x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - AUREN WATA SHIDDA

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 33392 words

Category: Romance Story +18

Views 116

02 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ya mutune"
Sbd ko motsi bataga yanayi ba "ahanzarce , Had'e da kid'ima ta nufi gefen gadon tana cewa Yaya Abdallah!Yaya Abdallah!!yaya Abdallah!!!Amma shiru Kuma Yana kallonta.
Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un kawai take maimaita wa had'e da Kama hannunsa Amma saitaji hannun asake kamar matacce"zaro ido tayi ta girgiza sa"tana cewa kayi mgn Dan ALLAH!
Hawaye tagani na zuba ta gefen idonsa hakan ya tabbatar mata yanada Rai" wani mummun abune ke Shirin samunsa koma yasamesa"runtse idanunta tayi sbd tuna mafarkinta nad'azun!da sauri ta saki hannunsa ta fice dg bed room d'in cikin tsantsar tashin hankali....
Yyinda Abdallah yyi zugudum akwance sbd ko hannunsa baya iya d'agawa balle Kuma yyi mgn "azatonsa ma ko mutuwa zaiyi,gashi yanajin maganar riyan Amma baya iya mgn shi,ko tashi balle har ya iya tafiya"abinda kawai yake iya amfani dashi ajikinsa....IDO..tun bayan sallar asuba ya kwanta bacci yyi wani mafarki da wata dattijuwar mace kyakykyawa tana kiransa Yana kok'arin zuwa Amma ta Masa nisa ga Daddy nason yaje gunta ga mom najan hannunsa ta hanasa zuwa da k'yar ya fisge hannunsa dg na mom zai tafi Gurin matar sai yaga Rami gabansa zai abka sai riyan tayi saurin rik'e sa... adedenan ya farka !Amma me ?sai yajisa cikin bak'on yanayin dabaitab'a riskarsaba arayuwarsa.
Yyi yayi yatashi ta kasa Koda motsa hannunsa balle bakinsa dayyi tamkar anrufe masashi "ambaton ALLAH kawai yake ana cikin hakan riyan ta fad'o dakin"to Wai meke Shirin faruwane Dani?"yafad'a azuciyarsa....

Riyan cikin tashin hankali ta kutsa Kai parlourn Abba "bbu ko sallama"akidime ta dubi Abba dake dining area tsaye Yana Shirin hadawa mom tea , yyinda mom ke zaune busa kujera 1 dake gaban dining table d'in"Abba! Abdallah..ne ..ne bashi...bashi... mitttsss dallah inzakiyi mgn kiyi inbazakiyiba ki fice kibawa mutane guri"cewar mom tana watsowa riyan muguwar harara"
Yyinda Abba gabansa yyi mummunan faduwa "da sauri yace lfy dai ko?meyasami Abdallan??"
Cikin kidi'ma tashiga sanar dasu...LA'ILAHA ILLA ANTASSUBA NAKA INNI KUNTI MINAL ZALIMINA!WALAHAULA WALAQUWATA ILLA BILLAH... abinda Abba keta maimaitawa, yyinda mom ta kurma uban ihu had'e da cewa nashiga ukku ni hafsatu"meya ke Shirin samunka Abdallah?"
Shiru riyan tayi tana dubansu kawai,kafin Abba cikin tashin hankali Yadubi mom yace muje mugansa...


Yadda tabarsa ,haka suka samesa!da gudu mom ta nufesa tana kuka da surutai tana girgiza sa da Kiran sunansa cikin zubda hawaye, yyinda Abba ketsaye gaban gadon yana kallonsa cikin tausayi da son D'an nasa tilo guda aduniya, idanunsa sunyi jajir "gefe guda Kuma riyan itama hawaye take sbd tausayin Abdallah,takuma k'ara Imani da ALLAH meyin yadda yaso alokacin dayaso "jiya iwar haka take fito Masa da kayansa har Yana cewa ta canza,Amma yanzun dubesa shida matacce banbanci kad'an me, lallai mutum ba'akin komai yakeba agurin ubangiji zaibaka lfy da rashinta assada yaso.... maganar Abba ce ta katse Mata tunani,daya ce bara na Kira ya'u direba da Hafiz abokinsa mukaisa asibiti "
Gimtse fuska mom tayi had'e da sakin Abdallah dake jikin ta ,ta maidasa kwance tace ah ah Alh basai anwani Kira Hafiz ba akiradai ya'u direba d'in"
Ok" yafad'a atakaice kafin ya fice da hanzarinsa...
Kallon Abdallah mom tayi taga yarufe ido,jikinsa ta duba taga jallabiya ce Fara yasaka,da alama da ita yyi sallar asuba kenan..
Cikin kuka tace Abdallah kana mgn ko baka iyawane?Kuma kanajina be?"
Cikin mamaki riyan ke sauraren wad'annan tambayoyi na mom dasuke da alamar ayi Mata itama tambaya"
Abin mamaki sai Abdallah be bud'e idonba koya motsa bakinsa"hakan yasa tasaki kuka tana cewa wayyo ALLAH yanxun ko ji da mgn bakayi Abdallah"
Oh ALLAH yabaaka lfy!

Kallonta ta maida akan riyan dake hawaye"cikin hantara da tab'e baki tace to ke asuwa kike kuka?"

Girgiza Kai riyan tayi,sbd yau taji kwata kwata yau bbu tsoron mom atare da ita.

Kai tsaye tace ,Ina kuka sbd Ina tausayinsane dakuma tausayin wasu mutane na cikin duniya dake zalinci da cin Amana basa tuna ranar da ALLAH zai kamasu ,yyi musu hukunci,wato a.....ke dallah rufemin baki!dak'kiya!uwar me kika sani,dazakice zakiyawa wani waazi....hmmm kiyi hakuri hjy Ni bance Miki inawa wani waazi ba... mittsss mom taja tsaki hade da cewa kikulamun da yaro na canxo kaya mutafi asibiti ta fad'a had'e da shafa kan Abdallah ta fice...

Abdallah kuwa duk abinda sukeyi yanajinsu da tambayar mom data Masa, sannan da amsar da riyan ta Bata yatsaya Masa arai yakuma yiwa amsar tata fassarori da yawa,saidai Kash bazai iya mgn ba ,balle ya tambayeta dalilin bawa mom wanna amsa...

Mom na fita"da hanxari riyan ta d'auki d'aya dg cikin wayoyin Abdallah dake kan bed side dirowa" talalubo number in Hafiz sbd tasanar Masa"aganinta Hafiz be kamata ace besan meke faruwa ba" tasaka Kira bugu2 yad'aga Yana cewa my man....bashi bane riyan ce...nan tashiga sanar dashi abinda yafaru...cikin tashin hankali Hafiz ke ta salati had'e da cewa dama Ina hanya bara na k'araso....ah ah yah Hafiz kabarshi,yyi saurin cewa meyasa?
Kallon Abdallah tayi haryanzun idonsa arufe...abinda Bata saniba! duk yanajin ta ,yaji dad'in sanarma da Hafiz datayi " cikin inda inda tace um muhade a hospital sbd can zamu!ok yace had'e da datse Kiran domin yagane cewa cikin2 dole guda ko mom ta hana asanar Masa ko Kuma tana Gurin ta nuna bataso yazo...
Riyan kuwa tak'i fad'a Masa mom ce taha na sbd ganin Abdallah k'ila yanaji tasan Kuma bazaiji dadiba....saurin aje wayar tayi sbd jin motsin za'a shigo.,,,,,,

Mom ce da Abba,abayansu ya'u direba ne,cike da tausayawa suka Kama Abdallah suka fito da shi sbd asakashi mota,juyawa riyan tayi sbd taje ta sako hijab tabisu"mom ta dubeta had'e da cewa Ina zuwa?"

"Xanje nasaka hijab be"ta fad'a atakaice.

Baza kijeba , sbd zuwanki beda wani amfani agaresa ko agaremu,Bata jira amsarta ba ta fice dg d'akin"

Shiru riyan tayi had'e da Zama ,tana mamakin halin mom"kafin ta d'auki wayar Abdallah tasaka number in umma ta Kira.

sallama umma tayi ,muryar riyan taji"murmushi tayi tace oh riyan kwana2 ya gdn?nan suka gaisa cike da alhini riyan ke sanar da umma lalurar datashafi Abdallah..

Cikin tausaya had'e da damuwa ,umma ta jajanta Mata had'e da cewa insha ALLAH acikin satin nan zatazo taga Abdallah d ajikin,nan suka Yi sallama umma nata kwantar Mata da hankali.

**** **** ****
Hafiz byn sun gama waya da riyan,Kai tsaye asibitin da amminsa ke aiki ne yanufa sbd yasan da wuya Suki zuwa can sbd tafi kusa dasu Kuma asibiti ce maitsada da kula.

Office din ammin yanufa ,tana duba patient,amatsayinta na babbar likita k'wararra"da mamaki ta amsa sallamar sbd basudade da rabuwaba yazo gaisheta"saidai yanayin data gansa tasan tabbasa bbu lfy! agaggauce ta sallami patient d'in"kafin ta dubesa tace lfy dai ko Hafiz?"

Cikin damuwa had'e da tausaya wa ,yashiga yimata bayanin matsalar Abdallah.

Kafin tayi mgn anyi Knocking"

Yes "kawai tace,wata nurse ta shigo had'e da cewa Dr kije emergency da gaggawa anason ganinki sbd ankawo wani patient Kuma doctor's da yawa akeson sutsaya akansa!

Ok kije ganinan zuwa"cewar ammin (Dr naja'at haruna)ta fad'a had'e da mik'e wa tsaye tasaka farar riga saman hijab nata ,kafin ta dubi Hafiz tace bara naje k'ila Abdallah ne.


Tashi yyi hade da cewa to mom muje nima na gansa"

Atare suka fito har zuwa kofar da zata sadaka da shiga emergency d'in... adedenan suka Sami Abba da mom had'e da ya'u direba, suna Kai komo" kallo d'aya zaka musu ka gano tsantsar tashin hankali acikin idanunsu....


Gun Abba Hafiz ya nufa , yyinda ammi ta nufi ciki kawai,dukda ta lura da mom na Mata kallon sani ,Amma saita waske ta nunama batasanta,dukda cewar akwai abota mai k'arfi atsakanin yaronsu to Amma basu tab'a ganin junaba,dukda ita ammin tasan mom ce mahaifiyar Abdallah .

Rungume Abba Hafiz yyi Yana kuka tamkar karamin yaro"

Bubbuga bynsa Abba keyi cikeda da rarrahi yace kayi hakuri insha ALLAH abokinka zai Sami lfy "addua zami yimasa ba kukaba"cikin gamsuwa Hafiz ya d'aga Kai.

Gum mom ya isa ,ya gaida ita, had'e da Mata jaje"

Fuska bbu yabo bbu fallasa ta amsa,tana mamakin ya'akayi yasani?"kasna zuciyarta nace wa Anya waccen matar ba naja'at bace?

Da wannan tunanane tunanen takira hjy ikilima ta sanar da ita halin dasuke ciki"
Sannan suka zauna jiran fitowar doctors din dake kan Abdallah.

Hafiz kuwa office d'in ammi ya koma , yafito da wayarsa yakira layin Abdallah da riyan ta kirasa dashi yaji miyasa batazo asibitin ba.

Riyan dake zaune jugudum a parlou..taji wayar na ringing,dubawa tayi,ganin Hafiz ya sakata saurin d'agawa,bbu wani boye boye tasanar dashi mom ta hana, girgiza Kai yyi had'e da kashe wayar"

#######

Kusan awa3 da wani Abu dashigar da Abdallah ,amma bbu wani Dr daya fito duk sub abba sunyi jigum jigum,tun safe ga shi har 1:saura.
Nan wasu doctors 2 suka fito suna sharce gumi"da hanxari Abba yanufeso har Yana tuntub'e"mom na Mara Masa baya
,Har suna had'a Baki Gurin cewa Yaya jikinsa?meke damun da?"

Girgiza Kai sukayi had'e da cewa ku kwantar da hankalinku,Dan ALLAH!yanxun zamuje muyi Sallah kafin mu ida bincikenmu "

Jiki asanyaye Abba yace to shikenan,kafin Yadubi mom cikin damuwa yace bara naje nayi Sallah,kiyi waya agd akawo wani abun bukata"

To "kawai tace,kafin ya fita"


Tana nan zaune Hafiz ya iso gurinta,Yana cewa mom Yaya dai jikin nasa?"

Cikin yatsina tace da sauk'i, had'e da cewa zaman me kake a hospital d'in nan?

Cike da mamaki azuciyarsa,yake sauraronta,Amma be nuna ba,sai yace na tsaya sbd naji yajikin Abdallah ne..Kuma nima ammina,wato mahaifiya ta anan take aiki..da sauri tace ko itace naja'at Musa ?"
Har zai ce eh ,sai kawai yatsintsi kansa da cewa ah ah itadai Dr naja'at haruna ta ke"

Ajiyar zuciya mom tayi ,wadda basan cewa hafis yajiba,tace ok inaga kamace.


Shikuwa Sarai Hafiz yasan ada da naja'at Musa take bearing ,byn abbansa yarasu ta maida da sunan mahaifinta ,wato naja'at haruna.
Sannan ya boyewa mom ne sbd besan miyasa take son sanin ammice koba amminceba gashi tasaki ajiyar zuciya to meke faruwa ne?Amma in hankali ya kwanta zai tambayi a mmi d'in.

Sallama yyimata akn xeje yyi Sallah.

Bayan awa3,hakan yyi Dede karfe 3:25pm, doctors d'in sufa fito sunata sharce gumi.

Da hanzari su Abba suka taresu,Dr naja'at ta cire eye glass d'in ta tace kusameni a office"Bata jira amsarsuba ta nufi hanyar office d'in ta da wani likita ,da alama ita dashi ne zasuyiwa su Abba bayanin ciwon dake damun Abdallah.

Babu Bata lokaci su Abba suka rufa masu baya zuwa office d'in.

Share

BY
MMM FAREESA
๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

๐ŸŒบ AUREN WATA SHIDDA๐ŸŒบ

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ


Story & written by mmn fareesa


Wannan shafin nakine halak malak Queen minart๐Ÿฅฐ๐Ÿ˜˜ kiyi yadda kikeso dashi...


Not edited

P 25

""Bayan duk sun zauna koya ya nutsu"kafin Dr naja'at ta Fara mgn kamar haka...da farko dai Alh inaso kuyi hakuri ku maida lamarinku ga ALLAH ta hanyar karb'ar k'addararku daya k'addareku da ita! sannan kucigaba da Masa addua sbd shi ciwo lokaci guda yake shiga jikin mutum ,Amma sauk'i ahankali yake zuwa ind....ya isa haka pls kusanar damu Mike damun yaron mune?"cewar mom dake kallon Dr naja'at dake musu bayani"Dr naja'at Bata kalletaba da dubi Abba dake kallon ta tace maganar gsky Alh bazan boye maka ,munyi iya bakin kok'arin mu zurfafa bincike naganin munsan meye ke damun d'anka "Amma amsar guda ce"cikin k'osawa mom tace meye amsar?"
Dr naja'at ta cigaba da cewa binkicenmu yanuna Mana cewa Yana cikin koshin lfy!abad'ini kenan"azahiri kuwa idanunsa kawai ke aiki ajikinsa, sannan abinda muka gane yanxun na damun shine jininsa Yana kok'arin yahau, Kuma zuciyarsa na bugawa.
Hakan Yana nuna alamar cewa yasaka damuwa aransa ne,Kuma munyi kok'arin shawo kan wannan matsalar...salati kawai Abba ke maimaita sbd tashin hankalinsa yakaru akan nada, yyinda mom keta kuka da surutai..
Dr kamar yadora da cewa duk asibitin da zaku kaisa indai tsakani da ALLAH zasu gaya muku to amsar d'aya ce da nan "sannan ayanzun abincinsa yakasance me ruwane sbd be iya motsa bakinsa balle har yatauna abinci"zamu rik'e sa sai zuwa gobe musallamesa"Amma dai yanada iyali ko?"eh yanada Mata ,cewar Abba kafin mom ta yi mgn yarugata.
Dr Kamal yace ok to yakamata tazo kusa dashi sbd Yana bukatar kulawarta amatsayinta na iyalinsa,tunda yanxun komai sai anmasa.,,,,,

Insha ALLAH yanxun inmunyi la'asar zamuje adakkota tana gd"cewar Abba Yana duk'ar da Kai sbd ganin yadda mom ke jifansa da kallon tuhuma"


Gyaran murya Dr naja'at ta yi hade da cewa inada shawara Alh!

Abba yadubeta ya ce miye shawarar likita?

Gsky ciwon danku bana asibiti bane,ayadda na fahimta,ciwonsa na....ah ah dakata bamasan Jaye Jaye tunda kun kasa gane abinda ke damunsa inkun sallamesa zamu can za hospital ko mufitar dashi waje..cewar mom tana tashi tsaye.

Murmushi Dr naja'at ta yi domin yanxun ta lura mom ta daina Mata kallon sani,Kuma itama bazata nuna ta Santana,sai kawai tace to shikenan hjy ALLAH yasa adace" cikin Shan k'amshi mom ta ce Amin"sbd azatonta k'ila Dr naja'at ta ji shakkuntane...

Atare mom da Abba suka fice dg office d'in Dr naja'at.

Hafiz dke cikin toilet d'in office d'in yyi ajiyar zuciya sbd yaji komai ,ya fito zuciyar sa cike da tausayin abokin nasa.

Saurin dubarsa ammi tayi had'e da hararan sa tace har kabani tsoro,miye anfanin hakan kamana labe?

Murmushi Hafiz yyi had'e da cewa yi hkri ammi inason jin abinda ke damun AK ne"

Ok to kaje gd hakan nan tunda kaji,tun safe kake nan ,itama fiddausi yakama ta kaduba kaga halin datake ciki"

Zan tafi ammi Amma Dan ALLAH Zan tambayeki?"

Ina jinka "miye tsakanunku d hjy hafsat (mom) mahaifiyar Abdallah?"

Murmushi ammi tayi had'e da cewa meyasa kamun wannan tambayar?

Nan yashiga sanar Mata yadda mom ta tambayesa akan ta.....ajiyar zuciya ammi tayi had'e da cewa Zan sanar dakai wacece HASSU TSIYA TSABA! amma ba yanxunba ,abinda nikeso dakai kada ka nuna Mata cewa nice naja'at Musa,kanajiko?"eh ammi
Ok zaka iya tafiya...

*******

Abba d mom na fita takama balbalesa da masifa akan wane dalili zai ce Abdallah nada iyaline?"
Girgiza Kai yyi Kai tsaye yace basa abinci ,wanka , alwalla,kulada abinda yashafi tsiraicinsa ke Zaki kula Masa da sune?"
Tabe baki mom tayi had'e da cewa eh hakane muje to sai akawota nan d'in"ta fad'a. Cike da mamakin Wai yau Abba ke gaya Mata mgn a tsaye lallai da sake....
Saida suka sake zuwa d'akin da akaje Abdallah ,suka samu Yana bacci ga drip an d'aura masa
Kafin su fice dg room d'in sukabar ya'u direba agunsa....
Byn Abba yyi Sallah suka nufi gd shida mom...

Byn mom tayi wanka tasaka zulfa ayi Mata Kiran riyan.
๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

๐ŸŒบ AUREN WATA SHIDDA๐ŸŒบ

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ


Story & written
by mmn fareesa


Not edited

p 26

Riyan na zaune kan abin Sallah yana azkar,byn ta idar da sallar la'asar wacce ta dad'e tanama Abdallah addua ,kafin ta soma azkar yyinda k'asan zuciyarta ke tunanin Yaya jikin Abdallah da sauk'i ko bbu?"
Knocking d'in da taji ne yasaka cewa ashigo...byn zulfa ta shigo tasanar da ita Aiken mom kafin ta fice...
Tab'e baki Riyan tayi had'e da tashi ta ajiye cazbaza d'in,kafin ta fice ta nufi part d'in mom.",,,,,

Fuska bbu yabo bbu fallasa tayi sallama had'e da Zama kan carpet tace ganiiii!
Cike da mamaki mom ke dubarta sbd ta lura dg yau da safe zuwa yanzun wani hayak'in rashin kunya ko me Riyan keji,Amma sai Bata nuna mamakin ta,tadaiyi kwafa azuciyarta sbd gab riyan din take da barin gdn...
Ayatsine tace abinda Zan gaya Miki shine kishirya yanzun ki dauki abinda zaku iya bukata keda my son" acikin driver's din my son wani zai kaiki hospital gurnsa ki kula dashi kafin muzo anjima nida abbansa!
To insha ALLAH"riyan ta fad'a had'e da tashi ta fice"mom ta rakata da harara...
Bbu bata lokaci riyan ta shirya cikin doguwar riga ta amfa red tasaka hijab red,kafin ta fito taje bed room d'in Abdallah ta fito Masa da kayansa irinsu vest boxers jallabiya sbd tasan be wuce su mom take nufi ta fito Masa dashiba.... sannan ta Kira Hafiz tasanar Masa su had'u a asibiti "yace to...

Basu iso abitinba sai kusan 5:12pm "har room d'in da Abdallah ya ke driver d'in yanunama riyan , sannan ya tafi"cikin faduwar gaba ta murd'a kofar tashiga,bakin ta d'auke da sallama.... Hafiz ya amsa Yana kallon ta "byn sun gaisa ta ce yamai jikin?Yadubi Abdallah dake jingine da pillow bisa gado yace da sauk'i...
Matsowa tayi jikin gadon tana kallonsa tace yajikin?" ALLAH ya baka lfy" k'uri da ido yyi Mata Yana hongo tsantsar tausayinsa acikin k'wayar idonta,Wanda be tsammaci hakanba,azatonsa k'ila ma tace dole sai yasaketa Amma gashi ita rashin lafiyarsa tadameta....Yaya Hafiz ya ci abinci kuwa da wanka da Sallah???
Tambayar da riyan tayi ta sakashi dawowa tunaninsa,yanadaita aikin kallonsu..

"Ahankali Hafiz yace ah ah be jima da falkawaba ai"dama fresh milk ce da tea akace mu basa to komai dai akwai shi"to bara na had'a Masa tea din sai yyi Sallah da wanka.

Ok toshiken, Hafiz ya fad'a had'e da matsawa kusada Abdallah sbd byn farfadowarsa Yana Masa nasiha akan ya rungumi k'addararsa,dadai nasiha anan yafahimci yanajin mgn ,bede iyayinta"
Ahankali yace my man inason in sanar da Kai wata shawara Dan ALLAH inbacin nida riyan kada ka nunawa kowa kanajin mgn,inafatan kagane?"
Da ido Abdallah yace sbd me?
Hafiz yace Zan fad'a maka Amma da sauran lokaci... adedenan riyan ta iso da cup d'in tea mai kauri a hannunta ta dubi Hafiz tace gashito"
Gira ad'age yace nayime dashi?"
Kabashi yasha Mana"
Ke Kuma kiyi me Inna basa?"haba riyan! aike yakamata kibasa kinji"
Batace komaiba,taja kujerar roba Fara dake cikin d'akin ta matsa sosai kusada Abdallah dukda tanajin faduwar gaba ,haka ta daure, Hafiz ya d'ago kansa"had'e da bud'e Masa Baki har ya shanye duka Yana kallonsu da ido,kafin ta sake fito da fresh milk itama ta dura nasa , sannan ta basa ruwa yasha ...

Byn kamar minti12 , Hafiz ya fice dg room d'in"

Bbu jumawa yadawo shida wani doctor da keke me kujera suka Kama Abdallah suka aza akai"Hafiz ya shige dashi toilet sbd yyi arwala ya Rama sallolin dake akansa tunda Yana a haiyacinsa.

Bayan shigarsu riyan ta gyare gadon had'e da share room d'in sbd tasan Abdallah bayason k'azanta.


Bata jima da gamawaba suka fito, Hafiz ya saitashi ga alk'ibla yaga batarda Sallah dg zaune sbd lalurarsa...

Bayn ya idar ne Hafiz ya turasa acikin toilet , yafito Yadubi riyan yace kije kiyi Masa wanka"Amma kibi ahankali kada yashaki sabili inkin gama Masa ki fito ,sai nazo na fito da shi"
Zaro ido riyan
End Ads