ga Zayd ya mike a dubu dari ya nufe ta , taku biyu kawai ya yi ya riko hannun ta ya janyo ta da karfi , ta fado saman fafadar kirjin shi
Baki sake Abdoul da malam ke kallon shi sannan su juyo su kali juna su na son su yi magana amma maganar ta kassam fitowa
Basu Ankara ba sai kawai ganin su ka ya dauke ta cak ya komo inda ya tashi ya kontar da ita, sannan ya kai hannu ya dauki glass din ruwa ya zuba kadan a hannun shi ya yarfa mata a fuska
A hankali ta ware idanun ta ta na karanto kalmar shahada
Ajiyar zuciya malam ya sauke ya na lumshe idanun shi a hankali sannan ya bude ya kali Abdoul ya ce " Abdoul meda ta dakin su "
Da to ya amsa mishi sannan ya mike tsaye ya kai hannu ya dauke ta cak kamar baby ya nufi bedroom din su da ita
Ya na barin wajen malam ya kali Zayd ya ce " Zayd na san kai ba kurma ba ne amma yau abun da na gani makaho bazai iya yin hakan ba "
Shiru Zayd ya yi ya na sauraron shi amma ya kassa bude baki ya yi magana yau dai asirin shi na shirin tonuwa
Dafa kafadar shi malam ya yi kafin ya ce " Zayd ni fa na yarda da kai, dalilin da ya sa na aura maka Inaya nassan ka na da kyakyawar zuciya amma ban San assalin ka ba kuma bazan ce ka fada min har sai randa ka yi ninya amma zan so in sani meyassa ka ke karyar wadanan nakassa al'halin ka na cikin koshin lafya ? "
Malam na gama fadar haka Abdoul ya fito da ga cikin dakin su Inaya ya dawo inda ya tashi ya zauna
Ya na zama Zayd ya ce " Ni ban taba ce muku ni kurma ne ko kuma makaho ku ne ku ka yi hassashen ku a haka a sani na dai ba wanda ya taba yi min wannan tambayar "
Dan zaro idanu malam ya yi dan fa maganar Zayd ba karya ba ce dan tun lokacin da su ka shigo garin kano su ka hadu da Zayd kullum shiru da shi ko an mishi magana sai dai ya girgiza kai ko ya jingina da haka har su ka yi tunanin ko shi kurma ne , gashi kullum ya na sanye da bakin glass wani lokaci ya na rike da sanda kamar makaho dalilin da ya sa su ke tunanin shi kurma ne kuma makaho
Kallon shi da kyau Abdoul ya yi kafin ya ce " Zayd ka na nufin yanzu ka na iya gani na "
Sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " of cours ina iya ganin ka, ka na sanye da jallabiya brown mai dogayen hannu , ni fa ba ni son yawwan magana dan Allah ku daina saka ni dole sai na bude baki na yi magana zan iya fadar abun da zai bata muku rai baki daya " ya fada kai a sunkuye
Jinjina kan shi Abdoul ya yi kafin ya ce " don Allah Zayd zan so na ga idanun ka ko da so guda ne ka ga yanzu four years kullum ina ganin ka da glass wannan karan ina so na gan su "
Dago kan shi ya yi a hankali ya na kallon Abdoul ta cikin glass din shi kafin ya sa hannu a hankali ya zame glass din shi
A tare zuciyar malam da Abdoul su ka buga da su ka ci karo da wadanan hazel eyes na Zayd ga shi ko ya na fuskantar lamps din wajen sai idanun shi su ka yi reflecting hasken lamps din sai su ka yi wani kyali na musaman su ka zama kamar idanun mage , tsakani da Allah har ni sai da na ji tsoro
Da sauri Abdoul ya ce " don Allah meda glass din ka wlh sai da na ji tsoro "
A hankali ya sunkuyar da kai ya Meda glass din shi sannan ya dago kai ya kali Abdoul ya ce " yanzu dai baza ka ce ba ka taba ganin idanu na ba "
" ni ko na gan so , ai wadanan ko a mafarki na gan su sai na gane su " ya kai karshen ya na yar karamar dariya
Malam dai ya yi sumar zaune ya rasa wane irin mutun ne Zayd , sam bai yi kama da mutanan Nigeria ba karewar zancen bai ma yi kama da mutanan Africa ba ki daya
Haka su ka ci gaba da hirar su wadda yawancin Abdoul da malam ke yin ta shi Zayd ya na zaune kamar gunki
Sai wajen karfe 10 na dare sannan ya mike zai koma gida, Abdoul ya dan raka shi kadan kafin ya komawar shi gida
Bayan ya koma gida bai tsaya bin ta kan Moussa ba kai tsaye ya wuce bedroom din shi
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
Yau ta kama week-end ce Inaya da Nesrine ba su tafi college ba, sai misalin karfe 9 na safe Nesrine ta farka da ga barci
Inaya kuma sai wajen karfe 10 ta farka , da wani mugun ciwon kai ta farka da ga barcin ta amma sai ta shanye
Ta mike ta fito dakin ta shiga toilet ta yi wanka sannan ta fito ta shirya cikin wando jeans baki da doguwar riga zuwa guyiwa pink colour ta saka dan karamin hijab zuwa kirji sai tashin kamshi ta ke
Kai tsaye kitchen ta nufa dan ta taya mama girki ita da Nesrine tun da yau week-end
A tare su ka yi dafuwar su cikin konciyar hankali su na hirar su har misalin karfe 12 na safe sannan su ka Kamala
Bayan sun ida Inaya na shirin shiga dakin ta ta tsinci Muryar malam ya na fadin " Auta dan Allah dauki abincin Zayd ki kai mishi " ya fada ya na ida shigowa cikin gidan
Dan murmushi ta yi sannan ta ce mishi to ta juya ta koma kitchen
Dama mama ta fida mishi na shi cikin wani kwano ta ajiye gefe dama sun saba fida mishi abincin rana kullum wani yaro da ke sangayar malam ke zowa ya kai mishi wannan karan ne na farko da za ta kai mishi da kan ta
Shi ma malam da gangan ya ce ta kai mishi , Allah kaɗai ya san manufar shi ta yin hakan
Jim kadan ta fito rike da wani dan basket a hannun ta, ta fita gidan, a lokacin har malam ya shiga dakin shi
A hankali ta ke tafiya saman hanya ta na kallon kassa kamar mai tunanin wani abu
Sai da ta karaso kofar gidan sannan ta dago kai, ta kai hannu ta tura kofar ta shiga ta na sallama
Wannan karan farko da ta shigo gidan shi ,
Ta sha ruwan mamaki ganin yanayin gidan, har da wata babbar mota fara
ta tambayi kanta ta ina motar ta shigo , in ta shigo ai fitar ba za ta yi wuya ba kuma ita kofa daya ta gani kuma karama ce
Da wannan tunanin ta ci gaba da takawa har ta isa terrace din gaban ta
Ta kai hannu ta bubuga kofar, sau daya
Shiru ba a bude ba sai ta sake bugawa karo na biyu
Wannan karan bai fi one minute ba ta ga kofar ta bude
Sai ga Moussa ya na tsaye rike da kofar ya na sanye da wando three cuter da t-shirt ya na shan iska
Sallama ta yi mishi ta gaishe da shi cikin fara'a sannan ta mika mishi basket din hannun ta ta ce ga abincin su in ji malam
Dan murmushi yayi kafin ya dan ja gefe kadan ya ce " bismillah shigo mana dama yunwa na ke ji idan mun ida sai ki koma da basket din ki ko ? "
Jinjina mishi kai ta yi ta na murmushi kafin ta sa kafa ta shiga falon ta na sallama
*Zayd
Ya na zaune saman sofa da ke fuskantar kofar shigowa, ya na sanye da jallabiya fara mai kananan hannu, ya na sanye da wadanan glass din na shi baki, ya jinjina a bayan sofar ya daga kai sama ya lumshe idanu duk da su na cikin glass
Ya ji sallamar ta amma ko motsi bai yi bare ya amsa mata
A hankali ta karaso cikin falon ta na bin shi da kallo gaskia ya yi mata kyau
Ta na cikin dube duben ta ta tsinci Muryar moussa ya na fadin " ko kin dawo nan da zama ? "
Girgiza mishi kai ta yi ta na murmushi sannan ta karasa ta ajiye basket din hannun ta saman table ta ce " ina wuni yaya Zayd "
Shiru bai amsa mata ba ko motsi bai yi ba
Amma sarai ya ji ta
Da sauri Moussa ya ce " barci ya ke " dan ya kare dan uwan shi
Murmushi ta yi sannan ta koma bakin sofar da ke wajen kofar shigowa ta zauna kassa saman carpet
Karasowa Moussa ya yi ya zauna saman sofar da Zayd ke zaune, ya kai hannu ya janyo table din gaban shi ya kai hannu ya ciro kwanonin da ke ciki da plate guda ya fara serving din kan shi ya fara ci ya na yi mata hira ta na amsa mishi a kai a kai
Duk abun da su ke Zayd na sauraron su dan ba barci ya ke ba kawai dai ya lumshe idanun shi bare kuma su na cikin bakin glass
Sai da ya Kamala cin abincin tass ya cinye komai sannan ya meda kayan cikin basket ya tashi ya je dining room ya bude fridge ya dauko gorar ruwa guda sannan ya dawo inda ya tashi ya zauna ya bude ya sha ruwan
Sai da ya ida sannan ya koma ya jingina a bayan sofar ya lumshe idanun ya bude a hankali ya kali Inaya ya ce " Gaskia abincin nan ya yi dadi "
Shiru ta yi ta kurewa waje guda ido babu ko kiftawa
" Inaya tunanin mi ki ke " ya tambayeta ya na kallon ta
Nan ma shiru ba ta motsa ba
Tasowa ya yi da ga jikin sofar ya kai hannu ya dan bubuga cinyar Zayd
A hankali ya ware idanun shi ya taso da jikin sofar shi ma ya kali Moussa
" duba ka ga, ko tunani me ta ke ? " Moussa ya fada ya na nuna mishi Inaya
A hankali ya juyo kan shi ya kale ta
Ta yi zugum waje guda kamar wadda ta suma
Mikewa tsaye ya yi ya koma saman sofar da ke bayan ta ya zauna ya kai hannun shi ya dafa kafadar ta
A razane ta dawo cikin hayacin ta , ta na sakin kara ta kai hannayan ta ta toshe kunnuwan ta ta na fadin " Ku kyale ni , ku kyale , kar ku tabani , wayo Abba na, aaaaaaaaaaaa "
A rude ya sauko kassa ya riko ta da hannayan shi biyu, shi ma Moussa da sauri ya tasso ya koma gaban ta ya tsuguna ya na fadin " Inaya lafya me ya faru "
Ina sam ba ta jin shi ta toshe kunnuwan ta , ta na sakin kara kamar mai aljanu
Da karfi Zayd ya sa hannayan shi duka biyu ya riko nata ya yanye su da karfi ya sauke su ya riko a bayan ta sannan ya kali Moussa ba tare da ya ce komai ba
Kamar ya san abun da ya ke nufi sai ya Jinjina mishi kai sannan ya fara karanto ayatul kursi'u dan a tunanin shi aljanu ne gare ta
Kamar da gaske ya na fara karanta, ta fara samun nitsuwa ta na kallon shi ta na sauke ajiyar zuciya a hankali ta lumshe idanun ta ta fada jikin Zayd
Sai da ya karanta ajatul kursi sau biyar sannan ya bari ya kali Zayd ya ce " Amir ba dai aljanu ne da ita ba ? "
Girgiza mishi kai Zayd ya yi ba tare da ya ce komai ba ya na rungume da ita
Ya na sauraron yadda ta ke sauke ajiyar zuciya a jere idanu a lumshe
Sai da ta ji ta nitsu sannan ta bude idanun ta, ta mike da ga jikin Zayd ta na kallon Moussa
Dan murmushi ta saki kafin ta mike tsaye ta ce " yaya Moussa ni zan koma gida "
" shikenan muje na raka ki " ya fada ya na mikewa tsaye ya dauki basket din saman table ya riko hannun ta ya ce mu tafi
Ba musu ta bi bayan shi su ka bar falon
Shi ma Zayd mike wa ya yi ya bi bayan su a hankali dan nesa kadan da su
Sai da su ka iso bakin kofar gidan sannan ya saki hannun ta ya mika mata basket din ta ya ce ta shiga
Karbar basket din ta yi sannan ta ce mishi sai an jima ta shige gidan su
Har ya juya zai bar wajen
Cak ya tsaya ya na kallon Zayd da ke tsaye bayan shi cike da mamaki " yaushe ya biyo mu kuma ? " ya tambayi kanshi
Ya na shirin magana Zayd ya riga shi cewa " shiga ka yi min magana da uncle "
Ba musu ya juya ya shiga gidan ya na sallama shi kuma ya tsaya nan ya na jiran su
Jim kadan Moussa ya fito , malam na bayan shi
Sallama malam ya yi mishi sannan ya bashi hannu su ka yi musbaha
Sai da su ka gaisa sannan Zayd ya ce " Uncle ina son muyi wata magana "
" ina sauraron ka, mi ka ke son muyi magana a kai ? " Malam ya fada ya na tsare shi da ido
Ajiyar zuciya Zayd ya yi kafin ya ce " uncle zan so ka fada min dalilin da ya sa ka aura min yarinyar nan tsawon shekara biyu duk lokacin da na tambaye ka ba ka ba ni amsa , a yau ina son na sani "
Nan take yanayin face din malam ta sauya ya rasa amsar da zai ba shi
Ga kuma Zayd ya tsare shi da ido har ga Allah bai shiriya fada wa Zayd wannan sirrin ba
Wasu yawu malam ya hadiye kafin ya ce " Zayd ba zan iya fada maka ba a yanzu , idan lokacin ya yi za ka gane komai "
" shikenan next week zan zo na dauki matata zan gano abun da ake boye min da kai na " ya na gama fadar haka ya juya ya bar wajen ya na taku cike da izza
(TO FA NA MULKIN SUN FARA TASHI 🤣 🥀 )
Yanayin da ya yi maganar shi Ba karamin kwarjini ya yi wa malam ba kawai ya tsaya ya na kallon shi ya rasa me zai ce
Kallon shi Moussa ya yi sannan ya ce mishi " malam zan tafi " sannan ya juya shi ma ya fara takawa ya bar wajen
Jinjina kan shi malam ya yi sannan ya fara takawa dama ya fito zai je mosque ya jiyo sallamar Moussa
Bayan sallar isha
Inaya
A hankali ta ke fitowa da ga cikin dakin su
Ta na sanye da gown pink colour mara nauyi da hijab pink shi ma zuwa guyiwa
A hankali ta ke takowa cike da nitsuwa ta nufi kitchen
Har ta kai kofar kitchen ta jiyo mama na magana sama sama da karfi
A hankali ta juyo ta nufi kofar dakin mama dan a tunanin ta ita ka dai ce ko da ita ta ke magana ba ta ji da kyau ba
Har kai kofar dakin ta bude baki za ta yi sallama ta ji Muryar malam ya na fadin " abun da ki ka ji Amina, auta dai na aurar da ita tun shekara biyu da su ka wuce kuma yanzu mijin ta ya ce ya na son ta koma gidan shi "
Dumm ta ji gaban ya buga da karfi nan take idanun ta su ka kawo ruwa
Ta na a haka ta jiyo muryar mama ta na fadin " Malam Inaya fa duk shekarun ta nawa , in da ma a ce Nesrine ce....... "
Da sauri malam ya katse ta da cewa " Amina , Inaya fa ba yarinya ba ce , gwara na san ta na gidan mijin ta hankali na zai fi konciya "
" yanzu me Inaya ta sani a kan aure "
" Shin wai me ki ke jin tsoro a kai , ki kontar da hankalin ki ba abun da zai faru da ita "
Duk maganar nan da su ke a kunnen Inaya
Lips din ta har kerma su ke ta bude baki ta na fadin " a....a....aure ni kuma ? A'a a'a " ta fada ta na girgiza kai
da gudu ta juya ta bar wajen
Maimakon ta koma bedroom din su , sai ta bar gidan baki ɗaya
Gudu ta ke da iya karfin ido a rufe
Da karfi ta bangaje kofar gidan shi ta shiga ta nufi wajen motar da ke cikin gidan ta buya a baya ta Zube saman guyiwowin ta ta aza kuka da iya karfin ta kamar wata mahaukaciya