da shi , idan ki na jin haushin hakan ki kashe kan ki ki huta "
( TO FA YAU A TABO BABYN ZAYD 🤣🤣🤣🤣 )
Ta kai karshen ta na juyawa za ta bar wajen kawai sai ta ji ta bugi mutun
Dan bayan kadan ta ja ta dago kai ta kaleshi ta ce " sorry "
Murmushi kadan Moctar ya yi kafin ya ce " ba komai "
Da sauri ta raba ta geffen shi za ta wuce
Da sauri ya riko hannun ta ya ce " haba ina kuma za ki je , ni fa wajen ki na zo "
Cikin bacin rai Inaya ta kwace hannun ta ta juya ta fara takawa za ta bar wajen
Da sauri ya sha gaban ta ya ce " ba da ke na ke ba , za ki wuce ki kyale ni ? "
Cikin bacin rai Inaya ta ce " ka ga malam ka ba ni hanya na wuce ni matar aure ce "
Dariya Moctar ya yi har da dafe ciki
Sai da ya tsagaita dariyar shi sannan ya ce " oh sannu madam to , shi ne za a yi biki ba'a gayace mu ba ? " ya kai karshen ya na kashe mata ido guda
Dan tsaki Inaya ta ja kafin ta raba ta geffen shi ta wucewar ta
Da kallo ya bi har sai da ta kurewa ganin shi sannan ya juyo ya kali inda Nesrine ke zaune
Sai dai kuma me ?
Babu ita babu mai kama da ita, tun lokacin da ya bata baya ta tatare kayan ta a hankali ta tsere dan ta sani tabass Moctar ya na tare da Hafiz , idan kuma Hafiz ya zo wajen ta san tabass ba zai kyale ta ba shi ya sa ta tsere
Abun da ba ta sani ba Moctar shi kadai ya ke tafe , Hafiz bai san da cewa college din zai zo kawai ya ce mishi zai fita ne
Tsaki kadan ya ja kafin ya fara takawa ya fice cafeteria din shi ma
▪Inaya
Ta na barin wajen ta koma kai tsaye class din su ta koma dai'dai lokacin da prof din su zai shiga class din
After some hours
Bayan sun sauka da ga school ko wace ta wuce gida , Inaya kuma gidan mijin ta kai tsaye ta wuce dan yau fa Nesrine da Moctar sun tado mata na bacin ran
▪Zayd
Su na zaune cikin falo shi da Moussa ko wane sai faman latsa wayar shi ya ke
Su na zaune a haka Inaya ta shigo falon ta na sallama kassa kassa
Dago kan shi Moussa ya yi ya na amsa mata sallamar ta da murmushi
Ya na shirin yi mata magana ya ga ta wuce corridor kai tsaye ko gaida su ba ta yi ba
Da kallo ya rakata har sai da ta shiga bedroom din Zayd sannan ya dawo da kallon shi kan Zayd ya ce " Amir ina ga yau wani ya tabo ran baby na "
Slowly Zayd ya dago kan shi ya zubawa Moussa wadanan hazel eyes din shi ta cikin glass kafin ya ce " wai wanene babyn ka cikin gidan nan ? "
Hararrar wassa Moussa ya yi mishi sannan ya ce " bayan wadda ka ke kira da matar ka wa ke cikin gidan nan, ita ce baby na mana, ka ga na ma tafi na rarrashi abu na " ya kai karshen ya na mikewa tsaye zai shiga corridor
Da sauri Zayd ya riko hannun shi ya ce " kai Diya ban san rainin sens matar tawa ka ke kira da baby ? "
Kwace hannun shi Moussa ya yi kafin ya ce " tun da kai ba ka so ni ina so wlh , ni wlh ka ci gaba da kyale ta ma , hakan ya yi min dadi , ko na samu son da ta ke yi maka ya dawo kai na , i really love her, i don't know how ko yaushe hakan ta faru i'm falling in love for her , ni da za ka min Alfarma ka sake ta na je na roki malam ya aura min ita tun da kai ba ka son ta "
" Diya wai ka na jin abun da ka ke fada ne "
" ka ga malam ni don Allah kyale ni , wai ba ka ga yadda baby na ta dawo ne gidan ko gaisuwar arziki ba ta yi min ba , ka ga ni na tafi rarrashin ta " ya kai karshen ya na juyawa ya shiga corridor ya nufi bedroom din Zayd
Sumar zaune Zayd ya yi ya na jin abun da Moussa ya ke fada mishi nan take ya ji wani uban kishi ya taso mishi yanzu shi Moussa zai yanka a baya ya zagayo ya ce matar shi ya ke so kuma
Da sauri ya girgiza kan shi ya ce " no ! No ! Impossible bazai yi yu ba "
Ya na gama fadar haka ya mike tsaye da sauri ya shiga corridor kai tsaye ya wuce bedroom din shi cikin zafin nama ya bude kofar dakin ya shiga
Cak ya tsaya bakin kofar ya na bin dakin da kallo , duk wajen a tirje ya ke , ga pillow duk an zubar da su kassa , an zare bedsheet an tila shi gefe guda
Cen ya hango Inaya zaune a kassa ta saka kan ta tsakanin cinyoyin ta, ga jakar school din ta cen gefe ta tila ta
Tsaya wa ya yi ya na bin dakin da kallo ya na son ya ga Moussa amma ita kadai ya gani
Abun da bai sani ba shi dama Moussa wassa ne ya ke yi mishi dan ya san abokin shi da mugun kishi nan take zai fara bibiyar Inaya duk wane abu da za ta yi sai ya Ankara da shi , dalilin da ya sa ya ke yi mishi wannan abun amma shi gaskia ba son Inaya ya ke ba ko yanzu da ya shiga corridor din bedroom din shi ya shiga ba na Zayd ba
A hankali ya fara takowa cikin dakin har ya karaso inda ta ke zaune shi ma ya zauna gaban ta ya yi irin zaman cin tuwo ya zuba mata idanu, da allamun ba kuka ta ke ba
Sai da ya gaji da kallon ta sannan ya kai hannu shi ya kyasta mata dan yatsun shi biyu saitin kunnen ta
Da sauri ta dago kan ta ta na kallon shi dan ita ba ta ji shigowar shi ba cikin dakin har lokacin da ya zauna gaban ta , duk ta yi nisa cikin tunanin ta
Dan murmushi ta saki kafin ta gyara zaman ta, ta yi irin zaman da ya yi ta sunkuyar da kai ta riko tafin kafarta guda da hannayan ta duka biyu
Ganin ba ta da niyar yi mishi magana ya sa ya kai hannu ya dago habar ta ya na kallon face din ta , sam babu digon hawaye a cikin idanun ta , to me ya faru kennan ?
Ita kuma murmushi kadan ta saki kafin ta ce " yaya Zayd me ya faru ? "
Janye hannun shi ya yi kafin ya girgiza mata kai sannan ya kai hannu ya nuna nata sannan ya mata allamu da hannu " me ya ke damun ki ? "
Sunkuyar da kan ta yi kafin ta ce " yaya Zayd wlh Nesrine ta na yawwan takura min wai na auri kurma kuma makaho duk cikin mazan da ke cikin duniyar nan wai shi na zaba, ban San minene matsalar ta ba , ni na fada mata ina son ka a hakan amma ta ki jin magana har wasu classmate din ta ta fadawa yanzu duk sun bi sun takura min a school , ni wlh in ba ta bani lafya sai na fadawa Abba , shin minene matsalar in baka gani ko baka magana na ga kai ma mutun ne ka na da tsoron Allah , ka na sallat ka na azumi ka yarda da Allah da manzon sa , kuma ka na da zuciya mai kyau , amma ita duk ba ta ganin wannan , wlh ina jiye mata duniya ba ta san abun da zai faru da ita ba nan gaba , sam ba ta ganin darajar mutane , duk abin da na ke son na gwada mata ta ki gani amma a haka wai ta ke ce maka makaho al'halin ita a bata gani "
Tun da ta fara magana ya tsare ta da idanu ya na kallon ta cikin ranshi kuma cewa ya ke " Moussa ya yi gaskia she is so innocente , her heart is so pure , ba ta jin tsoron fadin abun da ke cikin zuciyar ta , duk zaman da na yi a Nigeria ke ce mace ta farko da ta ce min ta na so na a matsayin makaho kuma kurma al'halin ba haka ba ne , ina ga zan yarda da maganar Moussa na amshi soyayyar ta , muyi sabuwar rayuwa nassan bazan samu wadda za ta zauna da ni tsakanin ta da Allah kamar ke ba "
Ya na gama fadar haka ya mike tsaye ya juya ya fara takawa ya fice dakin
tun da ya mike ta dago kai ta na kallon yadda ya ke tafiya cike da nitsuwa , ita ta rasa dalilin da ya sa komai na shi burge ta ya ke yi , haka kawai ta ci gaba da kallon shi har sai da ya fice sannan ta saki wani cool murmushi ta ce
" ina son ka yaya Zayd , kai ma na san wata rana za ka bude baki ka ce ka na so na "
ta na gama fadar haka ta tashi ta shiga gyaran dakin
Zayd kuma Ya na fitowa falon ya isko Moussa ya na konce saman sofa ya na latsa wayar shi
Ya na ganin Zayd ya fito ya mike zaune ya na murmushi ya ce " har ka ida rarrashin baby na "
Ko kallon shi Zayd bai yi ba ya sa kai ya fice falon, ya bar gidan baki daya
Tafiya ya ke cikin konciyar hankali ya na taku cike da izza har ya karaso bakin kofar gidan su Inaya, ko me ya zo yi oho !
Ya na shirin shiga gidan Malam ya fito da cikin gidan ya yi shirin tafiya massalaci dan lokacin sallat ya yi
Ya na ganin Zayd ya saki wani kyawatencen murmushi ya mika mishi hannu su ka yi musbaha sannan ya ce " a'a malam Zayd yau kai ne a gidan na mu haka , ina fatan ba dai laifi autar tawa ta yi maka ba "
Girgiza mishi kai Zayd ya yi kafin ya ce " no ba maganar ta ba ya kawo ni gidan nan uncle ! "
" toh , lafya kuma ? Maganar mi ta kawo ka in haka ne ? " malam ya fada ya na tsare shi da ido
Sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " uncle ina so in san dalilin ka na aura min Yarinyar nan al'halin ba ka san ko ni wanene ba ka san kowa nawa ba za ka dauki d'iyar ka ka bani ita haka kawai , Uncle na gaji wlh , na kassa gano komai , na tambaye ka , ka ki fada min ya ka ke so na yi ? "
Dan murmushi malam ya yi kafin ya ce " Ni daman na sani ba za ka gano komai ba , kawai na kyale ka ne ka kai matar ka dakin ka , Zayd na fada maka in lokacin ya yi za ka sani amma tun da ka matsa bara na fada maka wani dan karamin abu saman ta , Inaya da ka ke gani ba kamar kowane mutun ba ta ke , akwai wata baiwar da Allah ya yi mata wadda ko ita ba ta san da ita ba , a kan wannan baiwar a ke bibiyar rayuwar ta , abu guda ne zai iya sa ta iya gane ta na da wata baiwa har ta iya anfani da ita shi ne ta hanyar aure , kafin mu baro kaduna wasu azaluman mutane sun so su yi anfani da ita wajen mugayan manufar su , dalilin da ya sa na aura maka ita kenan, dan kar su samu damar cin ma manufar su , ni nassan har yanzu su na bibiyar rayuwar mu su na neman inda mu ke amma ka ga cikin wani ikon Allah har yanzu ba su gano inda mu ke ba , kai baza ka san dalilin hakan amma ni na sani abu guda zan roke ka , ka kula min da yarinya ta dan rayuwar ta na da matukar mahimanci musaman a cikin rayuwar ka "
Jinjina kan shi kawai Zayd ya yi ya na son ya ji wace irin baiwa ce haka wadda za ta sa ka a dinga bibiyar rayuwar mutun haka , to su da su ke bibiyar ta me su ke so da ita ? Ko kuma wannan baiwar da malam ke fada ita ce dalilin da ya sa ta ke wasu abubuwa kamar karamar yarinya ? Ya kamata ya ji micece wannan baiwar
" uncle zan so na ji wace irin baiwa ce wannan wadda zai sa a dinga bibiyar ku haka ? " Zayd ya tambayi malam
Murmushi malam ya yi kafin ya ce " Zayd bazan iya fada maka ba , amma zan so ka sani , Inaya ba ta tune da rayuwar mu ta baya , ko za ka bude baki ka tambaye a ina mu ka yi rayuwa kafin mu dawo kano baza ta iya fada maka ba , amma idan ka tambaye ta wani abu saman ka, ko da abun ya yi shekara 20 da wucewa za ta fada maka shi har ma wanda ba ka sani ba , amma hakan bazai yiyu ba har sai kun zama abu guda "
Daga gera guda Zayd ya yi cikin zuciyar shi ya ce " kennan madubiya ce ko kuwa ? "
A fili kuma ya ce ma malam " amma uncle ya za ayi ta manta rayuwar ta, amma ta san rayuwar wasu ko kuma amnesia ce ? "
Girgiza mishi kai Malam ya yi kafin ya ce " Zayd abun guda na sani , duk ranar da ku ka zama abu guda , ita da kan ta za ta ba ka wannan amsar , ni da kai na na jima ina neman wannan amsar amma na rasa , Ina ji a jiki na , Inaya kamar ba ita daya ba ce a cikin gangar jikin ta , amma zuciya ta ta kassa yarda da hakan , idan ma aljanu ne gare ta ko ma minene ita kadai za ta iya ba mu wannan amsar "
dan karamin tsaki Zayd ya yi ya na kauda kai gefe kafin ya juyo ya kali malam ya ce " uncle ku na son ku saka rayuwar ta cikin hatsari ne , ba ku san wanene ni ba , ba ku san da ga ina na fito ba , ba ku yi tunanin ko bibiya ta a ke ye ni ma , ba ku san irin hatsarin da ke cikin rayuwa ta ba ku na neman ku saka ta ta a cikin wannan kangin "
murmushi mai dan sauti Malam ya yi kafin ya kai hannun shi saitin zuciyar Zayd ya ce " ni wannan na duba , ban duba kyawon ka , ko arzikin ka , wannan kadai na duba , saboda na San sai wanda ke da zuciyar maza zai iya ba wa autar tawa kariyar da ta dace , Zuciyar ka mai kyau ce Zayd dalilin da ya sa na yarda da kai kennan " ya kai karshen ya na janye hannun shi
a hankali Zayd ya motsa lips din shi ya ce " Heart ?????? "
yar karamar Dariya malam ya yi kafin ya ce " yo malam Zayd kai ka san minene hakan dan ni ban yi boko ba, yanzu dai mu tafi lokacin sallat ya yi kar mu rasa jam'i "
Malam na shirin tafiya Zayd ya yi saurin cewa " uncle ina son nayi magana da Nesrine kafin mu tafi "
Juyowa malam ya yi ya na kallon cike da tambaya, ko dalilin mi ya ke son magana da Nesrine ? Ya tambayi kan shi
Shi kuma Zayd ya tsaya ya zuba mishi idanu ta cikin glass din shi ya kassa yi mishi magana fada mishi dalilin da ya ke son magana da ita , yau dai zai kawo karshen komai
TO FA NESRINE YAU ZA KI GA FUSHIN ZAYD 🤣🤣🤣
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne