x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 9 - EXILED PRINCE LOVE MEETS POWER BOOK 1

  • 24001 words
  • 27000 words
  • Out of 33271 words

Category: Love Stories

Views 158

25 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
kallon shi ya mike tsaye ya dawo gaba na ya zube saman guyiwowin shi ya ce min " don Allah Zayd ina son ka auri Inaya " a rude na mike tsaye ina fadin " what aure ? " mikewa malam ya yi ya na zaro idanu ya na kallo na ya ce " Zayd, dama ka na magana ? " ban amsa mishi tambayar shi ba na ce " uncle yi hakuri gaskia babu aure a sha'anin rayuwa ta bare kuma wannan yarinya ta yi min kannanta " komawa ya yi ya zube saman guyiwowin shi ya riko kafafuna ya roke ni da na yarda na aure ta in ba haka ba komai zai iya faruwa da ita kuma duk abun da ya faru da ita da hannu na a ciki tun da na samu damar ceton rayuwar ta amma na ki duk ya bi ya kashe min jiki ba yadda zan yi na yarda , a ranar a ka aure na da ita, limamin massalaci ya zama waliyi na, shi kuma malam na ta , na biya sadaki a ka aura mana aure , duk lokacin da na tambayi malam dalilin da ya sa a ka aura min ita sai ya ce min in bari in lokacin ya yi zan sani , dalilin da ya sa na ce yanzu ta dawo gaba na na dinga ganin ta ko zan gano dalilin da ya sa malam ya aura min ita " ya kai karshen ya sauke ajiyar zuciya ya dan lumshe idanun shi dan ba karamar wuya ya sha ba wajen yin wannan maganar duka , ji ya yi kamar harshen shi zai fado kassa


Jinjina kan shi Moussa ya yi kafin ya ce " yanzu me ka ke tunani a kai ? "

" duk yadda a ka yi akwai wanda ke bibiyar rayuwar ta , ka manta ranar nan ta na zaune ta fara sakin kara kamar wadda a ka dauke da karfi , wai ba ka lura da wasu abubuwa da ta ke kamar mara hankali ni ina jin yarinyar nan aljanu gare ta ma "


yar karamar Dariya Moussa ya yi kafin ya ce " O'O kenan ka na lure da duk wane abu da ta ke "

" of course ba matata ba ce " ya fada a takaice ya na mike wa ya wuce toilet

Da kallo Moussa ya raka shi har sai da shiga toilet sannan ya ce " matar ka ko , to za ka ga yadda zan yi wufff da ita dan rainin hankali "
Sai da ya ida sambatun shi sannan ya mike ya fice ya koma bedroom din shi

Bai jima da fita ba Zayd ya fito da ga cikin toilet ya yi Alwalla sannan ya nufi bedside drawer , ya dauki wayar shi ya sa cikin aljihu , ya kuma dauki wadanan bakake glass din shi ya saka sannan ya fito dakin kai tsaye corridor ya baro ya shigo falo
Inaya na nan zaune saman sofa ta na kallon Tv

Har ya yi gaba zai wuce ya tsaya cak a hankali ya juyo ya zuba mata ido
Ta na zaune waje guda kamar kungi ko kifta ido ba ta yi

Slowly ya tako ya tsaya gaban ta ya dan sunkuyo ya na kallon face din ta

Ko motsi ba ta yi kamar wanda ya suma

Yatsun shi biyu ya kai saitin face din ta ya kyasta mata

Da karfi zuciyar ta ta buga Ta ja wani dogon nunfashi ta yi baya ta fadi konce saman sofar ta na nunfashi sama sama idanu a lumshe

Shi duk ya bi ya rude ya rasa mai zaiyi ya tsaya kawai ya zuba mata idanu

Sannu sannu har nunfashin ta ya fara dawowa dai'dai
A hankali ta bude idanun ta ta na kallon ceiling din falon

A haka Moussa ya fito ya same su

Ya na ganin su a haka ya saki wani kyawatencen murmushi cikin ranshi ya ce " me kuma ka yi ma y'ar mutane ? "

Ya na gama fadar haka ya karaso geffen Zayd ya tsaya ya kale shi ya ce " Amir lafya wani abu ka yi mata ? "

Girgiza mishi kai Zayd ya yi ba tare da ya ce komai

Medo da kallon shi kan Inaya ya yi kafin ya kira sunan ta a hankali

" Na'am " ta amsa mishi ta na kallon ceiling din

" me ya faru ne ? " ya tambayeta ya na lekon face din ta

A hankali ta fara kokarin dagowa ta gyara zaman ta sannan ta ce " yaya Moussa ji na yi kamar an danne min zuciya, duk ta yi min nauyi "

Murmushi kadan Moussa ya yi kafin ya ce " shikenan ba komai har yanzu ki na jin hakan ? "

Girgiza mishi kai ta yi kafin ta dago kai a hankali

Idanun ta ba su sauka ko ina ba sai cikin nashi, shi ma ita ya ke kallon ta cikin bakin glass din shi

Da sauri ta sunkuyar da kan ta ta takure waje guda

Kai a sunkuye ta ga ya miko mata hannu

Da sauri ta dago kai ta kaleshi ta na son ta yi magana amma ta ki fitowa

A hankali ta medo da kallon ta kan hannun shi kafin ta dago nata slowly ta daura a saman na shi

Dum zuciyoyin su su ka buga lokacin guda , dalilin mi ? Oho su kadai su ka sani 🀣🀣🀣🀣🀣

Ta na daura hannun ta, ya janyo ta ta mike tsaye sannan ya juya su ka fara tafiya a hankali ya na rike da hannun ta

Sai da su ka shiga bedroom din shi sannan ya saki hannun da hannu ya mata allamun " ki shiga ki yi Alwalla ki yi sallat sai ki konta "

( WAI DAMA ANA MAGANA DA HANNU πŸ€”πŸ€” )

Jinjina mishi kai tayi ba tare da ta ce komai ba

Juya wa ya yi ya fara takawa har ya kai bakin kofar dakin ya tsinci Muryar ta, ta na fadin " a dawo lafya yaya Zayd ! "

Jinjina mata kai kawai ya yi ba tare da ya juyo ba ya ci gaba da tafiyar shi

Ya na fita ita ma ta juya ta shiga toilet din

Shi kuma ya na fitowa ya tardo Moussa zaune saman sofa ya na latsa wayar shi

Ya na ganin shi ya saki murmushi ya ce " na dauka , ka na cen ka na cin angoncin ka ka kyale ni nan "

Dan tsaki ya ja ya ci gaba da takawar shi zai bar falon

Dariya Moussa ya yi kafin ya mike ya bi bayan shi da sauri
Su na fitowa harabar gidan Moussa ya kaleshi ya ce " Amir ka gano abun da ke damun ta ne ? "

Sai da su ka fita gidan sannan ya ce " na gano nan gaba "
Jinjina mishi kai kawai Moussa ya yi su ka ci gaba da tafiyar su har su ka isa mosque

Basu dawo gidan ba sai bayan sallar isha, nan su ka isko ta gyara gidan tsab sai kamshin turare ya ke , har da abinci ta girka musu ta jera komai saman dining table

Kallon Zayd Moussa ya na murmushi ya ce " kai da ke cewa mu wuce restaurant mu sayo abinci, madam har ta shirya mana ashe "

Kauda kan shi gefe Zayd ya yi sannan ya ci gaba da takawa ya shiga corridor ya wuce bedroom din shi

Nan ma wajen a gyare ya ke sai tashin turare ya ke , ta share ko ina ta goge ta canza mishi bedsheet

Sai da ta gyara komai sannan ta yi wanka ta sauya kaya ta Haye bed din ta konta

Dan karamin murmushin geffen fuska ya yi sannan ya juya ya bar mata dakin dan ba ya son tada ta

Falo ya fito nan ya ga Moussa saman dining table sai cin abincin ya ke , kamar mai jin yunwa

Chair din da ke fuskantar tashi ya ja ya zauna sannan ya fara serving din kan shi dan shi ma fa yunwar ya ke ji , ya na iya jure komai a duniya amma banda yunwa shi ya sa duk irin fushin da zai yi bazai yi fushi da abinci ba

Bayan ya yi serving din kan shi ya deba a spoon ya kai baki
Sai da ya dan zaro idanu lokacin da ya ji taste din abincin, ba karamin dadi ya yi mishi ba

Duk abun da ya ke Moussa na kallon shi ta kassan ido, cikin ranshi ya ce " tukunna ma sannu sannu sai ta mamaye wannan zuciyar ta ka ta dutse "

Haka su ka ci gaba da cin abincin ba wanda ya ce ma wani kala har sai da su ka ida su ka sha ruwa su ka daura da juice sannan Moussa ya riga shi cewa " Amir gaskia da ga yau na daina cin abincin restaurant baby na zai dinga girka min "

Kallon shi da kyau Zayd ya yi kafin ya ce " wane baby kuma ? "

Dariya sosai ya yi sannan ya mike tsaye ya tatare dishes din ya gyara wajen ya meda su kitchen sannan ya dawo ya wuce falo

Sai da ya zauna sannan shi ma Zayd ya taso ya shigo falon ya zauna
sai da ya zauna sannan Moussa ya ce mishi " ba za ka je wajen ta ba ne "

wani irin kukan kura ne Zayd ya yi ya tashi da gudu ya nufi Moussa
amma kafin ya karaso shi ma Moussa ya tashi da gudu ya nufi dining room ya na fadin " lafiya malam da ga tambaya "

" Diya , wlh ka shige min hanci , wai ba zan iya yin rana guda ba , ba ka sa na yi magana ba , Har ka sa na zama perrot " Zayd ya fada ya na tsaye bakin dining room ya na kallon Moussa

dariya sosai Moussa ya yi kafin ya ce " Laifi na ne ? ni fa kawai ina taimaka maka ne ka kula da matar ka "

" i don't need your help , please let me , ka bar ni na ji da wannan jarabar da a ka gama ni da ita "

" wait ! wait ! Amir ka na jin abun da ka ke fada kuwa , yanzu matar ta ka , ka ke kira da jaraba " Moussa ya fada cike da rudu

wani iska mai zafi Zayd ya furza da ga bakin shi kafin ya juya a hankali ya koma falo ya zauna saman sofa ya jingina bayan shi a jikin forehead din sofar ya daga kai sama ya lumshe idanun shi

a hankali Moussa ya tako shi ma ya karaso cikin falon ya zauna saman sofa , ya zauna ya na kallon Zayd

a hankali ya ce mishi " Amir , na san abun da ke cikin ran ka , kar ka manta ni kadai ne abokin ka , ni kadai ne wanda ka ke shawara da shi , kuma ba zan ga laifin ka ba dan ka ce jaraba , na san ba ka cikin hayacin ka , ko ni a ka yi wa irin wannan abun sai na ce jaraba , amma wannan abun ba jaraba ba ce , kaddarar ka ce , yarinyar nan wlh ita ce kaddarar ka , na ji hausawa na cewa Matar mutun kabarin sa , dubi wace uwar duniya ka baro ka zo nan , kawai dan ka auri yarinyar ne , kawai ka karbi kaddarar ka hannu bibiyu , wlh za ka yi dadin rayuwar ka da ita "

cikin nitsuwa Zayd ya katse shi da cewa " please keep quiet , ina son na yi barci "

dan zaro idanu Moussa ya yi ya na kallon shi cikin zuciyar shi ya ce " iyeeeee , sannu su yarima , ba shakka ! za ka ga aiki na "

da ga haka ba wanda ya ce ma wani ufan har sai da Moussa ya koma bedroom din shi ya bar Zayd nan a falon





β–ͺMisalin karfe 12 na dare





Ya na konce saman doguwar sofa ya daura hannun shi guda saman goshin dayan kuma saman ciki ya lumshe idanun shi

Ya na a haka ya jiyo takun mutun, a hankali ya ware idanun shi dan dama ba barci ya ke ba kawai ya lumshe idanun shi ne

A hankali ya dago kai ya kali saitin da ya ke jin takun mutun din

Sai da ya dan zaro idanu ganin ta tsaye cikin wannan daren , ta na tafiya a hankali idanu a rufe

Ya na kallon ta har ta shiga kitchen

Da sauri ya mike ya bi bayan ta , ya na shiga kitchen din ya gan ta rike da wuka ta na motsa lips din ta kamar mai magana

Dan zaro idanu yayi a dubu dari ya yi kan ta ya karbe wukar har sai da ta dan yanke shi , dan rumtse idanun kadan ya yi ya sake budewa a kan ta

Ta na tsaye waje guda sai tangal tangal ta ke ido rufe

" wai me ya ke damun yarinyar nan ' ya fada cikin zuciyar shi

A hankali ya kai hannu ya dauke ta cak kamar baby ya juya ya baro kitchen din, kai tsaye bedroom din shi ya meda ta ya kontar da ita saman gadon sannan shi ma ya Haye ya konta ya na kallon ta , a haka har barci ya dauke shi





β–ͺWashe gari





Misalin karfe 4 ya safe ya farka da ga barcin shi
Ya na bude idanu su ka sauka a kan ta , ta juyo su na fuskantar juna ta na sauke nunfashi a hankali

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya a hankali ya sauko kafafun shi kassa sannan ya mike tsaye ya nufi closet din kayan shi ya bude ya dauki kayan shi wandon jeans light blue da t-shirt fara sannan ya fice dakin


Kai tsaye dakin Moussa ya wuce babu ko sallama ya shigo dakin kai tsaye ya wuce toilet
Shi kuma Moussa sai kwana ya ke da ga shi sai short ko shigowar Zayd bai ji ba , sai da ya fara jin saukar ruwa sannan ya bude idanun a hankali ya na motsi

Kallon kofar toilet din ya yi ya ga dakwai dan haske
Murmushi kadan ya saki kafin ya fara karanto adu'ar tashi da ga barci ya mike zaune .............................



❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀



(LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯








( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )






STORY & WRITTEN BY : MEERAH❀πŸ”₯




Marubuciyar littafin


TAURIN ZUCIYA πŸ’–πŸ’πŸŒΊ











TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP

πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY








TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL

πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i













BOOK 1 β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦πŸ“šβœβœ






[15/08/2024]









β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘






PAGE 10 ❀πŸ”₯







After some minutes ya fito sanye da kayan da ya dauko da ga bedroom din shi

Kallon shi da kyau Moussa ya yi kafin ya ce " ango ! Me kuma ya kawo ka toilet di na "

Ko kallon shi Zayd bai yi ba ya sa kai ya fice bedroom din
Ya na fita Moussa ya mike ya na dariya ya shiga toilet shi ma




β–ͺInaya




Misalin karfe 6 ta farka da ga barcin ta
Ta na bude ido ta fara bin dakin da kallo ,

Sai da ta dan dauki lokaci sannan ta mike zaune ta sauko kafafun ta kassa sannan ta mike tsaye ta fara takawa ta nufi toilet

Bai fi five minutes ba da shigar ta toilet ya shigo dakin ya na sallama a tunanin shi ta farka
Sai ya ga dakin ba kowa ga kuma karar ruwa
Sai ya tako bakin gadon ya zauna ya kai hannu saman drawer ya dauki bakin glass din shi ya sa , ya sunkuyar da kan shi ya na kallon kassa kamar mai tunanin wani abu



β–ͺAFTER SOME MINUTES




Ya na zaune a haka ta fito da ga cikin toilet din ta na daure da towel a kirjin ta

Ta na ganin shi ta saki murmushi , ba tare da ce mishi komai ba ta tako wajen trolley din ta ta bude ta dauki uniform din ta

Har ta juya za ta koma toilet wata zuciyar ta ta ce mata " ina kuma za ki koma mutumin da ba gani ba ya ke "

Daga kafadun ta ta yi ta na turo baki nan na ta gaba ta koma ta ajiye kayan na ta saman trolley

Sannan ta kai hannu zame towel din jikin ta, ta koma naked

Hum kamar an ce mishi Zayd dago kai haka ya dago kai dai'dai lokacin da ta saki towel din ta ya fadi kassa ta duka ta dauki pant din ta

Da sauri ya rumtse idanun shi ya kauda kai gefe , tun da ya ke a rayuwar shi wannan ne karan farko da ya ga tsiraicin mace , sai da ya ji zuciyar shi ta buga, cikin ranshi ya ce " na shiga uku ni Nawfel ba ta ga da mutun ne cikin dakin ko ita ma ta koma makafniya "

Inaya kuma Tsab ta shirya war ta cikin
End Ads