi ka gudo?"
"Arya da akwai da tuni kin ganni, Aman kam sai dai ku tayashi da adu'a saboda Gara halin da nake ciki..."
Wani irin ihu khair ɗin ya tsala wanda yasa Granny da Arya shiga tsananin firgici, tashi ɗaya wayar ta katse, sunbi kiran amma shiru babu alamar zata shiga, Arya ta zube a gurin hawaye na wanke mata fuska, cikin Muryar kuka tace "gobe zamu fara aiki da izinin Ubangiji bazan iya ƙara koda kwana biyu bane ban ceto rayuwar Khair ba, Granny ta dafa kafaɗarta cikin Muryar ƙarfin hali tace "tabbas ke jinin Alee ce, akwai wata sarƙa da zan baki ki ɗaura a ƙafarki da zarar kin shiga gurin hankalin kowa zai ɗauke har ki shiga kiyi abinda zakiyi ki fito,
Anan dake raɓe a jikin ƙofar Granny tai saurin ja da baya tare da komawa ɗakin Arya ta zauna saman sallahya tare da mimmiƙe ƙafafunta alamar tayi sallah, tsabar takaici da baƙinciki Arya kwanciya tayi a gadon Granny har lokacin kiran sallahar magriba tayi,
Granny kam hankalinta in yayi dubu ya tashi, ta ɗaga hannu sama tana gayawa Ubangiji damuwarta tare da adu'ar Allah ya kawo musu mafita ta Alkairi.
Ganin gidan yayi shiru sosai, yasa ta miƙe bayan ta cire hijab ɗin ta shiga toilet ta kunna ƴar ƙaramar wayarta dake silent koda wane lokaci, gurin text message naga ta shiga, ko me take rubutawa oho sai ta tura saƙon sannan ta kashe wayar ta mayar aljihun wandonta na ciki,
Da sauri ta fito sai haɗa gumi take alamomin rashin gaskiya suna neman su fara baiyana a kanta, lokaci ɗaya sannan kuma tashi ɗaya, sai kewaye ɗakin take tana haɗe hannayenta guri guda...!
Hii fans mai kuke tunanin Anan tana ƙullawa
Free pages yana daf da ƙarewa.
Littafin NISAN KIWO na kuɗi ne 500 normal group posting sau ɗaya a rana.
1k posting sau biyu a rana har weekend.
Account number 3175689751 Zainab habibu first bank shaidar biya tanan👉08141799224 zanyi adding ɗinki a paid group
Karku manta Book1&2
Ƴan Niger katin Airtel zaku tura ku ɗauki hotonsa ku turomin ta wannan number 08141799224
Wanda basa da account katin Mtn zaku tura screen shot ki turomin ta numberta 08141799224 Please banda vtu
Karfa ki bari ayi tafiyar babu keee💃
Mutanena na facebook da Whatsapp ina miƙo saƙon gaisuwa.
[11/3, 7:39 PM] Mom Islam 🍹💋: *NISAN KIWO❄️*
Page 13
Mom Islam
Masu amfani da arewabook zaku dinga ganin update ammafa idan kukayi following ɗina👇
https://arewabooks.com/u/momislam11
"Anan gobe fa zamuyi tafiyar nan"
Arya ta faɗa muryarta a dashe, sbda taci kuka ta godewa Allah.
Tun safe suke ɗaki ita da granny da Anan, dan babu wani abu da suka ɓoye mata na game da sirrikansu, har yamma duk suna ta tufka da warwara, Arya tana ta kanta bata sake bi ta kan Anan akan sallah ba, sbda tasan ai ita ba ƙaramar yarinya bace da za'ayita mata bita kullum.
Washe gari sun kammala shiri, shigar da sukayi kusan iri ɗaya ce, Pakistan ne na riga da wando pink color wandonsa milk color sai mayafinsa siriri shima milk yasha adon stone masu ɗaukar ido, sosai sukayi kyau gunin birgewa sbda shigar tasu ta amshi jikinsu, ba wani makeup sukayi ba, iya powder da lipstick da suka goga a lips ɗinsu, tunda suka fara shiri jikin Granny yake a sanyaye, ta wani ɓangaren tana ƙarawa kanta ƙwarin guwaiwar tafiyar tasu,
Anan kam bata da wasu kaya na canji, dole Arya ta ware mata kala huɗu wanda suka haɗa a tare a bag guda, ba wani abincin kirki sukaci ba, koda yake Gara ma Anan ta cinye wanda Granny ta saka mata, suka miƙe suna yi mata sallama, har parking space ta rakasu, ji take kamar idan suka tafi bazasu dawo ba, "zanyi kewarku" Granny ta faɗa zuciyarta a karye, sam ta kasa samawa kanta sukuni sbda alhinin tafiyar tasu, har suka shiga ƴar madai-daiciyar motar Arya tana tsaye a gurin har suka bar gidan idanunta na hanyar da suka fice, "Allah yasa fitarku da aikin da kuka tunkara ya zamo Alkairi da nasara" Granny ta faɗa take komawa ciki.
Hawansu babban titi yasa Anan sake waro idanuwanta tare da ƙarewa hanyoyin da suke bi kallo, sunyi tafiya mai nisan gaske kafin suka iso wata hanya wacce yawancin mutane basu san da zamanta ba, Arya ta matsa zoben dake hannunta get ɗin dake kange a gurin ya buɗe, ta kusa motar ciki suka ci gaba da tafiya, a ƙofa ta ƙarshe ne sai da ta matsa zoben sai uku kafin ta buɗe suka shiga, "welcome to Leela guest house" Abinda sukaga an rubuta kenan, har yanzu Anan tana kallon hanya ko runtse ido batayi.
A nesa da hanyar shiga tayi parking, lokacin da ta matsa zobenta lokacinwata babbar ƙofa ta faɗo, Khair da Aman suka fito jikinsu duk jini fuskarsu da bakinsu, cikin sauri Anan ta riƙe hannunsu cikin ɗaga murya take cewa "Arya zan tafi dasu ki taho da mota" Arya tace "babu buƙatar yin magana da ƙarfi Please ki rage sautin muryarki, Lokacin da Anan ta riƙe hannun Khair da Aman aka saki bindiga mai masifar ƙara, wacce ta sauka a kan ƙafar Arya, khair Anan da Aman duka a idanunsu akayi amma babu wanda yai yunƙurin tsayawa taimaka mata sai Aman dake cewa "Khair ƙanwarka ce bai kamata kayi mata haka ba, khair idan kayi haka Kaci amana"
Aman yana maganar suna gudu har suka iso gurin mota Anan ta shigar dasu suka ƙarawa motar wuta,
"Nasan bakusan koni wacce ba, Ubangiji ya turoni ne domin in taimaka muku bisa ga halin da kuka shiga" gyara zaman sumar kanta tayi wanda ya rufe mata fuska kafin taci gaba da cewa "waye khair a cikinku?"
Khair da tunda ta fara magana yake ƙarewa bakinta da hancinta kallo yanajin wani abu na tsirga masa tun daga tsakiyar kansa har zuwa tafin ƙafarsa, a hankali ya nuna kansa tare da share jinin dake cigaba da fito masa a gefen baki,
"okay yanzu hospital zan wuce daku akwai wani asibiti da Dadyna yake aiki bazaku samu matsala ba"
Tai maganar tana ƙarewa Khair kallo.
Driving take cikin ƙwarewa, suna tafe tana yi musu hirar Arya, sam na kasa jiyo me take gaya musu na game da Granny da Arya ɗin, lokaci ɗaya Khair yace "bazamu koma gida ba"
Aman yai saurin kallonsa sai kuma ya kawar da kai.
Har ta nufi wata hanyar, cikin sauri ta juya akalar motarta a hanyar da zata sadata da hospital, abin ya matuƙar bata tsoro kafin su kai ga shiga cikin asibitin duk babu numfashi a tare dasu, tsananin tsoro da firgici ya dirar mata a zuciya, jiki a sanyaye tai parking inda aka tanada dan ajiyar motoci, hankali a tashe ta fito tare da yaye ɗankwalin dake yane a kanta, ta wurga mota sannan ta tura hannunta cikin aljihun wandonta ta ciro wayarta ta danna wata number, ringing ɗaya zuwa biyu aka ɗaga, murya irin ta wacce ta kiɗima tace "Papa wlhi ina cikin wani hali, Papa nazo da wasu hospital ɗinka Please I need your help Papa" ta ƙarashe maganar tana fashewa da kuka mai tsuma zuciya,
A kiɗime Papa yace "ina tiyata room amma ki shigo ciki akwai Amer zanyi masa bayanin komai"
Hankali a tashe ta shige ciki da waya a hannunta, cikin Sa'a tayi arba dashi tana shiga, ta cakumeshi hawaye na ambaliya a idanunta tace "bro kayi taimakon ceton rai wlhi idan kace a'a zasu iya mutuwa dan Allah ka kace wani abu" zai yi magana kiran Papa ya shigo wayarsa, bayan ya ɗaga sukayi magana da Papa sannan ya kalli Anan lokacin da yake katse kiran yana sanya wayar a aljihu kafin ya kalli Anan ɗin yace "karki damu duk wasu abubuwa da suka dace zanyi amma akwai wata papper da zaki da hannu"
"Babu damuwa kawo"
Anan ta faɗa sanya yatsanta manuniya tayi baya da gashin kanta da ya ɗan zubo mata.
Yana miƙo mata tasa hannu ta miƙa masa cikin gaggawa aka shigar dasu,
Likitoci hudu ne suka haɗu a kansu ko wanne da aikin da yake yi, ita kuma tana can mota ta samu Hankey tana goge inda jini ya ɓata,
Har aka gama musu treatment dukkansu basu sani ba,