Aljanu"
Hayatu mai shago ya tuntsure da dariya tare da buga tebur kana yace "wato kace Allah ya haɗaka da ƙarfen ƙafa, ni tunda Allah ya haɗa aurena da Zainabu lutiya wlhi na kasa tsinana abin arziƙi, na rasa ya akeyi ko nayi ciniki a shago sai na tattaro kuɗin na kawo mata wannan ja'iba tayi yawa, kai Auwalu Gara kai sau dubu"
Hayatu ya ƙare maganar cikin jimami da tausayin kansa,
Tunowa da maganar sallah yasa shi cewa "Hayatu ko sallah banyi ba, nikam na shiga uku"
Hayatu ya zaro ido tare da kallon Auwalu kafin yace "yanzu ai lokacin yin sallahar walha ne"
Auwalu ya miƙe tare da wucewa inda butoci suke ya ɗauka tare da nufar banɗakin dake raɓe da shagon, sai da yayi alwalah kana ya dawo shagon ya karɓi sallahya kana ya kabbara sallah, koda ya idar bai tashi a gurin ba, ya daɗe yana zaune har gyangyaɗi ya fara, Hayatu ya taɓoshi tare da cewa "mutumina ya kamata ka koma gida fa"
"Eh wlhi kam dan ko Abin karin kumallo ban bar musu ba"
Auwalu ya faɗa yana shafa kansa, zai sake magana wayarsa tayi ringing, ya zura hannunsa a aljihu ya Ciro wayar tare da duba waye mai kiran nasa, ganin sunan Ummu yasa shi ɗagawa da sauri "Alhajin Allah lafiya kuwa daga zuwa yin alwalah har yanzu baka dawo ba?"
Ummu tai maganar tana sake danna saƙata a ɗakinta dan Arshi ta kafa ta tsare wai sai dai Ummu ta haura ta katanga ta kawo mata Anum,
Tunda Ummu taji haka ta danna saƙata a ƙofa dama lekowa tayi, kiran Auwalu da tayi neman agaji take dan idan Aljanun Arshi suka tashi ko gangar cochi albarka gurin dokuwa,
Har yanzu tana nan zaune a tsakar gidan, hannunta riƙe da shimfiɗeɗiyar bulala sai karkaɗa ƙafafu takeyi.
Iya nera Ɗari ne a aljihunsa, da ƙafa ya dawo daga shagon Hayatu, amma ya ciyo bashin Madara ƴar ɗari da milo, ya biya gurin mai ƙosai ya siyo na ɗari, a ƙafa ya dawo gida, yana tafe yana cewa "ina tunanin akwai ragowar sugan jiya da bredi ya ishemu shan shayi,
Yana tafe yana lissafin kuɗin abincin rana har Allah ya kawoshi ƙofar gidan, sai da ya gyara wuyan rigarsa sannan ya shigo gidan da sallama, kafin ya ƙarasa shiga gidan ya ciro wayarsa dake ruri a aljihu ya kara a kunne, yana tafe yana waya, cikin rashin tsammani yaji saukar bulala a bayansa, ware idanu ya shiga yi ko zai ga wanda yai hakan, tana zaune ta hakimce akan kujera gashi shi kuma yana tsaye a ƙofar ɗakin Ummu, ita kuma tana zaune a saitin ƙofar ɗakinta dan tana kallonsa duk da tsakaninsa da inda take zaune akwai rata, "bani abinda ke hannunka" Arshi ta faɗa cikin wata iriyar murya wacce tayi daban da ta ɗazu a taƙaice ma Muryar tafi kamanni da na jarirai, hankali a tashe jikinsa na rawa ya miƙa mata, ta miƙe tsaye tare da ajiye ƙosan akan kujera, yana tsaye yana kallonta ta zazzage madara da milo akan ƙosan kana ta koma ta zauna tare da nunashi da bulala, tsananin tsoro ya sanyashi sakin fitsari cikin daga murya yace "dan Allah Hajiya ki buɗe ina cikin gararin rayuwa" Ummu dake manne a jikin ƙofa tace "aiko idan baka koma inda ta fito ba, zuwa anjima sai ka sauya kamanni" Auwalu ya zame a gurin babu numfashi, bayan ta gama cin ƙosan ta koma ɗakinta tana kwashewa da dariya, ta window Ummu ta ɗan leƙo tare da yaye labule, ganin ba kowa yasa ta leƙa Auwalu ko ya tafi, ga mamakinta sai taji gurnanin mutum, sosai ta tsorata ta buɗe ƙofa, tare da tahowa gurinsa da gudu, cikin Muryar kuka take cewa "dan Allah ka tashi karka mutu na roƙeka, tana maganar hawaye nabin kumatunta, atishawar Arshi da taji ne yasa ta yin hamdala tasan mutanen kan nata sun tafi, cikin ɗaga murya tace "Arshi dan Allah kizo Kinga abinda kika janyomin ko?" Arshi ta fito a ɗakinta tana mutsike ido, "menayi?" Arshi ta tambaya dan bata ma san tayi ba,
"Insha Allah yau ɗinnan zamu tafi gidan magani ko kinƙi ko kinso wlhi wataran kashemu aljanunki zasuyi"
Arshi ta taɓe baki, kafin tace "Ummu nifa ban gane abinda kike nufi ba, wane aljanu?"
Ummu ta harareta kana tace "bani ruwa a buta" Arshi ta kawo mata, ta yayyafawa Auwalu ya mike zumbur tana cewa "wlhi dole a cikin biyu ayi ɗaya"
Ummu ta riƙe baki tare da fara jera masa sannu, Arshi ma sannu tayi masa ya watsa mata harara tare da kawar da kai gefe, a fusace ya wuce ɗakin Ummu cike da masifa yafara magana "Na dai gaya miki, yaufa kwana ɗaya da auranmu har mun fara fuskantar masifu nikam bazan iya zama da wannan yarinyar ba, kisan nayi da ita" yai maganar in seriously"
Cikin firgici Ummu tace "Auwalu ita kenan min fa ina kakeso in kaita?"
"Akwai wani abokina da matarsa take gallaza masa, tanayin Tuwon siyarwa ni bance tayi tallah ba, ko aikin abincin ta dinga tayata amma bazata dinga kwana mana a gida ba"
Har yanzu Ummu bata aminta da shawarsa ba, suna tsaka da magana akayo sallama, Ummu na daga ɗaki ta amsa sallamar tare da mikewa ta fito, Anty Hadiza ta gani a tsaye, Ummu ta washe baki tare da cewa "oyoyo mutuniyar kirki jiya na gama maganarki shiga nan ina zuwa"
Anty Hadiza tai sallama a ɗakin Arshi, Arshi ta amsa tare da washe baki, Anty Hadiza tace "Masha Allah Arshi anata girma ina Anum?"
"Tayi tafiya"
Arshi ta faɗa a takaice.
Ummu ko na can ɗaki Auwalu nayi maga gargaɗin Arshi, Ummu tace masa "idan muka dai-daita da Hadiza sai su tafi tare amma bazan iya bada Arshi zuwa aikatau ba"
Ummu ta fito tana cewa "Hadiza kiyi haƙuri gani nan zuwa"
Ummu ta shigo suka gaisa Hadiza take tambayarta ya bayan rabuwa?
Hadiza tace "uhm ni Bama wannan ya kawoni ba, labari naji ashe bayan tafiyarmu ƙasar waje kin karɓi key na gidanmu kin shiga ciki, to wlhi Alhaji yayi ajiyar kuɗi a lokar bedroom ɗinsa dubu ɗari bakwai an nemi dubu hamsin an rasa, kuma mutanen anguwa sunce babu wanda ya shiga gidan idan ba ke ba, dan haka ki fito masa da kuɗinsa, bari kiji recording ɗin maganarsa da nayi.
"Idan bata bata baki kuɗin ba, kice hukuma ce zata rabani da ita, idan bata taɓa kwana a bayan kanta ba yau zataje ko kaffara bazanyi ba sai ta biyani kuɗina"
Ummu ta waro ido tare da kallon wayar Anty Hadiza kafin tace"wato ya mayar dani ɓarauniya ko? Ubanme zanci da kuɗin wani ba nawa ba, to ko sisi ban gani ba bare in taɓa, na ɗauka zancen arziƙi ne ya kawoki ashe sharri kikazo ki laƙaba min" Hadiza ta mike cike da rashin mutunci, kafin ta nuna Ummu da yatsa tace "zaki amsa kira a station ki jira dawowata"
Hadiza ta ɗauki jakarta ta wuce fuuuu tabar ɗakin.
Hadiza na fita Arshi ta kalli Ummu kafin tace "Ummu idan kece kika ɗaukar musu kuɗi kiyi gaggawar basu dan nashiga ban ɗauka ba bata fidda ɓarawo, Ummu ta zaro ido kana tace "dan ubanki kema zargina kikeyi? daga naje shan AC da fanka shine abin zargi?" Ummu ta ƙarashe maganar kamar zata rufe Arshi da duka, "babu abinda suka isa suyi wanda Allah beyishi ba, ina nan daram babu inda zani" Ummu tai maganar tana shewa, Auwalu da ya shiga wanka ya fito yana sanye da jallabiya ya buɗe labulen ɗakin Arshi sai da ya karewa Arshi ɗin kallo yaga idanun nata ba irin na ɗazu ba, sannan yace "wai meke faruwa ne? Cikin masifa Ummu tace "yo Kai kuma meye naka banda gulma da tsegumi me kazo ji....!
Page11
Ina miƙa saƙon godiyata ga masoyana jiki Alhmdulilah Nagode sosai.
"Allah ya baki haƙuri naji kamar cewa akayi kuɗi ya ɓata"
Auwalu ya faɗa yana juyawa zuwa ɗakin Ummu,
"Da ka tsaya mana, in banda gulma da kinibibi mitsw"
Ummu tai tsaki tare da washe baki kamar ba itace ta gama masifa ba, "Arshi dan Allah ki amince da zuwa gidan Hadiza kwata-kwata aikin da zakiyi na wata biyu ne, Kinga an biyasu dubu hamsin ɗinsu kafin su miƙamu ga hukuma, gara muyi komai cikin rufin asiri"
"Ummu naji zanje amma da sharaɗin dole Anum ta dawo gidannan"
Arshi ta faɗa tana jinjina kai alamar maganar fa da gaske take yi,
Jikin Ummu na rawa tace "indai Anum ce kamar ta dawo an gama nayi miki alƙawari kedai kawai ki shirya ranar da zaki dawo ranar zansa Jannat ta kawo Anum ɗin" Arshi ta janyo jakar kayanta ta fara zaɓar wanda zataje dashi gidan anty Hadiza, wata ƴar ƙaramar jaka ta ɗauka wacce zata ci kaya kamar kala goma, sannan ta zuge zip ɗin bayan ta gama shiryawa, tana daga tsaye tace "Ummu yunwa nake ji ƙarfe 10:am ko karin kumallo banyi ba"
"Yo nima me nasa a bakina? ya fice tun tuni ya dawo hannu rabbana"
Cikin ɗaga murya Ummu tace "Auwalu ina abin karyarwar da kace zaka kawo?"
Yana leƙowa ta labule sukayi ido biyu da Arshi yaga idanunta na bashi tsoro cikin rawar murya yace "naajeee...najeee" Ummu ta fito a ɗakin tare da riƙe ƙugu kafin tace "turr da wannan rayuwa tun ba'aje ko ina ba ciyar dani yana neman gagarar ka? To wlhi ko kaƙi ko kaso sana'a zan kama yi wacce zan tsira da mutunci na"
Gabaki ɗaya bakinsa ya rufe kamar an ɗaureshi sam ya kasa bata amsa kwata-kwata, sai kallonta da yake yi, a cikin ransa kuma mamakin maganganun da ta gaggaya masa yakeyi, Ummu ta kunto bakin zaninta ta miƙawa Arshi ɗari biyar, kana tace "ki siyo mana katin Mtn na ɗari sannan ki karɓo kamu na ɗari suga na ɗari sai ƙosai shima na ɗari, yanzu zan haɗa gawayi insa ruwa kafin ki dawo Arshi kiyi sauri" Ummu ta faɗa tana harar Auwalu.
Hijab ɗinta ta ɗauka ta fice, kai tsaye ta sissiyo abubuwan da Ummu ta gaya mata, bata wani jima ba ta dawo lokacin wutar ta kama har Ummu ta ɗora ƴar tukunya,
"Ɗauko wayata a ɗaki kisa katinnan zan kirawo Hadiza yanzu" Ummu ta faɗa tana yiwa Arshi nuni da hannu.
Bayan ta sanya katin ta miƙawa Ummu tare da danna number Anty Hadiza, Ringing ɗaya zuwa biyu ta ɗaga kasancewar tanada number Ummu, "Nace ga Arshi nan zata zo tayi miki aiki na wata biyu a madadin kuɗinku ayi haƙuri nidai ba ni na ɗauki wannan kudi da ake zargina dashi ba, ko da yake nashiga ban ɗauka ba ai bata fidda ɓarawo"
Ummu ta faɗa tana karyar da murya,
Sai da Hadizan ta ɗau tsawon lokaci kafin tace "wlhi kin taimaki kanki, gashi nan breakfast yakeyi na shigo na sameshi ya gama shiryawa barin gaya masa abinda yace sai ki shirya" ta katse kiran.
Alhaji Kasim kenan, babban ɗan kasuwa wanda duniya tasan da zamansa, ba a iya nan ya tsaya ba, kasuwanci har a ƙasashen Turai yana taɓawa, ya kawo kayan su Nigeria sannan ya ɗibi na Nigeria wanda sukeso ya kai musu,
Zaune yake a saman lallausar kujara mai zaman mutum biyu, Anty Hadiza tana gefensa, cike da nuna kulawa tace "Yaya maganar ɗazu ce da ka turani gidan matar nan da tazo ta tare mana a gida bayan tafiyarmu London, tace wai yanzu zata turo yarinyarta.."
Alhaji Kasim ya dakatar da ita, kafin yace"zata turo yarinyarta me zatayi mana?"
"Aiki a madadin kuɗin nikuma na nuna amincewata tunda basu da halin nemo kuɗin bare su biya"
Anty Hadiza ta faɗa tana shafo gemunsa.
"Shikenan amman dai kinsan bana son hayaniya ko, idan har zata kiyaye ace mata tazo"
Sai da anty Hadiza tayi masa kiss kafin ta danna number Ummu tace "arshi ɗin tazo"
Ummu tace tana nan tahowa,
Sai da Arshi ɗan tayi karin kumallo kafin ta sake wanka dan gwana ce ta fannin tsafta kana ta sanya hijab sannan ta fito hannunta riƙe da jaka tace "Ummu na tafi"
"Ummu na ɗora ruwan wanka tace "ai ban baki kuɗin Adai-daita ba, dan Allah Arshi karki nuna musu halinki daga kinji ranki ya ɓaci ki ambaci sunan Allah ki samu ki kammala wannan aikin cikin kwanciyar hankali arshi ki taimakeni kinji?"
Gyaɗa kai tayi tare da karɓar ɗari biyu da Ummu ta miƙa mata kana ta fice, dama Auwalu yana laɓe a banɗaki, burinsa bai wuce yaga Arshi tabar gidan ba, yana tsananin son Ummu bayajin zai iya rabuwa da ita, komi wulaƙancin da zatayi masa, duk da dai ba wata ƙwaƙwarar sana'a bace dashi ba, amma yasan a hakan zasu dinga rufawa juna asiri.
Da sauri ya ajiye buta ya shige ɗakin Ummu sbda bata waje ta shige ciki, tana tsaye tayi ɗaurin ƙirji ya ƙaraso da fara'arsa, "Hajiyata a taimakeni a bani haƙƙina, da tunaninki na wuni yau"
Auwalu ya faɗa yana wani sake matsowa kusa da ita, sai da ta harareshi kafin tace "yunwa nake ji kasan kuwa babu abinda zan iya taɓukawa"
Ya zaro idanu, shidai yaji ta bada kuɗi a siyo kamu amma baiga inda sukayi dashi ba, daga ita har Arshi ɗin, saboda kar ya sake taso da wata masifar yasa shi cewa"dan Allah ko sau ɗaya ki bari inyi wlhi zan samo miki abinci haba me amfanin nemana idan ban ciyar da hajiyata ba"
Auwalu na rungume da Ummu ta rage murya kafin tace, "idan ka amince zan fara siyarda maganin maza kanayi min tallah, kaga ribar sai mu dinga rabawa nikuma ina siyar da maganin mata"
Ido waje yake kallonta, yayin da yaji abun wani banbarakwai babu daɗin ji, "haba hajiyata kamar ni da girmana da mutuncina da ƙimata a ganni ina tallan maganin maza ai zance ya ɓaci ina banzan iya ba"
Ummu ta riƙe ƙugu tana matsar da jikinta a nasa tace "aiko cefane safe da rana da dare ya zamo maka farillah aure kwana ɗaya?"
Koda Arshi ta fita bata wani sha wahala ba gurin samun abin hawa, kai tsaye anguwarsu Anty Hadiza aka wuce da ita, suna isowa ta mikawa mai Adai-daita kuɗinsa sannan ta fara nocking a jikin get ɗin gidan, mai gadi ya buɗe mata yana washe baki, kasancewar ya santa dan Ummu tana yawan aikosu gidan yawancin zuwan nasu ma roƙo yafi yawa, bayan sun gaisa ta shige ciki.
Koda ta iso bakin ƙofar shiga parlon nan ma nocking tayi, da kansa yazo ya buɗe mata kasancewar yana kusa da bakin ƙofa.
Har ƙasa ta durƙusa ta gaishe shi, ya amsa fuska ba yabo babu fallasa kana yace "kece Arshi?"
"Eh tace masa tana murmushi, yayi mata izinin shiga, koda ta shiga a ƙasa kan carpet ta zauna tare da takure ƴan ƙafafunta ta ɗaga kanta sama idanuwanta suka sauka kan tafkeken Tv dake ta aiki,
"Sanu da zuwa Arshi da fatan Ummu tayi miki bayanin abinda zakiyi?"
"Eh tace tare da sunkuyar da kai ƙasa"
"Okay shara wanke-wanke wanke toilet gyaran ɗaki parlo ɗakin yaya da kitchen da girki"
Gaban Arshi sai da ya faɗi, ita kam tunda take a gida bata taɓa wani haɗawa kanta aiyuka sosai ba.
"Banji kince komai ba, mahaifiyarki ce ta ja miki"
Da sauri Arshi ta kalli anty Hadiza kafin ta cije lip ɗinta na ƙasa, cikin takaici.
Shigowar Alhaji Kasim ne yasa Anty Hadiza mikewa taje ta rungumeshi a gaban Arshi, sai wani mannata yakeyi a jikinsa a haka suka wuce bedroom suka barta a parlo,
Kallon agogo tayi ƙarfe 12:pm zaman ya isheta ta miƙe tsaye tana ƙarewa frame na photon su Alhaji Kasim da Anty Hadiza sunyi kyau sosai, bayan wasu mintuna time ɗin ta dawo ta zauna, anty Hadiza ta fito sanye da ƙananun kaya, kana ta jefawa Arshi bedsheet cikin gadara tace "ki wanka yanzu, washing machine ɗina ya lalace, hannu zakisa gurinnan da yayi farin abu ki dirjeshi"
Babu musu ta mike tsaye tare da rungume zanin gadon a jikinta, sam bata san meye a jiki ba, ko da anty Hadizan ta nuna mata gurin yin wankin ta barta a gurin, kai tsaye ta nufi gurin akwai omo da sabulu da bucket, ta tari ruwa a famfo kana ta zuba omo, tana ɗago bedsheet ɗin taga wani irin farin Ruwa kwance a bedsheet ɗin, cikin ƙyanƙyami ta ɗauko tsintsiyar shara ta wanke kana ta sakashi a bucket ta sake wankewa, sannan ta ɗauraye ta shanya, har ta dawo parlon ƙyanƙyamin kanta takeyi, ƙarfe 1:pm Any Hadiza tace ta shiga kitchen, "me za a dafa?" kanki zaki dafa" anty Hadiza ta faɗa tana daga ɗaki, Arshi taji zafin maganar amma sai ta basar ta shige kitchen ɗin, tunanin abinda zata ɗora ta fara yi, kwatsam shawarar faten tsaki ta faɗo mata, cikin ƙanƙanin lokaci ta haɗa abubuwan buƙata kama daga yakuwa da ƙashi da sauransu, bayan ta kammala taje ta jere musu a dining, sannan ta dawo gurin jakar kayanta dake anan parlo wacce har yanzu ba'a nema mata gurin zama ba, ba wata gwanar cin abinci bace, ta nemi guri ta zauna.
A tare suka fito, lokacin har an shiga sallah, ta rakashi har bakin ƙofa ya wuce ita kuma ta dawo ciki, "me kika dafa?" Faten tsaki" Arshi ta faɗa ba tare da fargaba ba saboda ita a ganinta abin marmari ne.
"Kutumar bura'uba faten tsaki a gidana sannan a tukunya ta?"
Anty Hadiza ta faɗa tana bugar ƙirji,
"Gani nayi ai kince in dafa duk abinda..."
Kafin takai ƙarshen magana anty Hadiza ta watsa mata Mari, lokaci ɗaya idanuwan Arshi suka sauya launi, duk anty Hadiza bata lura ba sai balbala masifa takeyi, daga bayanta taji anata zuba mata bulala ana dariya da Muryar yara ita kuma Arshi tana tsaye dafe da kumatu, anty Hadiza ta fara ihu tana cewa "haba yaya, kai fa kace ka daina mai yasa zaka dawo da wannan mummunan halin?"
Wasu muryoyi guda biyu a tare sukayi magana,
"Muguwa daga yau a gidannan zamu dinga kwana tare dake"
Ta kwasa a guje tare da nufar ƙofar bedroom taji a rufe, ta duba kitchen nanma a rufe, sannan ta je buɗe ƙofar bedroom na Alhaji Kasim nan ma a rufe, cikin kiɗima tace "wai shin mutum ko aljan?" Kafin a bata amsa aka sake zula mata bulala ta durƙushe a gurin, tashi ɗaya jikinta ya hau ƙaiƙayi, ta fara ihu tare da fara cire kayan jikinta cikin gaggawa tana cewa "ke Arshi dan ubanki bazaki taimaka min ba, har yanzu bata