x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - NISAN KIWO

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 25414 words

Category: Love Stories

Views 57

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
wlhi tallahi idan tayi sai na saka mijin fitsari a wando, sun daɗe suna tattauna halin rayuwa, daga ƙarshe Anum ta miƙe tsaye, "ina zaki?"
"Zan yi wanka in sauya kaya saboda anty Jannat tace zata rakani wani gida in fara aiki"
Anum ta faɗa tana juya baya tare da samun zani ta ɗaura a ƙirjinta, Arshi na daga zaune tace "
Wai labarin yayi muku kuwa?
Dan Allah kuyi following account ɗina arewabook
Drop your comments
Shin wane ƙalubale zata fuskanta a gurin aiki, gafa maganar auren Ummu Arshi zata barta tasha ruwa kuwa?
Page4
Shigarta wanka bayan ta cire zanin jikinta zuciyarta ta sake tsinkewa sbda ƙarewa halittar jikinta kallo da ta dinga yi, duk da cewa bawai baƙon abu bane a gurinta amma takanji rashin daɗin ganin halittarta a hakan, abinda ya sata daɗewa a wanka kenan dan har takai tsawon one hour tana wankan, itada ba ma'abociyar daɗewa a wanka ba, ta ɗaura zani taji Arshi na cewa "anty Anum kiyi sauri ki fito Anty Jannat tazo"

Da sauri ta wanke sosan wankan kana ta fito tana washe baki, Ummu dake can ɗaki tana jiyo sallamar Jannat ɗin amma bata amsa ba.

"Oyoyo antyna ta kaina" Anum ta faɗa tana washe haƙora,

"Oyoyo ƙanwata da fatan kin shirya saboda time ɗin tafiyata school yayi, sbda kar in saɓa alƙawari ne yasa nace barin biyo idan na ajiye ki sai in wuce"
Jannat ta faɗa tana yi mata murmushi, Arshi tace "anty Jannat ki ƙaraso ciki kafin ta shirya, nima zan biku"

Cikin tausasa murya Jannat tace "kiyi haƙuri Arshi babbar matsalata Anum idan har ta samu mafaka insha Allah kema kamar kin samu ne" Arshi ta narke fuska kamar mai shirin yin kuka.
Ɗakin su Anum ɗin Jannat ta shiga, a gurguje Anum ta shafa mai sannan ta ɗauko powder zata shafa, Jannat ta dakatar da ita tare da cewa "karki shafa sa kaya sannan muga wane za'ayi" duk cikin kayanta riga da wando ne na maza sai hula P/cap shi take sawa, sbda tun tana ƙarama haka Ummun take sanya mata, ta ɗauko wani ƙaton wando zata sanya Jannat ta ƙwace tare da cewa "karki manta a matsayin cikakkiyar budurwa zakije ba a namiji ba, mai yasa kayan maza zasu shigo ciki?"

Anum ta shagwaɓe fuska kafin tace "bani da kayan da zasu dace"

Jannat ta kalli Arshi kana tace"miƙomin ledar da nazo da ita"

Arshi ɗin ta ɗauko ta kawo gaban Jannat, kasancewarta ƙwararriya ta fannin makeup batayi ƙasa a guwaiwa ba, ta fara fito da kayan kwalliya, sai da ta fara shaving ɗin gemun Anum ɗin sannan ta sanya cum ta gyara mata gashin kanta kafin ta fara tsara inda kwalliyar zata kasance, sun shafe tsawon lokaci anata gyaran fuska kafin daga ƙarshe ta ɓula mata kunne tasa mata ɗan kunne mai barima, sosai Anum tayi kyau, dan haka take kunnenta ko ɓuli babu, abin sai yai matuƙar burgeta duk da cewar taji zafin yin hakan,
"Bamu da isasshen lokaci Anum har yanayin tafiyarki dole ki sauya saboda yawanci kinayin abu kamar na maza, sannan ki rage gwada wa abu ƙarfinki, magana ma ki dinga dai-daita wa, Saboda gudun kar mu fuskanci matsala" Jannat ta faɗa tana buɗe ledar ta ciro riga da skirt na atamfa mai kyau, ta miƙawa Anum,
Anum ta jujuyasu tare da cewa "anty Jannat a jikina zan saka?"
"Eh sakawa zakiyi idan har Allah ya bamu nasara zan gayawa Ƙanwar momyn cewar duk kwana uku zaki dinga dawowa gida"
"Tom amma anty Jannat idan nasa kayannan kunyar tafiya dasu zan dinga ji"
Cikin jin haushi Jannat ta watsa mata daƙuwa kafin tace"ana ga yaƙi kina ga ƙura, kinsan dai na gaya miki zan wuce school ko akan rashin zuwa da banayi malaminmu zai iya kiran Dady, idan kuma zaki bari inje in dawo idan na dawo sai in biyo tanan"
Arshi dai tana kallonsu sosai tausayin Anum ɗin ya kamata, babu damuwa zan jiraki tunda ai bazaki daɗeba ko?"
"Eh ba daɗewa zanyi ba, naso ace ma mu wuce hospital daga nan sbda mu samu wasu bayanai a kanki"
"Shikenan babu damuwa Allah ya dawo dake lafiya"

Anum ta faɗa cike da nuna kulawa.
THAILAND
Yangon
Zaune suke a cikin wani hadaɗen parlo mai kyau sosai, parlon ya kasance madaidaici, yana ɗauke da tausasan kujeru guda uku, dukkansu masu zaman mutum ɗaɗɗaya ne, color na kujerun light blue ne, yayinda samansu yake kewaye da adon katako mai kyau, fentin jikin bangon fari ne, sannan kayan kallo da su fridge da sauransu, ɗakuna uku ne a gidan, bedroom biyu sai kitchen kowanne bedroom da toilet a cikinsa, acan parlo wasu kyawawan samari ne a zaune ko wanne fuskarsa babu walwalah dukkansu farare ne hakan shizai tabbatar muku da cewar haifaffun garinne, Masha Allah kaf cikinsu basu da wani makusa duk da cewar suɗin abokan juna ne, ɗaya daga cikin su mai suna Khair yace "ya kamata Ku hanzarta kunsan yau weekend su Leeela basa free idan har Allah ya bamu nasara sai mu taho da yaran" Aman ya kalli agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa kafin yace "tabbas bamu da wani enough time ku hanzarta" Bahi da sai yanzu yayi magana, murya a sanyaye yace "ni am ready ku nake jira" su biyun suka miƙe shima ya miƙe, dukkansu suka haɗa hannu alamar sunyiwa Juna alƙawarin babu wata matsala kana suka fito tare da kulle gidan, a inda suka tsara tun farko hakan ne ya kasance ko wanne zai hau tasa motar saboda tsaro, hakan yabawa Bahi damar kiran Leeela, ringing ɗaya Leela ɗin ya ɗaga, time ɗin yana tare da ƴan mata sai wani iyayi sukeyi masa, "oga su Aman fa basu daddara da gargaɗin da kayi musu ba, yanzu haka dukkanmu muna hanyar zuwa ɗibo ƴan matan ne"
Cikin sauri Leela ya mike tsaye zuciyarsa na zafi yace "har akwai wani wanda zai tsallake min layin da na zana, inaaa!.."
Yai maganar yana watsar da ƴan matan dake a kusa dashi, cikin zafin nama ya shiga wani ɗaki wanda ya kasance yana cike da makamai, ko me ya ɗauka oho ya fito ya ƙarasa ciki, kafin ya danna wasu numbobi a wayar tafi da gidanka, ringing ɗaya aka ɗaga cikin ɓacin rai yace "Raja kaje titin Haiphong cikin sauri akwai wasu motoci guda uku da zasuyi parking a gurin yanzu yanzu ka kawomin su nan" daga can ɓangaren Raja yace "an gama mai gida"
Cikin shiri ya fito daga gida, Raja baƙi ne sosai daga ganin yanayin fuskarsa zaka tabbatar da babu mutunci.
Suna cikin tafiya dukkansu ukun kafin su ƙarasa titin Haiphong ɗin motar Khair ta lalace, dama shi da Aman kusan a tare suke tafiya, shikam Bahi yayi nisa sosai, Aman ya fito cikin sauri tare da riƙe hannun Khair kafin yace "khair ga dukkan alamu Bahi bashi da gaskiya zomu juya komai zai iya faruwa damu anan" Hankali a tashe Aman yake magana, hakan kuma bai hana Khair durƙusawa a gaban motarsa ba, ya fara duba abinda yake bashi matsala, Aman ya kamo masa hannu Khair ɗin yana jan Aman, Aman yana jan khair, cikin zafin nama Khair ya mari Arman kafin yace "tabbas baka da hankali, mai yasa abokinmu aminin mu zaka dinga yi masa mummunan zato, Bahi bazai iya yarda a haɗa baki dashi....
Ƙarar Harbin bindigar da sukaji ne yasa ko wanne dai-daita nutsuwarsa, Arman yaja Khair suka gudu, saboda sun fara ƙure musu gudu, suna gudun har suka iso gurin motar Aman suka shiga cikin gaggawa ko rufe murfin motar basuyi ba, Arman ya fara driving, abin mamaki babu Bahi babu alamarsa, sukuma su Aman sunata gudu mutanen na binsu, mutanen Leeela suka dinga sakar musu bindiga har suka sace musu taya ɗaya, sosai tsoro ya kamasu tunda dai basu da wani makami da zasu kare kansu gashi kuma mutanen sunzo har gabansu, suka durƙusa a gurin kowannensu ya ɗaga hannu sama, cikin wata mummunar murya Raja yace "mai yasa zaku shiga hannun oga bayan kunsan bazaku iya dashi ba?" yai Maganar yana hanɓare Aman, wayar Khair ta fara ringing cikin tsoro ya kalli aljihunsa hannunsa na a sama, Raja ya sanya hannu ya ciro wayar kana ya kara a kunne, cikin ƙaraji yake cewa "wayeee!!" Nice kakarsa da fatan dai yana nan ƙalau ko?,
yau ne birthday ɗinsa har mun shirya nida ƙanwarsa ina fatan zaka sanar masa"

Raja ya daka mata tsawa cikin ƙaraji yace "keeee kaka, ba kaka kike ba ko kakus ne, jikanki ya shiga hannun Iyalan Leeela da fatan zaki cigaba da murnar shagalin bikin birthday ɗinsa"
Hannun granny na rawa ta miƙawa Arya wayar hannun granny yana karkarwa, da sauri Arya ta tallafi granny tare da kallon ƙasan ƙafafunta tace "granny lafiya naga kamar fitsari kikeyi?" idanun granny sun kakkafe tace "ba dole ba, tun daga nan na fara jiyo jiniyar sojoji sun garƙame Khair, nima Gara in mutu kawai"
Cikin kiɗima Arya tace "yimin bayani wani abun ne ya faru?" Wata uwar tusa da granny ta saki ne yasa Arya sake hannun granny tare da matsawa can gefe rai a ɓace tace "baki gayamin abinda ke faruwa ba, sannan kin cikawa mutane ciki da guba anya granny ba haka kikayi a yarintarki ba?"
Da sauri granny ta buɗe ido, ta ɗorasu a na Arya, a zuciyarta tace "inafama da wani baƙincikin ta sake cusamin wani" tsabar takaici granny ta kasa furta koda kalma ɗaya, tana zaune a gurin ta dinga banko tusa mai wari, Arya kam guduwa tayi sbda cikinta ya fara rikicewa, da gudu ta nufi toilet ta fara tsuga gudawa har tana riƙe cikinta, sosai ta haɗa gumi sbda abin babu sauƙi, tana fama da kashi granny ta leƙo cikin rage murya tace "Arya ki fito zan shiga ina tunanin abincin da nayi mana jiya shine ya lalata mana ciki" sam Arya bata jinta bare tasan da ita takeyi, murya a narke granny ta sake cewa "Arya fito zanyi a ƙasa kinsan ba pant na saka ba" wata uwar tusa granny ta sake sakewa wacce tasa Arya ɓarowa daga gurin kashin, da rarrafe ta fice cikinta na murɗawa, idanuwan granny sunyi ƙulu ƙulu ta haye gurin kashin tare da zakin zawo ɓirrrrrr a hankali ta sauke ajiyar zuciya tare da lumshe ido, ta daɗe tana tsigawa dan har wani irin gumi takeyi gashi sam jikinta babu wani ƙwari, da ƙyar ta sakko tare da kunna ruwa a pampo ta ɗauki buta ta tara murya kamar an sanyata magana dole take cewa "oh wannan Arya ɗin haka ta fice ko kashin bata wanke ba, inda take ma bazan dosa ba" granny tayi maganar tana dafe kwankwaso, a duƙe ta fice waje bayan ta kora kashin ya wuce, ta jingina da jikin bango, kira ya sake shigowa, wayar na ajiye saman kujera, da sauri granny takai hannu ta amsa kiran cikin marairaice murya tace "waye dan Allah ku sakarmin jikana shi kaɗai nake dashi" Khair yana kuka taji muryarsa yana cewa "granny ki sakamu a adu'a yanzu haka gidansu Leeela zamu wuuuu..."
Granny bata tsaya jin ƙarashen zancen ba ta zube a gurin ko numfashi batayi, Arya da ta koma ɗakinta ta watsa ruwa ta fito ta samu granny a kwance a gurin, ta kira sunanta yakai sau uku amma shiru bata amsa ba, hakan ya sake tabbatar mata da suma tayi, da sauri ta buɗe fridge ta ɗauko ruwa mai ƙanƙara ta tsiyaye a fuskar granny tana daga tsaye, a zabure granny ta miƙe tare da cakumo wuyan Arya tana cewa "Leeela ka sakarmin jikana kokuma inzo in gwada maka wasan dambe wanda nayishi tare da kakanka"
Arya ta waro idanu sam har yanzu bata fahimci inda granny ɗin ta dosa ba, sai wasu abubuwa takeyi kamar mai taɓin hankali, "shaƙe mata wuyan da granny ta sake yi a karo na biyu ne yasa ta fincike hannunta cikin rashin sa'a granny ta zube akan markaɗaɗen Attahiru dake a hannun Arya zata shiga kitchen samawa kanta abinci, sbda kashin da tayi cikinta ya zazzage, ihu granny ta kurma, cewa takeyi babu wando ku taimaka babu wando, Arya ɗauko min Vaseline in shafa ko pipi zeyi min sauƙi, ai duk kece muguwa mai hali irin na uwarta, nace Miki babu wando ki kawomin koda sabulu ne in wanke" Arya ta tsaya tana ta cashewa da rawa har da juyi cewa take new birthday in this time lol....!
Ina mutanen granny tace muku babu wando🤣🤣
5

Da ƙyar Granny ta samu ta dafa bango kana ta miƙe, tsabar ruɗu da azaba ya sanya ta cire bujen skirt ɗin dake jikinta, ta ƙarasa ɗakinta da gudu, tana zuwa ta kunna fanka ta matso da fankar jikin gadon, ta inda iska zai dinga ratsata sosai, da sauri ta haye gado tare da wangale ƙafafunta ta lumshe ido, duk da haka dai zafin na shigarta, sai can anjima barcin wahala ya ɗauketa,



Arya na tsaye har bayan tafiyar Granny gabaki ɗaya bata jin walwalah sbda tunowa da Khair da tayi rabonsa da gida tun safe dan har sunyi waya yake ce musu zai je anguwa idan ya dawo sai yayi musu photo dukkansu na murnar birthday ɗin nasa, ringing ɗin da wayar Granny ɗin tayi ne yasa Arya ɗagawa sbda new number ce, kafin tayi magana taji ance "ashe dai ba rayuwar ɗan naku bane a gabanku, kaka idan bakisan waye Leela ba yau zan gaya miki, shine masheƙi makashi wanda baya bari sannan kuma mayunwacin zaki ne shi bayan haka ran mutum tamkar ran kiyashi ne a gurinsa" jikin Arya a sanyaye ta kalli wayar kafin ta katse kiran, zuciyarta nayi mata zafi ta wuce ɗakin Granny, buɗe labulen da zatayi ta hango pipi a wangale, da sauri ta mayar da labulen ta rufe tare da fashewa da kuka, tana cewa Khair mai yasa ka kai kanka inda za'a halaka ka, sosai zuciyarta take yi mata zafi yayinda take ƙarfafawa ranta zuwa taimakonsa koda zata fuskanci wasu ƙalubale matsawar bazai taɓa mutuncinta ba, da wannan tunanin ta shiga ɗakinta ta fara haɗa kaya a ɗan madai-daicin akwati, haɗaɗun kaya masu masifar kyau ta zuba kana ta rufe akwatin, sannan ta ɗibi takardu masu muhimmaci a gareta kafin ta zuba a ƴar jakarta, kai tsaye ta faɗa toilet wanka tayi a gurguje kafin ta fito, ƙirjinta ɗaure da towel ta zauna gaban mudubi, so takeyi tayi haɗaɗiyar kwalliya duk da itaɗin mai kyau ce, ko bata shafa komai ba, tunowa da tayi da aikin dake gabanta yasa ta kawar da duk wasu tunani ta fara tsara kwalliya cikin nutsuwa, sosai tayi kyau dan idan ka ganta kamar ka saceta ka gudu tsabar kyau, ta ɗauko Pakistan milk color mai adon golden ɗin stone masu sheƙi da ɗaukar ido, sosai kayan suka amshi jikinta, mayafin ta rataye shi a kafaɗarta, kana ta maƙala ƴan kunne wajen guda huɗu sannan tasa zobe da warwaro da ƴar siririyar sarƙa, Masha Allah tayi kyau sosai, musamman ma da ta sake gyara gashinta wanda ya zubo mata har gadon baya ta sake tsaga tsakiyar gashin tayi style dashi tacan gefe, tasa abin kwantar da gashi ta kwantar ta mulke shi da mai, tana sunkuye tana ɗaura igiyar takalminta Granny ta shigo tana mutsike ido,

"Arya ina zakije bayan kinsan daga ni har ke rayuwarmu tana cikin hatsari, na shiga tashin hankali tunda naji ance Khair yana gurin Leela duk shine sanadiyar rikicewar cikina, yanzu ina zakije?"



Arya ta dafa kafaɗar Granny kafin tace "kowanne bawa da tasa ƙaddarar insha Allah bazan bari su cutar min da khair ba, koda yaushe mafarki na shine ace munyi aure dani dashi" Granny ta katse ta da cewa "Arya duk wannan lissafin da kike bakida ƙarfi da ikon tunkarar Leela"

Zan jarraba nayi miki alƙawarin tare zamu dawo dashi"



Arya ta faɗa tana saka madai-daiciyar wayarta a cikin handbag, kafin ta sake kallon kanta a mudubi tace "Granny ayimana fatan nasara"



Gabaki ɗaya gani takeyi kamar ta rasa su ne an gama,

Ta yi tagumi hawaye na zubowa,

KANO NIGERIA

A ƙurarrren lokaci Jannat ta dawo, duk da yamma da tayi bai hanata biyowa ta gidansu Anum ba, sai dai abinda kunnuwanta suka jiyo mata,

"Wlhi tallahi aure kamar nayi shi babu abinda zai hanani yin aure, dan ubanku tun zawarawan arziƙi suna zuwarmin musamman ke Arshi kinsa na koresu yanzu wanda zuciyata da hankalina ya kwanta dashi shima baza'a barni in aureshi ba? to albishirinku har na karɓi sadaki an gama komai, jiya ma munje gurin masu kayan ɗaki, kekuma mata maza karki sake ki zauna min a gida wlhi tsab zaki iya kashemin aure, kekuma Arshi kamar inda na faɗa idan kika tafi wani guri wlhi ban yafe Miki ba, jibi za'ayi ɗaurin aure da tarewa, kisan inda dare yayi miki, jikin Anum a sanyaye ta miƙe daga zaman da take idanunta na zubar da hawaye tace "tunda na taso nake fuskantar tsangwama da kyara daga gurinki, gami da kalmar kora da cewa kin yafeni, tabbas Ummu kalmar yau tafi ko wacce ɗaga min hankali duba da inda kike furicin in bar miki gida zakiyi aure, har kike kirana da mata maza Ummu kodai ba kece kika haifeni ba?" Cikin azama Ummun ta matso zata wanka mata Mari Jannat ta tare Anum marin ya sauka a gefen fuskarta, cikin Muryar kuka Anum ta riƙe hannun Jannat kana tace "akan mai yasa zakiyi haka anty Jannat?"

Rai a ɓace Jannat tace Babu, ɗibo kayanki kizo mu tafi, kekuma Ummu ki jira saƙo daga gidan barrister na zuwar musu gida da kikayi, an nemi dubu hamsin ba'a gani ba"



Jannat na gama faɗar haka ta kamo hannun Anum suka wuce ɗakinsu, a kwance suka samu arshi sai kuka take yi, Jannat ta dafa kafaɗarta kana tace "zata dinga leƙo ku kedai ki nutsu tunda Ummunku tana sonki"



Jannat tayi maganar cikin ƙarfin hali ne dan ko a tarihi bata taɓa jin tarihin uwar da ta watsar da ƴaƴanta har take aibantasu ba sai Ummu.

Ummu na daga ɗaki tace "sai su nemi ɓarawonsu nida ko kwana ma banyi a gidan ba, to ina ni ina dubu hamsin uban me zanci da ita,



A gaggauce suka shirya komai, ita da ta saba da sanya kayan maza da tasa atamfa sai taji wani iri, gabaki ɗaya ta takura, bayan sun kammala shiri Jannat ta ce "Anum kiyiwa Ummu sallama"

Anum ta kawar da kanta gefe gami da ɗaukar mayafi ta rataya
End Ads