x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 1 - NISAN KIWO

  • 1 words
  • 3000 words
  • Out of 25414 words

Category: Love Stories

Views 55

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*NISAN KIWO❄️*

_Mom Islam
Page1

"Shin kinsan da cewar ciwon mahaifiyarki baya buƙatar damuwa akan me zaki dinga kusantar ta bayan tace babu abinda ta tsana kamar ta buɗe ido ta ganki?"
Cikin shesheƙar kuka Anum tace "akan me zata dinga furta min irin waɗannan kalaman kodan saboda taga Allah yayini da Halitta ba irin taku ba?"
Tai maganar tana toshe da hannu saboda kuka yaci ƙarfinta. cike da tsananin damuwa gami da tsantsar tausayi Jannat ta kamo hannun Anum suka fito daga ɗakin da Ummu take, a parking space suka tsaya, inda jerin danƙara-danƙaran motocin masu gidan ke a parke, "Anum nasani abin da ciwo ace mahaifiyarka wace ta ɗauki cikinka tun yana watanni ɗai-ɗai har tara da kwanaki yau a wayi gari tace bata ƙaunarka duk inda zakaje kaje wannan sam ba ɗabi'a bace, sannan gaskiya anyiwa Allah butulci"
Jannat ta faɗa tana dafa kafaɗar Anum, magana take son yiwa Jannat ɗin amma ina bakinta da zuciyarta gabaki ɗaya rawa sukeyi yayinda takejin kanta nayi mata matsanancin ciwo kamar zai tsage, cikin ƙarfin hali tana dafe da kanta tace "anty Jannat Ummu fa musamman ta baro gidanmu saboda ni, ta dawo gidan mutanen da ba danginta ba ta tare, tace inci gaba da zama acan, nikam bazan iya zama ni kaɗai a gidan ba duk da akwai Arshi"
"Haba Anum ya ya inason kawo miki ingantacciyar shawara kina kawomin wani zaman gidanku, ki nutsu ki saurareni, duk da cewar Allah yayi miki Halitta guda biyu, mace da namiji kinga mudai ba wani hali ne damu da zamu iya taimakawa ayi miki aiki ba, tabbas Arshi tana bani tausayi kodan Lalurar juyewar ƙwaƙwalwa da take tare dashi, amma wlhi nafi tausaya miki, dama shawarar da zan baki itace.."
Kiran Ummu ya katse Jannat, ta amsa tare rugawa a guje.
Anum ta durƙushe a gurin zuciyarta na faman yi mata zafi, ta kalli takalmin mazan dake a ƙafarta sannan ta shafi gashin bakin da ko ta aske gurin a baƙi yake zama, sannan ta kalli nonuwanta da suke a tsaye ƙyam kafin ta taɓo gabanta da ya kasance akwai na maza a jiki, ta ɗaga idanunta sama tare da dawo dasu ƙara hawaye na zuba sharr kamar an buɗe famfo,
"Jannat wlhi tallahi idan kika ƙara dawomin da Anum cikin gidannan mai rabani dake sai Allah tunda na gaya miki bana sonta bana sonta ko ana dole ne? inace ni na haifeta sannan nace bana ƙaunarta?"
Ummu tai maganar tana nuna Jannat dake tsaye a bakin ƙofa bata ma samu damar ƙarasa shigowa ba, a hankali ta tako tare da zama gefen Ummu cikin tausasa murya tace Ummu mai yasa kikeyin abu sai kace ba musulma ba, karki manta idan har kina tunanin kin gujeta ne, nan gidan da kike gadara dashi wlhi masu gidan suna iya dawowa a koda wane lokaci sannan sai sun tozartaki dan ba isasshen mutunci ne dasu ba"
Ummu ta miƙe kamar mai shirin yin tafiya, sai ta dawo da baya ta watsawa Jannat mari tana hoci tace "kar Allah yasa su bari inkai safiya, gidane nazo bazan fita ba tunda dai kema bana ubanki bane ai saiki barni da masu gidan ko?"
Dafe da kumatu ta miƙe daga zaman da tayi akan gado, kana ta miƙe jiki a sanyaye ta raɓa ta gefen Ummu ta fice, tana fitowa harabar gidan ta hango Anum na a durƙushe a gurin da ta barta ga uban rana da akeyi mai zafi, da sauri ta karasa gurin Anum ɗin tare da kamo hannunta, sukayi hanyar fita bakin get.
Jiki a sanyaye Jannat ta buɗe get ɗin suka fice, duk da shirun da ya ratsa anguwar bai hanasu samun wani dakali a ƙofar gidan dake a kusa da wanda suka fito suka zauna ba, har yanzu Anum kuka takeyi, Jannat ta sanya hannu ta buɗe kan Anum, da sauri ta fashe da kuka tare da rungume Anum, cikin kukan take cewa "Anum akwai matsaloli a tare dake masu tarin yawa, gashin kanki irin na maza ga gemu sannan kuma ga nono bayan nan.."
"Anty Jannat ki sanar dani abinda kikeson gayamin lokacin da Ummu ta kiraki"
Anum ta faɗa sbda wannan dogon lissafin da sukeyi ba wani ƙarewa zeyi ba,
Jannat ta mammatsa hannayenta kafin ta shafi gefen fuskarta da yayi jajir sannan tace "naji kafin nan gayamin nan gurin ya tashi ko?" Kallon kumatun nata Anum tayi cikin raunatacciyar murya tace "Ummu ce ta mareki ko?"
Jannat ta gyaɗa kai kana tace "karki damu idan Ummu ce zatayimin abinda yafi haka tunda yanzu ina tare dake, amma bata tunanin rayuwar Hajna?"
Sosai takaici ya kama Anum sbda a halin yanzu zuciyarta ta fara bushewa sam bata tunanin wata Hajna tunda dukkansu abin a taimaka musu ne, amma yanzu kam kanta take tunani, "ki mance da Hajna"

Anum ta faɗa.
"Toh shikenan, dama shawarar itace kinga yau baki da gurin kwana, sannan a gidanmu ma ba lallai su yarda mu kwana a tare dake ba, amma da zaki yarda da nayiwa ƙanwar momyna magana ta ɗaukeki aiki duk wata kina turomin da kuɗin cikin account ɗina, sai mu dinga tarawa har ya isa wanda za'ayi miki aiki, wlhi har makaranta zata saki, matsalar ɗaya ce dole ki kasance a suffar mace saboda wlhi mijinta baya ƙaunar namiji a gidansa, akan hakan matarsa ta tsayar da aihuwa, yaransu biyu Jumayma da Arshi, hamshaƙin mai kuɗi ne sannan kuma dole ƴan aiki tare da yaransa suke kwana, amma fa ansha kawo masa ƴan aiki wlhi yana korarsu dan ranar da naji ƙanwar momyn tana faɗa ƴan aikin da aka yi musu korar kare sunkai su ashirin"
Anum ta zaro ido kafin tace "Anty Jannat gaskiya bazan iya ba, saboda daga lokacin da suka tabbatar da ni MATA MAZA ce kinsan na shiga uku, inaga nikam kasheni zeyi kamar inda Ummu take buƙata"
Jannat ta toshe mata baki, tare da cewa "haba kisa, shidai ya kasance mai baƙar zuciya ne, dan wlhi nima nan da kika ganni ko gidan bana zuwa saboda akwai ranar da Arshi tayimin leifi na duketa bakiga ɗan dukan ba wlhi yana shigowa ya tambayeta tace nice, kawai sai nayi tsuru-tsuru, gashi sangameme ya tako har inda nake zaune saman kujera ya shaƙemin wuya, yace min, wai su biyun sune rayuwarsa zai iya kashe kowa a kansu in kiyaye,
Sosai hantar cikin Anum ta kaɗa, cikin karyar zuciya Anum tace "tunda kince yaran basu da kunya aiko dai bazamu shirya ba, Gara na shimfiɗa kwali na nemi gurin kwana ko a gefen titi"

"No ki bari muje a gyara miki gashin bakinnan, saboda nikam bazan iya ganinki cikin damuwa ba"
Jannat ta faɗa tana rausayar da kanta.
Sosai tausayin Anum ɗin ya kama Jannat,
Shiru ne ya biyo baya na ƴan wasu lokuta kafin Jannat tace "bazaki kwana akan titi ba, zan tafi dake gidanmu zuwa gobe da Asbha kafin su momy su fito sai muyi shawarar abinda ya dace"
Tabbas Anum tana jinjina tausayi tare da jarumtaka irin na Jannat sbda tasan idan har iyayen Jannat ɗin suka samu labarin Jannat ɗin ta kwana tare da Anum tabbas zata fuskanci mummunan hukunci, domin mutane da yawa suna suffantata da namiji, ita kuma Anum ɗin abinda bata taɓa kawowa kanta ba kenan, tana sawa a ranta koda yaushe ita mace ce, "toh" Anum tace dan itama kanta ta fara tsoron kwana a titin.
"Inda abin zai kasance, tunda tsakaninki da gidanku akwai nisa sosai gashi har an fara kiran sallah, zan fara shiga gidanmu, sannan da zarar na shiga zan yaudare mai gadi akan yazo ya dubamin wani abu acan baya, kinaji nace "subahanallah sai ki shigo a hankali ki ɓuya gurin motocin Dady, nikuma zan zo sai muyi shawarar inda za'ayi ki shiga ciki"
Anum ta kalli Jannnat dake ta faman kawo musu mafita, kafin tace "Nagode anty Jannat Ubangiji ya saka miki da alkairi"
Jannat ɗin ta miƙe tana cewa "karki damu fatan nasara zakiyi mana"
Suka fara tafiya riƙe da hannun juna, koda suka fito bakin titi da yake gidansu Jannat ɗin dole sai sun tsallaka titi, mutane sai kallon Anum sukeyi, wasu na tsokanarta wasu na nunata da yatsa, daga Anum ɗin har Jannat ɗin sunji zafin hakan, musamman ma wacce abin yake a kanta, cikin tausasa murya Jannat tace "Anum daga yau karki sake yawo babu hijabi kinji?"
Anum ta zura hannayenta cikin aljihun wandonta kamar dai inda maza sukeyi kafin tace, "anty Jannat tun ina ƙarama Ummu ta sabarmin da rayuwa a haka, wlhi rannan da na kwatanta sanya hijabi jinayi ya shaƙemin wuya sai naji sam babu daɗi dole na cire"
Jannat ta zaro ido tare da cewa "aiko inhar bazaki dinga saka hijabi ba wlhi duk gidan aikin da za'a kaiki matsala zaki samu indai ba aikin gida kamar mai gadi da dai sauransu zaki samu ba"

"Anty Jannat wlhi dan kawai kar inyi miki musu ne, amma duk sanda na kalli kaina a mirror sai tausayin kaina ya kamani, duk da nasan saɓo nakeyi nakance, mai yasa Allah bai dauki rayuwata ba tun inda jaririya, dan bana raye babu wani ƙalubale da zan fuskanta musamman ma ga mutane uwa uba harda mahaifiyata"

Jannat ta dafe kanta, kana tace "idan har bazaki godewa Allah da baiwar da yayi miki ba wlhi bazaki godewa azabarsa ba, inaso ki sani kefa da ranki da lafiyarki sannan zaki iya yin komai na aiyuka banbancin halittace ce dake, ƴar uwarki fa? da yanzu zakiga ana wasa da dariya da ita yanzu zata juye kamar ba ita ba?"
Anum tace "inayiwa Allah godiya, kinsan sharrin zuciya babu abinda bata aiyyanowa ɗan adam musamman ma idan yana fuskantar tsangwama da tsana.."
Isowarsu bakin get ɗin gidansu Jannat ne yasa dukkansu yin shiru tare da kallon juna,
Jannat takai bakinta dai-dai saitin kunnen Anum, kome ta gaya mata oho naji Anum ɗin tace "toh"
Anum ta koma can baya Jannat ɗin taje kusa da get tayi nocking lokacin har an fito sallahar magriba, "waye" mai gadi ya faɗa, "Nice haba malam Lado ka buɗemin mana"
Ƙaramar ƙofar ya buɗe kafin ya washe haƙora yana cewa "aiko Hajiya jannatu ki shirya karɓar faɗa daga gurin Hajiya domin kuwa tun tuni take sababi" ya ƙare maganar yana tafa hannu, taɓe baki tayi tare da nuna shi da yatsanta kafin tace "ni dan Allah karka dameni ka matsamin in wuce"
Tai maganar tana gyara ɗan siririn mayafin dake a kafaɗarta, da sauri ya bata guri ta wuce, da sauri ta nufi can bayan ɗakin mai gadin gurin ya kasance da kyawawan flowers masu kyau da ban sha'awa, tsala ihu tayi tana cewa "Lado dan Allah zoka taimaka min Please bansan meye a gurin ba" yana tafe yana jin radio yana cewa "kedai Hajiya wani lokacin idan kina abu sai kace ƴar yaye, ke da zaki wuce ɓangarenku mai ya kawoki ɓangare na, koda ya iso gurin tana tsugunne kanta a ƙasa, ƙarar horn ɗin motar dadynta da ta karaɗe musu kunnuwa ne yasa tai saurin dafe ƙirji tare da waro ido sbda gabaki ɗaya zuciyarta ta tsinke ta riga ta gama rayawa a zuciyarta Dady yaga Anum angama shikenan kashinta ya bushe....!

Mai kuke tunani Anum zata samu damar shiga gidansu Jannat kuwa?
Idan masu gidan da Ummu take suka dawo ya zatayi?
Ya kuke tunanin Arshi zatayi bayan babu kowa a gidan sai ita kaɗai?

Amsarku tana cikin littafin NISAN KIWO

Drop your comments saboda ku samu update akan lokaci, and then karku manta kuyi following account ɗina a arewabook

Page2

"Oyoyo Alhaji Barka da dawowa" Lado mai gadi ya faɗa yana shirin zuwa buɗe masa get, kafin ya samu damar fara tafiya Jannat ta janyo wuyansa, murya ƙasa-ƙasa tace "wlhi inhar kace ina gurinnan sai na lahira ya fika samun rahama" tai maganar tana jujuya masa kunnuwa,
Yana rawar jiki gami da leƙen kada yai laifi saboda bai je ya buɗewa shugabansa get ba, yace "dan Allah ki barni inje kinsan halin Alhaji" ta sake ɓuya acan gurin flowers ɗin sbda tasan idan har ta koma gida babu wanda zai barta ta sake fitowa, daga Dadyn har momy, bayan mai gadin ya buɗe masa get ya shigo kai tsaye parking space ya wuce, acan yai parking motar kafin ya fito da sauri ya nufi ciki.

Cikin sanɗa Jannat ta fito tare da kallon Lado mai gadi kafin tace "Allah ya taimakeka" sannan ta buɗe get ta fice, murya ƙasa-ƙasa take cewa "Anum am sorry please kiyi haƙuri ki fito karkiyi fushi" tsahon wani lokaci bataji muryar Anum ɗin ba, sosai hankalinta yai mummunan tashi taci gaba da zagaye layin nasu da babu hayaniyar kowa tana kiran sunan Anum, ta cikin wani lungu Anum ɗin ta fito ta wani haɗa zufa sosai dan a tunaninta Dadyn Jannat ya ganta,

"Anty Jannat babu wanda dai ya ganni ko?"

Anum tayi maganar zuciyarta na a tsinke, "karki damu Anum babu wanda ya ganki inaso ki tsaya a bakin get kinsan Lado munafuki ne, nikuma zan yi magana sai ki biyoni"

"Oky insha Allah"

Anum ta faɗa idanunta sun ciciko da hawaye,

Jannat ta buɗe get ɗin a hankali kafin ta iso gurin Lado tace masa, kaje can gurin da na tsuguna ɗazu na yarda ɗari biyar idan ka gani nabaka"
Tana gama magana ya wuce da gudu yana tsalle,
Da sauri ta sake buɗe ƙofar dake jikin get ɗin ta fara ƙwalawa Anum kira murya a hankali, Anum ɗin ta taho ta kanannaɗe hannayenta a ƙirjinta da alamu sanyi takeji, Jannnat ta kamo hannunta suka shige ciki, har suka wuce mai gadi bai fito ba, ta ƙofar baya sukabi wanda idan ka shiga, hanyar zata sadaka da cikin gidan amma bata ɓangarensu momy ba, hanyar ta kasance akwai ɗakin Jannnat a gurin, daga buɗe ƙofar har shigarsu cikin sanɗa sukeyi sai kace masu kama kifi, har suka iso ƙofar ɗakin Jannat ɗin, a hankali Jannat ɗin ta buɗe door ɗin tare da tura Anum ciki, kafin itama tasa kai zata shige "waye....?" sukaji muryar momy tana magana, cikin ɗaga murya Jannat tace "nice momy" Muryar momy ta tsinkayo tana balbala masifa tana cewa "tunda kin raina mutane yau zakiyimin bayanin inda kika tafi wlhi zaki karɓi hukunci a gurin dadynki" tuni jikinta ya fara kyarma, sbda tasan Halinsa akwai tsanani ta kalli Anum da ta zauna saman lallausar katifar Jannat ɗin ita kuma Jannat ɗin tana riƙe da door ɗin murya ƙasa-ƙasa tace "Anum Please ki kula da zarar kinji motsin za'a shigo ko nice ki san inda zakiyi ki ɓuya wlhi momy komai nayi sai ta gayawa dady ina zuwa Kinga yanzu ma kirana takeyi, ki buɗe fridge inaga akwai hollondia ki fara sha kafin in shiga kitchen in samo mana abinci", Jannat ta ƙarashe maganar tana rufe ƙofar ta wuce gurin Momy, suna zaune a parlo amma suna jiyo ƙus-ƙus na maganar da take yiwa Anum, "Jannat wannan shine last time da zan gindaya miki sharaɗi, saboda momynki tasha kawomin ƙorafin idan kika fita sai dare kike dawowa"
Jannat ta zube guwaiwoyinta akan carpet tare da sunkuyar da kai tana nazarin kalaman da zata ƙwaci kanta dashi, cikin sanyin murya tace "Dady jikin Arshi ne ya tashi yarinyar Ummu mahaifiyar Anum" cikin sauri tare da ɓacin rai Dady ya miƙe yana nuna Jannat da yatsansa kana yace "Jannat ashe dama baki ji gargaɗin da nayi Miki akan zuwa gidan mutanen nan ba, mai yasa kika fiye taurin kai ne?" Momy ta katse masa zancen ta hanyar cewa "batada wani aboki da ya wuce mata maza yaron
End Ads