Cire hijabin ta Nesrine ta yi ta ajiye saman sannan ta zauna geffen gadon ta dago kai ta kali Inaya ta ce " Inaya ke karama ce baza ki gane ba amma wlh ki raba hanya da samarin nan ko cikin school in ki ka gan su ki tsere ki buya dan wlh ba mutanan kirki ba ne " ta na gama fadar haka ta tashi ta fice da ga dakin
Inaya dai ta na tsaye ta na kallon ta har ta ida maganar ta ta tashi ta bar dakin ba ta ce mata komai ba
Nesrine kuma bayan ta fita kai tsaye toilet ta shiga
Maimakon ta yi wanka sai ta jingina a jikin bangon toilet din ta aza kuka
Cikin kukan nata ta ke fadin " ya Allah na roke ka raba ni da Hafiz , ya Allah ko ba ka raba ni da shi ba kar ka bari ya kusan ci yar uwata , ban San me na yi mishi a duniya ba ya ke neman ya cutar da ni , na shiga uku ni Nesrine , RAMATOU kin cuce ni kin hada ni da bala'i da na sani bazan taba yarda da abotar ki ba, Allah ya isa tsakani na da ke "
Haka ta yi ta dimimuwan ta har ta gaji ta yi shiru sannan ta yi wanka ta fito ta koma bedroom din su
Ta na shiga ta tarda Inaya har ta yi barci dan gajiya
* Misalin karfe 5 na yamma
* Inaya
Zaune ta ke bakin kofar gidan su saman wasu duwatsu ta na faman wassa ita kadai kamar karamar yarinya
Tun da ga nesa ya hango ta zaune ta cikin bakin glass din shi
Ya na tare shi da Moussa, ya na sanye da wandon jeans baki da t-shirt dark blue , shi kuma Moussa jallabiya ce fara ya ke sanye da
Lokacin da Moussa ya gan ta ya saki murmushi ya kali Zayd ya ce " Amir ga fa babyn ka cen ta na wassa "
" ina ga yarinyar nan ta na da matsala a kwakwolwar ta gaskia " ya fada mishi cen kassa kassa ta yadda shi da Moussa kawai su ka ji abun da ya fada
Jinjina mishi kai Moussa ya yi dan ya lura yanayin ta bai yi kama da masu cikakiyar lafya ba a shekarun ta
Haka su ka ci gaba da tafiyar su har su ka karaso inda ta ke zaune su ka yi mata sallama
A hankali ta dago kan ta, ta na amsa musu sallamar su kafin ta ce " ina wuni yaya Moussa "
Dan murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " lafya lau babyn malam , ko dai in ce babyn Zayd "
Dan zaro idanu ta yi ta na kallon Moussa sannan ta kali Zayd da ya tsareta da ido
Turo dan bakin nan nata ta yi gaba ta shagwabe fuska sannan ta ce " a'a ni babyn malam ce ni na ma tafiya ta wajen Abba " ta kai karshen ta na mikewa ta fara tafiya
Da sauri Moussa ya ce " to tsaya mu raka ki mu ma cen za mu je "
Da sauri Zayd ya kale shi dan ya lura Moussa na neman ya kwabo mishi ruwa
Jinjina mishi kai kawai ta yi ta ci gaba da tafiyar ta
Su kuma juya su ka bi bayan ta, ba yadda Zayd ya iya dole ya hakura ya bi bayan shi su ka tafi
Tun da su ka kamo hanya ya ke kallon ta ta cikin glass
Ita kuma sai wasu juye'juye ta ke ta na halba kafa ta na wassa yadda kassan me shekara biyar haka ta ke
Shi kuma Zayd wannan abun da ta ke ya na yawwan tuno mishi da kanwar shi dan ita ma haka ta ke da rawan kai
Kawai sai ya tsinci kan shi ya na jin wani bakon yanayi , cikin zuciyar shi ya ce " she is so cute and innocente why malam zai aura min ita da karancin shekarun ta haka , ya kamata na tambaye shi dalilin shi na yin hakan "
Sai magana ya ke cikin zuciyar shi har su ka karaso sangayar Malam bai sani ba, sai da Moussa ya kai hannu ya taba shi ya na fadin " Amir ba ka ji ne malam na gaida ka ? "
A dan razane ya juyo ya kali Moussa sannan ya meda kallon shi kan Malam da ke zaune saman tabbarma sanye da manyan kaya ga Inaya geffen shi ta rungume shi ta na murmushi
Dan murmushi malam ya yi kafin ya ce " malam Zayd tunanin mi ka ke haka "
Girgiza mishi kai kawai Zayd ya yi allamun ba komai sannan ya dawo da kallon shi kan Moussa ya mishi allamun su tafi
Jinjina mishi kai ya yi sannan ya kali malam ya ce " malam za mu wuce sai mun dawo "
Dan murmushi malam ya yi ya ce " shikenan Allah kiyaye hanya , Auta baza ki raka su ba " ya fada ya na medo da kallon shi kan Inaya da ke konce a jikin shi kamar baby
Cikin shagwaba ta ce " Abba yanzu fa su ka rako ni , sannan kuma na sake rakiyar su , ni gaskia babu inda zan je "
Malam na shirin magana ya ga Zayd ya kama hannun Moussa ya ja shi su ka bar wurin
Ta na kallon su ta kassan ido har su ka bar wajen sannan ta mike da ga jikin malam ta ce " Abba , yaya Zayd sunnan shi ne hakan na gaskia ko "
Jinjina mata kai malam ya yi ya na son ya ji abun da za ta cewa
" to amma Abba me ya sa yaya Moussa ke kiran shi da Amir , Amir ai ya nufin yarima " ta fada ta na kallon malam
Shi kuma malam juya kan shi ya yi ya kali su Zayd da su ka yi nisa cikin tafiyar su
Ba tare da ya juyo ba ya ce " ni ma ban sani ba, halan sunnan da ya ke kiran shi ne da shi lokacin su na kanana kin San ba dole sai dan sarki ba a ke kira da Amir "
Cikin ranshi kuma ya na tambayar kanshi shin wanene assalin Zayd din da su ka sani
( TOOOO ! MU MA DAI MU NA SON MIJI WAYE AINAHIN ZAYD DIN NAN ๐ )
Haka ta zauna wajen malam ta na ta zuba mishi shagwaba shi kuma ya na biye mata sai da su ka ga magriba ta gaba to sannan su ka tashi su ka koma gida a tare , ta na rike da hannun shi ta na wassa da shi
( Ita dai wannan yarinyar da wuya ta zauna ba ta motsi ๐๐ )
Bayan sun koma gida , da kanta ta debo ma malam ruwa cikin buta ya yi Alwalla sannan ya tafi mosque
Bayan ya fita ita ma debo ruwa ta yi Alwalla ta koma bedroom din su dan ta yi sallat
Ta na shiga dakin ta tarda Nesrine ta na zaune saman dadduma ta daga hannayan ta sama ta na adu'a
Dauko daddumar ta Inaya ta yi ta zo ta shinfida geffen Nesrine sannan ta tada sallar ta
Ba su tashi da ga kan daddumar sai da su ka hada da sallar isha su ka yi a tare
Bayan sun ida Nesrine ta mike ta nade daddumar ta ta mayar da ita wajen ta sannan ta fito da ga dakin
Ta na fitowa ta ji sallamar Abdoul
Dum ta ji gaban ta ya buga dan ta san da wuya ya kyale ta bai mata fada ba
Kamar ko ta sani da sauri ta juya za ta koma dakin su ya kira sunan ta
Wasu yawu ta hadiye a hankali ta juyo ta ce " na'am "
Takowa ya yi ya zo gaban ta ya tsaya sannan ya ce " su waye samarin nan da na gan ku a tare "
Sunkuyar da kai ta yi , Cikin in'ina ta ce " ni ma ban san su ba kawai sun tseda mu ne saman hanya wai mu je su rage mana hanya "
Jinjina kan shi ya yi sannan ya ce " shikenan nan gaba kar ku sake tsaya wa ko sun muku magana ku kyale su "
" to yaya Abdoul " ta fada ba tare da ta dago kai ba dan tsoron ta ke ji ya wanke ta da mari
Shi kuma tsaya wa ya yi ya kare mata kallo da kyau ya ga yadda ta ke ta rawar jiki kamar ya ce zai dake ta
Sai da ya dan jima a haka sannan ya juya ba tare da ya ce komai ba ya shiga bedroom din shi
Ita kuma ta na jin ya fara takawa ta dago kai ta ga ya nufi dakin shi ta sauke ajiyar zuciya har da dafe saitin zuciyar ta ta na jan nunfashi a hankali
Sai da ta nitsu da kyau sannan ta kama hanyar kitchen
โคโ EXILED PRINCE โโค
(LOVE MEETS POWER ) ๐๐ฅ
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
BOOK 1 โฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆ๐โโ
โกโกโกโกโกโกโกโกโกโกโกโก
PAGE 4 โค๐ฅ
Da sallama a bakin ta ta shigo kitchen din, nan ta isko mama gaban murhu, har ta gaba girki
Dan juyo wa mama ta yi ta kali Nesrine sannan ta ce " lafya idanun ki duk sun kumbura haka ? "
Ta na shirin magana ta tsinci muryar Inaya ta na fadin " kuka ta yi shi ya sa su ka kunbura "
A tare duk su ka jiyo su ka kale ta
Ta na tsaye bakin kofar kitchen din ta na sanye da doguwar riga mara nauyi ta saka dan karamin hijab zuwa kirji
Hararrar ta Nesrine ta yi kafin ta ce " tooo malama miye ruwan ki a ciki ? "
Hannayan ta duka biyu Inaya ta sa ta rike kugun ta, ta ce " da ruwana , sai dai ki yi abun da za ki yi " ta kai karshen ta na murguna mata baki
Da sauri Nesrine ta dauki wani plate ta juya za ta bugawa Inaya
Da gudu Inaya ta juya ta bar kitchen din ta na kara
Ita ma Nesrine bayan ta ta bi da gudu ta na fadin " yau sai na yi maganin ki mara kunya kawai "
Inaya kuma ido a rufe ta yi da gudu za ta bar gidan
Har ta kai bakin kofa ba ta sani ba, kawai sai ji ta yi ta bugi wani abu da karfi ta yi baya za ta fadi ta na sakin kara mai karfi, wanda ya sanya shi toshe kunnuwan shi da duka hannayan shi biyu
Cak Nesrine ta tsaya ta na kallon su ta na zaro idanu
Malam ne da Zayd su ka shigo gidan sai da su ka yi sallama amma Inaya ba ta ji su ba , har sai da ta bugi kirjin Zayd da karfi
Shi kuma ya kassa taro ta dan ya na tsoron ya taro ta wani ya lura da hakan ya yi mishi wata magana da za ta bata mishi rai shi ya sa ya kyale ta ta fadi
Inaya kuma ta na faduwa kan ta ya bugu dum ga kassa har sai kassar ta dan girgiza
Da gudu Nesrine ta saki plate din hannun ta ta nufo ta da gudu ta na fadin " Inaya, Inaya , Inaya " kamar ta yi kuka
Shi ma malam da ke tsaye geffen Zayd da gudu ya yi kan ta ya talabo ta ya na kiran sunan ta
Ina ita ko jin su ba ta yi sai kuka ta ke kamar karamar yarinya
Ganin yadda su ka bi su ka rude ya sa shi kauda kan shi gefe ya saki dan siririn tsaki
A hankali ya fara takowa inda ta ke konce ta na kuka
Dukowa ya yi gaban ta, ya sanya hannayan shi duka biyu ya dauke ta cak kamar baby ya mike tsaye sannan ya nufi tabbarma da ya gani a shinfide kussan dakin Abdoul
Da sauri malam ya bi bayan shi , ita kuma Nesrine ta tsaya ta na kare mishi kallo cikin ran ta, ta na tunanin ya akayi ya san tabbarma ta na cen wajen , mutumin da ba shi gani
Malam kuwa bai kawo komai a ran shi ba dan ya san akwaye makafi dayawa da su ke aiki kamar ma su idanu ba mamaki ya hadace inda su ke zama kullum shi ya sa ya nufi wajen kai tsaye
( HAKAN NA NUFIN MALAM YA SAN ZAYD BA KURMA BA NE AMMA BAI SAN SHI BA MAKAHO BA NE ๐ค )
Sai da ya karaso wajen tabbarma sannan ya kontar da ita a wajen ya koma gefe ya zauna , ita kuma har yanzu kuka ta ke kamar baby ba ta ma san an dauke ta ba
Ya na kontar da ita malam ya karaso wajen ya zauna geffen ta ya talabo kan ta ya zaunar da ita ya rungume ta ya na fadin " ya isa haka auta daina na kukan nan haka kar ki janyo wa kan ki ciwo "
A hankali ta fara rage sautin kukan ta ta na hadiyar zuciya
Ta na a haka ta ji an tabo mata kafar ta
Ta na konce a jikin malam din ta dago kan ta ta kale shi
Ya na ganin ta dago kan ta ya kai hannayan shi biyu ya rike kunnuwan shi ya dan sunkuyar da kai allamun ya na bata hakuri
Wata yar karamar dariya ta yi cikin kukan nata sai da dan dimple din ta na geffen dama ya banyana karan farko kenan da na gan shi kuma gashi ba karamin kyau ya na kara mata ba
A hankali ya dago kan shi ya na kallon ta ta cikin glass din shi, abun har dariya ya so ya bashi yadda ta ke dariya ta na kuka lokaci guda
" Shikenan auta ya wuce ko ? " malam ya fada ya na kai hannun shi ya goge mata hawayen ta
Jinjina mishi kai ta kafin ta kai hannun ta bayan kanta ta ce " Abba wajen zafi ya ke min " ta kai karshen cikin shagwaba
Dan murmushi malam ya yi kafin ya ce " babu komai auta na zai wuce tashi ki je daki, ki konta "
Da to ta amsa mishi sannan ta fara kokarin mike wa da ga jikin shi
Da sauri Nesrine da ke tsaye waje guda tun dazu ta na kallon su , ta karaso wajen ta kamo hannun Inaya ta taimaka mata ta mike tsaye su ka nufi cikin daki su
Su na shiga cikin dakin Inaya ta Haye saman gadon ta yi rub da ciki ta na sauke nunfashi a hankali ta lumshe idanun ta
Ita kuma Nesrine ta juya ta baro dakin ta tafi kitchen dan ta taimaka wa mama
Ta na shiga malam ya kali Zayd ya ce " Zayd me ya sa ba ka taro ta ba, yanzu da ta ji ciwo fa, dama ta na da tabo a kan ta na dauka shi ne ya motsa yadda na ga ta na kukan nan "
Kallon shi Zayd ya yi cikin sanyi murya ya ce " sorry uncle ban gan ta ba ne kai ma kai sani , amma wane tabo ne wannan ? " ya tambaya ya na son ya ji karin bayani
Ya na shirin magana Abdoul ya fito da ga dakin shi ya na sanye da jallabiya brown mai dogayen hannu ya karaso geffen su ya zauna ya na yi musu sallama
A tare su ka amsa sallamar ta shi amma ta kadai a ka ji , dan Zayd in ba kallon bakin shi ka yi ba baza ka gane ya amsa ba
Sai da ya zauna sannan ya ce "malam, na ji wani ya yi kara, cikin gidan nan ne ? "
Dan murmushi malam ya yi kafin ya ce " ba komai, auta ce ta dan fadi amma ba ta ji ciwo ba "
Jinjina kan shi kawai Abdoul ya yi ba tare da ya ce komai
Su na a haka Nesrine ta fito da ga kitchen ta na rike da plate ta shiga dakin su
Ta na shiga mama ta fito da ga kitchen din ta na rike da tray madaidaici ta karaso wajen su malam ta yi musu sallama ta ajiye tray din gaban su , sannan ta koma kitchen ta dauko musu jug na ruwa da glass biyu ta ka ta ajiye musu sannan ta wuce dakin ta
Ta na shiga dakin Abdoul ya bude musu tray din ya mika ma kowane spoon guda sannan ya ce musu bismillah
Kamar yadda su ka saba haka wannan karan ma haka su ka ci
Sai da su ka Kamala ba wanda ya ce ma wani ufan , sannan Abdul ya zuba mishi ruwa ya riko hannun shi ya daura cup din a sama
godiya zayd ya yi mishi sannan ya kai cup din a baki
Ya na tsaka da shan ruwan Inaya ta fito da ga dakin su ta na dafe kai da hannu guda ta na dan lumshe idanu kamar mai jin barci
A tare duka su ka dago kai su na kallon ta ba wanda ya ce da ita komai
Ta na tsaka da tafiyar ta ta ji wani mugun jiri ya debe ta ta yi fuuuuu baya ta tafi za ta fadi
Da sauri Abdoul ya yi kokarin tashi dan ya taro ta amma sai dai mi ?