uniform din ta, ita ta ma manta da mutun a cikin dakin
Sai da ta gama shiryawa sannan ta dauki towel din da ta yadda kassa ta meda shi toilet sannan ta fice dakin
Duk takun ta ya na jin ta amma ya ki bude idanu ya na tsoron ya sake bude su ya yi arba da abun da ya fi karfin shi
Sai da ya ji ta bude kofa ta fita sannan ya bude idanun shi slowly ya kali saitin kofar ya na ganin ta fice ya sauke wata ajiyar zuciya mai mai nauyi
Inaya kuma bayan ta fita kitchen ta wuce dan ta shirya musu breakfast
Sai wajen karfe 7 cib sannan ta baro kitchen din ta shirya musu komai saman dining table sannan ta koma bedroom din ta
Ya na nan zaune inda ta bar shi ko motsi bai yi ba
Bakin ta dauke da sallama ta shigo dakin
Cen cikin zuciyar shi ya amsa mata
A hankali ta tako gaban shi ta tsaya sannan ta Zube saman guyiwowin ta ta ce " ina kwana yaya Zayd "
Jinjina mata kai kawai ya yi bai ce mata komai ba
Murmushi ta yi kafin ta mike ta nufi trolley din ta, ta dauki hijabin ta ta saka ta dauki school bag din ta sannan ta dawo gaban shi dan nesa kadan ta ce " yaya Zayd zan biya wajen Nesrine sai mu ta fi tare "
Jinjina mata kai ya yi kafin ya sa hannu shi cikin aljihun wandon shi ya ciro kudi yan dubu dubu sun kai ashirin sabi gal sannan ya mika mata
Dan zaro idanu ta yi ta na kallon kudin ta na tunanin ina ya sami wadanan kudade duka
Ganin har yanzu ba ta karba ba ya sa shi dago kai a hankali ya kale ta
Da sauri ya rumtse idanun shi dan ya tino kallon da ya yi mata ta na naked
Ita kuma ba ta lura ba da ya datse idanun shi ba dan ya na sanye da glass bakake
Ajiyar zuciya ta sauke ta yi murmushi kafin ta ce " yaya Zayd ka barshi kawai "
Girgiza mata kai ya yi ya mike tsaye ya tako a hankali gaban ta ya kara mika mata kudin
Wannan karan ba yadda za ta yi sai da ta karba ta na yi mishi godiya sannan ta saka su cikin bag din ta
Sai da ya ga ta sa kudin cikin jakar ta sannan ya juya ya fice
Da sauri ta bi bayan shi ita ma ta fito dakin
A nan falo su ka isko Moussa ya na zaune saman sofa ya na latsa wayar shi
Ya na dago kai ya gan su ya saki dan murmushi ba karamin kyau su ka yi mishi ba , cike da Fara'a ya ce " baby na har kin fito ? "
Sunkuyar da kai kassa ta yi ta na fadin " ina kwana yaya Moussa "
" lafya lau baby na , da fatan wannan jarabbaben bai takura miki ba " ya kai karshen ya na medo da kallon shi kan Zayd da ya zauna saman sofa da ke fuskantar tashi
Girgiza mishi kai tayi kafin ta ce " yaya Moussa na shirya muku breakfast din ku , ko ku na bukatar wani abu ne ? "
Girgiza mata kai ya yi kafin ya ce " no baby hakan ma ya isa , sai kin dawo Allah kiyaye hanya "
Da amine ta amsa mishi sannan ta fara takawa ta fita falon
Ya na jin ta fita ya sa hannu ya janye glass din shi ya ajiye su geffen shi ya zubawa Moussa wadanan hazel eyes din shi
Sarai Moussa ya lura da shi amma ya yi banza da shi ya tashi ya nufi dining room ya fara breakfast
sai da Moussa ya Kamala breakfast din shi sannan ya dawo cikin parlourn ya zauna saman sofa geffen Zayd ya kale shi ya ce " wai ka san wani abu "
a hankali Zayd ya girgiza mishi kai allamun a'a
" dama na san ba za ka sani ba , na ji labarin cewa gimbiya RIANNA ta samu tambayar aure da ga Daular Ottoman "
a dubu dari Zayd ya juyo ya kali Moussa cike da rudu ya ke fadin " wassa ka ke yi amma ko "
a hankali Moussa ya girgiza mishi kai allamun a'a sannan ya daura da cewa " ba wassa na ke ba , amma ba ta yarda ba , maganar dai har yanzu ta na a wajen Malik tukunna bai yanke shawara ba "
dauke kallon shi Zayd ya yi da ga saman Moussa
shiru ya yi na dan wani lokaci kafin ya bude baki a hankali ya ce " Wanene ya nemi auren na ta ? "
" ni ma ban sani ba , Samarin da ke cikin Daular Ottoman su na dayawa gaskia , ba mamaki sarkin da kan shi ke son auren ta "
" dole akwai abun da su ka shirya ta hanyar auren nan "
cikin ko in kula Moussa ya ce mishi " Ya wuce Mulkin saudiya su ke so "
a hankali Zayd ya juyo da kan shi ya kali Moussa ya ce " kamar ya kennan "
" Amir yi tunani mana , Gimbiya RIANNA ita ce babbar yarinyar Malik , yayar ka ce , Kuma kai kadai ne magajin Malik , yanzu ba ka tunanin duk ranar da Malik ya fadi ya mutu , al'halin ya rasa yaron shi tilo da zai gaje shi , wa zai hawa Mulkin saudiya ? dole Mijin Gimbiya RIANNA shi zai hawa , ka fi kowa sanin irin alakar da ke tsakanin Daular Saudiya da kuma Daular Ottoman , har yanzu ba wani jituwa a dakwai tsakanin su , kuma har yanzu Daular Ottoman na da kudurin nan na ta na hawa Mulkin Saudiya baki dayan ta "
a hankali Zayd ya gyada kan shi dan fa maganar Moussa ba kariya ba ce " yanzu me ka ke tunani a kai ? "
" me kuma na ke tunani , kawai ka koma Daular Saudiya , ka fada musu dama ba mutuwa ka yi ba , bayanar ka ita za ruguza duk wani makircin da su ke shirin kulawa ta hanyar auren nan "
girgiza mishi kai Zayd ya yi kafin ya ce " sai dai ka yi hakuri amma Batun komawa Daular Saudiya ka bar shi kawai "
" why ba za ka koma ba , Amir yanzu kennan ka hakura da ahalin ka , ba za su sake ganin ka ba ? "
shiru shi dai Zayd ya yi bai ce mishi komai ya na kallon gaban shi Allah kadai ya san abun da ya ke tunani
ganin yadda ya yi shiru bai ce komai ba ya sa Moussa sakin wani cool murmushi ya rage sautin Muryar shi ya ce " Ko dai ba za ka iya rabuwa da babyn ka ba "
" Ba zan iya tafiya na bar ta ba gaskiya , kuma ba zan iya raba ta da ahalin ta ba , ba zan so ta ji kewar su ba kamar yadda na ke jin kewar nawa " Zayd ya fada ba tare da ya kali Moussa ja
shi a tunanin shi cikin zuciyar shi ya yi wannan maganar kawai sai jiyo Muryar Moussa ya yi ya bushe da dariya
a hankali Zayd ya juyo kai ya kale shi cike da rudu ya ce " lafiya ka ke dariya kai kadai ? "
tsagaita dariyar shi Moussa ya yi ya na girgiza mishi kai ya ce " ba komai Mister Love "
dan karamin tsaki Zayd ya yi kafin ya ce " minene kuma Mister love ? Diya ban san dalilin da ya sa kullum sai mun fara magana da kai sai ka kawo shirme a ciki "
yar karamar dariya Moussa ya yi kafin ya ce " Sorry sorry...... "
bai kai karshen maganar shi ba ya ga Zayd ya mike ya nufi corridor
da sauri Moussa ya ce " a'a Mister love ina za ka je haka ? "
ko sannu Zayd bai ce mishi ba ya sa kafa ya shige corridor din ya nufi bedroom din shi
sai da ya shige corridor din sannan Moussa ya sake bushewa da dariya ya na fadin " wa ya ga Inaya da cikin Amir , ni dai na gani " ya na gama fadar haka ya sake bushewa da dariya shi kadai kamar zautace
▪Inaya
Bayan ta fita gidan ta fara tafiyar ta cikin konciyar hankali , kai tsaye gidan su ta nufa
Da sallama a bakin ta ta shigo cikin gidan
Mama na zaune bakin kofar dakin ta , dai'dai lokacin da Nesrine ke fitowa da ga dakin su ta na sanye da uniform ita ma
Ta na ganin Inaya ta saki wani kyawatencen murmushi da gudu ta je ta rungume ta ta na fadin " na yi kewar ki sosai "
Rungume ta ita ma Inaya ta yi ta na murmushi
Cen su ka tsinci Muryar mama ta na fadin " toh malama kin sake ta, ta zo ta gaishe ni ko ? "
A tare su ka yi dariya su na raba jikin su da na juna sannan Nesrine ta riko hannun ta su ka nufi mama
Ta na isa mama ta bude mata hanayan ta akan ta zo
Ba musu ta fada jikin ta ta na murmushi ta ce " ina kwana mama ? "
" lafya lau autar mama ya ki ke komai dai'dai ko " ta fada ta raba jikin ta da na Inaya
Kallon ta da kyau mama ta yi cike da mamaki ta ce " ban gane ba school za ki koma tun wuri haka "
Murmushi Inaya ta yi kafin ta ce " eh mama yaya Zayd da kan shi ya sayo min uniform ki na gani ? " ta kai karshen ta na juyawa
Mama na shirin magana Nesrine ta riga ta cewa " wuce mu tafi don Allah kar mu yi late"
" shikenan wuce ku tafi , sai kun dawo " mama ta fada ta na murmushi
Hannu Nesrine Inaya ta kamo su ka juya ta ce " mu tafi "
Jinjina mata kai Nesrine ta yi kafin ta juya su fara takawa su ka bar gidan
A tare su ke tafiyar su cikin konciyar hankali su na tafe su na hira gwanin ban sha'awa
Sai da su ka kawo bakin kofar college din , Inaya ta ga masu sayarda kayan marmari
Da sauri ta saki hannun Nesrine ta nufi guda da ga cikin su
Karasowa wajen Nesrine ta yi ta kai hannu ta daura a kafadar ta ta na fadin " to sarkin ciye² me kuma za ki saya "
Kallon ta Inaya ta yi sannan ta ce " Apple mana , ina marmarin Apple sosai wlh dama ban tsaya breakfast ba "
Ta kai karshen ta na meda kallon ta kan mai sayarwar ta ce da shi ya saka mata Apple shida ta na kai hannu cikin jakar ta, ta ciro kudin da Zayd ya bata
Zaro idanu Nesrine ta yi ta na kallon kudin cike da mamaki ta ce " ke Inaya ina ki ka samu uban kudi haka ? "
Ba tare da ta kaleta ba ta na kokarin ciro dubu biyu ta bawa mai sayarwa ta ce " yaya Zayd ne ya bani " ta kai karshen ta na karbar ledar Apple din ta juyo ta kali Nesrine ta ce " mu tafi ? "
Ba musu su ka juya su ka shiga cikin college din su na tafe su na hira har sai da su ka kai bakin kofar class din su sannan su ka rabu
▪After some hours
Zaune su ke saman chair a cikin cafeteria , Inaya sai faman cin Apple ta ke ,Nesrine kuma na kallon ta ta na murmushi har ga Allah ta yi kewar Yar uwarta sosai , tun tafiyar ta har yanzu ba ta samu ta yi barcin kirki ba , ta saba kullum sai ta rungume Inaya cikin barcin ta , yanzu kuma ba ta nan ita daya saman gadon sai dai ta yi ta juyi idan ta gaji ta rungume pillow
Sai da ta kusa kamalawa ta dago kai ta kali Nesrine , murmushi kadan ta yi kafin ta mika mata Apple din hannun ta ta ce " za ki ci ne ? "
Girgiza mata kai Nesrine ta yi ta na murmushi ta ce " a'a ci kayan ki babyn Zayd "
Daga kafadun ta Inaya ta yi ta ci gaba da cin Apple din ta hankali konce , ita komai na ta irin na yara ne
Sai da Nesrine ta ga ta Kamala sannan ta ce " Inaya zan so na tambaye ki wani abu "
Jinjina mata kai Inaya ta yi ta na fadin " wane abu kuma ? "
Ajiyar zuciya Nesrine ta sauke sannan ta ce " da gaske ki na son yaya Zayd , a yadda ya ke hakan ba ya magana kuma ba ya gani ? "
Murmushi kadan Inaya ta yi kafin ta jinjina mata kai allamun e sannan ta daura da cewa " ina son shi a haka , kuma ai yanzu miji na ne , tsakanin shi da Allah ya ke tare da ni , ni ma tsakani da Allah na ke tare da shi , Ni ma ban san ya a ka yi na kamu da son shi haka , lokaci guda ya shiga cikin zuciya ta , kuma ba na fatan ya fita , ko bayan mutuwa ta , rashin ganin shi ko rashin maganar shi hakan ba zai sauya abun da ke cikin zuciya ta ba har abada "
" why Inaya ? Ki duba duk mazan da ke cikin duniya , ki rasa wanda za ki so sai kurma kuma makaho , me na sama ya ci bare ya ba na kassa , da wane idon zai kula da ke , mutumin da ko magana ba ya yi miki , wai a haka za ki bude baki ki Ce ki na son shi , me ya mallaka da su sauran mazajen duniya ba su mallaka ba , da har soyayyar shi za ta rufe miki ido ki kasa ganin minene al'heri a gare ki , ko ke ma kin zama makafniya kamar shi ? "
" wai Nesrine wa ya fada miki yaya Zayd kurma ne , ko kuma shi ya fada miki shi makaho ne " Inaya ta fada cikin bacin rai
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
BY : MEERAH ❤✌
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION
Dan zaro idanu Nesrine ta yi ta na kallon ta cike da tantama ta ce " wai Inaya me ya ke damun ki ne , inda ya na magana duk shekaru hudun nan da mu ka yi tare da shi me ya sa ko kalma daya ban ji ta fito da ga bakin shi ba , kennan a haka ku ke rayuwa cikin gidan na shi , kennan rayuwa da kurma na yi miki dadi ? "
Mikewa tsaye Inaya ta yi ta dauki jakar ta ta na fadin " kin ga Nesrine ban san me ya sa ba ki son yaya Zayd ba, ni fa ina son shi a haka kuma duk abun da za ki fada bazai sa na daina son shi ba , ku duka kallon kurma da makaho ku ke yi mishi amma ai ni ina gane abun da ya ke fada kuma da makaftar tashi ya ke aiki , kin ga ya fi karfin a ce mishi makaho kin ga idan ba za ki fadi abun al'heri a kan yaya Zayd ba ki daina yi min magana "
" Inaya yanzu saboda wancen banzan za ki fada min haka , minene shi a wajen ki , da ga na fada miki abun ya ke gaskiya "
" Gaskiya guda ce , ina son shi a haka , wai shi makaho ko kurma ba shi da zuciya ne , kafin ki yi min wannan maganar ki je ki fadawa Abba , ai shi ya bawa yaya Zayd aure na , da bai yarda da shi ba , ba zai yarda ya aura mishi ni ba "
marairaice fuska Nesrine ta yi ta na fadin " yanzu Inaya kin fi son wacen mutum a kai na , ni Nesi din ki , me Zayd din nan gare shi da har idanun ki za su rufe a kan soyayyar shi , me ya ke da shi , da sauran mazan duniya ba su da shi , dama zama da makafi na meda mutum makaho ? "
a hankali Inaya ta girgiza mata kai cikin sanyin murya ta ce mata " a'a Nesrine ke ce dai makafniyar , har yanzu idanun ki sun kassa gwada miki , kyakyawar zuciyar yaya Zayd , Soyayya ta ita ce ya ke da , kuma har abada babu namijin da zai same ta , Nesi wai ya ki ka sauya lokaci guda haka ? a sani na ba haka ki ke ba , ba ki kaskantar da mutane kamar haka ko ma dai minene zan so ki sani , yaya Zayd dai miji na , kuma a hakan na ke son shi , a hakan zan zauna