ta da Hira tun bata kulashi ta har ta Fara bihe mishi,sun cikin hirar a ka shigo da abincin.
Wurin Zama na musamman Wanda akayi don cin abinci a office d'in ajiye Mata akayi,tashi tayi a nitse ta nufi inda abincin yake tana ganin abincin tun Kan ta Fara ci yawunta ya tsinke, ganin irin kallon da Ammar ke mata hakan ya sanya ta nitsu ta fara cin abincin,sai da taci Mai isarta Kan ta tashi daga kan abincin,ta Sanar Masa da zata duba Asiyah, tare suka fita.
Hashim na zaune akan gurer dake gefen gadon da Asiyah ke kwance sai faman gyangyad'i yake, Sallamar da sukayi ne yasa ya Bud'e idanunsa ya d'aura su akan Badiyya,ganin Ammar na biye da ita yayi saurin kauda kansa.
Ammar Kan ta Asiya ya nufa Yana duba idonta da aka rufe da bandaji da jini akai Hashim yace "When will you remove the bandage?"
"After three days"
"Alright"
" Please can I talk to you for a moment?"
" Are you talking to me?" Hashim ke wannan Tambayar
" Yeah you" sai ya fice Hashim ya bi bayan sa.
Office din Ammar suka nufa bayan sun zauna,ammar ya Fara bashi hakuri kana ya Kara Masa bayani akan abinda ya gani Shirin Hashim yayi Yana kallon sa har ya gama sannan yace "Okay I believe you"
"Thanks does that mean you're going to marry Diyya right?"
" Nooo I can't marry her"
" But....but why?"
"cos I don't love her"
" No hash is a lie, you're lying you Love her,and you'll forever love her"
"Hmm no I don't the only girl in my heart is Asiyah"
" The girl you bring here?"
" Yeah"
" But hash you can marry two wives or more,you can marry them both, after all you're rich you can take care of them all."
"You're right but I don't have interest of marrying two wives"
"Is okay I won't force you since you are not interested"
"hmm.... But Ammar....... You can marry her you know"
"hahaha are you kidding me I can't marry the woman I don't love and am already married to the woman I love, and we have two children"
"Wow that's very fast,stay blessed"
Mikewa yayi had'e da Mika Masa hannu yace "Thanks" Hashim ya amsa da "You're welcome"
Badiyya da tun d'azun ta lab'e tana jin dukkanin abinda suke cewa, tayi saurin barin gun ta koma d'akin da Asiyah take.
Kalaman sa ne suke yawo a zuciyar ta "The only girl in my heart is Asiyah"
Hakan yasa ta fashe da kuka "Aunty kukan me kike?"
Muryar Asiyah ne ya sa ta yin shiru.
"Aunty na san sabida Ya Hashim kike kuka ko?"
"A....a a ba...baa shi bane kawaii dai bana Jin dad'i ne"
"Hmmm haba aunty na zauna dake tsawon watanni nasan Wace ce ke,ke jarumar mace ce, Amma na lura weekness d'in ki Hashim ne, kina matukar son sa fiye da tunanin me tunani,Amma aunty me yasa Baki Sanar dani cewar kunyi soyayya a baya ba?"
Cikin muryar kuka Tace "Sabida baida amfani, ke yake so yanzu ba ni ba like he said am his past and you're his present,so it's not a big deal"
" No ba haka bane Hashim Yana sonki, har kuka yayi d'azu bayan haka maganganun sa sun nuna cewar haryanzu Yana Jin haushin Dr Ammar in da ace baya sonki da zuwan yanzu da ya manta da ke Amma Bai Manta dake ba"
"Hmm Asiyah Kennan ya jikin naki hope ba Kya Jin komai?"
"Bana Jin komai,meyasa Kika canza zancen?"
" Sabida bana bukatar hakan,Kinga da ace muna da Kayan aiki ni zan Miki aikin a nija Amma Sabida rashin Kayan aiki masu Karfi shiyasa na Bari aka kawo ki Nan"
"Amma aunty kina ganin zan sake gani?"
"Eh da yardan Allah, Ammar na da kokari sosai Abokina ne,Kuma ta tabbatar Mana da cewar aikin nakin is a success,Nan da kwana uku za a cire Miki bandejin"
Murmushi tayi Tace " Nagode sosai aunty ba don ke ba da ban San halin da nake ciki ba yanzu"
" Shhhsh, karki Ce haka,Allah baya barin wani don wani ki daina fad'in haka kinji"
"Insha Allah bazan sake ba"
"Asiyah kin San mene ne burukana a yanzu?"
"A'a sai kin fada"
"A baya baban burina shine na Zama likitan Ido,sannan na Aurin na mijin da yake Sona nake son sa,Allah ya cika min burina na farko Amma na biyun Sam ya fita a Raina,tun sanda na had'u dake nake burin naga kin samu lafiya dake nake kwana nake tashi sai yau Allah ya cika min wannan burin nawa abinda ya rage shine a Kama wannan Mara imanin Baraka da yarta"
"Ni kaina na kosa na samu lafiya sanida na dauki fansar mahaifana da kanwata da ta kashe"
" Insha Allah ni zan cika Miki wannan burin naki" Hashim ke wannar maganar zagayawa yayi ya rike hannun ta "Banji kin ambaci maganar auren mu ba ko dai kin fasa be?"
Murmushi kawaii tayi batace Masa komai ba ita a ganin ta cin fuska ne yake yiwa Diyya hakan yasa ta zare hannun ta a nashi a hankali.
Babu Wanda ya sake cewa komai sun d'auki tsawon mintuna ashirin Kan yace "Ni zan koma masauki,akwai wani abunda kuke so ne na kawo muku?" Yana maganar idonsa akan Diyya.
Kawar da kanta tayi yace "Diyya magana nake kinyi shiru, babu abunda kuke bukata?"
Murya na rawa Tace "Wanka"
Zaro Ido yayi ya kalle yace "Wanka zan kawo Miki?"
"Ina nufin Wanka nake son yi"
"Oh okay,but idan muka tafi wa zai kular min da my queen?"
Asiyah tayi saurin fad'in "Kar ka damu akwai nurse ai zata kula dani,yanzun ma nace Mata yunwa nake ji zata kawo min abinci,Amma asibitin Nan yayi daga cewa ina jin yunwa sai a ce za a kawo min"
Dariya Hashim yayi yace " Malama kud'in mu zaki ci duk Yana cikin hospital bills so ba kyauta zasu Baki ba"
" Oh to sai yanzu na fahimta"
Shafa kanta yayi yace "You look more beautiful when you smile queen"
Ya Maida kallon sa ga Diyya yace
"Muje ko?"
Kai kawaii ta d'aga masa, ta fice, ganin ta fita ya manna wa Asiyah kiss an goshi yace "Sai mun dawo"
"Take care."
Tarar da ita yayi tana tsaye a katafaren gate na asibitin sai da ya tare taxi yace "Muje ko?"
Ko kallon sa batayi ba ta shige motar, d'aga kafad'a yayi "Kinyi a banza" Yan aiyana hakana a ransa.
Bayan sun Isa hotel din da suka sauka, ta shige d'akin su Shima ya shige nasa, Diyya Kai da gwiwa ta had'a Banda kuka babu abinda take yi sai kuka ta dad'e a Haka na ta tashi ta shiga ban d'aki ta d'auro alwala dake tayi sallar azahar a asibiti, sallar la'asar kawaii tayi akan sallayar baccin wahala yayi awun gaba da ita, ganin bata fito ba hakan yasa ya nufo d'akin su ya dad'e Yana kwankwasa kofan Amma shiru hakan ya sa ya tura kofan ya shiga.
Ganin ta dukun kune sai sharar baccin ta take yace "lallai ma wato Nan baccin ta ma take hankali kwance ni Kuma na tsaya Zaman jiranta" hannu yasa zai tada ta sai kuma ya fasa "maybe baccin take bukata zan tafi kawaii idan ta tashi ta same ni a chan, ficewar sa yayi ya ja kofar.
Hiran su suke Sha sosai da Masoyiyar sa,tun farkon Soyayyar su basu tab'a Hira sama da mintuna talatin ba hakan yasa yake Jin wani irin farin ciki na musamman.
Diyya na tashi daga bacci ta sa hanni ta d'auki wayarta karfe Bakwai saura, tsaki tayi Tace "Me yake yi haka tun dazu Bai min magana ba"
Message ta gani a fuskar wayarta "Na shigo na samu kina bacci shiyasa ban tashe ki ba, idan kin tashi ni na wuce asibiti sai kin zo"
Tsaki kawaii tayi ta shiga bathroom ta watsa ruwa sannan ta shirya ta d'auki Kaya set biyu wa Asiyah tasan Dole zata bukaci wanka.
Taxi ta hau ta wuce asibiti, tana shiga d'akin ta tarar dasu sai dariya suke sai taji ba Dad'i da sallama ta shiga Asiyah ce kad'ai ta amsa Mata sallamar "Aunty kin tashi? D'axu nake tambayar Ya Hashim inda ya baro min ke yace min Kanki na ciwo kina bacci da fatan kinji sauki ko?"
Kallon shi tayi taga ya kauda Kai "To meyasa ya mata karya?" A ranta ta aiyana hakan a bayyane kuwa tace "Alhamdulillah da sauki stress ne kawaii dama"
"Allah sarki Allah ya sa kaffarane"
"Ameen"
"Ya kamata ki watsa ruwa tun safe rabon ki da wanka, gashi Kuma nasan bakiyi sallah ba"
Murmushi tayi Tace "Zanyi"
Da taimakon ta suka shiga ban d'aki tayi wanka,duk a ban d'akin tasa kaya sannan suka fito tare.
Zaunar da ita tayi a bakin gado tana shafa mata Mai suna Hira sama sama.
Hashim mamakin diyya yake meyaay take taimakata bayan yasan halin Diyya da muguwar kishi duk da tasan cewar Yana son Asiyah hakan bai Hana ta daina kula da ita ba, Allah ya sa ba da wata manufa take ba..
Kwana a tashi ba wuya a wurin Allah a yaune za a bud'ewa Asiyah Dr Ammar ne a kanta Saida ya Mata wasu allurai yace Nan da awa d'aya zai Bud'e Amma Kan ya fita yace da ita wane ne take son fara gani idan aka Bud'e Mata ido, ga mamakin su ta ambaci sunan Badiyya, duk sun d'auka Hashim zata ce har ita kanta Diyya tayi mamakin Jin hakan Tace "Amma Asiyah me yasa kikace ni kike son fara gani?"
"Aunty you're like an angel to me, I just want to see you"
Murmushi kawaii tayi,yayin da Hashim yake mamakin irin shakuwar dake tsakanin Asiyah da Diyya, Ammar fita yayi awa d'aya na cika ya shigo da nurses guda biyu a biye dashi.
Ba Asiyah kad'ai ba hatta Diyya da Hashim Saida sukaji kirjin su ya soma bugawa.
💦💦💦💦💦💦💦💦
Please share and comment
💦💦💦💦💦💦💦💦
*MATAR UBA*
💦💦💦💦💦💦💦💦
Daga Alkalamin ✍️
*Milly*
Fadilah Yakub
*(MILHAAT)*
*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️*
*M. W. A*
*Bismillahir Rahmanir Rahim*
```NOT EDITED
CHAPTER 26```
"Aunty you're like an angel to me, I just want to see you"
Murmushi kawaii tayi,yayin da Hashim yake mamakin irin shakuwar dake tsakanin Asiyah da Diyya, Ammar fita yayi awa d'aya na cika ya shigo da nurses guda biyu a biye dashi.
Ba Asiyah kad'ai ba hatta Diyya da Hashim Saida sukaji kirjin su ya soma bugawa.
💦💦💦💦💦💦💦💦
.......... "Are you ready?"
Ammar ke wa Asiya wannan tambayar Murmushi tayi ta d'aga Masa Kai alamun eh, Shima Murmushin yayi ya kalli Hashim yace "She likes laughing"
Murmushi kawaii ya Masa.
A hankali ya Fara cire bandage d'in Diyya da Hashim duk hankalin su na kanta , sai da ya rage bandage d'aya Ammar ya ummurci Diyya da ta tsaya a gaban Asiyah hakan kuwa akayi, bayan ya cire idanun ta a rufe yace "Open your eyes slowly and carefully"
A hankali take Bud'e idanun ta tana ganin wuri bashi bashi ba idanunta na wassakewa ta sauke su akan wata kyakkyawar halitta fara, ba doguwar bace sannan ba gajera bace Murmushi tayi Mata ita ma Maida Mata "Aunty Diyya kece?"
"Eh nice" idanun ta ya cika faal da hawaye mikewa Asiya tayi ta rungume ta kyam a jikin ta cikin kuka take Mata godiya.
Gyaran murya Hashim yayi "Wato ni ba a damu dani ba ko? kin ma manta Dani?" Yadda yadda maganar ne ya sanya ta dariya Yana magana Kamar d'an shekara biyar harda langwab'ar da Kai, Kare Masa kallo tayi ganin yanda ya canza ya Kara haske ya Kara kyau.
Karasowa yayai gaf da ita Diyya ganin zai iya ture ta, ta matsa ta basu wuri, kallon kallo sukeyiwa juna, wani irin wutar son junnan su ne ke tafarfasa a cikin zukatan su, hannu ta ya riko yace "Nayi matukar murna da idanun ki suka dawo Baki ji yanda nake ji ba ba yau"
"Hmm nago..... " Saurin rufe Mata Baki yayi da lausassan hannun sa ya gyad'a Mata Kai had'e da fad'in "Ban bukatar kalmar godiya daga gare ki, Nayi wannan ne a matsayin ki na wacce na fiso, wannan kad'an ne, sannan kofa a Bud'e take idan kina bukatar wani abu just tell me"
"Ko wacce irin bukatar da Zama maka dashi zaka min?"
"Eh insha Allah just name it"
Diyya har ta Isa kofa zata fita Asiyah Tace "Aunty Dan Allah kizo"
Ba musu ta karasa inda suke, kallon sa tayi Tace "Inaso ka had'a ni da Aunty Diyya ma'ana ka aure mu"
Zaro Ido yayi yace "Amma wasa kike ko?"
"Dagaske nake"
Iska ya hura Mai zafi yace "Na amince" ya Maida kallon sa ga Diyya "Da fatan zaki amince da hakan My Diyya?"
Saurin 'dago kanta tayi tana kallon sa cike da mamaki sakin hannun Asiyah ya nufi inda ta tsaya Murmushi yayi yace "Kina mamaki ne?"
Kai kawaii ta d'aga Masa Murmushi yayi yace "Maganar aure ne ya baki mamaki ko Kuma Kiran ki da nayi da My Diyya?"
Kai a kasa murya chan ciki Tace "Duka biyu"
"To ki daina mamaki kinji"
Kai ta d'aga Masa idanun ta hawayene ,d'aga habarta yayi yace "Kuka? Please ki daina" ai kuwa kamar ce mata yayi ta kara, ganin kukan yayi yawa ya rungume ta, a tare suka sauke wani ajiyar zuciya.
Asiyah sai Murmushi take (Ni ko nace Asiya Murmushi Kuma ko Yar kishin Nan babu) Diyya da Hashim sun Lula wata duniyar,dama gogan naku Yana so Yana kaiwa kasuwane a kunne ya rad'a Mata "I miss you Bae"
"I miss you too" Kara kankame ta yayi a jikin sa kamar zai Maida ta cikin cikin sa.
Gyaran muryar da ammar yayi ne suka tuna Basu kad'ai bane yayi saurin sakinta kamar wani Mara gaskiya.
Dariya Ammar yayi yace "Congratulations Asiyah"
"Thank you Dr"
Hashim yace "Is there anything left?"
"No I have already discharge her"
"Good in that case we are going back to Nija tommorow"
" What so soon?"
"Yeah what will we wait for?"
"you're right, but Amma gonna miss you guys"
"Same here bro, you'll attend our wedding right? Cos you'll be our guest of honor"
"Insha Allah, ill be there."
A motar sa ya Maida su har masukin su, sannan yace zai dawo da yamma su fita cin dinner, Hakan kuwa akayi karfe takwas ya dawo ya d'auke su suka fita,tare da matar sa suka zo, Sunci sun Sha har sai karfe goma saura ya dawo da su, sannan ya musu alkwarin Kai su airport.
Baccin su suka Sha Mai dad'i Amma Banda Asiyah tana ta tunanin abinda zata tarar indan ta koma gida sai kusan karfe uku amba dare ya barci ya sace ta,karfe biyar saura ya kwankwasa musu kofa, tashi sukayi sukayi sallah sannan suka shirya, karfe biyar da Rabi Amma ya kirasu cewar Yana waje, already sun so jakar su kawaii suka d'auka suka fita, Hashim na ganin jakar hannayen su yasa hannu ya karb'a.
Hira suke Sha duk su ukun har suka karasa inda motar Ammar yake,ban kwana suka Masa,shi kuwa yace Yana Nan Yana zaman jiran IV.
Suna shiga jirgin ko wannen su ya duba sit d'insa wannan karon shi ya zauna a tsakiyar su, kallon shi sukayi sai ya d'aga musu gira kallon juna Asiyah da Diyya sukayi suka tuntsire da dariya, Zama sukayi Sabida Ana sanarwa jirgin zai tashi,Hira suke sama Asiyah ce ta Fara bacci, ba a d'au lokaci Mai tsawo ba Diyya ma bacci ya d'auke ta sai zuba surutu yake Jin ba mai bashi amsa ya Dubai yaga duk sunyi bacci,ganin yanayin baccin nasu zai iya sanya musu ciwon wuya ya rungume Diyya da hannu d'aya kana ya kwantar da Asiyah a cinyar sa, daga bisani Shima baccin ya d'auke sa.
Diyya ce ta Fara farkawa, Murmushi kawaii tayi ta sake komawa baccin ta, basu farka ba har sai da jirgin su ya sauka Nija, a hankali Suma fara Bud'e idanun su. Idanun shi ya sauke Akan Diyya dake ta kallon sa gira ya d'aga mata Yana Mata kallon lafiya, Murmushi tayi Masa ya sa hannu ya shafa fuskar ta, Asiyah kuwa Mika ta shiga yi "Wayyo bayana"
Dariya sukayi yace "Allah ya bani hakuri Ni da kuka danne Ni"
Asiya Tace "hakkin Kane kula da mu,ko ba haka bane aunty?"
" Hakane Kanwata"
"Au had'e min Kai zakuyi lallai sai nayi da gaske"
Dariya kawaii sukayi,suna fita suka Tarar da Faysal na jiran su,Gidan su Diyya suka wuce yace "Zan zo Hira anjima" sukayi wucewar su.
Umma tayi matukar farin cikin ganin su musamman da yanzu Asiyah tana gani "Haba Badiyya tunda Kuka tafi ba Kira shiru haka gashi Ni ko na kira ba samun ki nake ba"
"Yi hakuri Ummu wallahi tunda mukaje muke ta fama da zuwa asibiti ban zauna ba shiyasa"
"Tunda an Samu abunda aka je nema ai Shikenan"
"Yanzu Asiyah ya ake ciki da maganar Baraka take da suna ko?"
"Eh umma Baraka,ban San yanda ake ciki ba,Amma insha Allah gobe zanje Ni gidan maman Yesmin naji yanda ake ciki"
"Har sai mun jira gobe? Ai ki tashi mu tafi kawaii yanzu,baza ki gane yanda na damu da aka Mata ba"
"Aunty daga dawowar mu sai mu fita ga gajiya ko hutawa ba muyi ba,ki Bari sai gobe kawai"
"Gaskiya Asiyah take fad'a ku bari sai gobe kuje d'in" umma ke wannan maganar.
"To" kawai Diyya tace don taso su je a yau d'in nan.
Mummy tayi mutukar farin ciki duk da Bata San dalilin sa na tafiyar ba, kwata kwata kwanaki biyar yayi baya gidan Amma ji take kamar ya fi wata,bayan ya huta ne ta zaunar da ita duk abubuwan dake tafiya, Kama daga kan Maganar Shirin auren da yayi na karya da Safiyya, har izuwa 'batan da Asiyah tayi da samun lafiyarta da Kuma Shirin da suke na kama Baraka, har izuwa alkawarin auren da yayi wa Asiyah da Diyya
"Oh Hashim duk wannan abubuwan dake faruwa Amma baka sanar Dani ba sai yanzu? Dama da Badiyya kuka yi tafiyar?"
"Eh da ita mukayi,sabida itace take kula da ita, Am sorry Mom naga Sam Baki kaunar yarinyar ne shiysa"
"A'a Hashim ba Haka bane kawaii dai naga yanda duk baka damu da kanka bane sai ita shiysa Kuma kasan bani da wani buri da ya wuce ka koma Kan aikin Mahaifin ka"
" Insha Allah Mom satin Nan zan Fara zuwa aiki"
" Aiko da na ji dad'i, yarinyar Nan Badiyya Yar Albarka ce duk irin Soyayyar