kin fi kowa sanin hatsarin da ke bibiyar Inaya cikin rayuwar ta tun shigowar ta duniya me a ba mu fuskanta ba , a dalilin ta mu ka baro Kaduna saboda barazanar da a ke mana , yanzu in su ka samu labarin mu na nan kin san fa baza mu tsira ba , ni ko makarantar da su ke zuwa dan kin matsa ne na hakura na bar ta, ta na tafiya , ba dan Zayd ya na bibiyar ta ba ban san abun da zai faru da ita ba , dan Allah ki bar barin ta na fita wlh bazan iya jure rashin ta ba " ya fada cikin rauni zuciya
( GA DUKAN ALLAMU AKWAI WANI BOYAYEN AL'AMARI A TATARE DA AHALIN GA 🤔🤔 )
Wasu hawaye ne su ka zubo mata ta cikin zafin zuciya ta ce " yanzu dan Allah malam haka za mu ida rayuwar mu kullum mu na gudu , mi mu ka yi musu da za su ringa bibiyar mu haka , kawai dan ka hana ma d'an su auren Inaya shi ne su ke neman su kashe mana ita, meye laifin ta a cikin wannan abun yarinya karama su na neman su lalata mana rayuwar ta " ta kai karchen kuka na kubce mata
Da sauri ta juya ta koma cikin dakin ta
Ajiyar zuciya Abba ya sauke kafin ya bi bayan ta shi ma ya shiga dakin ya na sallama
Bakin gadon ya isko ta zaune ta na kukan ta
Geffen ta ya je ya zauna ya kai hannu shi bayan ta ya na dan bubugawa ya ce " kiyi hakuri Amina, in sha Allah ba abun da zai faru da ita dan na mallaka ta a hannun wanda zai kulla min da ita fiye da mu "
Dago kai ta yi ta kale shi cikin kuka ta ce " ban gane ba malam, wa ka mallakawa ita kuma me ka ke nufi "
Hannun shi ya kai ya goge hawayen ta sannan ya mike tsaye ya ce " in sha Allah in lokaci ya yi za ki san komai "
Ya na gama fadar haka ya juya ya bar dakin
Ya na fitowa harabar gidan Inaya ta shigo ta na sallama hannun ta rike da leda baka sai murmushi ta ke gwanin ban sha'awa
Ya na ganin ta ya saki murmushi shi ya ce " Auta har kin dawo "
Jinjina mishi kai kawai ta yi ta ci gaba da takawa ta shiga kitchen
Ta na shiga shi ma ya fara takawa ya nufi hanyar fita gidan
Ya na fitowa waje ya isko Zayd ya na tsaye bakin kofar gidan ya jingina da bangon gidan ya na rike da sandar shi ya dan daga kan shi ya na kallon gaban shi
Abba na ganin shi ya saki murmushi ya ce " A Zayd ashe tare ku ke "
Jinjina mishi kai Zayd ya yi sannan ya juya ya fara takawa
Murmushi Abba ya yi ya girgiza kan shi ya bi bayan shi su ka ci gaba da tafiya a tare
Sai da su ka karaso kofar wani gida dan nesa kadan da na Abba su ka tsaya a tare sannan Abba ya kale shi ya ce " Zayd za ka zo cin abincin da dadare dai ko na ga jiya ba ka zo ba "
Girgiza mishi kai kawai ba ta tare da ya ce komai ba
Dan murmushi Abba ya yi kafin ya ce " haba Zayd wai in ka na tare da ni din ma sai ka yi min kurmancin na ka "
Dan karamin murmushi geffen fuska ya yi kafin ya yi magana cikin wata zazzakar murya cike da nitsuwa ya ce " uncle ba na jin dadin maganar ne , so ku bar matsa min ina magana please " ya fada cikin wata kwarbabiyar haoussa kamar wanda ke koyo
( WAIT ! WAIT ! WAIT ! BAN GANE BA KENAN DAMA BA KURMA BA NE KO YA NE WANNAN ZANCEN YAKE 😳😳😳😳😳 )
Jinjina kan shi Abba ya yi kafin ya ce " ba komai, amma fa mu na jiran ka yau kar ka zauna ba ka zo ba " ya na gama fadar haka ya yi gaba ya ci gaba da tafiyar shi
Ya na fara tafiya shi ma Zayd ya juya ya nufi kofar gidan ya na sa hannu shi cikin aljihu
Sai da ya karaso kofar gidan ya tsaya ya ciro wasu keys da ga cikin aljihun shi ya bude kofar sannan ya shiga ya na medo kofar
Gida ne mai kyau dai'dai me hali amma fa ya fi na Abba Girma da kyau
A hankali ya ke takowa ya nufi terrace din gaban shi ya Haye
Nan ma ya sa key ya bude kofar shiga falon
Masha Allah duk da falon karami ne amma ya hadu , an saka mike wasu sofas red colour , buyi two seaters, daya three seater sai guda one seater , a tsakiyar su kuma wata yar karamar table ce ta glass sai wasu remote da ke saman ta
Da ka shigo bangaran dama ka na fuskantar wata yar karamar dining room mai dauke da dining table karama mai kujeru guda hudu
Sai wata yar drawer da ke karshen dining room din ta na dauke da kayan breakfast kamar su madara sugar coffee da sauren su
Bangaran hagu kuma wata door ce wadda za ta sada ka kitchen din
Bayan sofa mai three seater wani corridor ne mai dauke da wasu door guda biyu wanda ina kwaytata zaton bedroom ne
Bai tsaya bin ta falon ba ya wuce kai tsaye corridor din
Door ta karshe ya nufa ya kama handle din kofar ya murda ya shiga ciki ya rufo kofar
SAI MUN HADU GOBE 🤘 KAR KU MANTA KU NA TARE DA ALKALAMIN ANISH , WANNAN SO MA TABI NE
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
After some minutes ya fito sanye da wandon three cuter black colour da t-shirt fara mara nauyi , babu takalmi a kafar shi , ya na sanye da bakaken glass kamar kullum
Takowa ya ke cike da izza da kwarjini , hannun shi na rike da wata dankareriar waya kirar Iphone 13 pro max mai launin Gold sai shining ta ke kamar zinaryar gaske
A hankali ya shigo falon ya nufi sofa three seaters ya Haye ya konta
Bayan ya konta ya daura hannun shi daya saman forehead din shi, dayan kuma ya fara latsa wayar shi
( A IYA SANI NA DAI MAKAHO BA YA LATSA WAYAR SHI HAKA 🤔🤔 )
Bai fi ten minutes ba da konciyar shi wani kyakyawan matashi ya shigo falon ya na sallama hannun shi rike da ledodin restaurant
Ko motsawa Zayd bai yi ba , ko sallamar shi cen kassan makoshi ya amsa mishi ita
Dan karamin murmushi saurayin ya yi kafin ya tako ya zauna saman sofa two seaters da ke geffen wadda Zayd ke konce sannan ya ajiye ledodin hannun shi saman table
" Nawfel ga abinci ka nan " ya fada ya na kallon shi ta wutsiyar ido
A dubu dari Zayd ya mike zaune ya matse fuska ya nuna saurayin da dan yatsa cikin turanci ya ce " kar na sake jin ka kira ni da wannan sunnan Diya idan ba haka ba "
Dariya sosai saurayin ya yi shi ma da turanci ya ce " In haka ne ni ma ka daina kira na da Diya , ni fa yanzu suna na Moussa " ya kai karshen ya na kashe mishi ido guda
Dan tsaki Zayd ya ja kafin ya ajiye wayar shi gefe ya matso bakin sofar , ya kai hannu ya janyo table din gaban shi sannan ya bude ledodin da Diya wato Moussa ya kawo mishi
Moussa kuma kallon shi ya ke ya na murmushi har sai da ya ga ya fara cin abincin sannan ya ce " Amir wai ka na da labarin......... "
Bai karasa maganar shi ba Zayd ya daga mishi hannu akan ya isa haka
" Haba Amir yanzu haka za mu ci gaba da zama yanzu wajen shekara hudu kenan , ba ka kewar Al-Amira Tesnim da Malikat ka na tunanin halin da su ke ciki , ko kuma ka manta da Malik "
Shiru Zayd ya yi bai ce komai , ya ci gaba da cin abincin shi
Sai da ya ida sannan ya mike tsaye ya nufi dining room ya bude fridge ya dauki gorar ruwa guda ya dawo ya zauna inda ya tashi sannan ya bude ta ya fara sha
Jinjina kan shi Moussa ya yi cikin ranshi ya ce " Gaskia kam jinin sarauta ba wassa ba ne , ko da ba cikin masarautar ya ke ba "
" Amir wai yanzu haka za mu ci gaba da wannan zaman , ka san halin da masarauta ke ciki , kar fa ka manta jinin mayakka ne kai , bai kama ta a ce ka baro filin yakin ka ba " Moussa ya fada cikin raunin murya
Sai da Ya ida shan ruwan shi sannan ya mike ya nufi corridor ya na fadin " ai ka san hanyar komawa ni ban tare ka ba "
Ya na gama fadar haka ya shige corridor ya shiga bedroom din da ya fito
Jinjina kan shi kawai moussa ya yi ya na murmushi ya ce " ni anya ba diyar malan din nan ya fara so ba , ka san dama an ce soyayya ke meda sarki bawa " ya kai karshen ya na bushewa da dariya
Sai da ya yi dariyar shi iya son ran shi sannan ya mike ya dauki ledodin saman table ya kai kitchen sannan ya dawo ya nufi corridor ya shiga dayan bedroom da ke kussan wanda Zayd ya shiga
* Misalin karfe 8 na dare
* Gidan su Inaya
Zaune su ke cikin harabar gidan saman tabbarma su na sanye da hijab dark blue har kassa , ko wace ta na rike da littafi
Malan na gaban su zaune ya na karatun kur'ani , su kuma sun sunkuyar da kai su na sauraron shi
Mama kuma ta na zaune geffen shi ita ma ta na sanye da hijab amma fari
Su na a haka wani dan matashin saurayi ya fito da ga cikin dakin da ke fuskantar na su Inaya
Ya hadu ba laifi skin din shi chocolate kamar ta Inaya amma ta Inaya ta fi dan haske
Ya na da dogon hanci da kontancen saje , ya na da dara daren idanu brown colour , ya na da dan tsayi da mudewar jiki amma ba sosai ba a shekaru ba zai wuce 26 ba amma ya tare kassunba ga kwarjini
Sanye ya ke da wando three cuter Fari da shirt red kamar jini ya na rike da waya kirar Tecno pop 6
Bai bi ta kan mutanan gidan da ke zaune kussan kofar dakin shi ba ya sa kai ya fice da ga gidan
Malan na kallon shi ta kassan ido amma bai ce da shi komai ba , sai da ya ida karatun shi saman ya dago kai ya kali su Inaya ya ce " Auta, ina ga za mu tsaya a nan gobe sai mu ci gaba "
Jinjina mishi kai su ka yi a tare ba su ce komai ba , su ka mike su ka shiga dakin su dan su ajiye littafan su
Bayan mintina goma Inaya ta fara fitowa ta na sanye da doguwar riga irin ta barci da dan guntun kyale ta ya yafa a kan ta
Ta na fitowa ta ji ana sallama
Cak ta tsaya ta na kallon kofar gidan kafin ta amsa sallamar
Wani dan karamin murmushi ta saki ganin waye ke tare da yayan na ta
Da gudu ta je ta fada jikin yayan ta ta na fadin " yaya Abdoul kenan yaya Zayd ka je nemowa " ta fada ta na kallon Zayd ta geffen ido
Raba jikin ta ta yi da na Abdoul sannan ta ce " sannu da zuwa yaya Zayd "
Jinjina mata kai kawai ya yi bai ce komai ba
Duk abun da su ke Malan ya na kallon su amma bai ce komai ba sai ma murmushi da ya ke
" malan Zayd ku karaso mana " malam ya fada cikin zolaya
Yar dariya Inaya ta yi ta riko hannun Abdoul, shi kuma ya riko hannun Zayd su ka fara takawa a jere
Saman tabbarma da malam ke zaune su ka karaso
Saki hannun ta Abdoul ya yi sannan ya ce ma Zayd su zauna
A tare suka zauna geffen Malam su ka sa Zayd a tsakiya
Ta na ganin sun zauna ta juya ta fara takawa ta nufi hanyar kitchen dan ta taimaka wa mama
Kamar an ce ya dago kai ya kali gaban shi
Ya na dagowa idanun shi ba su sauka ko ina ba sai saman hips din ta , gashi rigar da ta ke sanye yar shara shara ce a na ganin shape din ta
Sai da ya ji zuciyar shi ta buga a dubu dari ya sunkuyar da kan shi dan ya yi arba da abun da ya fi karfin shi
Malam da Abdoul sarai su ka lura da shi, dan Abdoul har kumshe dariya ya ke
Dan murmushi Malam ya yi kafin ya matso cikin rada ya ce " Zayd in ka shirya ni ban da matsala ka zo ka dauki matar ka ta tare a dakin ka "
Dago kai ya yi ya kali malam ya na zaro idanu duk da su na cikin bakin glass
Yar dariya malam ya yi dan dama tsokanar shi ya ke son yi
Shi ma Abdoul yar dariya ya yi kafin ya daura hannun shi saman kafadar Zayd ya ce " Bro ka yi sauri fa dan kar ayi maka wufff da ita "
Dan tsaki Zayd ya ja ya na kauda kan shi gefe
Dai'dai lokacin da Inaya je fitowa da ga kitchen ta na rike da tray
Da sauri ya kauda kan shi dayan geffen cikin ranshi ya na fara danasanin abun da ya yi shekarun da su ka wuce
Gaban su ta zo ta ajiye tray din sannan ta mike ta juya ta koma dakin su
Ta na barin wajen Abdoul ya kai hannu ya janye tray din na sama , ya dauki spoon ya mika ma Zayd da malam sannan ya ce musu bismillah
A tare su ka fara cin abincin , har su ka Kamala ba wanda ya ce ma dan uwan shi wani abu
Sai da su ka ida mama ta zo ta gyara wajen ta kawo musu jug na ruwa da glass biyu , su ka sha sannan Zayd ya ce da Abdoul ya raka shi gida
Sai da ya tsokane shi sannan su ka tashi su ka bar gidan a tare
Ya na fita Inaya ta fito da ga dakin su
Ta na ganin malam zaune shi kadai
Da sauri ta karaso wajen shi ta ce " Abba yaya Zayd har ya tafi " ta kai karshen ta na kallon wajen kofar gidan
Dan murmushi yayi kafin ya mata nuni da gefen shi
Ba musu ta tako ta zauna geffen shi ta na sunkuyar da kai ta fara wassa da yatsun ta
Hannu shi ya daura saman kan ta kafin ya ce " Auta , fada min gaskia , ki na son Zayd "
A razane ta dago kai ta kaleshi ta na zaro idanu, ta ma rasa amsar da za ta bashi
Daga mata gera yayi kafin ya ce " ba ki ba ni amsa ba "
Da sauri ta ce " a'a Abba ba ni son shi , kawai dai na dauke shi a matsayin yaya na , kuma ai ku ku ka ce na dauke shi tamkar yaya Abdoul " ta fada cikin shagwaba
" kennan ba ki son yayan ki Abdoul "
Da sauri ta ce mishi " ina son shi mana "
Dan karamin murmushi ya yi kafin ya janye hannun shi da ga saman kan ta ya ce " to shi Zayd me ya sa ba ki son shi , ko ba yayan ki ba ne ?"
" ai shi da yaya Abdoul ba daya ba ne , ba zan iya cewa ina son shi kamar yadda na ke son yaya Abdoul "
" kamar ya kenan ? "
Turo dan bakin nan nata ta yi cike da shagwaba ta ce " Abba ni ma ban sani ba , ni na ma tafiya ta barci na ke ji " ta na gama fadar haka ta tashi da sauri ta koma cikin dakin su
Ya na kallon ta har ta shiga dakin su , sannan ya saki murmushi ya na girgiza kan shi , ita dai har yanzu ta na fama da yarinta , da ga yanayin maganar ta kadai ya isa ka gane
Bangaran Inaya kuma ta na shiga dakin su ta fada saman gadon su ta yi rub da ciki
Bugun ta a baya Nesrine ta yi kafin ta ce " ke dan Allah malama yi a hankali kar ki kare mana gado "
Dago kai Inaya ta yi ta zauna ta na kallon ta
Dan turo baki tayi cikin shagwaba ta ce