x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - EXILED PRINCE LOVE MEETS POWER BOOK 1

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 33271 words

Category: Love Stories

Views 162

25 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
Moussa da Zayd su ka fito da ga cikin falon
Su na sanye da jeans baki da t-shirt amma ta Zayd fara ce ta Moussa kuma blue

Su na tsaka da tafiyar su su ka jiyo kukan mutun
Cak su ka tsaya a tare su na kallon juna su na zaro idanu

A hankali su ka fara bin wajen da kallo ba su ga kowa ba
Cen Moussa ya ce " ko dai aljanu ne ke wannan kukan ? "


Girgiza mishi kai Zayd ya yi kafin ya fara takawa a hankali ya nufi motar shi

( WATA SABUA MAKAHO DA TUKA MOTA 🀣✌)

ya na kara nufo motar sautin kukan na karuwa
A hankali ya fara zagayen motar har ya iso inda ta ke


Ta na zaune ta cusa kan ta tsakanin cinyoyin ta sai kuka ta ke kamar ba gobe

A hankali ya tako ya zo geffen ta ya zauna shi ma sannan ya kai hannu ya dafa kafadar ta , Moussa kuma ya na tsaye gaban su


A hankali ta dago kan ta cikin kukan nata fuskar ta duk ta yi jaga'jaga da hawaye har da majina
Ta na Ι—aura ido saman shi ta ji wani kukan ya zo mata ta kara sautin kukan ta ta na meda kan ta tsakanin cinyoyin ta

Da sauri Moussa ya ce " Inaya lafiya ki ke irin wannan kukan wani abu ya faru ne ? "

Ki dagi kai ba ta yi ba bare ta amsa mishi asali ma ita ko jin shi ba ta yi ba , ta na ta kukan ta , Allah kadai ya san abun da ta ke yi wa irin wannan kukan


Tsugunawa gaban ta Moussa ya yi duk ya bi ya rude ya na fadin " Babyn malam don Allah ki daina kukan nan ki fada min abun da ke faruwa , kar ki janyo wa kan ki illa "

Shi dai malam Zayd ya na zaune gefe ya zuba musu ido ta cikin glass din shi kamar ya na son ya karance wani abu


Tabi shi Moussa ya yi ya na fadin " Amir please ka yi mata magana , may be ta saurare ka , ka ga ni ta ki yi min magana "


Gyada mishi kai Zayd ya yi kafin ya kai hannun shi a hankali ya dan bubuga shoulder din ta


Slowly ta dago da kan ta , ta kale shi

dama jira ya ke sai ya yi mata allamun " minene ki na kuka ? " da hannu





TO A NAN ZAN DASSA AYA SAI MUN HADU GOBE✌✌✌✌
KAR KU MANTA KU NA TARE DA ALKALAMIN ANISH ❀





❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀
(LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯







( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )








STORY & WRITTEN BY : ANISH




Marubuciyar littafin



TAURIN ZUCIYA πŸ’–πŸ’πŸŒΊ





https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i



TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY








BOOK 1 β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦πŸ“šβœβœ






[11/08/2024]






β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘


PAGE 6 ❀πŸ”₯


Da hannu ya mata allamun " minene ki na kuka haka ? "

Cikin wata disashashiyar murya ta ce " yaya Zayd wai Abba ya yi min aure "

Da sauri Moussa ya ce " to mine matsalar ba ki na son wadan a ka aura miki ba "

Medo da kallon ta ta yi kan Moussa cikin kukan ta ce " yaya Moussa ni fa ina da wanda na ke so , kuma ni ban ma san wanda Abba ya aura min , ni ko ma wanene ba na son shi , dan Allah yaya Moussa ka je ka same shi ka ce ya raba auren nan wlh ba ni son shi " ta kai karshen ta na meda kan tsakanin cinyoyin ta

Dan satar kallon Zayd ya yi ta kassan ido kafin ya ce " shikenan babyn malam , ya isa haka dainan kukan nan , yanzu fada min wa ne wannan wanda ki ke so "

Da sauri ta dago kai ta ce " ni fa yaya ..........." kut maganar ta yanke ta zaro idanu ta na kallon Moussa

Shi dai Zayd ya na zaune ya zuba mata ido ya na jiran ya ji sauran maganar in da gaske akwai wanda su ke soyayya to zai sake ta ya aura mata wanda ta ke so da kan shi


Ganin ta yi shiru ta tsaya sai kallon Moussa ta ke sai ya kai dan yatsun shi saitin face din ta ya kyasta mata

Sai da ta dan razane sannan ta medo da kallon ta kan shi

Tambayar ta ya yi minene

Girgiza mishi kawai sannan ta meda shi tsakanin cinyoyin ta amma ba kuka ta ke ba wannan karan


Kallon Moussa ya yi sannan ya daga mishi gera guda

Jinjina mishi kai Moussa ya yi sannan ya sunkuyo gaban ta ya ce " shikenan yanzu tashi mu koma gida ko "

Ba tare da ta dago kai ba ta ce " ni wlh ba inda zan je "

Ya na shirin magana Zayd ya daga mishi hannu ya na girgiza mishi kai

Mikewa tsaye moussa ya yi ya dan ja baya kadan

Shi ma Zayd mike wa tsaye ya yi sannan ya fara takawa ya nufi kofar fita ya bar gidan

Ta na jin ya fara takawa ta dago kai a hankali ta na kallon shi ta wutsiyar ido

Sai da ta ga ya fita gidan sannan ta sake sakin wani sabon kukan

( yarinyar nan da a gaba na ta ke sai na wanka mata biyar πŸ˜‘πŸ˜‘πŸ˜‘ )


Juyawa Moussa ya yi zai bar wajen sai ya dawo ya ce mata " tashi ki shiga cikin gidan tun da baza ki koma cen gidan ku ba "

Ya na gama fadar haka ya sa kai ya fice shi ma

Cen ya hango Zayd har ya yi nisa da tafiyar shi

Da sauri ya fara takawa har ya kamo shi dai'dai ya karaso kofar gidan su Inaya

Su na karasowa wajen Abdoul da malam su ka fito da sauri kamar sun ga wani abun gudu

Da sauri Moussa ya taro su ya na cewa " Abdoul ina za ku je haka da sauri wani abu ya faru "

Abdoul na shirin magana malam ya riga shi cewa " Inaya ce ba ta cikin gidan nan ban San inda ta yi ba "

Dan murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " ku kontar da hankalin ku , yanzu nan mu ka baro ta gidan mu, kar ku damu ba abun da ya same ta "

wata nanauyar Ajiyar zuciya malam da Abdoul su ka sauke a tare

" uncle kun san da yarinyar nan ta na da wanda ta ke so " su ka tsinci Muryar Zayd ya na fada

Kallon juna Abdoul da malam su ka yi kafin su kali Zayd har su na hada baki wajen cewa " ita da kanta ta fada maka hakan ? "

Jinjina musu kai a hankali ya yi bai ce komai ba

Dan murmushi malam ya yi sannan ya ce " yo ai wannan ba matsala ba ce dan..... "

Da sauri Zayd ya katse shi da cewa " kamar ya ba matsala ba ce ? no uncle tun da ta na da wanda ta ke so ni zan nemo shi in aura mata shi da kai na , baza ta ji dadin zama da mutuman da ba ta so , a karancin shekarun nan na ta bai kama ta ta shiga cikin irin wannan kunci ba , dama ni ta yi min karama sosai " bai jira amsar malam ba ya juya ya bar wajen


Sai da ya bar wajen sannan malam ya kali Moussa ya ce " wai maganar me ya ke yi ne haka ? "

Dan karamin murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " wai zai saki babyn malam tun da ta ce ta na da wanda ta ke so ya aura mata shi , ku kyale shi yayi ta neman kan shi har ya gaji , zan koma gida sai da safe " ya juya ya bar wajen

Da sauri Abdoul ya yi shirin bin bayan shi, amma malam ya riko hannun shi ya ce " nassan auta ce za ka je daukowa kyale ta, da safe ta dawo da kan ta "

Jinjina mishi kai Abdoul ya yi sannan ya juya ya koma cikin gidan malam ya bi bayan shi

Da sallama su ka shigo cikin gidan a tare

Da sauri Nesrine da ke konce ta tada kai da cinyar mama ta na kuka, ta tasso ta tarbo malam cikin kukan ta ke cewa " Abba ina Inaya ta yi ne "

Dan murmushi yayi kafin ya ce " kontar da hankalin ki, ta na gidan mijin ta "

Dan zaro idanu ta yi ta na maimaita kalmar miji cikin ranta

Ta geffen ta malam ya raba ya wuce ya karaso inda mama ke zaune shi ma ya zauna

Shi kuma Abdoul ya wuce bedroom din shi

Ya na zama Nesrine ta juyo da sauri ta nufo malam ta zo gaban shi ta tsaya ta ce " Abba wane mijin kuma, Abba Inaya fa shekarun ta 14 ina ta kai aure ko period fa ba ta fara ba " duk cikin kukan ta ke mishi wannan maganar ta ma manta da mahaifin ta ta ke magana


Malam na shirin magana mama ta riga shi cewa " yanzu dan Allah malam ina Inaya ta isa aure me ma ta sani a kai , ka hada ta da wanda ba mu san shi ba , wanda ba son shi ta ke ba yanzu in ya je ya cutar mana da ita da wane za muji malam bibiyar da ake mana ko wannan " ta kai karshen ta na sakin kuka

Da sauri Nesrine ta karaso wajen ta ta Zube saman guyiwowin ta ta rungume mama ita ma ta na sakin kuka

( shi kukan kawai dan an yi mata aure ne πŸ€”πŸ€”????? )


" yanzu Amina ya ki ke son na yi kin fi son na saka ido wancen yaron ya gano inda muke ya zo ya dauke mana ita, kuma na fada miki auren ya yi wajen shekara biyu yanzu , kuma ta na son mijin na ta , dan ni da kai na na tambaye ta in ta na son shi , ku yanzu a tunanin ku in Sudais ya gano inda muke ba sai ta fi shiga cikin matsa la ba dan Allah ku kontar da hankalin ba abun da zai faru da ita " ya kai karshen ya na kai hannun shi saman kafadar mama


A hankali mama ta dago da ga jikin Nesrine ta kali malam ta ce " shikenan na ji abun ka fada amma ba ka fada min wanene wanda ka aura mata "

Jinjina kan shi ya yi kadan sannan ya ce " ba kowa ba ne face Zayd "

A dubu dari Nesrine ta mike tsaye ta na fadin " Zayd ???? " da karfi ta na zaro idanu, yanzu mutumin da ko hanya ba ta fatan ta hada su wai shi ne mijin kanwar ta, mutumin da ko gani ba ya yi kamm akwai ta


" e Zayd , wanda ke zowa gidan nan wanda ku ke ma kallon makaho da kurma shi din dai " malam ya fada ya na kallon ta

Cikin bacin rai mama ta ce " haba malam, wannan makaho ta ya zai iya kare mana yarinyar mu , ko shi ta kan shi ya ke , ya zai kula da ita, inda ma abokin shi Moussa ne da sauki amma Zayd ? "


Mikewa tsaye malam ya yi cikin bacin rai ya ce " bara ku ji aure dai an riga da an aura kuma ba zai sake ta ba in kun ga dama ku karbe shi in kun ki ku ta matsewa "
Ya na gama fadar haka ya kama hanyar dakin shi ya shige ya bar su nan zaune


Juya wa ita ma Nesrine ta yi ta koma dakin ta da gudu ta na sakin sabon kuka

Ita ma mama ta juya ta koma dakin ta zuciya ba dadi

Duk abun da su ke Abdoul na jin su amma ya yi banza da su ya yi konciyar shi


Zayd


Bayan ya koma gida kai tsaye bedroom din shi ya wuce, ga Dukan allamu ya manta da Inaya da ke cikin gidan


Shi ma Moussa ya na shigo wa ya wuce kai tsaye cikin falo

A tunanin shi ta na nan amma da ya shigo ya ga ba kowa a cikin falon

Da sauri ya juya ya fita falon ya koma wajen da su ka baro ta

Ta na nan kamar yadda ya baro ta , amma ta daina kuka sai ajiyar zuciya ta ke saukewa a hankali allamun ta yi barci


Dan murmushi yayi kafin ya juya ya koma cikin gidan a hankali

Kai tsaye bedroom din Zayd ya wuce

Sai da ya yi mishi knocking sannan ya shiga dakin ya na sallama

Ya na zaune saman gadon shi ya jingina a bayan gadon ga computer a gaban shi , ya cire wadanan glass din na shi na gado


Karasowa wajen shi Moussa ya yi ya tsaya gaban shi ya ce " Amir don Allah je ka dauko babyn malam ta yi barci a wajen motar "

Ba tare da ya dago kai ba ya ce " kai me ya hana ka dauko ta ? "

Hararrar shi Moussa ya yi kafin ya ce " Amir ban San rainin sens ka fi kowa sani ba muharama ta ba ce bazan iya dauko ta ba , dan haka malam tashi ka je ka dauko matar ka "

Dago kai Zayd ya yi ya wurga ma Moussa wani mugun kallo

Shi Moussa dariya ma abun ya bashi dama da gangan ya ki dauko ta , ya zo ya tada shi ya je ya dauko ta


Wani file da ke geffen shi Zayd ya doko ya tila wa Moussa

Da sauri Moussa ya kwace gefe ya na dariya ya ce " to malam da ga taimako na ga dai matar ka ce ba tawa ba in ka ga dama ka bar ta a cen ta mutu "
Ya na gama fadar haka ya juya ya fice dakin ya shiga bedroom din shi ya na dariya


Dan kauda kai gefe Zayd ya yi ya na jan tsaki a fili ya ce " wlh sai na yi maganin ka, jarabbabe kawai "

Ya na gama fadar haka ya ajiye computer din geffen shi sannan ya sauko da ga saman gadon ya fito dakin

Kai tsaye parking space ya nufa inda su ka baro ta

Ya na zuwa bai tsaya wani dogon tunani ba ya sa hannayan shi biyu ya dauke ta cak kamar baby ya koma cikin gidan da ita


Maimakon ya wuce bedroom din shi da ita sai ya kontar da ita saman doguwar sofa sannan ya juya ya koma bedroom din shi ya ci gaba da aikin shi



β–ͺWashe gari



β–ͺInaya




Washe gari ba ta farka da ga barcin wahalar ta ba sai wajen karfe 10 na safe, ko da ta farka ta ga ba motsin kowa a cikin gidan allamun sun fita


Jin hakan ya sa ta mikewa ta fara takawa ta bar falon ta fito harabar gidan
Abun mamaki babu motar nan a cikin gidan, to ta ina ta fita ?

(Ko ni wannan tambayar ta tsaya min a rai , ta ina motar nan ke shigowa bare har ta fita )

Ganin ba ta da me ba ta amsa kawai sai ta sa kai ta bar gidan baki daya ta koma gidan su

A hankali ta ke tafiya kamar wadda a ka zarewa lakar jiki har ta karaso gidan su

Bakin ta dauke da sallama ta shigo gidan

A hankali mama ta dago kan ta, ta amsa mata sallamar ta

Ganin ita ce ya sa mama sakin wani dan murmushi ta ce " Auta zo nan ina son magana da ke "

Ba musu ta tako a hankali ta zo geffen mama ta zauna ta na sunkuyar da kai ta na gaishe ta


Sai da mama ta amsa mata gaisuwar ta sannan ta ce " Auta a ina ki ka kwana ? "

Ba tare da ta dago kai ba ta ce " gidan su yaya Moussa " ta fada a takaice

Jinjina kan ta mama ta yi kafin ta ce " Auta fada min gaskia ki na son Zayd a yadda ya ke hakan ? "

Sai da ta dan doki lokacin kafin ta dago kan ta slowly ta ce " shin mama ko ina son shi ai yanzu lokaci ya kure, Abba ya aura min wani cen daban wanda ban sani ba , ba na kuma so , ni gaskiya ba a yi min adalci ba " ta kai karshen kuka na kubce mata
Ta tashi da gudu ta shige dakin su


Mama sai kiran ta take amma ina sam ba ta jin ta

Dama tambayar da ta yi mata dan ta tabbatar da abun da malam ya ce ne na Inaya na son mijin ta, gashi ta tabbatar amma ta lura ita Inaya ba ta san waye mijin na ta ba , ta so ta fada mata ta ki tsaya wa


Jinjina kanta kawai mama ta yi ta ci gaba da yanke kayan lambun da ke gaban ta

NI MA NA DAUKI TAKARDU NA , NA BI BAYAN INAYA
End Ads