x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - NISAN KIWO

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 25414 words

Category: Love Stories

Views 62

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
Ayra tanada jiki anan kuwa siririya ce, "wayo Allah yau naga aihuwar asara yarinya ta biyo halin uwarta" Granny ta faɗa tana mimiƙe ƙafafu, Anan kam tsayuwa tayi tare da jingina da jikin bango, dariya take son yi amma tana tsoron Granny dole ta haɗiye dariya ta juya zata wuce ɗakin Arya ɗin.
"Ke baƙuwa harda ke a guduna ko kun haɗa baki ne?" Anan ta girgiza kai alamar a'a kafin ta taho gurin Granny tace "bazan iya ɗagaki ni kaɗai ba"
Granny tayi tsaki mtsew tare da cewa "amma wanda ke baku abinci yayi asara gaskiya ace duk tsayin nan naki kamar bishiya bazaki iya ɗagani ba, niɗin guda nawa nake ko ance Miki inada nauyi ne?"
Dariya ce ta kufcewa Anan sai da tayi mai isarta kafin ta kamo hannun Granny daƙyar ta taimaka mata ta miƙe, ga yanayi na jikin tsufa, cikin ƙarfin hali suke tafiyar Granny na dafe da bango har suka ƙarasa ɗakinta, tayiwa Anan godiya tare da zaunar da ita tace ta zauna suyi hira, Anan tayi murmushi kafin ta zauna a saman carpet tana kallon Granny da ta karkace hular dake kanta,
"Akwai wani jikana, in gaya miki jarumi ne kyakkyawa mai kyau da cikar zati ga iya biyayya, hamm yaron nan ina matuƙar sonsa, iyayensa ne suka yi hatsarin mota duka suka mutu, shine na riƙeshi, yanzu an wayi gari ya barni wanda ya fimu ƙarfin arziƙi ya sacemin shi" Granny tai maganar tana share hawayen dake kwaranyowa a idanunta"
"Kiyi haƙuri granny zai fito nayi miki alƙawari" da sauri Granny ta share hawayen tare da yin murmushi kafin tace "kinyi min alƙawari?" Anan tace "eh nayi" sunata hirarsu wanda har yanzu anan ɗin bata basu labarin addininta da wasu abubuwa da suka shafeta ba.
Acan kitchen Arya ta kammala girkin dare, tazo ta jere a dining, batayi musu magana ba ta wuce ɗakinta tayi wanka ta sauya kaya sannan ta fito ta goge jikinta kana ta shafa mayuka masu gyara jiki da ƙamshi, sosai zagin mahaifiyarta da granny tayi ya ɓata mata rai, yau kam sunyi faɗa fushi take yi da granny dan ko maganar ta kammala batayi ba, duk da tasan Granny ɗin da saurin jin yunwa, tun kafin ayi magriba take cin abinci, itakam ta riga da ta ɗauro alwalah koda ta duba agogo lokaci ya ƙure, haka tayi sallar zuciyarta babu daɗi dan batason kaucewa lokacin sallah, kasancewar la'asar tayi.
Hamdala tayi na kammala girkin da wuri ta haye gado tare da kunna Whatsapp ta kunna data, saƙon Monir ne a farko dan haka ta fara dubawa sabda saƙonnin sunyi mugun jan hankalinta a hankali ta furta ya ilahi kafin ta fara karantawa kamar haka....!

Following ɗina shine zai sa ku dinga samun update a arewabook sau biyu a rana, Please masoyan gaskiya ku nunamin love ta hanyar following ɗina@momislam11


# Granny
# Arya
# Anan
# Monir
# Leela

Drop your comments waye gwaninku🤸



Page9

"Arya na samu duk wasu bayanai na sirri akan Leela ku zamo cikin shiri"

Da sauri ta gyara zama kafin tayi masa voice.
"Monir na yake shawarar zamu je a matsayin masu neman taimako, daga nan kaga zai ɗaukemu a matsayin masu yi masa hidima, ni zan fito a matsayin makauniya ita kuma Anan zata fito a matsayin gurguwa, kana ganin hakan yayi?"

Tai maganar tana tura masa emoji mai alamar damuwa,

Ya ɗan jima bai bata amsa akan mafitar da ta samo ba, daga ƙarshe ya fara yi mata typing..
"Bakya tunanin za'a iya samun matsala idan har ya gano Basaja kukayi masa?"
Arya tayi murmushi kafin ta mayar masa da cewar "zamuyi ƙoƙarin kiyaye faruwar matsalar" ya turo mata da amsar Allah ya bada Sa'a zanci gaba da bincika muku"
"Amin" tace tana saukowa daga kan gado.
KANO NIGERIA
Ƙarfe 8:am lokacin Jannat ta kammala shirin tafiya gida, tun kafin su fito parlo take gargaɗin Anum kar tayi kuka ko da bayan tafiyarta ne, tunda ta lura da yanayin fuskar Anum ɗin, iya mom da Anum ne suka rakata parking space inda motarsu take, driver yayiwa motar key Jannat tana ɗagawa Anum hannu, mom tayi murmushi kafin tace "ki saki jikinki babu wata matsala"
A tare suka dawo ciki, "Allah sarki rayuwa" Anum ta faɗa a zuciyarta, kamar inda mom ɗin ta faɗa yau Dad yake hanya, tun bayan tafiyar Jannat suka shiga kitchen suke ta hada-hadar haɗa abinci, su sauke wannan su ɗora wancan, Anum kam tunda taji mom tace dad yana airport gabaki ɗaya hankalinta ya tashi, zuciyarta ta tsinke, amma duk da hakan bata bari mom din ta gano ta ba, ƙarar shigowar motoci ne yaja hankalinta, wanda ko ba a gaya mata ba, tasan baya rasa nasaba da isowar mai gidan, hankali a tashe ta tsame hannunta a ruwan kumfa na wanke-wanken da takeyi na kayan da sukaɓata, tana tsaye a kitchen ɗin kamar wacce ruwa ya cinye ta dafe hannayenta a ƙirji taji sallamar mom, da sauri ta waiga tare da ƙoƙarin kawar da damuwar dake shinfiɗe a fuskarta, "Anum yi sauri ki ɗauki wannan kunun tunda an kammala ki miƙawa Dad yana parlo ki tabbatar da kin nutsu gurin bashi" wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi, lokaci ɗaya gumi yayi mata lulluɓi, kamar wacce ta watsa ruwa, kanta a sunkuye ta miƙa hannu ta karɓi kyakkyawan jug ɗin, Mom ta miƙa mata tana cewa "zan taho masa da ƙosan kin sanshi"
Tsabar kiɗimewa har tana mancewa da hanyar da zata sadata da parlo, sai da ta juyo ta dawo kitchen jikinta na rawa tace "Hajiya hanyar parlon fa?"
Mom tayi murmushi kafin tace "Anum ko ɗazu mafa ke kika fita da kanki yau kuma kin mance?, zo muje in nuna miki" koda suka fito da hannu mom tayi mata nuni kana ta koma kitchen, tafiya ta fara yi kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, tsananin tsoro gami da fargaba sun dirar mata ƙahon zuciya, tana tafe tana ambaton innalililahi wa Inna ilahiri raji'un, tsawar da ya daka mata ne yasa tai saurin ƙarasowa, domin kuwa ya riga da ya ganta har yanayin tafiyar da takeyi, kamar zata kifa tsabar sauri, ta ƙaraso gurinsa murya na rawa tace...
"Barka da isowa Alhaji" sai da ya ƙare mata kallo kafin yace "barka" kasancewarsa mai ƙaramin jiki yasa yawan shekarunsa ɓuya, sbda a ƙalla zaiyi shekaru hamsin a duniya, fari ne amma ba can ba, sannan yanada cikar zati da kwarjini gami da isa tare da tsaurarawa,
Har ta miƙe zata juya ya kirata da Cold voice ɗinsa, jikinta na rawa ta dawo ta tsuguna kafin tace "gani" ƙafafunsa suna saman table ya jingina kansa da kujera ya ɗan matso kusa kafin ya ɗaga hannu ya watsa mata Mari, da sauri ta miƙe ita ba kuka ba ita ba jimami ba, tana tsaye kanta a sunkuye yace "a gidanku haka kike yiwa mahaifinki ko dama baki samu ingantacciyar tarbiyya bane?"
Da sauri ta ɗago idanuwanta ta kalleshi, kafin ta juyar da kai gefe, a zuciyarta tana maimaita "da mahaifina yana da rai ko kallo baka isheni ba, duk da shiɗin talaka ne" ta faɗi hakan kusan sau uku, tsinkayo tsawar da ya daka mata da tayi ne yasa tai saurin barin gurin ta dawo kitchen, "sannu da Aiki Hajiya" Anum ta faɗa hawaye na shirin zubowa a idanunta, "yauwa sannu amma Anum banji daɗin abinda kikayiwa Dad ba yanzu ya kirani yake gayamin bakisan waye dad ba ko?"
"Hajiya kiyi haƙuri insha Allah hakan bazata sake faruwa ba"
Jumayma da Arshi suka fito,
📢kasancewar sunan Arshi yazo ɗaya da na ƙanwar Anum zamu dinga kiranta da sunan da Dad yake kiranta dashi, Little Hajo, sunan yayarsa kenan Hajo.
Dariyarsu da yaji ne yasa shi saurin ɗago kansa tare da faɗaɗa fara'arsa cike da nuna kulawa ya ware musu hannayensa alamar su taho, da gudu suka taho har suna rige rige, yana dariya yace "Jumayma kekam bakya girma" Little Hajo ta kamo hannunsa kafin tace "Dad munyi missing ɗinka amma dai bazaka ƙara komawa ba ko?" janyota yayi kana ya ɗorata a saman cinyarsa cike da nuna kulawa yace "idan kikace kar in koma zan zauna my Little" dariya tayi wanda yasa point ɗin dake kumatunta loɓawa kafin tace "Dad an kawo sabuwar ƴar aiki ka ganta?"
Sai a lokacin Jumayma dake gefen Dad ɗin tayi magana, "Dad Please ka ce ta koma gidansu nikam bana sonta"
"Big girl menene dalilin da yasa bakya sonta tayi miki wani abunne" Jumayma ta turo baki tare da gyaɗa kai alamar a'a,
"Idan har naga zata takura muku dole ta koma inda ta fito"
Dad ya faɗa yana mikewa tsaye, "Dad bakasha kunun ba ga ƙosan nan" Jumayma ta faɗa tana kallonsa, "eh kusha kawai"
Ya faɗa yana wucewa ciki,
Dad wani irin mutum ne, wanda idan har yayi faɗa akan abu to bazai cishi ba komi muƙaminsa kuma komai sonsa da abin.
Kai tsaye ɗakinsa ya wuce, mom kuma sun kammala komai dan ƙosan ma Jumayma ta bawa ta kawo ta ajiye masa, iya Anum ce a kitchen ɗin, itama da ta kammala ta dawo ɗakin da yake a mazaunin nata, ta zabga tagumi, tunani takeyi anya zamanta zai ɗore a wannan gidan kuwa?"
Tayi nisa a tunani taji an hankaɗo labule, cikin isa da gadara take cewa "ki tashi ki soyamin bread and egg yanzu yanzu" sam bata ma ɗauki murya ba, dan bata san wace a tsaye a kanta ba, sai da ta ɗago da idanunta ta kalleta kafin tace "dan Allah kiyi haƙuri wlhi na gaji, akwai ragowar wanda aka soyawa Alhaji a kitchen nasan zai isheki"
Little Hajo ta wani galla mata harara tare da nunata da yatsa, bata dai ce mata komai ba, ta fice, da kuka ta ƙarasa bedroom ɗin mom ta samu mom ɗin tana sallahar magriba, cikin shagoɓa ta fice fuuu tare da wucewa bedroom ɗin dad, yana tsaye ya sanya farar jallabiya yana ɓalle botir na gaban rigarsa ta rungumeshi murya kamar zatayi kuka tace "Dad kayi wa ƴar aiki magana inason cin bredi da ƙwai taƙi soyamin nidai Dad shi zanci" da sauri ya fito fuu zai wuce, ganin mom a tsaye ta rungume hannaye tana jifansa da murmushi yasa shi tahowa gurinta, cikin faɗa yake cewa "kiyi gaggawar korar waccar yarinyar, matsawar bazata yi mana biyayya ba ta yiwa ƴayana wlhi bazata zauna min a gida ba" tunda ya fara maganar mom take rungume dashi har ya kammala, ta janyo hannunsa suka dawo ɗakinta, wani haɗaɗen ƙamshi yayiwa hancinsa sallama, "kayi sallah ne?"
"Eh nayi isha'i nake jira" Dad ya faɗa yana kashe mata ido, tasani bai ci abinda Anum ta kawo masa ba, dan haka wanda ta kawo ɗakinta ta bashi da kanta har sai da ya ƙoshi, sam bata yi masa maganar Anum ba, tafison zuwa safiya su tattauna akanta, "Dad idan kayi sallah ka kwanta ka huta kasha hanya" mom ta faɗa cike da nuna kulawa" wane irin Hutu zanyi bayan gaki" yau a gunki zan warware gajiya hajiyata"
Little Hajo dake saman bed ɗin dad tana jiran dawowarsa sannan taji hukuncin da ya yanke akan Anum, har barci ya fara ɗaukarta bai dawo ɗakin nasa ba, tun tana barcin tana buɗe ido har mai ƙarfin yayi gaba da ita,
Tunda Jannat ta gargaɗeta akan yin Sallah da hijab, bata saɓa alƙawarin da tayiwa Jannat ɗin ba, a tsakanin 2days har ta fara sabawa, bayan ta idar da sallahar isha'i ta ɗaga hannunta sama tare da fashewa da kuka ta fara gayawa Ubangiji halin da take ciki tare da rokonsa ya kawo mata mafita, sannan ta shafa adu'ar hawaye na bin kumatunta, tunowa da tozarcin da take fuskanta a gurin mahaifiyarta yasa ta sake ƙarfafawa kanta guwaiwa, tasan a halin yanzu Allah gatanta Jannat gatanta sannan wannan gidan da take aiki shima gatanta, babban abin da yake damunta bai wuce ace mahaifiyarka wace ta ɗauki cikinka ta jure laulayi da naƙuda da raino amma daga baya ta nuna bata ƙaunarka dama hakan tana faruwa?"
Sai da tayi kuka mai isarta kafin ta dafe kanta dake tsananin sara mata, idanunta sunyi jajir ta miƙe tsaye ta cire hijab tare da ninke sallahya ta haye gado bayan ta ajiye su a mazauninsu,
Bataji sallamarta ba shigowarta kawai taji cikin masifa take cewa "tashi ki haɗamin tea" Anum ta ɗago jajayen idanunta da sam bata wani iya buɗesu sosai saboda tsabar ciwo da kanta yakeyi mata har wani duhu take gani, kafin ta riƙe kan nata sanan tace "dan Allah kuyi haƙuri Kinga yanzu ina fama da ciwon kai ne, akwai ruwan zafi a flaks ɗazu Hajiya ta sani na dafa harda su na'ana a ciki" Jumayma dake tsaye ta riƙe ƙugu tace "ke kalleni ubanwa kike gayawa haka? ta sake yin maganar cikin ɗaga murya, "Nace ubanwa kike gayawa haka, dama Hutu kikazo yi? gida babu AC da lallausar katifa ko? to bazan je in haɗa da kaina ba, idan bazakije ki haɗamin ba ki barshi tunda ni kina ganin damata zan isar da saƙon ga Dad"
Anum ta miƙe jiki karkarwa kafin ta dafe kanta ta raɓa ta gefen Jumayma ta wuce, koda ta shiga kitchen ɗin, dole sai da ta sake ɗora wani ruwan shayin sbda flaks ɗin ma baya kitchen, tana cikin dafawa tana tunani, ruwan yana tafasa ta tsumbula hannu, da sauri ta cire tare da matsar ƙwalla tana yarfe hannu, Ta juye a cup kenan Jannat ta shigo tana ce mata, "idan kin gama dafawa ki shanye time ɗin barcina yayi"
Tana faɗar haka ta juya tabar gurin.
Zuciyar Anum na yi mata ƙuna, ta jingina da bango tare da ƙarewa shayin da ta dafa ta juyeshi a cup kallo, ta jima a tsaye tana kallonsa, daga ƙarshe ta rufe da murfin cup ɗin ta barshi a gurin dan ko kuɗi za'a bata bazata iya kaishi bakinta ba, sai da ta tabbatar da ta kashe komai wanda yake aiki da wutar lantarki kafin ta koma ɗakinta ta turo ƙofa dan bata saka key ba, duk da sanyin AC dake ratsa fatar jikinta bai hanata jin zufa na damuna ba, ta yakice ɗankwalin kanta kanta wanda ya kasance babu gashi irin na maza ya bayyana, sannan ta cire riga da skirt a taƙaice dai tayi zigidir, alamun shigowar da taji za'ayi ne yasa ta....!

Afuwan masoya makaranta littafin NISAN KIWO jiya ban samu damar yi muku posting ba kuyi haƙuri.

Me kuke tunani shin waye yazo ɗakin Anum sannan a wane hali zai ganta?
# Anum
# Jumayma
#Dad
#Little Hajo
Waye gwaninku?
Kar a manta ayi following ɗina arewabook momislam11
Ga wanda sukeson number wayata ga tan kuyi saving 08141799224 nima kuyimin magana inyi taku sannan zanyi adding ɗinku a group wanda nake posting.


Page10
Janyo ƙaton hijabin da Jannat ta bata tayi, cikin sauri ta sanya ta tare da zubawa ƙofa ido,
"Anum kinci abinci kuwa naga kamar bakici komai ba"

Mom ta tambayeta yayin da take ƙarasowa cikin ɗakin,
"Eh naci Hajiya"
Anum ta mayar mata da amsar kanta a ƙasa, mom ta ƙarasa shigowa tana cewa "yauwa dama ina son in gargaɗeki game da Dad, gobe insha Allah zai zo ya tambaye ki akan ki koma aiki gidan wansa, gaskiya wanda mugu ne walhi idan kika kuskura kikaje zaki gwammace kiɗa da karatu dan bashi da tausayi, Anum ta ɗago jajayen idanuwanta kafin ta ɗorasu a fuskar mom, a ranta tace "kenan har ya zarce Alhaji a mugunta?" da sauri tace "Hajiya in Allah ya yarda bazan jeba, har mom ta juya zata fice, Anum tace "sai dai Hajiya ina tsoron sake haɗa fuska dashi"
Mom tayi murmushi batace mata komai ba ta fice.
Har gari ya waye kaf ɗinsu babu wanda yasan anyi sallahar Asbha, sabda basu samu damar yin barci da wuri ba, can tsakar gida tun kafin gari yayi haske ta share ko ina tare da kafa kujera ta zauna, da kaganta zaka san babu lafiya, tana sanye da atamfa ɗinkin riga da zani kasancewar ɗankwalin wadatacce ne yasa ta kafa ɗauri, a zaune take amma hankalinta sam baya jikinta, idanuwanta sun wani juye ita kanta bata san halin da take ciki ba,
Ƙarfe 7:am mijin Ummu Auwalu ya fito daga ɗakin Ummu yana hamma, kallo ɗaya tayi masa kana ta kawar da kanta gefe, cikin wata iriyar murya mai sanya wanda ya saurareta shiga ruɗu da tsananin firgici, "Kai Auwalu yalo ina zakaje zo ka fara yin tsallen kwaɗo" mijin Ummu ya zaro ido tare da cewa "ke Arwa kike ko Arshi? in banda fitsara da tacewar rashin kunya ina mijin mahaifiyarki inda kara ai ni mahaifinki ne, amma kike rainani"
Yana gama faɗar maganar ya fara tafiya kenan ya sule ya faɗi a gurin timm, Arshi na zaune sam Bama shi take kallo ba, ya miƙe daƙyar zai fara tafiya ya sake jin murya irin ta ɗazu wacce Arshi ɗin tayi masa, "idan har kana son zaman lafiya dole kayi tsallen kwaɗo saboda ka saɓawa Allah, lokaci ya ƙure a safiyar yau aljanu miliyan biyu ne suka je ƙasar Makka suka dawo kai kana barcin asara, tunda yaji ance Aljanu ai ya fice da uban gudu ko takalmi babu, yana gudun yana cewa "wlhi gamo nayi jama'a ku taimaka min nayi gamo da mutanen ɓoye"
Yayi gudu wanda idan da kuɗi zai bawa mai Adai-daita sai ya biya ɗari da hamsin in few minutes yayi tafiyar da bai san yayita ba, dai-dai shagon abokinsa ya yada zango, tunda ya hangoshi a furgice ya fito a shagon nasa cikin tuhuma yake cewa "Auwalu mai ya faru, kai da ya kamata ace kana gida gurin amaryarka?"
"Wace amarya ina cikin gararin rayuwa, tun daga gida nake ta tafiya da uban gudu na rasa inda zan dosa ne kawai nayo nan"
"Kardai kace min baka da kuɗin mashin?"
"A'a Hayatu inada kuɗi wlhi masifa ce ta koroni"
Hayatu mai shago ya kamo hannun Auwalu suka shiga shagon nasa, ya ƙarewa Auwalu kallo kafin yace "tabbas fuskarka ta nuna alamun kana cikin tashin hankali amma bani labari meye matsalar?"
Auwalu ya numfasa kafin yace "wato yarinyar matar da na aura gidan Aljanu gareta dan har cewa takeyi wai aljanu miliyan ne sukaje inane ma tace" kai koma dai menene wlhi yau idan na koma gida dole ta zaɓi ɗaya, ko zama dani ko tasan inda zatayi da wannan ƴar Tata mai ruwan
End Ads