x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - NISAN KIWO

  • 9001 words
  • 12000 words
  • Out of 25414 words

Category: Love Stories

Views 59

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
a wuya kamar za'a ɗaure wuyan saniya, da sauri Jannat ta janyota tare da cewa "tun yanzu kina neman bamu problems ko?" Anum ta sunkuyar da kanta ƙasa.

"Allah ya kiyaye hanya anty Anum dan Allah ki dinga waiwayomu karki damu da cin mutuncin da Ummu take yi miki"

Sosai takejin idanuwanta duk sun ciko sbda tasan dole zatayi kewar ƙanwar tata, hawaye na shirin zubowa Anum tace "karki damu insha Allah, "kar dai ki sake kiyi kuka ki ɓata makeup dan wlhi zaki sake ja mana aiki" Jannat ta faɗa tana sanya tissue tana gyara mata gefen idanunta, dole ta mayar da kukan suka fito tsakar gida dukkansu, Ummu tana waya dole yasa suka tsaya har ta kammala, ashe ɗaurin auren nata gobe ne, kaf cikinsu basu da labari, Jannat tai ƙarfin halin cewa "Ummu mun fito" washe da baki Ummun ta yaye labule tana daga zaune da wasu kwalaben magunguna a gabanta tace "Allah ya tsare da fatan zaki haramtawa kanki zuwa gidana" ta gayawa Anum kafin ta sauke labulen suka wuce, suna tafe har da Arshi idanunta sunyi jajir sbda kewar yayar Tata, wayar Jannat tayi ringing, da sauri ta ɗaga cikin shagoɓa naji tace "Anty muna hanya ne, kinsan yarinyar yanada mata lafiya, so sai da ta gama sallamarta tukunna" Jannat ɗin ta kai ƙarshen zancen da cewa "insha Allah mun kusa"

Tunda suka fita can waje gaban Anum yake ta faɗuwa, ga yamma tayi dan ƙarfe 5:pm zatayi,

Kai tsaye suka fito zuwa gurin drivernsu Jannat, Arshi na kuka Anum ta shiga mota backside ita da Jannat suna ɗaga mata hannu, har motarsu ta wuce bata koma gida ba sai da taga an fara iska alamar gari ya haɗa hadari, jiki a sanyaye ta kaucewa jinginar da tayi a bango kafin ta ƙarasa cikin gidan, zuciyarta a cunkushe ta wuce ɗakinsu tare da kwanciya a didigaggiyar katifar da a yanzu ta kasance nata, sosai take kuka bakinta har wani karkarwa yake, can ta tsinkayo Muryar Ummu a ɗakinta tana yiwa bazawarin da zata aura kirari, jin Ummun tace "Tom idan ka ƙaraso sai ka kirani a waya in fito" Anum ta sauke sassanyar ajiyar zuciya, a fili tace " yanzu wasan ya fara billahi".

Tana kwance ƙamshin wani haɗaɗen turare ya doki hancinta, a hankali ta tashi zaune gami da ware idanunta, "Arshi na fito ki kula da gida, sannan ki tace min kamu yanzu zamu ci gaba da sana'a, ga ɗari biyar kiyi abincin rana da na dare"

Arshi ta taso tazo bakin ƙofa inda Ummun take tsaye tana sanye da riga da zani na leshi light blue, Ummun tayi kyau sosai, " Ummu mai zan siya na ɗari biyar rana da dare?"

"Ubanki ne ke ciyar dake ko ni? Tunda garin Allah ya waye ko ruwa ban kai bakina ba"

Arshi tace "muma ai babu abinda mukaci"

"Kinga ko me kikaga dama ki dafa nikam natafi siyayya" Ummu ta faɗa tana cigaba da tafiya.

Bayan fitar Ummun da jimawa Arshi ta shiga ɗakin Ummu, wanda rabonta da shiga tunda ta fara nuna musu bambanci tsakaninta da yayarta, tana daga tsaye jingine da bango ta hango wani ɗan akwati mai kyau, ta sakko dashi ƙasa kana ta mimmiƙe ƙafafu, kafin ta zuge zip ɗin idanunta suka fara cin karo da wasu kwalaben magunguna, a jikin wasu harda hoton nono da mace babu wando, kasancewar tayi karatu kuma ta iya Hausar boko da turanci, yasa ta fara karanta amfanin maganin tunda yana a rubuce jikin kwalbar, tunda taga an rubuta yana matse gaban mace, tai saurin mikewa taje ɗakinsu ta ɗauko man da take shafawa a bayanta, ta dawo ɗakin Ummu ta lakaci man ta kwaɓa da maganin matsin, cikin sauri ta cigaba da firfito da ragowar tana lakatawa tana zubawa daga ƙarshe ta gyara ta inda baza'a gane ba, sannan ta rufe akwatin ta mayar tana dariyar, kwalbar hannunta ta kalla sai kuma ta sake tuntsurewa da dariya a fili yana cewa "Aboniki haɗe da Loko" sai kuma ta tafa hannayenta ta koma ɗakinsu, ta ɗauko hijab sannan ta fito waje, shafi ta wuce ta siyi yoghurt da cincin irin ɗan kanti, kana ta koma gida ta gyara zama ta buɗe murfin gorar, tana sha tana lumshe idanu.

Suna tafe a mota yana jifanta da wani irin kallo mai cike da so da ƙauna, bazamu kirashi da yaro ba, dan a ƙalla zaiyi shekaru 45yrs a duniya, Ummu kuma zatayi shekaru 40yrs

"Babban farincikina bai wuce inji an ɗaura aurenmu ba" Ummu tayi murmushi gami da cewa "me kakaci na baka na zuba, aure inhar munada rai da lafiya ai kamar yau ne" tayi maganar tana jifansa da murmushi, "kinsan me?"

"A'a" Ummu ta bashi amsa.

"Akwai wani gida da mai gidana ya bani kafin in kammala nawa, acan zamu zauna, ya kamata in kaiki ki ganshi,"

"Ummu ta rausayar da kai, "na gaji mu bari har gobe in Allah ya kaimu yanzu dai muje kasuwar kawai"

"Na mance ban sanar dake ba, ai ɗazu mama ta kirani wai an gama siyayya shine nace to bari ko can gidan muje sai a duba abinda ya dace a siya"

Itakam har ga Allah ba haka taso ba, karta fara complain ne kawai yasa yace "masa kanta na ciwo ya dawo da ita gida, shima ya ɗan fahimci wani abu sai ya basar"...!
Page6
Washe gari tun safe ƙawayen Ummu suka cika gida, anata hada hadar ɗora tukunyar abinci, abinka da Ummu ƴar gaye ansha kitso da lalle tayi rass abinta, babu wanda zai san da akwai Arshi a cikin gidan idai ba ɗakinsu ka leƙa ba, anyi hidimar biki an kammala ko ƙofar ɗaki bata fito ba, Allah ma yasa bata sallah kawai tai kwanciyarta,da la asar aka wuce da Ummu gidanta Masha Allah gidan babu makusa domin na mutum ɗaya ne sai ɗakuna uku harda kicin huɗu, da yake bata samu matsala dashi gurin sanar masa da zata tare da Arshi ba, ya riga ya amince, da akazo tafiya Arshi kam cewa tayi sam babu inda zataje, daƙyar da siɗin goshi ta yarda ta bisu, suna isowa gidan bayan sun sauka an fara firfitowa ta leƙa ɗakunan, babu laifi tsaf tsaf suke, ta nemi ɗakin dake can gefe kusa dana Ummu ta zauna a ciki, dan har da ƴar madai-daiciyar katifa da pillow, kowa sai sam barka yake har maƙota duk sunyi kara an rako Ummu, zuwa magriba duk aka watse ya rage daga Ummu sai Arshi a gidan, ɗakin na Ummu ciki da parlo ne, duk da ba wasu tarkace ne a ciki ba yayi kyau, parlon kuwa kujeru uku ne a ciki, irin na hannu sai Tv irin wanda ake ajiye shi asaman tebur, tsakar ɗakin malale yake da ledar tsakar daki, acan waje, cikin kitchen jerin tukwane ne da kuloli sai randar ruwa, sai da akayi sallahar isha'i sannan Ummu ta fito tana sanye da atamfa ɗinkin doguwar riga yayi mata kyau, tai sallama a ɗakin Arshi, murya a sanyaye arshi ɗin ta amsa da "wa'alaikumussalam" kafin ta miƙe daga zaman da take ta kwanta, Ummu ta ajiye abincin saman kujera ƙarama kafin tace "ki tashi kici abinci banga amfanin zama da yunwa ba" Arshi ta yamutsa fuska gami da cewa "zanci" Ummun ta fice, tana komawa ɗaki ta sake gyara kanta tare da feshe ko ina da turaruka, wayarta dake ajiye saman kujera tayi ringing, da sauri ta ɗaga tare da karawa a kunnenta cikin ƙissa take cewa "aminci Allah ya tabbata ga Alhajin Allah" daga can ɓangaren yace "tare dake Hajiya, ina fatan an shirya komai aiki kawai zan fara" Ummu ta kwashe da dariya kana tace "wasu ma sai kazo a sake shirya su" yana dariya yace gani a ƙofar gida, ai ko abokai na hana su rakoni" ya katse kiran.
Fuskarsa ɗauke da fara'a yai sallama gami da ƙarasowa ciki, Ummu na daga ɗaki tana cewa "Alhajin Allah sannu da ƙarasowa" tare da zuwa tai hugging ɗinsa" kiss ya yi mata a goshi tare da rungumeta suka zauna, bayan yayi mata ya gajiyar biki ya ajiye ledar a saman tebur na katako mai ɗan faɗi, ta mike ta fito zuwa kitchen ta ɗauko plate da cokali tare da cup ta kawo, already an riga da an yayyanka naman juyewa kawai tayi, suka fara ci, bayan sun kammala sai ragowa ta rufe kana suka sha drinks ɗin sannan ta kawar da kayan, ta nufi toilet tunda yana a cikin ɗakin, bayan ta fito shima ya shiga, ta wuce taje tasa sleeping dress mai shara-shara, Alhajinku yahau haɗiyar miyau, ya kasa haƙuri har sai da yaje gareta "ina maganin da na baki ajiya?" Ummu na murmishi ta nuna masa wani ɗan ƙaramin akwati, kasancewar dukkansu suna uwar ɗaki ne, bayan ta buɗe ta miƙa masa ya lakata ya shafa a gabansa, itama ta shafa nata, cikin sauri naga ya riƙe gurin, hankali a tashe yace "anya habiba masu siyar da maganinan ba bugar hancinmu sukayi ba kuwa?" Itama ta wani yamutsa fuska cikin nuna dauriya tace "me kaji?" Zai yi magana ya kasa ya kurma ihu saboda Aboniki da Loko sun fara aiki, sai rawa yakeyi da sauri ya cire wando tare da ɗaukar mafifici yahau fifita, Arshi na jiyo hayaniyarsu sai dariya take, a hankali ta mike tare da fitowa waje ƙafarta babu ko takalmi kai tsaye ta wuce kitchen, tana shiga ta buɗe murfin butocin dukka sannan ta ɗauko dakaken barkonu wanda yake a cikin roba mai murfi ta zuba a duka butocin kana ta rufe sannan ta jijiga ta koma ɗaki a hankali, komawarta keda wuya taji Ummu na ihu tana cewa "Auwalu nikam wlhi zafin da nakeji ya ninka naka" ta wani sake kurma ihu, shi ma yi yake har da wani gwalo ido wani mahaukacin zafi da ya ratsa Ummu ta ƙamƙame shi tana cewa "wayo Allah asibiti kusa, nikam kayi ko zafin zai ragu" Malam Auwalu ya haɗa zufa cikin mawuyacin hali yace "inyi me? kina ganin gabaki ɗaya na ƙurje gurin tsabar susa da azaba"
A tare suka fito, Ummu ta ɗauki babbar buta da sabulu shima ya ɗauki butar, murya ƙasa-ƙasa yake cewa "idan kin saɓa sabulun nima ki bani" suka wuce banɗakin dake waje,
Kamar haɗin baki, koda yake dama da tsautsayi, a tare sukayi tsarkin sannan a tare suka sake butar a ƙasa, tare da kurma wata mahaukaciyar ƙara, jikin Auwalu har yana ɓari, Ummu da zafin barkono ya gama gigitata cewa tayi "da safe ya kawo mai ruqiyya ƙila Aljanu sun tayata haɗa kaya ne lokacin da zata taho, yana kuka tana kuka, dukkansu sunyi shaɓe-shaɓe da majina sai kuka sukeyi tsabar ruwan azaba,
Arshi kam har tayi barci cikin kwanciyar hankali tare da mafarkin Anum ɗinta, wai ta kawo musu ziyara sunata yawo.
Ihun da ke ratsa kunnuwanta ne yasa ta farka tare da miƙewa zaune, a fili ta furta "Ummu da Ango mai ke faruwa?" Sai kuma ta koma ta kwanta taci gaba da barci, Gabaki ɗaya robar Vaseline na baby care sun kusa shafeshi a pipinsu, amma yaji da zafi ga iska dake shiga bai daina ba, a ranar dai sun jima suna bidiri dan Ummu zama ya gagareta, daga ƙarshe nashi yai sauƙi nata kam yana nan yanayi taci kuka idanu sunyi jajir, har yayi barcin wahala ko wando babu a wangale itako idanu sun kumbura, sai wajen ƙarfe 3:am na dare kafin barci ya ɗauketa.
"Anum ki nutsu dan Allah kinga babbar damuwata itace rashin iya dressing da baki iya ba, sannan sometimes kinayin abu kamar namiji Please idan aka samu matsala zan iya fuskantar hukunci dan har gidanmu zata zo"
Jannat ta faɗa tana kallon Anum.
Jikin Anum ɗin a sanyaye tace "insha Allah zan yi ƙoƙarin kiyayewa anty Jannat karki damu"
Jannat ta saka mata shaving cream a bag ɗin da ta bawa Anum ɗin, isowarsu anguwar ne yasa Anum raina kanta, dan ko a mafarki bata taɓa ganin haɗaɗun gine gine irin waɗannan ba, sabda babu inda take zuwa, yawanci rayuwarta a cikin gidansu ta yi ta, duk wasu kayan alatu na more rayuwa bata sansu ba, a bakin wani tafkeken get drivern ya tsaya tare da yin horn, zuciyar Anum taci gaba da lugude sbda Gabaki ɗaya ta rasa nutsuwarta, sai da Jannat ɗin ta fito mai gadi ya ganta kafin ya shiga ya nema musu izinin shiga, sannan ya barsu suka ƙarasa ciki, suna tafe Anum na ganin ɗawisu sunata yawo, ga wani dogon titi da suke ta lulaƙawa, a zuciyarta tace "gidanma gari guda ne" abinda ya bata mamaki ba wai gida take gani a tafiyar tasu ba, kyawawan shuke shuke ne irin na turawa, daga ƙarshe dai drivern yayi kwana zuwa wani farin get shikam a buɗe yake kuma da securities a gurin, sosai cikinta ya sake ɗurar ruwa dan a tunaninta lalubesu za'ayi, Jannat ta ɗaga musu hannu tana dariya, suma dariyar sukayi mata kana suka ɗaga musu hannu suka wuce, sosai Anum take ware idanu sakamakon ganin wani get da suka sake shiga wanda shine na ƙarshe daga shi sai cikin gidan, babu kowa anan hakan ya basu damar ƙarasawa drivern yayi parking a inda aka tanada dan ajiye motoci, motoci biyar ne a parke dukkansu sabbi sannan kuma masu tsadar gaske, Jannat ta kalli Anum kafin tace "mun iso ki kula Please nikam Allah yasa mugunnan baya nan" Jannat ta faɗa tana kamo hannun Anum suka shige ciki.
Kafin su kai ga shiga asalin parlon sai da sukaci karo da wata haɗaɗiyar ƙofa ta Glass, Anum kam tsayawa kallo tayi dan Gabaki ɗaya kanta ya kanta ya kulle, suna kutsa kai ciki ana kiran sallahar magriba a masallacin dake gidan, gaban Jannat ya bata rass sbda tasan ba lallai antyn ta barta ta fito daga gidan ba, da shigarsu wani irin ni'imtaccen ƙamshi ya bugi hancinsu, a hankali suka ƙarasa ciki Anum kam tana ta bawa idanunta abinci, a zuciyarta ko cewa take "gaskiya ginin gidannan yayi kyau, wani gurin ma har ka mutu bazaka shigesa ba, ga parlo kamar baza'a mutu ba, anya kuwa ba ƙamshin Aljannah na fara jiyowa ba" zaunar da ita da Jannat tayi ne yasa numfashinta yin sama "ya ilahi wannan kujera sai kace tsafaffiya, ina zama tana bada wani lumm tare da ƙamshi mai daɗi, Anum ta sake ƙarewa parlon kallo kafin ta daidaita nutsuwarta, sbda taga wata yarinya ta fito daga wani ɗaki, "Oyoyo Jannat wannan kuma waye mai fuskar maza?" Jannat ta harari Budurwar kafin tace "bana son iskanci ya za'ayi ki kalli mace kice namiji"
"Hamm barin kira mom da Dad su ganta" budurwar ta faɗa tana juyawa, ba Anum kaɗai ba, har Jannat cikinta ƙugi yakeyi saboda ta fara tuno makomarta a gurin Dad ɗin su, baya ƙaunar yaga mai kama da namiji a gidansa inhar ba ɗan uwansa bane,
Jumayma kenan itace babba kuma budurwa ce, zatakai 18yrs, tana shigewa Arshi ƙanwarta ta fito, harara ce ta haɗasu da Jannat dan ko gaisuwa babu, duk da ƙaracin shekarunta sam batada kunya ko kaɗan, "momy tace tana zuwa" Arshi ta faɗa tana juyawa, Anum ta kalli Jannat kafin tace "anya zan iya kuwa?"
Jannat ta harareta kafin tace "zaki iya mana, duk wahala da ɗaukar rainin nan da nake fuskanta duk saboda ke ne amma kicemin bazaki iya ba wlhi da kin taƙaitani" Anum ta haɗiyi wani irin miyau kafin ta sunkuyar da kai tana wasa da ƴan yatsunta,
"Aslamu alaikum" mom tayi sallama, tana sanye da dakakken leshi mai tsadar gaske anyi mata ɗinkin doguwar riga, harda aljihu a gefe da gefe, fara ce tasss kamar inda momyn Jannat take fara, sannan sunada fashin goshi hakan ya sake ƙawata fuskar tata, bakinta baƙi ne amma ba sosai ba, sai ƙamshi ke fita a jikinta, washe da baki ta ƙaraso tana cewa "my Janna yau kece a gidan namu?" Jannat tayi murmushi har yanzu gabanta na faɗuwa sbda idan burinta bai cika na nemawa Anum aiki ba, sam bazataji daɗi ba, ga ƙalu balen da ta dinga fuskanta daga gurin iyayenta har yanzu ma bata tunanin ta tsira tunda basu gama da nan ɗinba,
"Mom wlhi na kawo ƴar uwar Dadyna ne ki taimaka mata, basu da cin yau bare na gobe sannan tanada ƙanwa mai ciwon larura, shine nace barin kawota ta dinga yi muku aiki kuna biyanta"
Jannat ta faɗa muryarta na karkarwa, Anum kam gabaki ɗaya ta haɗa gumi saura ƙiris ya rage ta saki fitsari saboda wani irin kallo da mom ɗin keyi mata, shigowar Jumayma ne ya katse musu shirun, wani irin kallo take bin Anum dashi cikin suɓutar baki tace...!
Page 7

"Mom wannan bata yi miki kama da namiji?"

Sanin ciwon mayar da jinsin mace i zuwa namiji ne yasa Mom cewa "Jumayma kinada hankali kuwa? mace ce gata nan kina ganinta amma kike kiranta da sunan namiji?"
Jumayma ta turo baki tare da mikewa tabar gurin, mom ta sake ƙarewa Anum kallo a karo na biyu, kafin ta juyar da kallonta ga Jannat, "Momynki tasan da zuwanki?"
Bakin Jannat na rawa tace "ba..bata..sani ba mom Please karki gaya mata, tsorona ma bai wuce dare da yayi ba" mom tace "shikenan barin kirata"

Sosai Jannat ta damu da kiran da taga mom ɗin na yi zuciyarta ma bata gama tsinkewa ba sai da taji mom tace "eh gurina tazo,aiki ne yayimin yawa shine nace tazo ta tayani ashe ma bata sanar miki ba?"

Daga can ɓangaren momy tace "dama Dadynta ne yake faɗa shiyasa duk nabi na damu, amma tunda tana gurinki babu damuwa"

Kasancewar wayar a handsfree mom ɗin tasa, Jannat har tana sauke gauron numfashi, Anum ma taji daɗi sosai da hakan ta kasance, abinda bai yiwa Jannat daɗi ba, ɓatawa drivern time da tayi, amma ta fita ta bashi haƙuri akan ya kwana gobe insha Allah sai ya mayar da ita gida da wuri, bai nuna mata damuwarsa ba, yace "Allah ya kaimu"

Sai da sukayi sallahar magriba da isha'i sannan aka zauna zaman cin abinci, Jumayma da Arshi ƙanwarta ƙin fitowa sukayi, a cewarsu Anum tana basu ƙyama, babu inda mom ɗin ta iya dasu dan bata isa ta dakesu ko tayi musu tsawa ba, sai fitina ta tashi ta ɓangaren Dadynsu,
Bayan sun gama ci Jannat ta karɓi na driver ta
End Ads