x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - NISAN KIWO

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 25414 words

Category: Love Stories

Views 56

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
Ummu, wlhi Dadyn Jannat ko san ganinsa banayi, sbda idan ka gansa kamarsa ma wlhi abin ƙyama ce, amma jannat take taraiyya dashi nikam ka shiga tsakaninta dashi kafin yaje yayi mata ciki"
Momy na rufe baki Dady ya waro ido gami da cewa "mata maza" ya ciro belt dake a jikin wandon jeans ɗinsa kana yace "kaf cikin danginmu babu wace ta taɓa ɗauko mana abin kunya ina tunanin kekam sai nayi miki tabon da idan kika ganshi zaki tuna da faɗan da nakeyi miki"
Jannat ta miƙe tana ja da baya Dady ya ɗaya bulala zai kai mata ta ruga ɗakinta da gudu, takowa yakeyi zuwa hanyar ɗakinta yana hoci tare da masifa, Anum na ganin haka ta shige ciki babbar drowar dake can gefe tunda tanada zurfin da zata ɗauketa, saƙata tasa ta ciki, Jannat ɗin na kuka tana murɗa key a drowar tana jin shigowar Dady ta tura key ɗin ƙarƙashin gado, "kina tunanin kin tsira ne ko? da nayi tunanin ƙyaleki tunda akace abota kikeyi da mata maza wlhi yau sai kin banbance min, ya zabga mata bulala, Jannat ta saki kuka tana cewa "Dady dan Allah kayi haƙuri bazan sake ba" zama yayi a bakin gado tare da kallon drowa da wani abu ke gangarowa kamar ruwa, da sauri ya miƙe gami da zuwa gurin drowar yana cewa "wannan kamar ruwa kamar fitsari dan na jishi da zarni" cikin Jannat ya kaɗa sosai, har wani ƙugi yakeyi tanada yaƙinin tana zuwa toilet gudawa zatayi, da sauri ta shiga toilet sbda hankalin Dadyn ya koma gurin drowar, tana tsuga gudawa tana matsar ƙwallah, sosai cikinta ya rikice dan har wani murɗawa yakeyi, "shin idan Dady ya buɗe drowar nan ya hango Anum a ciki itakam ƙaddarawa zatayi ta mutu saboda zai iya kasheta, ta daɗe a toilet ɗin bata fito ba har wani gumi take yakicewa, daga ƙarshe tayi tsarki tare da kora ruwa ta fito jikinta babu inda baya ɓari, ji tayi Dady yana cigaba da cewa "wato yarinyar nan ajiyar ruwa tayi ko meye a cikin drowar nan oho, nidai zarni nakeji, cikin kakkausar murya Dadyn ya kalli Jannat da cikinta ya ɗuri ruwa yace "tashi ki kawomin key inga meye a ciki"
Yanzu kam tafi kowane lokaci rikicewa dan bakinta har ɓari ya kamayi, murya na rawa tace "Dady ban...ba..ba...bansaaa..inda..." Dady ya daka mata tsawa, "ace abin yana ɗakinki kicemin wani bakisan inda yake ba, ko ba anan kike ajiyar kayanki ba?"
"Eh bana ajiy anan"

Jannat ta faɗa jiki na rawa, Dady zai ƙara magana sukaji tusa ɓurrrrrrr, mai masifar wari kuma ta cikin drowar, da sauri dukkansu suka toshe hanci, momy ta shigo tana cewa "Dady kazo kayi wanka dare yayi sosai" da gudu ta fice sakamakon wani uban wari daya bugi hancinta, Dady na riƙe da belt a hannunsa yace "akwai mutum a ɗakinan"
Cikin sauri Jannat tace "Dady babu kowa bansan dai ko magen da na kawo daga gidansu Arshi ce ba"
"Dan ubanki zoki fice da ita, bazaki kawo mana cuta gida ba"
Dady ya fice zuwa neman buhun shinkafa a kitchen, Jannat tai saurin buɗewa Anum ƙofa ta shige toilet sannan ta kulle drowar, bayan Dadyn ya samu buhu sai da ya biya ta ɗakin momy ya karɓo key sbda drowar tasu iri ɗaya ce, kana ya dawo ɗakin Jannat ya fara ƙoƙarin buɗe drowar itako har yanzu gabanta bai dena lugude ba, yana buɗe drowar yaga wata leda ɓaka a ƙulle sai wari takeyi, daga can sama kuma kayan Jannat ɗinne, shikuma a nan tsakiya yana baƙar ledar, cikin tsagina gini ya kunce laidar abinda ya gani ne ya sanyashi ja da baya gabansa na tsananta faɗuwa, cikin ɗaga murya yace "kashi a leda Jannat dan ubanki waye a ɗakinan?" jannat tai wuri wuri da idanu, da Muryar kuka tace "Dady nikam bansan komai ba tare dakai muka shigo, Dady yace "fitsarin da ya gangaro shikuma fa?" Jannat ta dafe kanta, ta cikin toilet sukaji ana cewa "idan har bazaku bamu jini ba tabbas zamu iya yin komai.."
Dady ya fice da gudu, sai gashi ya dawo hannunsa riƙe dana momy yace "zoki jiyewa kunnuwanki abinda nakeji daga toilet ɗinnan"
Muryar da suka sake ji ta banbanta da ta ɗazu, aka sake cewa "duk inda kuka shiga sai mun bibiyeku muna gaiyyatarku zuwa ɗaurin auren Aljani ɗan duƙususu sannan kuje ku shirya domin a nan gidan za'ayi taron"
Momy ta kalli Dady Dady ya kalli Jannat, itama ta kalleshi tare da waro ido, kan kace me momy ta ruga da gudu hakama Dady sukabar jannat ɗin a bedroom ɗin, ashe suna laɓe a bakin ƙofa, itama Anum ɗin taji maganar su, tunda window na toilet ɗin yana jikin inda suke tsaye, cikin ɗaga murya akace "hahahaha bazakuje ku shirya ba, gashi Aljani ɗan ƙarami harya shirya?" Momy da Dady suka ruga da uban gudu, kai tsaye ɗakin farko na momy suka shiga, sukayi tsuru-tsuru, ko wanne da abinda yake saƙawa a ransa, Muryar Anum ta katsesu, dan sun haɗa baki da Jannat tace "ta rama mata dukan da Dady yayi mata ta hanyar firgitasu" aiko Jannat taje window ɗin momy ta sake sauya murya tace "hahahaha ku kaɗai muke jira saboda Aljanu sun taru a can inda kuke cin abinci bil adama ne kawai babu, ado zakuyi irin na bikin bil adama saboda muma munsha kwalliya" cikin sauri Dady da momy sukayi zigidir, tare da shawarar wane kaya zasu sanya, "Lokaci fa yana wucewa karku fusata shugabanmu Aljani mai feshin wuta" su momy na jin haka jikinsu na cigaba da rawa kowanne ya ɗauko sabon kaya wanda suke burin sakawa a bikin ƙanwar Dady da za'ayi, sosai sukayi kyau, kasancewar momy fara ce kyakkyawa shima Dadyn yayi kyau sosai momy ta sanya shadda less ɗinkin doguwar riga shikuma Dady dakakkiyar shadda mai yauƙi kalar sararin samaniya sai ɗaukar ido takeyi yasa hula momy tasa mayafi marar nauyi, acan parlo sukaji sautin kiɗa na tashi, inda aketa waƙe-waƙe, Jannat tasanya muryoyi biyu domin su sake rikita su momy jannat ta koma ɗaki ita kuma Anum tana can bayan window na parlo, a hankali suka tako suka iso parlon Anum dake durƙushe ta leƙa ta hangosu, sai da tayi dariya mai isarta kafin tace "rawa zakuyi sannan kuyi a hankali karku bige ɗan autanmu" Dady ya maimaita "rawa kuma? nida ko rawa banayi za'acamin wani inyi rawa, gaskiya bazan iya ba, badan dare ba wlhi da barin gidannan zamuyi ya kalli momy yace "Aljanu ne suka saukar mana a gida ya kamata mu bar gidannan"
"Zakuyi abinda muka ce ne ko sai mun fito muku a siffar mu?"
Dady yana turo baki yace "zamuyi, momy ma tayi harara tana kumbure-kumbure kai kace yarinya tace "yifa mukeyi"
Dady ya fara rawa shida momy sai wani sunkuyar da kai yakeyi, acan jikin window ɗin aka sake cewa "girki a cikin minti goma shinkafa da miya shawara ta rage gareku sai ku shiga kicin"
Momy tace "damu suke" Dady yace "ke muda aka samu yin rawa taya za'a sakamu yin girki?" Wani rudududu sukaji ai da gudu suka wuce kitchen Dady ya kalli momy kana ya haye kujerar tare da rafka tagumi, momy tace "minti goma fa aka bamu"...!

Drop your comments domin samun cigaba.
Tabbas akwai cakwakiya a ciki muje zuwa..
Page3

Shiru ne ya ratsa gidan, hakan ya bawa Dady damar yin magana, "momyn Jannat inaga fa mutanen nan sun tafi tashi mu koma ɗakina dan wlhi bazani ɗakinki ba"
Jikin momy na rawa tace "Dadyn Jannat karfa mu tafi su kuma dawowa" hannunta ya kamo kana yace "Allah ya fisu nikam nayi nan, tunda baki kunna gas ba zomu wuce, ina zamukai uban abincin da sukace a girka?" suna tafe suna waige har suka wuce hanyar ɗakin jannat, momy tace "Dadyn Jannat Please barin je in duba ko tana lafiya" hararta yayi sbda abin ta cikin ɗakin Jannat ɗin ya fara, kafin yace "babu inda zaki ga dukkan alamu garin yawace-yawacenta ne ta kwaso Aljanu gobe insha Allah zan nemi malamin da zai zo yayi mata ruqiya da sassafe zan fice" Dady ya faɗa yana buɗe door na ɗakinsa.

Koda suka shiga ɗakin har yanzu shida momy a tsorace suke daga abu yayi ɓurum sai su miƙe a zabure, tsabar tsoro ko kayan basu cire ba haka suka kwanta,
Acan ɗakin Jannat Anum ta fito daga toilet tana dafe ciki, Jannat dake kwance wari ya addabeta sannan ta kasa tashi ta kawar da ledar cikin faɗa tace "haba Anum bayan fitsari kuma harda kashi kinsan kin cutar dani sosai kuwa?" ƙarasowa gaban drowar Anum tayi kafin ta kalli Jannat ɗin sannan tace "dan Allah kiyi haƙuri na tsorata ne sosai, yanzu zan fita dashi" Anum ɗin tayi magana kamar zatayi kuka, Jannat na kwance ta fitar da kashin zuwa toilet ta juye kana ta kora ruwa ya tafi, ledar kuma ta buɗe ƙofar waje ta wurga ta katanga kana ta dawo ciki tasa omo ta goge sannan ta ɗauki room freshener ta fesa kana tazo zata kwanta,
"Kinyi sallah?"
Jannat ta tambayeta, a'a banyi ba naga kema bakiyi ba" banayi ne" Jannat ta bata amsa a taƙaice, toilet taje tayo alwalah kana ta fara haramar yin Sallah dan har ta shimfiɗa sallahya komai nata irin na maza sometimes kuma takanyi abu irin na mata, "mai yasa bazakisa hijab ba?" Anum ta juyo da kallonta ga Jannat tana yamutsa fuska tace "yana shaƙemin wuya"
"Kince kinason ki zamo mace akan me zaki dinga abubuwan maza, ki ɗauki hijab ɗina kisa"
Badan taso ba ta ɗauki hijab tasa a kaikaice sannan ta tada sallahar, magriba da isha'i tayi, bayan ta idar ta ɗaga hannunta sama tana roƙon Allah ta jima a gurin daga ƙarshe ta miƙe ta ninke sallahya da hijab ɗin ta haye gado, can gefe ta kwanta tare da takure jikinta, itakam Jannat ta riga da tayi barci, sam Anum ta kasa barci babbar damuwarta Arshi da kuma idan gari ya waye wane babin zata kama, sannan a wane irin hali Arshi ɗin take?" sosai zuciyarta ta tsinke ta ƙaddarawa zuciyarta bazata sake samun farinciki ba, ta juya ta kalli Jannat da sai barcinta takeyi, a zuciyarta tace "Allah sarki zaman mutunci ne ya haɗani da ita tun ina makarantar primary kafin in shiga secondary na fara fuskantar tsangwama da tsana" wasu zafafan hawaye suka samu nasarar zubowa a idanunta, ta sanya hannu ta share, tana cikin tunin barci yayi gaba da ita,

Ƙarfe 4:am Jannat ta farka, kana ta miƙe zaune tare da jingina kanta da jikin gado, tunanin mafita da zasu fuskanta ne ya faɗo mata, tabbas tasan ba ƙaramin ganganci tayi ba, na shigo da Anum cikin gidannan hankali a tashe take ta saƙa da warwara sbda ta fara tunanin idan har ta samawa Anum Aiki a gidan ƴar uwar momy wataran idan momy taje ko sistern nata tazo zata labarta mata cewar itace ta kawo mata mai aiki, can kuma Jannat ta tura yatsanta ɗaya a baki sbda tanada burin ingantawa Anum rayuwa duk da itama a karkashin iyayenta take, mahaifinta yanada arziƙi amma bawai yana sakar mata bane, 5k ta tambaya sai tayi masa dogon bayani, hakan yasa wasu lokutan take zama sisi bata magani, juyin da Anum tayi ne yasa Jannat tashin ta cikin sanyin murya tace "Anum yanzu fa ba lokacin barci bane ki tashi mu fara shawarar inda zamu ɓullowa lamarin zuwanki gidan aiki idan kuma gidanku zaki koma Tom, saboda wlhi ina cikin wani hali ko da wanne lokaci su momy suna iya shigowa, tunda Kinga jiya hankalinsu ya tashi"
"Anty Jannat nafi son zuwa gidan Aikin saboda in cika burina na komawa mace sannan inci gaba da karatu kamar kowa"
Anum ta faɗa tana kallon Jannat ɗin.
"Shikenan ana kiran sallahar Asbha ki shirya zan baki Naira ɗari wlhi bani da kuɗi, ki hau Adai-daita zuwa anguwarku nikuma anjima zan zo gidanku sai muyi magana"
Anum tayiwa Jannat ɗin godiya, Anum ɗin ta sakko daga kan bed tare da shiga toilet, alwalah kawai tayi ta fito sannan ta ɗauki hijabi ta kabbara sallah, lokacin da ta zauna zaman yin adu'oi aka fara kiraye-kirayen sallaha,
Har tayi sallah ta idar idon Jannat a kanta, tasan yanzu Dady bai dawo daga masallaci ba, ta miƙawa Anum Naira ɗari tace "muje in rakaki amma ki tabbatar kin saka hijabi ki tafi dashi na baki kyauta" godiya ta sake yiwa Jannat ɗin kafin suka fito harabar gidan, sai a lokacin ma Lado mai gadi yake yin Sallah, ta buɗewa Anum ta fice sannan ta rufe ƙofar kana ta tsaya tana jiran ya idar da sallah, tana tsaye yayi sallama sannan yayi adu'oinsa ya shafa, yana shirin naɗe dardumarsa tace "Lado idan har naji labarin ka gayawa wani fitar ƙawata da na raka yanzu wlhi zaka fuskanci mummun hukunci tunda kai ka iya munafurci"
Ta faɗa tana nuna shi da yatsanta, jikinsa na rawa tabbas yasan barazanar kora takeyi masa, yace "insha Allah babu wanda zai ji" ta wuce ba tare da ta ƙara bi ta kansa ba.
Cikin sanɗa ta wuce ɗakinta tare da kullo ƙofa ta haye gado sannan taja blanket ta rufa har kanta,
A hankali momy ta turo ƙofa tare da yin sallama, momyn ta tsaya daga bakin ƙofa sabda a zahiri tsoron Jannat ɗin takeji, "Jannat kinyi sallah kuwa?"
"Eh nayi"
Jannat ɗin ta faɗa tana daga cikin blanket.
Duk da tsoron Jannat ɗin da takeji bai hanata cewa "tashi mu shiga kitchen yau da asbha tafiya ta kama dadynki da wuri zai fita yana dawowa daga masallaci" Jannat ta zuro ƙafafunta ƙasa kafin ta miƙe tana turo baki, momy ta jinjina kai kana tace "wato wuyanki ya isa yanka ko? daga ki tayani aiki sau turo baki, na ma mance ina kwana?"
Jannat ta sunkuyar da kanta ƙasa kafin tace "good morning momy"
Kallon banza ta watsa mata kafin tace "wuce muje"
Kai tsaye suka wuce kitchen suka fara hada hadar haɗa abin karyawa, momy take bata labarin abinda ya faru jiya, a maimakon Jannat ɗin ta jajanta musu sai kawai ta fashe da dariya harda tafa hannu, abin ya matuƙar bawa momy mamaki, Dady ya shigo lokacin gari ya fara haske, har ƙasa Jannat ta durƙusa ta gaishe shi kafin ta ɗago sukaci gaba da aiki, bayan ya amsa ya wuce bedroom ɗinsa, ƙarfe 8:am suka kammala komai da komai, lokacin Dady ya fito sanye da riga t-shirt fara da baƙin wandon jeans, Jannat taje tayi brush ta dawo dining suka fara karyawa bayan momy ta zubawa kowa.
A hankali take tafiya har ta iso bakin titi, cikin sa'a tana tare wani mai napep ya tsaya, ta shiga tare da gaya mata anguwar da zai kaita, suna tafe tana ta tunani duk da dai ma tunanin nata bai wuce akan abu biyu ba, suna isowa ta fito kana ta miƙa masa kuɗinsa sannan ta fara tafiya har ta iso ƙofar gidansu, gidane da zamu iya kiransa da gida na masu ƙaramin ƙarfi dan su Anum ba wasu masu hali bane, sai Ummu tayi sana'ar siyarda kamu take samun kuɗin da zasu ci su sha, bakinta ɗauke da sallama Anum ta tura ƙofar galan galan ɗin gidansu, tana tafe tana tunanin koyaya Arshi ta kwana, sallama tasake yi kafin ta tura ƙofar ɗakin da suke kwana, juyowa tayi ta kalli ƙofar ɗakin Ummu ga mamakinta taga takalmi a gurin, fasa shiga ɗakin nasu tayi ta dawo da baya zuwa ɗakin Ummun, ta yaye labule tare da yin sallama, jin Muryar Anum yasa Ummu toshe kunnuwanta, cikin tsananin ɓacin rai da tsantsar tsana tace "mai ya dawo dake nan gidan ban riga da na sallameki ba? akan halittar nan taki mutane suka daina shigomin gida har cewa akeyi wai kina tsorata mutane, to yanzu hankalinki ya kwanta sun daina zuwa mun zauna bamu da cin yau bare na gobe" Ummu takai ƙarshen maganar tana miƙewa tsaye,
"Haba Ummu wai shin ba Allah bane ya baki anty Anum ba?"
Arshi tayi maganar tana zarewa Ummu idanu, "Allah ne ya bani ita nace bana sonta ko ana dole ne?" Arshi tayi wani irin gurnani kamar zaki kana ta taho da gudu tayi ciki da Ummu, ta kamo hannayenta ta kamo ƙafafuwanta ta haɗesu guri ɗaya kafin tace "ko kin ƙi ko kinzo anty Anum jininki ce babu inda za'ayi ki sauyata, Arshi tayi maganar cikin ƙaraji, zuciyar Anum na dukan uku-uku damuwarta kar Arshi ta yi kisan kai, duk da hawayen dake zubowa a idanunta jikinta na kyarma bai hanata ƙarasa shiga cikin ɗakin Ummun ba, ta sanya hannunta ana Arshi cikin Muryar kuka tace "ki rabu da ita koba komai taci darajar uwa a gurinmu" tabbas Ummu ta maguzu dan bakinnan yayi ƙato, dama gashi lafcece Arshi ta fice a ɗakin tana kamo hannun Anum, can ɗakinsu suka wuce, ta zauna akan tabarma kasancewar itace arziƙinsu a ɗakin sai katifa wace duk ta yayyage ga kuɗin cizo shima yana zuba shagalinsa, "anty Anum mai zai hana mu samawa kanmu mafita mubar gidannan"
"Arshi Gara ma ke nikam duk inda naje guduna zasu dinga yi kekam matsalarki ɗaya ce, idan akayi miki maganin Aljanun kanki komai zai zo da sauƙi" rai a ɓace Arshi tace "anty Anum Please stop saying that bani da larurar komai, idan zaki yarda ki yarda Ummu bata sonmu" Muryar Ummun suka tsinkayo tana daga tsaye ta riƙe ƙugu tace "iya Anum nace tabar gidanan Arshi idan kika fita ba da yawona ba, Anum da abin yaso bata dariya duk da tana cikin takaici tace "wai Ummu ya akayi kika dawo daga wancan gidan bayan kince babu uban da ya isa?" Ummu tayi shiru batace komai ba, tana daga tsaye Arshi tace "Ummu tunda dai bakyason anty Anum nima zan tafi Kinga sai ki zauna ke kaɗai, "wato Allah ya kawo mu zamanin da ɗan cikinka sai ya gaya maka magana son ransa? duk kuyi zanyi maganinku, kekuma Arshi ki tashi ki shirya naji labarin wani mai maganin iskoki dan wlhi naci gaba da zama dake a cikin wannan gidan zuwa gaba kasheni kawai zakiyi"
Ummu ta faɗa tana harar Anum.
"Nikam babu inda zani"
Arshi ta faɗa tana turo baki,
Ummu na tafiya Arshi tace "kinga dole mu samowa kanmu mafita, naji labarin wai Ummu zatayi aure,
End Ads