x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 14 - MATAR UBA

  • 39001 words
  • 42000 words
  • Out of 48848 words

Category: Love Stories

Views 639

02 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
dariya"
" Tunda ke baza ki fita ba Ni bara na fita bar Miki d'akin"
Wayar say ya d'auka ya nufi hanyar fita sai da yazo daf kofar yace "Idan kin gama ki rufe min kofar" yayi ficewar da, Badiyya bin bayan sa tayi da kallo ita gani take abin kamar Wasa Amma dagaske yake,zama tayi a bakin gado ta shiga kuka sai da tayi Mai isarta kana ta shiga toilet ta wanko fuskar ta, tana fitowa da fice daga d'akin ta rufe Masa kofar kamar yadda yace ta ajiye Masa makulli a inda yake ajiyewa.

Yana ganin fitowar ta yayi saurin d'aura waya a kunnen sa kamar Yana waya, kallon sa ta tsayi tafi minti biyar tana kallonsa,Hashim ganin zata iya Karya Mata zuciya hakan yasa yayi saurin barin gun, kad'a Kai tayi ta fice da ga compound d'in.

Yana ganin ta tafi ya koma d'akin,kwanciya yayi Yana jallony saman d'akin yana tunanin happy moments da sukayi spending da ita,tabbas Yana kaunar ta Amma bazai iya auranta ba.

Badiyya bata gaji da bibiyarsa ba,amma ganin wulakancin a yake Mata hakan yasa ta hakura,har suka kammala projects d'insu Bai bari sun hadu ba haka Kuma baya picking calls d'inta d'ga bisa ni yayi blocking d'in ta,ya goge duk wani abun da ya shade ta, number ne kad'ai ya bari Shima Kuma bai San dalilin da yasa ya kasa gogewa ba.

NIGERIA
A tsawace yace "Baka da hankali dama ban sani ba? Ni kake so ka kunyata a idon duniya Hashim?"
Kai a kasa yace "No  daddy ba haka  bane, babu yanda za'a yi na jawo maka abin kunya,Amma idan ka bari aka d'aura aure na da Badiyya shine abun kunya ba auren ta ba"

Zama Daddy yayi yace " Me yasa kace haka,akwai wani abinda ya kamata na sani wanda ban sani ba?"
"Eh Daddy"
" Uhmn ina sauraron ka" Maida hankalin sa yayi don ya fahimci inda Maganar tasa ta dosa, bai rage komai ba haka Bai Kara komai ba, Mummy dake zaune tun d'azu akan sofa Tace "Kai Hashim kaji tsoron Allah ka fad'a mana gaskiya dukkanin mu mu mun San Badiyya yarinya ce mai tarbiya"

" Hakane Mummy amma Badiyya da kuka sani a baya dabance da ta yanzu"
Ta amsa da " Allah ya kyauta"
Suka amsa da "Ameen"
Daddy yace "Tashi ka je zan duba na ga yanda za'a yi"
Yace "Toh Daddy na gode"
Ya tashi ya fice.

Daddy Maida kallon sa yayi ga Mummy yace "Amina,ya kike ganin zamu b'ullowa al'amarin yaran nan,wallahi kaina ya kulle"
" Nima haka Alhaji,to Amma ya zamuyi yaron Nan dai shi ga yarinyar Nan yace Yana so,Kuma yanzu yace ya fasa bai kamata mu sa shi yin abinda baya so ba"

"Okay idan ma fahimce ki,so kike na janye Maganar auren sa da Badiyya Kar ki manta fa, Mahaifin yarinyar Nan amini na ne fa,idan na Masa haka ai ban kyauta Masa ba"
" Hakane Alhaji,Amma ya kamata ka Sani yaran yanzu ka haife sune Amma baka haifi halinsu ba,tunda yace baya so a janye Maganar Kar Kuma a Zo Ana da na sani"
"Kai Amma banji Dadi ba ko kad'an yanzu ban San yanda zan tin Kari Alhaji Usman ba"

" Ka kwantar da hankali Alhaji,yanzu tunda dama jiran su Hashim ake a had'a auren su day Fadeelah ina ga kawai gara a Sanar dasu ayi bikin Nan Nan da wata d'aya"

"Toh Shikenan zan duba na gani"
Tashi yayi yace "bari na watsa ruwa idan yaso zan nemi shi Mahaifin Suraj d'in in yaso zanje har gida na Sami Usman muyi Magana ta fahimta don wannan ba Maganar waya bace"
"To alhaji a fito lafiya,kamun Nan bara na kawo maka abinci"
"A a hajiya bar abincin Nan duk ina ji ba Ni da appetite"
"Toh Shikenan yanda kake so hakan za'ayi."

Bayan ya fito Kai tsaye ya zarce gidan su Badiyya, ya Sanar da mahifin ta Akan cewar Hashim ya janye Maganar auren yarsa, sannnan ya bashi hakuri, Alhaji Usman mutum ne Mai hakuri sannan ya d'auki hakan a matsayin kaddarar Badiyya, ya Kuma Masa alkawarin hakan bazai shafi abotar su ba,yayi Masa godiya ya tashi ya koma gida,ya sanar da mummy yanda sukayi jikinta yayi sanyi matuka.

Tace "banji dadin abin Nan ba Sam,Nima insha Allah gobe da safe zanji Ni gidan nasu na bawa mahaifiyar ta hakuri, yanzun ma don dare yayi ne da naje"
" Sai Kuma kiyi,duk laifin kine duk kin bi kin sangarta yaro"
Yana kai Nan ya haura sama sai surutai yake ya na d'aga hannu.

Mummy Tace "Oh 'ya 'yan kuka mai jawo wa uwar sa jifa,Allah shi kyauta" sai ji tayi yace "Ameen" ba tayi tunanin yaji ba hakan yasa tayi ficewa daga part d'in say ta koma part d'inta, hashim ta tarar a parlor a kishingide kana ganin sa kasan Yana cikin damuwa,cewa tayi "Damuwa ko? Baka ga komai ba tukanna"

"Haba mummy ya kuma Zaki ce haka?"
"Me kake so Na ce maka Hashim? Tunda burinka shine kaci mutuncin Mahaifin ka,to yaje gidan su Badiyya an janye auren hankalin ka ya kwanta?"
Ji yayi kirjin sa na duka uku uku, wani hawaye ne masu zafi suka Fara zubowa daga idanunsa yace "an janye?"

Ta amsa da "Eh hankalin ka ya kwanta ko? Mu Kuma ka tada Mana namu"
Jin shesshekar kukan sa yasa tayi saurin kallon sa Tace "Hashim!!! Kuka?"
Baice Mata komai ba, tayi saurin karasowa inda yake ta dafa shi a kafad'a Tace "Hashim ya kuma Naga kana kuka ba Kai kace baka son auren ba?"
Ya d'aga Mata Kai alamun eh, Tace "To Kai da ya kamata kayi farin ciki Mai yasa kake kuka?"
"mummy ina fa sonta"
" And so? Kuma kace baka sonta, Wai me yake faruwane?"

Kwantar da kansa yayi a kafad'ar ta, yayin da ita Kuma take d'an bubbuga Masa baya, a dai dai Nan Daddy ya shigo yace "Ga irinta Nan ai kina Nan kina lalata yaro"
"Amma Alhaji baka ga halin da yake ciki bane?"
" To sai me ya mutu Mana, mtsww Dan Allah ki d'auko min chaja na ki kawo min d'aki yanzun Nan"
Ya yi ficewar sa.

Daddy yayi fushi sosai, don dakyar yake amsa Masa gaisuwa Amma hakan Bai Hana Hashim  basa hakuri ba, daga bisani ya huce.

An d'aura auren Fadeelah da Suraj cikin farin ciki da kaunar juna.

BAYAN SHEKARA 'DAYA
mummy na zaune a parlor tana kallon News kwasam taga Ana sanarwa jirgi yayi hatsari from Dubai to Nigeria, aciki harda wannan shahararren Dan kasuwa Mai suna Alhj Ahmad Shettima, mummy hannu ta sa a Kai ta saki Kara a gun ta yanke jiki ta fad'i.

Hashim da already yaji Labarin mutuwar Mahaifin Nasa yayi saurin dawowa gida daga gidan su faisal, shigowar sa Kenan yaji news din da take ji, Kan ya nufi ta harta yanke jiki ta fad'i.
💦💦💦💦💦💦💦💦

Please Vote and comment


💦💦💦💦💦💦💦💦
*MATAR UBA*
💦💦💦💦💦💦💦💦

Daga Alkalamin ✍️

*Milly*

Fadilah Yakub
*(MILHAAT)*

*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️*
*M. W. A*

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

```Not Edited
CHAPTER 24```
Hashim da already yaji Labarin mutuwar Mahaifin Nasa yayi saurin dawowa gida daga gidan su faisal, shigowar sa Kenan yaji news din da take ji, Kan ya nufi ta harta yanke jiki ta fad'i.
💦💦💦💦💦💦💦💦
........... Cikin muryar kuka yake Kiran sunan ta, 'dagata yayi ya d'aura kanta akan cinyar sa yana "Fad'in Mummy!! Mummy!!! Dan Allah ki tashi Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un" Talatu Yar aikin gidan najin ihun ta ta fito parlor da gudu a gigice take ambaton "Innalillahi na shiga uku" hannu ta d'aura akai ta durkusa a gaban su cikin kuka Tace "Dan Allah mu kaita asibiti" Bai ce komai ba ya d'aga yayi waje ita ko da gudun ta ta bud'e Masa sit na baya, Mai gadi na ganin halin da ake ciki yayi saurin bud'e katafaren gate na gidan, Kai tsaye sai FMC suka nufa a Emergency room aka Kai ta, Nan da Nan likitoci sukayi kanta, ba dad'e wa suka fito.

Likita nufu Hashim yayi dake ta safa da marwa kasa kuka ma yayi don shi Bai ma San kukan Rashin mahaifinsa zaiyi ba ko Kuma halin da mahaifiyar sai take ciki ba, 'dan dafa shi yayi yace "Hashim" d'aga jajayen idanun sa yayi Yana kallon sa ba tare da yace komai ba ya d'aura da fad'in "kayi hakuri Hashim da Rashin da akayi maka, duk mai Rai mamacine" Murmushi yayi ganin irin kallon da Hashim ke masa, yace "mamaki kake yanda akayi na San ka ko?" Kai ya d'aga Masa alamun Eh, murmushin gefen Baki yayi yace "ka daina mamaki Hashim Ahmad shettima, familyn ku ai ba 'boyayye bane a garin gombe" kirkirarren Murmushi yayi yace " Hakane"

"Labarin rasuwar Mahaifin ka ya karad'a gari,lungu da sako babba da yaro, Ka kwantar da hankalin ka kayi musu addu'a"
A zabure ya mike yace "ban gane ba Dr? Kamarya na musu addu'a? Ban fahimce ka ba?"
"Am sorry ka kwantar da hankalin ka, mahaifiyar ka lafiyan ta kalau?"
"To meyasa ta yanke jiki ta fad'i?"
"Suma tayi ssbida firgice,sannan jinin ta ya hau Amma yanzu ya sauka don yanzu ma bacci take...." Kasa karasa Maganar da yake yi yayi jiyo murya kuka sukayi daga waje, hashim na juyowa ya hango Fadeelah na kuka jab'e jab'e kallon ta suka tsayi harta karaso inda suke Hashim kasa magana yayi dai hawaye wiwiwi, sai yaji tausayin ta ya kamashi ga tsohon ciki a tattare da ita haihuwa ko yau ko gobe, ganin Hashim na zub da hawaye Kai a langwab'e tace "Shikenan ita ma mutu ko?" Ganin ya kauda kansa ta Fara rera sabon kuka, Dr yace "Babu abinda ya same ta ki shiga d'aki tana ciki" yana Maganar Yana nuna Mata d'akin da take da yar yatsa.

Da saurin gaske ta nufi d'akin,wani Kara ta yi Mai uban sauti hannu tasa ta rike cikin ta, ihu ta Kuma yi a Karo na biyu Duk su biyun suka nufe ta da gudu,Dr ganin jini na sauka a kafarta ya Fara Kiran "Nurse!!! Nurse!!!" Da gudu nurses guda biyu suka nufu cikin murya Mai 'dan Karfi yace "Je ki d'auko wheel chair" 'dayar ta koma da gudu,Hashim kasa magana yayi,yayinda Fadeelah sai aikin Kuka take tana kukan cikin ta.

Labour room aka kaita, sanadiyar tsorata da tayi nakuda ta tashi Mata tun a gida Amma,zafin rashin Mahaifin ta ya hanata Jin zafin nakudan, Tasha wahala sosai Kan ta haihu,ta haifi d'anta Wanda yaci sunan Daddy Wanda ake Kira da Adnan,sun shiga jimami sosai mummy Kuma sai da tayi sati d'aya churr a kwance a gadon asibiti,da taimakon Allah da Hashim mummy da Fadeelah suka rungumi kaddara.

Tun daga wannan lokacin farin ciki da kwanciyar hankalin da ke gidan Alhj Ahmad shettima ya gushe, Fadeelah na gidan ta, mummy ce  kad'ai da Hashim a gidan sai Yan aikin gidan,tun daga lokacin da Badiyya da Hashim suka rabu a school Bai sake kulata ba ko sai d'aro zata Kira bazai d'aga hakan ne yasa yaki picking calls d'inta har sai yau da Allah yayi zai ga Masoyiyar sa wato Asiya.

CIGABAN LABARI
........Wani irin kallo Badiyya takeyi wa Asiyah Wanda ita Kanta Bata San tanayi ba, (Niko nace Badiyya Kar a biye wa son zuciya dai,kishine ke cin ki).

Hashim na barin asibitin Kai tsaye gidan su faysal yayi, yasanar Masa da ya ga Asiyah,faysal yayi matukar farin ciki yace "Alhamdulillah Allah ba azzulumin bawan sa bane sai da Wanda ya zalunci kansa yau idan Safiyya taji cewar kaga Asiya ina ga mutuwa ce kawaii baza tayi ba"

Murmushi Hashim yayi yace "Idan ta ga dama ta had'i yi ranta I don't care" Yana maganar had'e da d'aga kafad'a kana fuskar sa nanu Yana cikin tsananin farin ciki.

Baba Mai gadi yace "Dr mun gode sosai Allah ya saka da Alhairi"
Shiru Bata ce komai ba,alamun suna nuna hankalin ta Sam baya jikinta ta,Nana dake kusa da ita ne ta dafe kafad'ar ta Tace "Likita lafiya kuwa? Ana Miki magana Baki ji ba?"
A 'dan razane Tace "Na'am Na'am"

Baba Mai gadi ya Kuma maimaita abinda yace kirkirarren Murmushi tayi tace "Kar ka dumu baba,ai Asiya Tamkar kanwa take a gareni,so kaga ai yi wa Kaine"
Murmushi yayi yace "Hakane Hakane"

Khamal yace (Baban Yesmin) "Dr yanzu ya samu sauki ko za a iya sallamar mu?"
"Eh za a iya bari na dubo likitar dake kula dashi" tana Kai Nan ta fice.
Khamal yace "Baba yanzu ya zamuyi zaka koma gidana da aiki? Sabida a dalili na ka rasa aikin ka"
"A'a yallab'ai,ko da kuwa baka Bugeni ba dole na bar aiki a gidan Baraka don na tabbata korata zatayi tunda na sake na taimaki yarinyar Nan Asiyah"
"To Shikenan zan taimaka maka insha Allah,akwai gidana take Nan unguwar dawaki, karamar gida ce two bedrooms sai babban parlor sai kitchen da store, sannnan akwai shago a kofar gidan zan cika maka shi da Kayan shago Wanda zaka taimaki kanka da iyalin ka,yauwa nace a ina iyalan ka suke?"

"Suna Nan cikin bajoga,ita da 'ya 'yana shida"
"okay Masha Allah"
"Ashe kana 'ya 'ya Kuma suka barka Haka?" Nana ke wannar maganar,wani irin kallo khamal yayi Mata,kallo irin na kina da matsala, Murmushi baba yayi yace "Ai duk cikin su babu Wanda ya haura shekaru ashirin, Hafsatu ce babba Kuma ita din shekarunta shatakwas ne, sai kannen ta Fauziya, halima,maryama,Jamila sai d"an auta Abubakar"

Tace "Allah sarki Allah ya Raya"
Ya amsa da "Ameen, Nagode sosai yallab'ai Allah ya saka da alkhairi"
Ya amsa da "Amin"
Asiyah Tace "Baba Ashe kana da 'ya kamata na d'auka duk sun girmeni"
Yar karamar dariya yayi yace "Eh Asiyah Ina dashi Ni d'in fa yaro ne tunda ban bawa shekaru hamsin baya ba,kawaii wahalace irin ta yau da kullum"
"Allah sarki na fahimta"
Shigowar Badiyya yasa duk suka Maida kallon su gare ta,Tace "an Sallame shi,Amma akwai sauran kud'in da ba a karasa ba"
Khamal ya amsa da "okay ba matsala" ya Maida kallon sa ga Baba Mai gadi yace " Muje ko?"
Yace "Asiyah kuma fa ya zamuyi da ita?"
Nana tayi saurin fad'in "Ai suna tare da Dr Badiyya"
Kirkirarren Murmushi Badiyya tayi tace "Kar ka damu baba tana karkashin kulawata"
Yace "To to Allah ya bada Lada"
Duk suka amsa da Amin,Nana,khamal da baba me gadi duk suka fice, mota suka jira shi ya gama duk abubuwan da ya kamata suka zarce gida, sai da yaci ya Sha Kan aka Kaishi gidan sa mallakin sa takardun gidan da makullan gidan ya danka Masa,baba farin ciki bazai misaltu ba sai godiya yake da sa Masa Albarka.

Karfe takwas na yamma Badiyya ta riko hannun Asiyah suka fice daga asibitin, napep suka shiga tunda suka shiga babu Wanda ya sake magana, Asiyah Jin shirun tayi yawa tace "Aunty kina lafiya kuwa?"
"Lafiya lau,me Kika gani?"
"Ji nayi kinyi shiru kamar ba ke ba"
Murmushi tayi tace "Bakomai gajiya ce kawai tayi min yawa Baki ga yau ko Zama banyi munyi Hira ba?"
Tace "Hakane"
Federal low-cost suka nufa,suna Isa gida ta sallami mai napep suka shige gida, Momy suka Tarar a parlor bayan sun gaisheta ta musu sannu da zuwa suka shige d'aki, Badiyya ban d'aki ta fad'a tayi wanka kana ta riko hannun Asiyah har zata cire Mata Kaya,cike da Jin kunya Tace "Aunty zan iya wankan,kawai ki kunna min shower" Murmushi tayi,tayi yanda tace ba tare da Tace Mata komai ba,

Bayan ta fito suka koma parlor suka ci abinci, Badiyya abincin kawaii take ci bata Jin dadin sa, Momy da ta lura da alamu tana cikin damuwa bayan sun gama ta kirata d'akin ta,cikin kuka ta Sanar da ita dalilin da yasa Hashim ya fasa auren ta kana ta fad'a Mata matsayin Asiyah a gunta, Momy nasiha ta mata sosai Mai shiga jiki sannan ta jawo hankalin ta Akan Kar ta kuskura son zuciya yasa ta ki Asiya tace "Naga alama yau sai wani shashshareta kike yi,to wallahi kul Kar naji Kar na gani" wayarta ne ta Fara ringing, sunan Hashim ta gani Momy ta d'an leka tace "Ki d'ga mana"
Ji nayi Tace "To"
Momy tace "Ya akayi me yace?" Ganin yanda Badiyya ta b'ata Rai.

"cewa yayi na fito da Asiya"
"To Tashi kuje,ki saki ranki karki bari ya gane abinda ke ranki"
Tashi tayi ta fice, suna fita suka tarar Yana harabar gidan Murmushin takaici ci tayi tuno sanda yake zuwa gunta Hira tayi,a wannan tunanin suka karasa inda yake bayan sun gaisa  yace "Maganar tafiyar mu India ne, na Mana passport"
Cikin rashin fahimta Tace " Bangane ka Muku passport ba?kai dawa?"

" Ni da ke,da Asiyah,you know how caring I am idan ina son Abu"
Kai ta d'aga alamun eh,yace " Asiyah ta,ya naji kinyi shiru ba magana ne?"
Murmushi kawaii tayi Tace " Kawaii ina farin cikine da Jin dad'in yanda Kyle damuwa da lafiya ta, sannan naji dad'i da duk mu ukun zamuje"
Murmushi yayi yace "kin chanchanci fiye da haka My princess"
Wani irin kallo Badiyya tayi masa, murmushin gefen Baki yayi don yasan baza taji dadin hakan ba,a zuciyar sa yace "Ke ma kiji inda Dadi wani abun ma sai ta warke"
A fili Kuma yace " Ni zan koma,karfe Bakwai na safe flight din mu zai Tashi zan Zo na d'auke ku karfe shida"
Kai kawaii ta d'aga Masa ta shige motar sa,leko wa yayi yace "Dan Allah ki Kularmin da My princess" key ya Danna ya fice.
Badiyya takaicin duniya ce ta ishe ta ta rasa yanda zatayi, rike hannunta tayi ta jaa ta suka shige gida.

Khamal ya d'auki aniyar d'aukar fansar abinda akayi was Sadeeq da 'ya  'yan sa,hakan yasa ya koma bakin aikin don samun Karin Hutu yayi sa'a ya samu hutun sati uku, bai d'au lokaci ba ya dawo garin gombe.

Hashim na barin gidan su Badiyya gun Safiyya yayi ya Sanar Mata da cewar zaiyi tafiya har Na tsawon sati biyu Rai a b'ace Tace "wallahi baka Isa ba,a satin da za'a yi bikin zaka dawo?"
Ransa yayi mugun 'baci a ransa yace "yarinyar Nan ta samu kanta Amma Bakomai zanyi maganin ki" kirkirarren Murmushi yayi riko hannunta yayi yace "Am sorry gimbiya ta kin San bana son 'bacin ranki tafiyar Nan fa dazanyi saudi zanje na had'o miki Kayan lefe kin San Kina da daraja a guna baxaiyu ace kina gimbiyar Hashim ace a sa Miki Kayan
End Ads