" ina ruwa na tashi muje na raka ki ma " ta fada ta na meda kallon ta saman book din hannun ta
Marairaice fuska Inaya ta yi kafin ta ce " Nesrine, wai Abba tambaya ta ya yi in ina son yaya Zayd " ta kai karshen kamar ta yi kuka
Dago kai Nesrine ta yi ta kale ta da kyau kafin ta bushe da wata shegiyar dariya har da dafe ciki
Marairaice fuska Inaya ta yi kamar ta yi kuka ta ce " haba Nesrine ya zan yi miki magana ki yi zaune ki na yi min dariya "
Dan tsagaita dariyar ta Nesrine ta yi kafin ta ce " Yau ni tambayar Abba ce ta bani dariya , yo mi ne abun so cikin wannan abun , mutumin da ba ya magana , ba ya gani wa zai iya zama da shi ai ni ko sadaka a ke bani shi wlh ba ni so " ta kai karshen ta na sake bushewa da dariya
Hararrar ta Inaya ta yi kafin ta ce " kin ga matsala ta da ke wlh ba a iya magana da ke "
" yo ai wannan ba magana ba ce zancen gaskia wa zai iya son Zayd, ba dan kyawon shi ba ai ko kallo bai isa wani ba "
" wai ke me ya sa ki ke yawwan cin zarafin mutane, me ya yi miki, kullum sai kin kaskantar da shi , ko dan kin ga ba ya da kowa ba ya da idon gani , ba ya da bakin magana ko dan bashi da kudi , kin je makaranta ki yi karatun kur'ani ki san Allah ba ya son mai kaskantar na kassa da shi , yanzu in kin wayi gari kin koma kurma ko makafniya ki na tunanin wani zai so ki ne , Ka zamto mai furta abin alkhairi fiye dana sharri. Domin furta sharri yakan haddasa damuwa , na alkhairi kuwa ya kan sanya walwala da farin ciki. Kasani cewa mara godiyar Allah basa cigaba. Hakama mai furta sharri , wlh Nesrine ki ji tsoron duniya wannan jiji da kai da ki ka dauko ba na familyn mu ba ne , ba mu gado wannan ba gwara tun wuri ki tambayi kan ki ina ki ka dauko su "
" ke dan Allah malama ya isa dan kawai na tabo wani banza cen shi ne za ki yi zaune ki na min fada kamar wata uwa ta , ai ba karya na yi ba dan ko ke da kan ki da ki ke protecting din shi ba son shi ki ke ba dan haka ki bani lfy sakara kawai , kamata ya yi ki tafi massalaci ki dauki speaker ki ringa yi musu wa'azi ko ba komi kin samu lada no sens " ta kai karshen ta na saukowa da ga saman gadon ta fice da ga dakin
da kallo Inaya ta rakata har sai da ta fita sannan ta ce a fili " wlh karya ki ke, duk abun da zai sa mace ta so namiji yaya Zayd ya malake shi , dan ya ma fi sauran mazan wlh ko cikin dubu za ki duba da wuya ki samu kamar yaya Zayd " ta kai karshen hawaye na zubo mata
Da sauri ta koma ta yi rub da ciki ta fara kuka kassa kassa
* Zayd
Tafiya su ke saman hanya shi da Abdoul, sai zuba ya ke mishi amma shi kuma ko kalma daya bai ce da shi ba
" Zayd wai minene cikeken sunan ka " Abdoul ya tambaye shi
Cak ya tsaya da tafya ya na kallon gaban shi kamar ya ga wani abu ya kassa gaba ya kassa baya
A hankali ya medo da kallon shi kan Abdoul ya zuba mishi ido mai ce komai
Ganin ya yi shiru kuma ya tsaya ya na kallon shi ya sa Abdoul cewa " ko sunnan na ka ma ka manta "
Jinjina mishi kai Zayd kafin ya fara takawa ya yi gaba
Dan murmushi Abdoul ya yi kafin ya ce " to tun da ka san hanya ni zan koma gida " ya fada ya na daga mishi murya
Bai ce mishi komai ya ci gaba da tafiyar shi
Ganin bai ce komai ba ya sa Abdoul juyawa ya koma gida
Shi ma Zayd hanyar gidan shi ya kama
Bai fi minti biyu ba ya iso gida
Da sallama bakin shi ya shigo falon gidan nan ya isko Moussa ya na zaune saman sofa da ga shi sai short da singlet ya na latsa wayar shi
Dago kai ya yi ya na amsa mishi sallamar shi kafin ya ce " Amir wai ina ka tsaya ne haka tun dazu ni ke jira ka "
A hankali ya sa hannu ya zame glass din idanun shi
Allahuma barik ashe ba banza ba ya ke saka glass ba , ko ni sai da na yaba kyawon idanun shi
Ya na da dara daran idanu Farare kal kamar madara
Launin idanun shi Hazel mai bala'in kyau , har wani green ya ke yi , sai shining ya ke abun har ya ba ka tsoro kamar idanun mage cikin dare haka su ke
Karasowa ya yi cikin falon ya ajiye glass din saman table sannan ya zauna Saman sofa jingina bayan shi a jikin forehead din sofar ya daga kan shi sama ya lumshe idanun shi
Duk abun da ya ke Moussa ya na kallon shi amma bai ce da shi komai ba dan ya san abokin na shi ba karamin miskili ba ne ba bazan ba a ka kassa gano shi ba kurma ba ne
Ajiye wayar shi Moussa ya yi saman table kafin ya matso bakin sofar ya kai hannu shi ya dafe cinyar Zayd
Medo kan shi ya yi a hankali sannan ya bude idanun shi ya daga mishi gera allamar minene ?
" Amir wai me ya ke damun ka ne , duk ka bi ka sauya kamar ba Nawfel din da na sani ba , kamar ba magajin Malik , ko dai ka fada soyayya ne " ya kai karshen ya na kashe mishi ido guda
Dan tsaki Zayd ya ja kafin ya kauda kan shi gefe kafin ya ce " Diya dan Allah ka bar kira na da wannan su nan, wannan sunnan ya goge da ga cikin rayuwa ta tun lokacin da mu ka shigo garin nan "
" in haka ne ka daina kira na da Diya ni ma , yanzu Amir baza ka koma ka karbi mulkin ka ba "
Da sauri ya katse shi da cewa " ai Malik bai mutu ba , har yanzu ya na kan mulki kuma ko ya mutu ba ni son mulkin, a kan shi a ka nemi halaka ni dan haka su je na bar musu kayan su , na ga ai kaima yarima mai jiran gado ne me ya sa baza ka koma masarautar ku ba ka karbi mulkin ta ba "
Yar dariya Moussa ya yi ya na dauke hannun shi da ga saman cinyar Zayd sannan ya ce " haba kai ma Amir ta ya zan karbi mulki bayan ni ne na uku babban yayan mu na raye zan ce na karbi mulki ? shi ya sa na baro musu kayan su , ni fa mulki sam ba ya cikin tsarin rayuwa ta ba yadda za ka yi an haifo ka cikin jinin sarauta dole ka hakura "
Mikewa tsaye Zayd ya yi ya bar falon
Har zai shiga corridor ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya ce " ka na da labarin Amira da Malikat ? "
Dan murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " kar ka damu su na cikin koshin lafya "
Jinjina kan shi kawai ya yi sannan ya fara takawa ya shiga corridor din ya shiga bedroom din shi
Ya na shiga shi ma Moussa ya mike ya koma bedroom dinshi shi ma
* Washe gari
* AMINU KANO COLLEGE OF EDUCATION
*Nesrine
Zaune ta ke kassan wata bishiya cikin harabar college din ta na rike da wani book ta na karatu
Kamar da ga sama ta ji an zabce mata book din ta
A dubu dari ta dago kai , wata irin mumunar faduwa gaban ta ya yi lokacin da ta yi arba da wanda ya zabce mata book din ta
Wasu samari ne guda biyu su na tsaye gaban ta
Wanda ke rike da littafin ta ya fi dayan tsayi kadan ya kuma fi shi haske a shekaru zai kai 25 haka ya na da dogon hanci da kananan idanu ya dan tara gashin kai
Ya na sanye da crazy jeans blue da t-shirt blue ita ma
Daya kuma ya na da dan duhu kadan amma kamanin su daya sai dai wannan bai tara gashin kai ba, idanun shi kuma brown colour ne , kuma ya na da saje , lips din shi kuma sun dan yi pink kadan a shekaru ba Zai wuce 23 years ba
Shi kuma ya na sanye da jeans baki da t-shirt white color
Wanda ke rike da book din ta ya fara magana ya ce " baby wai ba na ce da ke ba ki ringa samu na a wajen parking space lokacin break ba "
Wasu yawu Nesrine ta hadiye murya na kerma ta ce " yi hakuri Hafiz bazan sake ba "
Geffen ta ya zo ya zauna ya na mika mata book din ta ya ce " ba komai baby nan din ma ya na da dadin zama sai dai da mutane dayawa shi ya sa na ce ki ringa tarda ni parking space "
Ta na shirin magana ta ji Muryar Inaya ta na yi musu sallama
A tsorace ta dago kai ta kale ta
Inaya kuma ta yi zaton classmate din nesrine ne sai ba ta ka komai a ran ta ba ta kali yar uwarta ta ce " Nesrine dan Allah in kin tashi tafya gida ki jira ni "
Ta na gama fadar haka ta juya da gudu ta bar wajen kamar ta ga wani abun tsoro
Tun da ta iso wajen saurayin da ke tsaye ya tsare ta da idanu sai kallon ta ya ke ya na hadiye yawu
Sai da ta bar wajen ya na kallon ta har ta kure wa kallon shi sannan ya dawo da kallon shi kan hafiz ya ce " bro wacece wacen yarinyar ta hadu fa, she look so innocent "
Dum Nesrine ta ji gaban ta ya fadi dan ta san in Moctar ya lakewa Inaya ta shi ga uku cikin college din nan dan sai ya azabtar da ita shi ma ba karamin mugu ba ne ga mugun son mata , dama dama Hafiz a kan shi
Ta yi nisa cikin tunanin ta sai ji ta yi an daura hannu saman cinyar ta
A razane ta dawo cikin hayacin ta, ta na kallon hannun hafiz da ke saman cinyar ta
" lfy baby ina tambayar ki kin yi shiru " ya fada ya na leko face din ta
" minene ? " ta fada cen kassan makoshi
Dan murmushi yayi kafin ya ce " who is she , ko sister din ki ce "
Da sauri ta ce " a'a kawai saman hanya na hadu da ita "
" okay meye sunnan ta " ya tambayeta ya na tsare ta da ido
Wasu yawu ta hadiye kafin ta ce " ban sani ba " Lips din ta har kerma su ke yi
Ba ta gama rufe bakin ta ba , ta ji Tass saukar mari a face din ta
Da sauri ta kai hannu ta saman kumatun ta ta na dafe wajen wasu hawaye na zubo mata
Mike wa tsaye ya yi cikin bacin rai ya daga mata murya ya ce " ni za ki raina wa hankali ke har kin isa ki min karya "
Ya na gama fadar haka ya kai hannu ya shake ta ya hada kan ta da bishiyar cikin tsawa ya ce " meye sunnan ta na ce miki "
Cikin kuka ta ce mishi " Maryam sunnan ta Maryam " da kyair kalmar ta karshe ta fito dan ba karamar shaga ya yi mata ba
Ganin ya na neman ya kashe ta ya sa Moctar kai hannun shi ya dafa kafadar shi ya ce " bro sake ta kar ta mutu "
Da sauri ya janye hannun shi da ga wuyan ta , ya ja baya kadan kafin ya ce " nan gaba ki san irin amsar da za ki ba ni in na tambaye ki " ya na gama fadar haka ya juya ya bar wajen
Bin bayan shi Moctar ya yi su ka bar wajen
Su na barin wajen ta fadi kassa ta konta ta na sauke kuka mai cin rai
Sai da ta share wajen good 30 minutes ta na kukan sannan ta mike a hankali ta na jan kafa ta nufi toilet din mata ta wanke face din ta sannan ta dawo ta dauki school bag din ta ta tafi class
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
Tafiya su ke saman titi a jere , Nesrine ta yi nisa cikin tunanin ta , ita kuma Inaya sai wassan nin ta ta ke kamar karamar yarinya
Su na tsaka da tafiyar su wata mota fara kirar Mercedes ta tsaya a gaban su ta tare musu hanyar wuce
Dum Nesrine ta ji gaban ta ya fadi dan ta san ko wanene
Inaya kuma ta yi tsaye ta na kallon motar dan ita ba ta san ko su waye ba
Su na tsaye a hakan su ka ga an bude kofofin gaban na motar Hafiz da Moctar su ka fito
Gaban su ka zo su tsaye sannan Moctar ya ce " yan mata ku zo mu rage muku hanya mana "
Dan murmushi Inaya ta yi sannan ta riko hannun Nesrine ta ce " mun gode amma mun iso gidan ai " ta kai karshen ta na rabawa ta geffen su za ta wuce
Da sauri Moctar ya sha gaban su ya ce " haba yan mata taimako ne fa "
" babu komai mun gode gidan mu fa cen karshen layin ne , ka ga kuma ba ni son Abban mu ya kan ki zai mana fada "
Ba ta gama rufe bakin ta ba ta tsinci Muryar Hafiz ya na fadin " ke Nesi wuce cikin motar nan na kai ku gida "
Wasu yawu Nesrine ta hadiye ta na tsoron ta shiga motar in malam ya gan ta zai yi mata fada, in kuma ta ki ta san halin Hafiz yanzu zai yi mata Dukan mutuwa kuma ba izinin ramawa, kawai sai ta tsaya ta na faman muzurai
Ta yi nisa cikin tunanin ta sai tsintar Muryar Abdoul su ka yi ya na fadin " Nesrine me ku ke yi a nan ? "
A razane ta juyo ta na kallon shi zuciya na duka uku uku
Ya ko tsare da wadanan dara daren idanun shi
" yaya Abdoul dama classmate din su Nesrine ne su ka ce wai su rage mana hanya shi ne na ce musu mun ma iso gida amma su ka ki yarda " Inaya ta fada babu ko tsoro
" shikenan ba komai wuce ko tafi gida yanzu "
Tun bai rufe bakin shi ba Nesrine ta kamo hannun Inaya ta raba ta geffen Moctar da sauri ta bar wajen
Su na barin wajen Abdoul ya juyawar shi shi ma ya yi tafiyar shi su ka bar Hafiz da Moctar tsaye a wajen
Bayan Abdoul ya bar wajen Moctar ya kali Hafiz da ke ta hura hanci ya ce " kai dan malam rage wannan fushin na ka, ga shi yanzu sun tafiyar su ba tare da mun ga gidan su ba "
Dan tsaki Hafiz ya ja sannan ya juya ya fara takawa ya na fadin " ai mun hadu school "
" kai malam kar ka manta ba college din ba mu ke , yawwan zuwan mu cen ya janyo mana matsala "
Geffen driver Hafiz ya bude ya shiga
Ya na ganin ya shiga motar shi ma ya bude geffen mai zaman banza ya shiga
Bayan ya shiga Hafiz ya tada motar su ka bar wajen da mugun gudu
Duk abun da ya faru a kan idon Zayd , dan ya na biye da su Inaya amma su ba su gan shi ba , ya na shirin ya je ya yi ma su Hafiz Dukan tsiya ya ga Abdoul ya shawo kwanar ya nufi su Inaya kawai sai ya yi tsayiwar shi sai da ya ga tafiyar su sannan ya juya ya kama hanyar komawa gidan shi
Bangaran Inaya kuma , sai da su ka isa cikin gidan babu wanda ta ce da yar uwarta wani abu
Sai da suka shiga cikin bedroom din su sannan Inaya ta kwace hannun ta da karfi ta dan ja baya ta na kallon Nesrine ta ce " wai me ya same ki Nesrine kin ga yadda saurayin cen ya yi miki tsawa kuma ki ka kassa ce mishi wani abu