x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - MATAR UBA

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 48848 words

Category: Love Stories

Views 633

02 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ta saka, sannan tayi sallar Maghriba da Isha da Bata samu damar yi ba, bayan ta idar ne ta fad'awa shamsiyya abinda ya faru ran shamsiyya ya b'aci sosai sannan taji tausayin kawarta ta ,Amma babu yanda ta iya tunda a matsayin iwa baraka take a gareta don da Asiyah tabi ta Tata da sun dad'e da Kai karanta human right.

"Yanzu tashi Muje mu Sanarwa Ammi kina Nan Kinga Bata San kin shigo ba ko? "
Ba musu suka fita, Ammi na ganin Asiyah tayi mamakin ganin ta baking bud'e Tace "Asiya kece da Daren Nan lafiya kuwa?"
Tab'e baki shamsiyya tayi Tace "Ammi Nan ma Baki gan ta sanda ta shigo ba a haukace" Nan ta jero Mata komai kamar yanda Asiyah ta fad'a Mata, kad'a Kai Mama tayi Tace "Baraka baza ta tab'a canzawa ba Kenan,Toh Allah ya kyauta, kuje kice ki bata abinci taci ku samu ku kwanta" tana kaina ta tashi ta shige d'akin ta.
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
KUYI HAKURI DA WANNAN, NAYI TYPING NE SABIDA YANZU AN SAMU HUTUN GOOD FRIDAY INSHA ALLAH ZANYI TYPING NA KWANAKIN NAN KAN MU KOMA MAKARANTA

INA MAI KARA BAKU HAKURI FANS SANAN INA GODIYA GA IRIN YANDA KUKE NUNAWA LITTAFIN SO, SANNAN SHIRU NA BA YANA NUFIN NA MANTA KU BANE KUNA RAINA ALLAH YA BAR KAUNA TAKU A KULLUM MILHAT YAR TERAWA

Please vote and comment
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
*MATAR UBA*
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
_(A True Life Story_ )
*Short story*
```Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)```
Follow me on Wattpad @milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ
_('Kungiya d'aya tamkar da dubu)_ _____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* much Love.

NOT EDITED
CHAPTER 11
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
"Yanzu tashi Muje mu Sanarwa Ammi kina Nan Kinga Bata San kin shigo ba ko? "
Ba musu suka fita, Ammi na ganin Asiyah tayi mamakin ganin ta baking bud'e Tace "Asiya kece da Daren Nan lafiya kuwa?"
Tab'e baki shamsiyya tayi Tace "Ammi Nan ma Baki gan ta sanda ta shigo ba a haukace" Nan ta jero Mata komai kamar yanda Asiyah ta fad'a Mata, kad'a Kai Mama tayi Tace "Baraka baza ta tab'a canzawa ba Kenan,Toh Allah ya kyauta, kuje kice ki bata abinci taci ku samu ku kwanta" tana kaina ta tashi ta shige d'akin ta.
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦

WASHE GARI
Da Sallama ta Shiga makeken parlor jikin a Sanyaye, cikin sauri ta Fara haurawa sama, cikin tsawa ta ji ance "And where do you think you are going?"

Baraka na gani a tsaye tana bubbuga kafa had'e dayi Mata wani irin muguwar kallo,jiki a Sanyaye ta Fara saukowa daka stairs, da gwiwowinta ta zube kasa, tana kokarin b'oye hawayen da ya gangaro Mata, cikin Rawar murya Tace "Mummy ina kwana"
Wata gigiticiyar maruka ta shafa Mata sannan Tace " Yar iska karuwar banza daga ina kike?"

Cikin kuka Mai cin Rai Tace " Mummy gidan su shamsiyya nake"
"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Asiyah Ashe haka Kika kware gun karya ki dubi tsabar idona kice min gidan su shamsiyya Kika kwana?" Tana maganar tana yarfa hannu.

" Wallahi daga chan nake Ni ba Yar iska bace"
Tab'e baki tayi Tace " Chan Miki matsalar kice ba tawa ba,tashi ki bani wuri ko yanzun Nan na Tara Miki na jaki"

Cikin sauri ta haura sama,tana Shiga d'akin ta ta sauke ajiyar zuciya, a bakin kofa ta zauna ta had'a Kai da gwiwa kuka take sosai Wanda hakan yasa idanun ta sukayi jajir jiyoyin kanta suka you rad'a rad'a, sai da tayi kuka Mai isarta ta Fad'a toilet tati wanka sannan ta d'auro alwala, bayan ta idar da sallar walha, ta d'auko kayan ta masu datti da niyar wankewa, backyard na gidan ta nufa ta Fara wankin kayan ta, zuciyar ta faal bakin Ciki duk duniyar taji ta daina Mata Dadi a fili Tace "Dama ace ni matattiyace, Ina ma ace nice ba mutu ba ku ba" ta karasa maganar tana kuka tasa hannu ta sharce majinan hancin ta.

Ba ta ankare ba sai gani tayi an waso mata Kaya masu uban yawa a razane ta mike ga mamakin ta Safiyya ce tsaye a gaban ta tana wurga Mata harara tsaki taja sannan Tace "Malama ki bar wanke kayan Nan da kike ki wanke min nawa yanzun Nan"

Murmushin takaici tayi sannan Tace " Safiyya nice zan Miki wanki" tana maganar tana nuna kanta, "eh ke Zaki wanke ko ban Kai na saki bane?"

"Lallai Safiyya wuyanki yayi kauri,ko ba komai ina gaba dake Amma kike min magana kamar wata sa'ar ki?"
" An Miki din Kuma dolen uwarki ki wanke"
" Uwata?"

Cikin sauri Asiyah ta shige cikin fidan tana Kiran sunan Mummy, cikin sauri ta fito "lafiya me ta Faru kike min irin wannan kiran haka?"
" Mummy Zo ki gani"

Cikin Rashin fahimta ta bi bayan Asiyah, Asiyah Tace "Mummy jinga abinda tayi Wai nice zan Mata wanki bayan nace Mata nice gaba da ita ta nemi ta zage Ni"

Yarfa hannu ta Shiga yi sannan Tace " Amma Asiyah kinyi mugun Raina Ni, yanzu ke don uwarki Kiran da Kika min Kenan, to me a Ciki don tace ki Mata wanki?"

" Mummy wanki fa wa Safiyya kanwatace Amma Kuma na Mata a gani na hakan Bai dace ba"
A tsawace Tace " Would you shut up your dirty mouth, ki wanke su sannan ki tabbatar sunfita idan Naga Basu fita ba sai kin sake wanke su, bayan haka Kuma ki goge Mata su, wuwuyar banza idan Kika sake min haka wallahi zan Miki illa"

Ta Maida kallon ta ga Safiyya ta ce " Ke Kuma ki wuce d'aki weather da zafi kije ki Sha sanyin AC"
Murmushi tayi Tace "Toh mummy" tare suka shige suka barta a gun zubewa tayi a kasa duk damuwar duniya ta hadu ta Mata yawa, kukan ma yanzu kasa yin shi tayi, a ranar wunu tayi tana wanki bayan sun bushe ta goge su, sai daff da la'asar ta gama , d'akin ta tashiga tayi wanka
Sannan tayi alwala, bayan ta fito ta saka jallabiyar da take sallah dashi ta shimfida prayer mat 'yar karamar tsaki ta jaa sannan Tace "An sa mutum zaiyi tarikussalat" tana idar da sallah Bata tsaya shafa Mai ba ta zurma uniform d'in islamiyar ta, d'akin Baraka ta nufa tayi Sallama Amma taji Shiru, a fili Tace maybe suna garden, cikin nitsuwa take tafiya harta Isa garden d'in sannan ne ta lura motar Baraka Bata Nan hakan ya tabbatar Mata da Bata gidan, "Safiyya idan Mummy ta dawo kice Mata naje islamiya"

Shiru Bata tanka Mata ba,ta sake Mata magana a Karo na biyu, Bata tanka ba, tab'e Baki tayi ta nufi gate, Cikin gadara da izza safiyya ta kwala Mata Kira "Asiyah!!!"
A nitse Asiyah ta waigo, hannu ta d'aga Maya alamun kizo, har ta juya zata tafi sai Kuma ta dawo da baya, "Gani lafiya?"

Sai da ta d'auki tsawon mintuna biyu tana tsaye Kan Safiyya Tace "Jinga wanchan" tana nuna Mata ledan pure water guda biyu sai tray na silver, da ido tabi hannun ta sannan ta Maida kallon ta gareta Tace "Eh ba gani ya akayi"

"Mummy Tace na Fad'a Miki ki d'auka kije ki sayar sannan idan baki sayar ba Kar ki dawo gidan Nan"
" Islamiyar da?"
" Oho chan Miki, idan Zaki Koma kije ki cire uniform d'in da zai fi Miki kizo ki d'auka Kiyi yanda Tace"
Shiru tayi na 'dan wasu lukata sanan ta hura iska Mai zafi sannan ta shige cikin gida, Safiyya kuwa tabi bayanta da kallo sannan ta kwashe da dariya, "Yarinya Baki ga komai ba, Wanda mummy take Miki nafila ne Akan Wanda Ni zan Miki, Mummy da Bata San da maganar pure wata ba"

Bata dad'e ba ta fito jikinta sanye yake da Pakistan dress green an mishi kwalliya da flowers jaa, da gyallen kayan tayi rolling sannnan ta d'auka ta fita, Mai gadi tausayin ta yaji sosai ganin yanda kamar Abubuwan da suke Mata bai dameta ba, ya Mata fatan Allah ya tsare ta amsa da ameen.

Tasha ta nufa don ta tabbata zaiyi saurin karewa hakan kuwa akayi Bata d'auki awa d'aya ba ta sayar dashi Tass, ta nufi hanyar gida sai da ta shigo estate dinsu ta nemi inuwar wata bishiya ta zauna tana huta gajiyan da tayi don ta tabbata in ta Koma ba barin ta za'a yi ta huta ba.

********
Motar Hashim na gani yana tukin Yana dube dube ko Allah zaisa ya ga wucewar ta don ya tabbata zuwa yanzu an tashi daga islamiya, parking a gefen titi kansa ya d'aura a Kan steering motan, da zaran ya rufe idon say ita ce take Masa gizo kullum cikin tunanin ta yake baida aiki sai tunaninta yayin da wutar so da kaunar ta yake Kara kururuwa a birnin zuciyar sa, hannu yasa a aljihunsa ya Ciro d'ankwalin ta da Bari ya sa a fuskan sa ya d'auki tsawon lokaci a haka, ganin basa ta Zo ba ya jaa taking ya kalli gefen motar sa, har ya tada motar sai Kuma yayi saurin kallon gidin bishiyar dake gefen motar sa, zaro idon sa yayi don ganin ita dince ko gizo ta ke masa, Murmushi yayi had'e da dariya Wanda baisan sanda yayi ba, da sauri ya bud'e kofar motar ya fito, ya dad'e a tsaye a kantaΒ  ganin kamar kuka take yasa yayi sauri ya sunkuya yace "Kuka?"
A razane ta d'ago Kai ta kalle shi, ganinsa yasa ta d'an jaa da baya,cikin tashin hankali yace "Meyasa kike kuka? Me aka Miki?"
Tashi tayi da niyar barin gun yayi saurin fad'in "Dan Allah ki saurare Ni, yau shine Karo na uku ina neman magana dake Amma kin hanani Dan Allah kinda shine zai Zama taimako na karshe da zan nema a gunki ki saurare Ni"

Shiru tayi a zuciyar ta Tace " Asiyah ki saurare Shi kiji da me yazo Miki, ko h
Ba komai ya ceci rayurwar ki a gun Yan iskan Nan, da Allah ne kad'ai yasan abinda zasu Miki"

Kai a kasa tana Wasa da hannun ta Tace "Ina sauraron ka"
Murmushin samun nasara yayi yace "Daga farko dai Ni suna na Hashim,ko zan iya sanin sunan ki?"
Chan Ciki ta amsa " Suna Na Asiyah"
Murmushi yayi yace " Nice name Asiyah, Ina so mu kulla abota da ke ,idan Kuma Zaki bani dama na zame Miki jigo a Rayuwar ki?"

'dago kanta tayi Tace " Jigo kuma? Kamarya?"
Murmushi yayi yace " kina da murya Mai Dadi,Ina nufin na zame Miki Dan Uwa Amma fa idan baza ki damu ba?"
Murmushi tayi Tace " Na amince , nagode ranar ka Shiga tsakanina da mugayen nan"

Shafe kansa yayi, sai ya juya Mata baya Yana Jin wani Dadi a ransa ko ba komai yasan baza ta manta dashi ba, sai ya juya da niyar Mata magana, ga mamakin sa bata gun, a gigice ya Fara duba ta Bai ganta ba , ya duba yaga ta manta tray d'inta , ya d'auka da sauri ya Shiga mota ya kunna Mata key, ya Fara yawon duba ta, Cikin Sa'a ya hango bayan ta tana Shiga cikin gida, Murmushi yayi yace "So Nan ne gidan su" sai ya juya ya bar gun.
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
PLEASE SHARE AND COMMENTS

πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
*MATAR UBA*
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
_(A True Life Story_ )
*Short story*
```Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)```
Follow me on Wattpad @milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ
_('Kungiya d'aya tamkar da dubu)_ _____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* much Love.

```NOT EDITED
CHAPTER 12
PREVIOUSLY```
Shafe kansa yayi, sai ya juya Mata baya Yana Jin wani Dadi a ransa ko ba komai yasan baza ta manta dashi ba, sai ya juya da niyar Mata magana, ga mamakin sa bata gun, a gigice ya Fara duba ta Bai ganta ba , ya duba yaga ta manta tray d'inta , ya d'auka da sauri ya Shiga mota ya kunna Mata key, ya Fara yawon duba ta, Cikin Sa'a ya hango bayan ta tana Shiga cikin gida, Murmushi yayi yace "So Nan ne gidan su" sai ya juya ya bar gun.
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
.......... Driving yake Yana Murmushi, shafa gashin kansa yayi sannan yace "Ya Allah ka mallakamin yarinyar Nan" sai Kuma yayi shiru na 'dan wasu lokuta Kan yace "Amma me yake damin ta kullum cikin kuka take, damn it" ya fad'a a tsawace had'i da boga Kan stirring motar sa, cikin wannan tunanin ya Koma gida.


Tana Shiga gida ta sauke ajiyar zuciya Hadi da Zama a Kan Yar karamar kujerar Mai gadi, zamanta yayi dai dai da fitowar sa daga ban d'aki hannun sa rike da buta Yana d'aure mazargin wandon sa, cikin sauri ta kau da kanta had'e da mikewa, cikin sanyin murya ya ambaci sunan ta a hankali ta Juyo ta amsa da "na'am" "lafiya kike kuwa?"

"Eh lafiya Lau baba"
"kin tabbata?"
" Eh"
" Toh Shikenan Shiga gida abinki" Kai kawai ta d'aga Masa ta shige cikin gida, Kai tsaye d'akin Safiyya ta nufa, ganin bata d'akin ta ajiye kud'in da ta sayar da pure water a Kan gado tayi ficewar ta.


Bayan ta Koma d'akinta ta tayi wanka, wata irin muguwar yunwa take ji, jiki na Karfi ta sauko ta Shiga kitchen dukkanin jikin ta ciwo yake Mata, indomie ta girka ba b'ata lokaci ya nuna da ke Alan gas cooker ne, bayan ta gama ta zauna a kitchen din ta cinye Tass ta had'a tea d'inta Mai kauri ta Sha bayan ta gama ne ta wanke kwanon da kofin da ta Sha tea din ta gyara kitchen 'din tsaf kamar ba'a yi komai a cikinta ba, d'akin ta ta Koma tayi sallar Maghriba kana ta Fara tilawar haddar ta, bata tashi a gun ba har sai da aka kira sallar Isha bayan ta idar ta jero azkar 'din da ta Saba kana ta tashi ta sawa kofar d'akin ta key ta Koma ta kwanta, bacci Tasha sosai don har sai da ta kusa makara sallar asuba,mamaki ne ya kamata ganin babu Wanda ya neme ta ba Safiyya bare Baraka.

Tashi tayi da addu'ar tashi daga bacci kana ta Shiga ban d'aki ta d'aura alwala tayi Sallah kana ta Fara gyran gidan, karfe Bakwai ta gama komai ta had'a musu breakfast ta jera akan dinning already dama taci nata sai da taji ta koshi Kan ta fita daga kitchen 'din, ta haura don Shirin makaranta.

Baraka na saukowa daga d'akin ta ta Fara dube dube da kalle kalle ko zata ga wani Abu Wanda ba dai dai ba, girgiza Kai tayi a bayyane Tace "Allah ya taimake ki."

Bayan ta gama Shirin ne ta fito har kasa ta durkusa ta gaida ta,chan Ciki ta amsa, Bata tsaya 'bata lokaci ba tayi ficewarta, bayan ta fita Bata yi nisa sosai ba ta hango motar su shamsiyya da sauri ta karasa inda suke tana waigawa a ganin ta Baraka na kallon ta, tana Shiga ya sawa motar key Bai tsaya ko Ina ba sai school.


Safiyya na gani tana saukowa tana tauna chin gam, hannun ta rike da wayar ta yayin da d'ayar Kuma na rike da jakar ta, dinning ta nufa ko kallon inda Baraka take batayi ba, a tsawace Tace "Ke don ubanki baki ganni bane?"

A 'dan tsorace Tace "Haba mummy kin tsorata Ni wallahii"
A Karo na biyu ta Kuma cewa "Baki ganni bane nace?"

"Na ganki Mana mummy"
"Okay kin ganni Amma baza ki iya ce min ina kwana ba?"
"Kar ki Zama Haka Mana please gaisuwa Kam ai ba Dole bane ba,kawai kin Zo kin tsorata mutum?"

" Lallai wuyan ki ya Kai na yanka ,iyee Ni kike fad'a wa haka?"
Tashi tayi Tace. " Ni wallahii kin isheni ke Baki da aiki sai surutu da shegen masifa Kya Kya Kya kamar agwagwa Bari na tafi na bar Miki gidan Kiyi ta surutanki ke kad'ai"

Tana Kai Nan ta fita, driver ya jaa motar suka bar gidan, Baraka Kam kasa Motsi tayi, dafe kirjin ta tayi Tace "Yau me zan gani Safiyya yace take Gaya min magana Haka? Ni Kya kya, aiko Banga ta Zama ba , alamu sun nuna maganin Nan ya daina aiki Dole na sake komawa gun Malamin Nan, cikin sauri ta haura sama, ba 'bata lokaci ta sauko hannun ta d'auke da jaka, ta saka wata shegiyar eye glass kamar na baba ari🀭 , Bata zarce ko Ina ba sai gidan kawar ta, ta kwashe Mata yanda sukayi da Safiyya, "tirkashi Aiko Baki ga tazama safiyyar ce ta ce Miki haka? Gaba gaba Kam ai dukan ki zatayi Naga alama"

" Ke dai bari kawata yanzu ai tashi zakiyi Muje gun malam gobe da nisa"
" Toh muje barina d'auko wayata ko?"
" Okay ta Shikenan zan jira ki a mota"
" Alright"


Bayan ta d'auko wayar tata ta iske Baraka na jiran ta a mota,tana Shiga ta sa wa motar key suka bar gidan sai gun malam.



Wata iriyar dariya yayi yace "Ai na fad'a Miki maganin bazai dad'e a jikinta ba sabida Soyayyar da 'yar ki take yiwa yarinyar Nan sone na Yan uwan taka, baza ki iya Shiga tsakanin suba"


Kallon juna sukayi kana maman Yesmin Tace "Amma boka ya kamata ace akwaiwata mafita ai ko?"
Ya amsa da " Eh to baza a rasa ba"

Gyara Zama Baraka tayi tana Murmushi had'e da fad'in "yauwa"
Dariya yayi kana yace "daka ta kiji Ko mene ne tukunna"
"Boka ko mene ne zanyi in dai bukata ta zata biya"

" Aljani 'dan maliki Yana bukatar jikin ki, idan kin shirya ki Shiga daga Ciki" Yana nuna Mata d'akin dake bayan sa, dafe
End Ads