Bayan ta shiga bedroom din su , kai tsaye saman gadon ta Haye ta yi rub da ciki ta na sakin sabon kukan
Ta na shiga bedroom din su Nesrine ta shigo gidan ta na sallama hannun ta rike wasu ledodi allamun mama ta aike ta cepane , amma duk yanayin face din ta babu alamun fara'a a cikin
Inda mama ke zaune ta karaso ta zauna ta na ajiye ledodin gaban ta sannan ta ce " mama wai har yanzu Inaya ba ta dawo ba ? "
Murmushi mama ta yi kafin ta ce " hmmmm ta dawo ta na cikin dakin ku "
Da sauri Nesrine ta mike ta nufi dakin su da gudu
Kallon ta mama ta yi ta saki wani dan karamin murmushi ta ce " ke ma Allah ya ka miki mijin auren in rabu da wannan shirman naki "
Nesrine kuma ta shiga dakin su ba bu ko sallama ta hango Inaya konce saman gado ta yi rub da ciki sai kuka ta ke
A hankali ta tako ta karaso bakin gadon ta zauna ta kai hannu ta, ta dan bubugi kafar Inaya
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta juya a hankali ta mike zaune ta kai hannu ta dauki pillow din ta , ta rungume shi a kirjin ta ta na kallon Nesrine
Dan murmushi Nesrine ta yi kafin ta kai hannu kan face din ta , ta goge mata hawayen ta sannan ta ce " haba sister di na, na miye kuka kuma ? "
Hadiyar zuciya Inaya ta yi kafin ta ce " Nesi wai fa ki na ji Abba aure ya yi min , ni fa wlh ina da wanda na ke so ba ni son wadan aka aura min " ta kai karshen ta na boye face din ta cikin pillow
" sannu malama yanzu har kin San minene so ? " Nesrine ta fada cikin sigar zolaya
Dago kan ta ta yi ta wurga mata hararra
Yar dariya Nesrine ta yi kafin ta ce " shikenan yi hakuri ai ni dama sai da na fada miki , ba wadda za ta iya son wacen makaho ga shi kuma kurma am........."
Ba ta ida maganar ta ba Inaya ta katse ta da cewa " wai dan Allah me ya yi miki a duniya da ki ka tsane shi haka, na ga bai taba shiga harkar ki ba , ko gaisuwa ba ta taba shiga tsakanin ku ba amma kin dauki tsanar duniyar nan kin daura mishi, in ke baki son shi toh wlh akwaye ma su son shi dayawa a duniya ciki har da ni "
Ta na gama fadar haka ta tila pillow din hannun ta gefe sannan ta diro da ga saman gadon ta fice dakin
Ta na fita Nesrine ta rike habar ta ta ce " yanzu fa ta ce ba ta son shi amma wai shi har da kare shi yanzu ko a tunanin ta ita kadai ke iya cewa ta na son shi ko ba ta son shi "
Dan tsaki ta ja sannan ta mike ta fito dakin
Ta dawo inda mama ke zaune ta zauna ta na tsuke fuska ta ce " wai wannan yarinyar minene matsalar ta , yanzu fa ta ce ba ta son yaya Zayd, yanzu kuma za ta sake cewa ta na son shi "
Yar dariya mama ta yi kafin ta ce " kyale ta haba ina ga ba ta san da shi ne Abba ya aura mata "
Kauda kai gefe Nesrine ta yi ta na tsaki ta ce " yanzu dan Allah mama haka za mu zuba ido mu na kallo Abba ya bawa wacen makahon auren Inaya, yanzu da wane ido zai kula da ita , da wane bakin zai yi mata magana ni fa gaskia ban yarda da hakan ba "
" toh Nesrine ya za ki yi na ga ba ki da izinin raba auren nan , ko kin ki, ko kin so Inaya matar Zayd ce , ni gwara ZAYD din ma da wancen dan iskan Sudais , ko ba komi ya na da tarbiya da kyawawen halaye kuma nakassar shi bai sa ya zama rago ba, ki na gani tun safe ya ke fita ya tafi aiki duk da baya gani da kan shi ya ke neman abincin shi, to me ya fi wannan ka ci halal din ka , ko wa ya na maka shedar mutumin gwarai, bara ki ji , ni wlh ko da ya fi makaho da kurma, zan aura mishi Inaya dan na san zai kula da ita duk da ba mu San assalin shi ba shekara hudun nan da mu ka yi da shi ya isa ka gane shi wane irin mutun ne "
" hmmmm yanzu kennan mama kin yarda da auren nan, autar ta mu guda za a dauka a bawa kurma, makaho wanda bai ma san da me ta ke kama ba "
Yar dariya mama ta yi kafin ta ce " to ina ruwan Allah da wannan ai zuciyar mutun ya kamata ki duba , sai ki ga mutun kamar shi ya yi kan shi dan kyau amma zuciyar a bushe ta ke kamar kafiran farko, amma sai ki ga wanda bashi da kyau ya na da zuciya mai kyau tsarkakiya, ke yanzu a ganin ki Zayd bai fi Inaya kyau ba kuma a hakan ya yarda ya aure ta , duk da bai gan ta ba kin ga wannan auren na su ya ishe ki ishara Allah ba ya barci , kaddara ce kawai ta hada su , amma ba dan haka ba ni na san inda zayd na da cikakiyar lafya wlh ko inda ya taka ba ki kai ki taka ba "
Nesrine na shirin magana Inaya ta fito da toilet, ta wuce bedroom din su ko kallon inda su mama su ke ba ta yi ba
Dan zaro mama ta yi ta na girgiza kai sannan ta ce ma Nesrine " kin ga tashi ni ki yi min aiki na "
Da to Nesrine ta amsa mata sannan ta tashi ta shiga kitchen
A takaice ranar yau Inaya a cikin bedroom din su ta yi ta, ko harabar gidan ba ta leko ba, abinci ma sai Nesrine ta kai mata daki su ci , abu guda ke fido ta sallat ,
Zayd kuma yau tun safe da su ka bar gidan shi da Moussa har bayan sallar isha ba su dawo ba
Washe gari
Yau ta kama ranar monday, tun karfe 6 Nesrine da Inaya su ka tashi su ka yi duk wani aiki na gidan sannan su ka shirya sai karfe 7:30 su ka bar gidan su ka kama hanyar college
Tun bisa hanya Nesrine ke yi ma Inaya magana amma ta kyale ta ko kallon ta ba ta yi ba
Sai da abun ya bawa Nesrine haushi ta daina mata magana ma
Har sai da su ka iso AMINU KANO COLLEGE OF EDUCATION sannan ko wace ta wuce class din ta
11pm
Zaune ta ke cikin cafeteria din school din , ta na rike da book , ga bottle drinks nan a gaban ta saman table ta na karatun ta cikin konciyar hankali
Ta na a haka wasu yan mata guda biyu su ka zo table din ta su na mata sallama
Ko dago kai ba ta yi ba ta kale su amma ta amsa musu sallamar su cen kassan makoshi shi ma dan ya zama dole a matsayin ta na musulma
Dayar na mini skert da yar t-shirt colour din uniform din college din babu hijab a jikin ta sai wani dan karamin veil da ta nada a kan ta , ta yi simple make up
Dayar kuma ta na sanye da uniform din ta kamar na Nesrine wato wando da riga zuwa guyiwa da hijab zuwa kirji , ta na rike da hand bag guda biyu
Wadda ke sanye da mini skert din ta ja chair din da ke fuskantar ta Nesrine ta zauna sannan ta kai hannu ta karbe book din hannun ta ta na fadin " me ki ke karantawa ne haka ? "
Hararrar ta Nesrine ta yi kafin ta mike tsaye ta tatare kayan ta sannan ta mika wa yarinyar hannu ta ce " ban Book di na don Allah zan koma class "
Mikewa tsaye yarinyar ta yi ta ce " haba Nesi me ya yi zafi haka "
" kin ga Ramatou ki ban book di na, sannan kuma sunana Nesrine ba Nesi ba "
Dayar yarinyar da ke tsaye ta ce " tooo ! Me ya yi zafi haka ? "
Cikin fushi Nesrine ta kale ta ta ce " kin ga Halima ban sanyo da ke ba "
Dariya yarinyar da ta kira da RAMATOU ta yi kafin ta ce " yanzu wannan fushin Nesi duk dan Hafiz ya miki fada ne jiya ? "
Dawo da kallon ta kan RAMATOU ta yi sannan ta ce " kin ga ko wlh tun wuri ki ce mishi ya fita da ga harka ta , ba ni son shi , in kuma ya matsa na sa yaya na ya yi mishi dan banzan duka "
Dariya RAMATOU ta yi har da dafe ciki sannan ta ce " to sai mi in kin fada mishi me zai yi , wlh ko karar shi ya kai gaban yan sanda ba abun da za ayi mishi dan haka tun wuri gwara ki karbi soyayyar shi, ni ban ma ga abun so cikin dirty girl irin ki ba , ni ko abotar da mu ke kawai dan ki na temakamin ne ina samun good grades ba dan haka ba ko kallo ba ki ishe ni ba , ke ba ki san yan mata nawa ne ke biyar yaya na ba da sunnan soyayya amma ya ki dan ya ce ya na son ki shi ne za ki wani ja mishi aji, yar rainin sens kawai, sannan ki ji yaya Moctar ya ga kanwar ki kuma ya ce ya na son ta , na fada mishi gaskiyar sunnan ta da kuma karyar da kika yi mishi na cewa hanya ce kawai ta hada ku wlh idan ki ka matsawa Inaya ta ce ba ta son shi " ta kai karshen ta na kyasta mata dan yatsun ta saitin fuskar ta
Cike da izza ta ce " to wlh ki kuka da kan ki "
Ta na gama fadar haka ta tila mata book din ta a fuska sannan ta juya ta bar cafeteria din Halima na biye da bayan ta
Su na barin wajen Nesrine ta koma ta zauna ta daura kan ta saman table din sannan ta saki kuka kassa kassa
Sai da a ka koma cikin class sannan ta tashi ta fara shiga toilet ta wanke face din ta sannan ta wuce class
Nassan kowa ya na son ya ji wanene Hafiz , to nima ina son ji ๐โ
Hafiz dai babban d'a ne ga governor din Kano, Moctar na bi mishi sannan Ramatou sai autar su Nabila , a shekaru zai kai 25 , Moctar kuma 21 , Ramatou 19 years sai Nabila da baza ta wuce 15 years ba
Tun bayan mahaifin shi ya zama governor wata izza da jiji da kai su ka saukar mishi
Duk abun da ya gani ya ce ya na so to sai ya same shi ko da ta karfi ce
Ga shi ba ya da mutunci ko kadan mahaifin nashi ma in ya bata mishi rai sai ya mishi kaca'kaca dan ba raga mishi ya ke ba
Tun haifuwar Nabila mahaifiyar su ta rasu , mahaifin na su ya sake aure har wajen sau uku
Amma duk wadda ya auro ba ta one month ta ke barin gidan sakamakon Dukan tsiyar da Hafiz ke yi musu
Mahaifin shi na sane amma ya ki yi mishi magana dan ya san ba karamin aikin Hafiz ne ba shi ma ya rufe shi da duka
Shi ya sa ya ja bakin shi ya yi shirin ya zuba mishi ido dan ya fi karfin shi
Duk wata badakala sa ya ke yi mahaifin shi na sane , sannu sannu har ya fara janyo Moctar cikin badakalar ta shi
Kullum su ne tafiya nightclub, ga shan giya da kayan maye
ร takaice ba abun da ba su sha, sai dai ba su taba kusantar mace ba da sunnan Zina
Karewar zancen Nesrine da Inaya su ne mata na farko da su ka gani su ka ji su na son su
Yadda a ka yi Hafiz ya hadu da Nesrine
Wata rana ce driver din Ramatou bai zo daukar ta ba sai ta kira Moctar a kan ya zo ya dauke ta
A lokacin su na tare da Hafiz
Da su ka iso school din , su na tsaye bakin gate ita da Nesrine
Tun da Hafiz ya daura ido saman ta ya ji ya na son ta
Sai bayan sun koma gida ne ya ke tambayar RAMATOU wacece wanan yarinyar da su ke tare
Nan ta fada mishi wacece Nesrine sai dai ba ta fada mishi ba ta na da kanwa
Goben shi tun karfe 7 ya je bakin gate fin school din ya jiran ta
Amma wani ikon Allah ranar nan Nesrine ba ta zo school ba
Sai da ya gama tsayuwar shi ya gaji sannan ya koma gida ,
Goben shi ma haka ya dawo school din
Wannan karan ta zo amma ta na baya dan Inaya ta riga ta fitowa shi ya sa bai gane Inaya kanwar ta ba ce
Babu ko sallama ya kira ta cike da girman kai
Kallo guda ta yi mishi ta gane yayan Ramatou ne dalilin da ya sa ta fara sakin mishi fuska
Sannu sannu ta fara ganin halayan shi na gaskiya
Kullum sai ya zo college din su dan ya gan ta
Wata rana har waya mai tsada ya kama ta amma ta ki karba
Haka kuma ba karamin bata mishi rai ya yi ba har ya tsinka mata mari cikin fushi sannan ya bata wayar da karfi ya ce zai kire ta
Inda ya ajiye wayar nan ta bar ta ta yi tafiyar ta ko wa ya dauke ta oho !
Washe gari bayan ta zo school ya isko ta ya ke tambayar ta ina wayar da ya bata
Nan ta mishi karyar wai Mamar ta ta gan ta kuma ta amshe ta
Bai yi mata magana ba kawai ya bar school din , sai da ya yi wajen sati bai zo ba
Nan Ramatou ta zo ta hura mata kunne a kan Hafiz tsakani da Allah ya ke son ta ta daure ta ringa kula shi ko ya ji dadi
Abotar da ke tsakanin su ya sa ta yarda da zancen ta, dan ko ba komi yayan ta ne bai kamata ta wulakan tashi haka ba
Sannu sannu ta fara kula shi har ta fada soyayyar shi
Amma shi kuma ya na nan kamar dai kullum, bai sauya ba sam dan wani lokaci in ta bata mishi har marin ta ya ke wai a haka wai ya na son ta ( ni dai na ce humm)
Babu irin gift din da bai kama ta ba amma ko wane lokaci sai dai ta yar da shi tsakar hanya ko kuma ta bar shi nan inda ya bata shi
Sannu har soyayyar da ke mishi har ta fita zuciyar ta dan a ganin ta, Hafiz ba al'heri ba ne a rayuwar ta shi ya sa yanzu ta daina kula shi, shi kuma hakan ba karamin zafi ya ke mishi ba
TO KUN DAI JI WANENE HAFIZ DA KUMA ABUN DA KE TSAKANIN SHI DA NESRINE โ
โคโ EXILED PRINCE โโค
(LOVE MEETS POWER ) ๐๐ฅ
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
Zaune ya ke cikin motar su wajen mai zaman banza ya na rike da wayar shi ya na latsa wa ya na sanye da tracksuit sky blue colour ya na sanye da wadanan bakin glglass din nashi na gado
Yayin da Moussa shi kuma ke tukin, ya na sanye da Jeans baki da t-shirt Red colour
Su na a haka Moussa ya katse shirun na su da cewa " wai Amir ka fada ma babyn ka za ka yi tafiya ne ? " ya kai karshen ya na dan satar kallon shi ta wutsiyar ido
Shiru bai amsa mishi ba ko dago kai bai yi ba ya ci gaba da aikin shi
Dan murmushi geffen fuska Moussa ya yi sannan ya ce " Amir wai me ya sa ba ka kula yarinyar nan , ya kamata a ce yanzu ka fara yi mata magana tun da har za ta dawo tare da mu da zama "