x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 5 - NISAN KIWO

  • 12001 words
  • 15000 words
  • Out of 25414 words

Category: Love Stories

Views 58

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
kai masa kana ta dawo, mom ta nuna musu ɗaki suka shiga,
Komai na gidan yana matuƙar burge Jannat damuwarta bai wuce wulaƙanci da tozarcin da zata fuskanta a gidan ba, "Anum nan shine ɗakin da zaki dinga kwana"

Jannat ta faɗa yayin da take kwanciya a kan bed,
Ɗago kanta tayi tare da kallon Anum ɗin da tayi nisa cikin tunani, Jannat ta taɓo ta kafin tace "Anum tunanin mai kikeyi, a tunanina farinciki zakiyi? tunda har mom ta karɓeki hannu bibbiyu"
"Babu komai anty Jannat Nagode Allah ya saka da alkairi kin yimin halacci Allah ya bani abinda zan saka Miki"
Jannat tayi murmushi kana tace "ki kwanta kawai, mom tace zuwa gobe zata nuna miki aiyukan da zaki dinga yi, ki kwantar da hankalinki, shima mijin nata idan kika karanci halinsa bazaki wani sha wahala ba"

"Insha Allah zanyi ƙoƙarin kiyayewa"
Anum ta faɗa tana kwanciya can nesa da Jannat.
Can cikin dare bayan jannat tayi barci ta farka, ta tashi zaune tare da ƙarewa Anum kallo, tasani Allah ne ya haɗa jininta da na Anum amma kuma idan aka ƙyamaceta tana matuƙar jin takaici da ɗacin rai,
Abu ɗaya ne yake firgitata da Anum bai wuce gabanta dake nuna alamun akwai halittar namiji a jiki ba, sai gashin bakin dake yawan fitowa, to idan ta ɗauki tsawon lokaci bata da abinda zata aske fa? Duk da dai ta siya mata man shafawa a gurin, ga nonuwa suma tubarkalla abin da sai dai ace Allah buwayi gagara misali" ta mayar da kanta kan pillow ta kwanta zuciyarta ta kasa nutsuwa da zamanta a gidan,
Washe gari kiran sallahar farko a kunnen Anum, ta tashi zaune tana rarraba idanu, ɗazu Jannat ce ta nuna mata inda zatayi ta kunna pampo yanzu kam koda taje ba iyawa zatayi ba dan tama mance, "anty Jannat tashi asbha tayi, dan Allah taimaka min da kunna pampo" jannat ɗin ta buɗe idanunta tare da tashi ta zauna kana ta mike ta je toilet ɗin ta kunnawa Anum ɗin sannan ta fito, Alwalah tayi kana ta fito,Jannat ta shiga, kasancewar tun jiya da safe ta fara sallah, tana fitowa tayi tsaki tare da cewa "dole ki sauya sallahar nan idan har ba so kikeyi a dinga kiranki da sunan namiji ba"
Tama mance Jannat tayi mata faɗan yin Sallah babu hijabi, batace komai ba ta zuge zip na jakar kayan da Jannat ɗin ta bata sannan ta ɗauko ƙaton hijabi tasa a kaikaice sannan ta kabbara sallah, tana yin sallama ta yakice hijabin, sannan ta fara adu'oi, gabaki ɗaya ɗankwalin kanta ya isheta, ta cire shi ta ajiye a gefe, Jannat na idar da sallah tana shafa adu'a tace "Anum wannan wane irin abu ne, kina neman ki janyomin duka ne ko? wlhi tallahi inhar suka gano suffar da kike kin shiga uku tunda bakiji abinda na gaya miki ba koh?"
Anum ta dinga bawa Jannat haƙuri zuciyarta babu daɗi,
Suna cikin tattaunawa mom ta turo ƙofa, Allah ya taimaki Anum ta ɗaura ɗankwali, bayan sun gaishe ta, tace "Anum tazo mu shiga kitchen yau zata fara aiki, sbda zuwa yamma dad yana hanya" jiki a sanyaye Anum ta miƙe tana kallon Jannat, mom ta riga da tayi gaba, a hanyar da zai sadaka da kitchen ta tsaya Anum ta taho ta sameta a gurin, abin ya matuƙar bata mamaki duk wasu abubuwa da take tunanin koyawa Anum ta iyasu, sakamakon yawan karance karance da takeyi, a safiyar yau ita ta haɗa musu breakfast mai rai da lafiya, dukkansu suka hallara a dining har dasu Jumayma da Arshi, sosai Jannat da mom suketa santin abincin, yayinda Arshi ta miƙe da gudu tana riƙe da wuya sai kakatun amai takeyi, hankali a tashe mom tayi gurinta, Jumayma ma ta rufa mata baya, kai tsaye ta wuce toilet ɗinsu ta fara yunƙurin amai amma yaƙi zuwa, idanunta sunyi jajir ta ɗago ta kalli Mom kafin tace "nikam bana son cin wannan abincin momy gaskiya a sauya wannan ƴar aikin" mom tace "ke Arshi bana son iskanci in zaki nutsu ki nutsu babu inda zataje" Jumayma ta wani harari mom kafin tace "komai na naɗe a memory idan Dad ya dawo zai ji labari da ɗuminsa"
Mom tace "yanzu ma zaku iya kiransa ku gaya masa"

Anum da Jannat kam abin yafara fin ƙarfinsu, Jannat sai kwantarwa da Anum hankali take tana rarrashinta, damuwarta bai wuce Jannat ɗin ta tafi ta barta ba, tasan zatasha baƙar wuya a gurin yarannan,
THAILAND
Yangon

Ko parking space granny ta kasa yiwa Arya rakiya, sai kuka take harda majina.
Tana zuwa parking space ta shiga ƴar madai-daiciyar motarta fara mai kyau sannan ta ajiye kayanta a backside handbag ɗinta a kusa da ita, sannan tayiwa motar key, a hankali ta fice daga gidan yayinda ta hau titi ta fara gudu kamar zata tashi sama, tun kafin ta shiga mota take gwada number Khair shiru a kashe, duk da tanajin karayar zuciya sai ta basar ta hanyar ƙarfafawa kanta, tayi nisa sosai a tafiyarta wayarta tayi ringing "tana driving da hannun dama ta riƙe wayar da hannun hagu tare da sanyawa a kunne bayan ta danna kore "Granny ina hanya ne zan kiraki idan na sauka" cikin dakusashuyar murya Granny tace "Arya ki riƙe waya karki katse ki dawo gida bana son kema in rasaki please Arya karki ƙarasa gurinsu" wani irin ƙara Granny taji ƙiiiiiiiiii, hankali a tashe ta kalli wayarta da number Arya taga kuɗi nata tafiya amma bata jin motsin komai sai numfashi mai kama da kuka, ido waje Granny ya zaro tare da tsala ihu tana cewa "wannan wace irin ƙaddara ce, Ubangiji ka kawo mana komai da sauƙi shikenan sun kashe Arya" hawaye wanda ya ninka na da ya fara zarya a kumatun Granny, ta taɓi zaninta da ya jiƙe da fitsari, kan kace me ta saki tusa kamar ɗazu Booom, kasancewarta mai saurin shiga ruɗu,
Tana ƙoƙarin yakice zanin jikinta wayarta tayi ringing, ganin number Arya yasa ta yin saurin ɗagawa sai yarari take da fitsari, "Arya babu abinda da dai sukayi miki ko?"
"Muryar Arya na cikin firgici tace "Granny ban ma kai ga zuwa gurinsu ba, na bige wata budurwa ne wlhi har taji ciwo yanzu ma hospital zamu wuce" Granny tayi ajiyar zuciya Kafin ta cire zanin ta sanya a bucket sannan tace "to alhamdulilah ya jikin ita yarinyar" Granny zan kiraki anjima ko numfashi batayi" Granny ta zaro ido tana shirin yin magana Arya ta katse kiran, Budurwar sa'ar Arya ɗinne koda zata girme mata bai fi da one year ba dan ita kanta Arya ɗin zatayi 20yrs, hankali a tashe Arya ta riƙe hand bag ɗin dake rataye a kafaɗar yarinyar sannan ta fara ƙokarin goge mata jinin dake zuba a hannunta, cikin ƙarfin hali da jarumtaka ta turata a mota sannan ta rufe, tana isowa hospital batayi ƙasa a guwaiwa ba gurin kiran ɗan uwan Granny dake aiki a hospital ɗin kuma jam'i ne na sirri, a harabar Asibitin yazo ya sameta hawaye ya gama wanke mata fuska, kasa cewar tayi masa bayanin komai da taimakonsa aka kwantar da Budurwar tare da fara bata kulawar gaggawa, bayan wasu lokuta Likitoci suka sanar musu hannunta ne kawai ya samu matsala sai kuma ciwon jiki amma babu wani abu da ya sameta bayan haka, Arya da ɗan uwan Granny suka fito waje, cikin sanyin murya tace "Monir muna cikin matsala ga wata ta sake afkuwa" cikin rashin fahimta ɗan uwan Granny da ta kira da Monir yace "ban gane mai kike nufi ba, wace irin matsala?"
"Khair shida abokansa suna hannun Leela sannan ga wannan wace na kawo, zata tsallaka titi na bigeta ban sani ba"
Arya tai maganar muryarta a raunace,
"Subahanallah mai ya haɗa su Khair da Leela kuma, ita wannan ai ko yau ana iya sallamarta, matsalar dai bata wuce na su khair ɗin ba" ta share hawayen da suka zubo mata kafin tace "zan taimaka masa koda zan rasa rayuwata" Monir yai murmushi kana yace "ki dai yi fatan rabuwa da Leela lafiya dan idan ka shiga gonarsa faɗansa ba mai ƙarewa bane"
Sosai Monir ɗin ya sake ƙarfafa mata guwaiwa tare da bata shawarwari,

Bayan fitar su Arya Budurwar dake kwance kan gadon asibitin ta ciro wayarta wata ƴar mitsitsiya a cikin aljihun skirt ɗin jeans na jikinta, ta danna wata number, magana takeyi ƙasa-ƙasa wacce nima bansan me take cewa ba, tai saurin mayar da wayar cikin aljihu kana ta koma ta kwanta kamar inda suka barta,
A tare suka shigo, ko wanne fuskarsa ɗauke da tausayi, hannun Monir riƙe da leda mai kyau wanda kayan marmari ne a cikinta, har suka zauna bata buɗe ido ba, Monir ya ɗan taɓi ciwon hannunta, buɗe idanu tayi a hankali tare da yamutsa fuska ta kalli Arya sannan ta kalli Monir ɗin kana ta saukar da idanunta ƙasa, "ya ƙarfin jikin?" Arya ta faɗa tana yiwa Budurwar murmushi, itama murmishin tayi kana tace "yayi sauƙi" haka ma Monir yayi mata ya jiki tare da gaya mata sunansa sannan ya faɗa mata sunan Arya, wani irin kallo tabi Arya dashi, wanda dukkansu basu san tayishi ba, kafin ta ƙirƙiro murmishi, Arya tace "baki faɗa mana sunanki ba"
Sai da ta cije lips kafin tace "Anan" Monir yace "suna mai daɗi, kafin yaci gaba da cewa ina tunanin yau za'a sallameki anjima ai zaki iya zuwa gida ko?" Anan ta wani marairaice murya kafin tace "bani da kowa iyayena dangina duk ya kashe su" Monir yai saurin cewa "waye?"
Bakinta na rawa tace "lee..Le ..la"
Monir ya kalli Arya kana suka kalli Anan a tare...!

Page 8

Gobe akwai zazzafar cakwakiya da safe zan ɗora page 9 a arewabook ammafa idan kukayi following ɗina tare da comments 👇
https://arewabooks.com/u/momislam11



"Turr da wannan mummunan hali irin na Leela, ya zamo shaiɗani azzalumi marar tausayi da tunanin abinda zuwa gaba zai riska"

Arya ta faɗa tana tafa hannayenta,
Da sauri ta matso kusa da Anan, cikin sanyin murya tace "idan har kina ganin kin shirya ɗaukar fansar abinda yayi miki a shirye nake da in taimaka miki" Anan ta gyaɗa kai da sauri, kafin ta share hawayen dake sintiri a fuskarta, sannan tace "na amince, hakiƙe ke Alkairi ce" Anan ta faɗa tana ƙoƙarin ɗago hannun ciwon.
"Amman dai yanzu bakya jin ciwo a jikinki koh?"
Monir ya tambayeta.
"Eh sai dai hannuna da yake yimin ciwo amma babbar damuwata shine inda zan nufa" takai ƙarshen maganar tana sake fashewa da kuka, Monir ya matso kusa da ita tare da dafa kafaɗarta cikin ƙarfafa mata guwaiwa yace "tabbas idan aka daure aka jure sannan aka jajirce za'a iya cin galabar Leela abin abin tsoron anan shine, idan shine yaci galaba fa?"
Arya ta matso kusa dashi, sai da ta sauke gauron numfashi kafin tace "bana tunanin hakan"

Sun daɗe suna shawarar inda zasu ɓulowa lamarin, har doctor ya shigo ya rubutawa Anan sallama tare da magunguna, ganin takarda mai nuna alamun an biya kuɗi yasa Arya kallon Monir kafin tace "kaine koh?" Gira ya ɗaga mata tayi masa godiya kana sukaci gaba da shawarwarin har zuwa ƙarfe 3:pm,
"Yanzu tunda case ɗin Anan ya shigo ciki dole ku koma ku sake shiri saboda cimma nasara a tafiyarku"
"Eh Monir hakan za'ayi amma inason ka taimakeni da nemo wasu muhimman bayanai akan Leela shima hakan nasan zai taimaka mana koh Anan?"
Arya ta faɗa tana kallon Anan.
Anan ɗin ta gyaɗa kai tana jingine da jikin bango dan ta tashi zaune,

"Babu damuwa Arya zanyi komai cikin hikima dan Allah ki kula da Anan Please kinsan yanzu dole ta zamo tana cikin ƙarkashin kulawar mu" Monir ya faɗa yana kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa.
Arya ta gyara zaman gashin kanta da ya zubo mata har fuska, duk da mayafin da tasa ta yane kanta dashi, kafin tace "zan kula da Anan kamar inda zan kula da kaina Please ka duba mana duk abinda ka samu ka turomin Whatsapp zamu zama cikin shiri"
Ya amsa musu da "toh" kana yace su fito tunda anyi sallama,
Anan bata samu damar cin komai ba, har sai da suka shiga mota ta ɗan ci apple suka ɗaga masa hannu yayinda Arya tayiwa motar key suka wuce.
"Yanzu ina kike ganin zan ajiye ki" Anan da ta gaji da gayawa Arya damuwarta tace "bani da kowa" Arya ta juyo ta kalleta kana ta mayar da hankalinta ga titi sannan tace "shikenan zan wuce dake gidanmu nima ina tare da kakata ne, tun bayan rasuwar iyayena sunyi hatsari a zuwa bikin cikarsu shekara goma da aure, an rasa ya akayi hatsarin ya faru, daga ƙarshe ba wani tsananta bincike akayi ba, ni kaɗai ce na rayu kuma ni kaɗai suka haifa, ban bi motarsu ba, ina tare da granny, shikuma Shakur da mahaifinsa da mahaifina uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, Kinga ta inda zumuncinmu ya ƙullu ko? duk a tare iyayen namu sukayi hatsarin, shine kakarmu wato mahaifiyar su babanmu ta ɗaukemu muke tare da ita, gashi Shakur ya faɗa hannun Leela nayi alƙawari rayuwarsa bazata wulaƙanta ba, sbda ina matuƙar sonsa shine mafarkina"
Tunda Arya ta fara bada labari, Anan take ta kallonta cike da tausayawa kafin daga ƙarshe tace "Allah sarki Allah ya gafarta musu" Arya ta amsa da "Amen lokacin tayi kwanar shigowa anguwarsu,
Koda Anum taga zubin gidan nasu tasan ba talakawa bane su ɗin, sannan kuma ba za'a kirasu da hamshaƙan masu kuɗi ba, Granny na daga kan bed a kwance taji motsin tsayuwar mota, daga ita sai gajeren wando ta fito tana cewa "oyoyo Shakur ina fatan dai Arya babu abinda ya samu Shakur?"
Arya ta dafe goshinta tare da takowa tazo kusa da granny ta dafa kafaɗarta cikin tausasa murya gami da kwantar da hankali tace "ba tare muka dawo ba, Granny ki tayani da murna yarinyar da na bige har nace Miki zamuje hospital itama su Leela ne suka kashe iyayenta, Kinga na samu mai taimakamin,mun rabu da Monir ma yace "mu tsaya muyi komai cikin nutsuwa sannan yace zai taimaka mana"
Granny ta sauke ajiyar zuciya Kafin ta kalli Anan dake zaune gaban mota tana ta watsa da yatsun hannunta, Granny tace "tare da ita kenan zamu zauna?" Eh Granny inason mu haɗa aikin da ita ne"
Arya ta faɗa tana waigen anan ɗin.
"Toh shikenan kice mata ta fito" sai a lokacin Arya ta lura da ɗan gajeren wandon dake jikin Granny ta tuntsure da dariya tana cewa "Granny kin ganki kuwa" sunkuyar da kanta tayi ta kalli wandon kana ta ruga da gudu tana cewa "Arya kwai shegiyar yarinya yanzu wandon nawa kikeyiwa dariya ai na mance dashi na fito"
Anan ma dake cikin mota, da ta ɗago kai yanzu ta sheƙe da dariya, ganin Arya ta taho zata buɗe murfin motar yasa Anan ɗin daidaita nutsuwarta,
"Ki fito barkanki da zuwa gidanmu Allah yasa zaki iya zama da granny dan akwaita da yawan surutu" Anan tayi dariya kafin tai rau-rau da idanu, kafin tace "Allah sarki harda kakata mai sanyani nishaɗi mutanen Leela suka kashe" sai kuma ta kawar da kanta gefe,
Sosai Arya take tausaya mata, duk da tausayin kanta da takeyi na rashin iyaye sai taga ai gara ita tunda tanada Granny gashi sam bata son taga ɓacin ranta.
Riƙe da hannun juna suka ƙaraso cikin gidan, kai tsaye babban parlon Granny suka shiga, tana kitchen tana haɗo musu abinci, Arya tace "ina zuwa barin duba mai tsohuwar nan take yi ne" Anan tayi mata murmushi.
A tare suka dawo da Arya da granny duka hannun su riƙe da tray wanda aka jere abinci a kai da ruwa, a saman carpet suka ajiye, tare da ruwan wanke hannu, Anan tayi musu godiya lokacin da granny take ce mata ta sauko suci abinci.
Sunaci Granny na basu labarin abin dariya sai dariya sukeyi har sukaci suka ƙoshi.
Arya ta kwashe kayan abincin takai kitchen kana ta dawo tace wa Anan "muje ɗakina" granny tace "babu inda zataje sai ta bani labarin ahalinta" Arya ta ɓata rai kafin tace "a yanzu dai hutawa zatayi sai dai zuwa gobe" Arya ɗin ta kalli Anan tace "ki sha magani kiyi sallah sai ki kwanta"
"Toh" Anan ɗin tace dan ita ba musulma bace bama tasan ya akeyin sallahar ba, amma ta ƙudurta a ranta zata dinga kallon inda Arya ɗin takeyi itama ta dinga kwatantawa saboda kar Arya taga gane bata sallah tasan ƴan garin da riƙon Addini basa son munafurcin addini musamman ita da take son zama cikinsu.
A tare suka shiga ɗakin Arya ɗin, suna shiga Anan ta nemi guri a saman bed ta kwanta, Arya ta fara zuwa tayi alwalah ta fito, Anan ta ƙare mata kallo na tsanaki kafin ta kalli ƙafafuwanta suma taga a jike suke, tana kwance Arya ta kabbara sallah, sosai ta mayar da hankali ga abubuwan da Arya ɗin takeyi har ta kammala, sannan ta miƙe ta shiga toilet ɗin, ta daɗe a tsaye daga ƙarshe ta shafa ruwa a fuskarta kana ta shafa a hannunta da ƙafafuwanta sannan ta fito, lokacin Arya ta riga da ta fita, hakan ya bata damar sakewa sosai bata yi sallahar ba, amma ta zauna kan sallahya ta ɗaga hannu sama sai motsi take da bakinta, ko me take cewa oho, daga ƙarshe ta cire hijab ɗin ta ninke ta tashi akan sallayar kana ta dawo kan gado ta kwanta,
Hayaniyar da taji a tsakar gida ne yasa ta fitowa da sauri, a bakin ƙofa ta tsaya tana rarraba idanu, "Arya ki bari nace miki cikina har yau be gyaru ba mai yasa zaki yi mana abinci wanda nan da nan zai sake rikice mana ciki?"
Granny ta faɗa tana lallatsa wayarta,
"Ki kwantar da hankalinki kamar kin mutu" Granny tabi Arya da gudu har tana faɗuwa sabda santsin ɓawon ayaba da ya kwashe ta ji kake Timmm ta tsala ihu tana cewa "ke baƙuwar nan zoki ɗagani ki dubamin cinyoyina ko wata tsokar ta fice dan naji naman cinyata yana ƙuluf-ƙuluf" Anan ta taho da sauri tana cewa "Arya zomu taimaki Granny mana"
Kafin Anan ɗin ta ƙarasa idda magana Arya ta fito ta kama Granny suka ɗagata, cikin hikima Granny ta dage ta mintsini Ayra a hannu, Ayra dake riƙe da ita sun kusa zuwa ɗaki ta saketa a ƙasa, dama tafi Anan ƙarfi tunda ƙirar jikinsu ma ba ɗaya ba,
End Ads