wata alfarma?Β ya kamata ki daina tan kamata idan tana magana"
"Meyasa kikace haka?"
"Sabida zata kashe mu wataran idan Kika cigaba da Mata Haka"
Murmushi tayi Tace "To Asiyah me banbanci mu da matattu, ba abinci, ba zuwa makaranta muke ba, ba kayan sawa kin San duk ta Kona Mana su,ba Uwa ba uba, har yaran da suke gidan marayu sun fimu da komai, to me Kuma ya rage? A raye muke dai Amma ta kashe mu"
"Na San da hakan Anisah Amma ya kamata ki d'auki magana ta Kinga nice gaba dake ko?"
"To shikenan zanyi yanda kikace"
Asiyah tashi tayi tace "Yauwa ko kefa Tashi muje muyi sallah muyi Shirin zuwa islamiyya"
"Gaskiya ni bazanje ba jiri ma nake ji Ina sallah zanyi bacci"
"To shikenan Nima baccin zanyi kawai."
Ganin ta nayi ta fito daga kitchen hannun ta rike yake da plate, fried rice ne aciki da cinyoyin kaji manya manya, d'ayan hannun Kuma kwalin Hollandia ne, Kai tsaye dinning table ta nufa tana ajiye plate d'in wayan ta ya Fara ringing tana picking ta amsa da "Hello qawata"
Bayan sun gaisa Tace "Ke dai Bari kawai qawata nayi duk yanda zanyi Amma shiru kike ji na rasa meyasa ban haihu ba sai faman bauta nake wa yan iskan yaran Nan."
Tana d'an yi shiru da alama tana Mata magana Wanda Ni na kasa ji sai ji nayi Tace "Ai wallahi Ina haihuwa Zan Kori monkeys d'in Nan a gida na, Kema kin sanni ai wallahi ba ruwana da inda zasu je suma mutu Mana"
"Okay to shikenan ki gaida min 'yarki" kashe wayar tayi ta cigaba da cin abincin ta, suna shigowa suka tarar da ita ta na yagar nama ganin suna kallon ta banka musu wata muguwar harara had'e da fad'in "baza ku bar Nan ba?"
Da saurin gaske suka bar gun, a Haka suka kwana da yunwa sai Ruwan da sukayi ta Sha.
Yau ma tun safe suka fita don sayar da lemo da pure wata.
Wata bakar motar na gani kirar Benz tazo ta gifta su.
Cikin motar wata yarinya sa'ar su Asiyah tana kallon su Asiyah cike da mamakiΒ Tace "Mom ya akayi na ga su Asiyah suna tallah?"
Murmushi tayi ta Maida hankalin ta sosai Kan tukin da take, sai Tace "Toh mene ne aciki don sunyi tallah akan su aka Fara ne?"
"Toh Amma Meyasa Ni bana yi"
A tsawace Tace "yimin Shiru Allah ya raba ki da tallah, Suma d'in kaddara ce kuma Kar naji kin sake fad'in Haka, kuma kar ki fad'awa kowa kina jina ko?"
"Toh bazan fad'a ba"
Shafa kanta tayi Tace "Yauwa YesmiinΒ 'yar Albarka,Bari nayi sauri nayi dropping d'inki a makaranta Kar ki makara ko?"
Tace "To mommy"
Sai yamma liss suka gama sayar da komai da komai babu abinda ya rage, a galabaice suke tafiya Asiyah Tace "Anisah har yanzu zazzab'in Bai sake ki ba?"
Cikin kasala Tace "Eh jiri nake ji, ji nake kamar zan fad'i"
"Sannu bari na rike ki, mun ma kusa Isa gidan" rike ta tayi suna tafiya Kan ta Ankara Anisah ta zube a kasa, ihu Asiyah ta Fara yi tana kuka tana neman taimako dake a GRA suke unguwan Shiru ba kowa ta dad'e a Haka Kan ta hango wasu Samari su biyu da gudu suka nufota, d'aya daga cikin su yace "Me ya same ta Haka?" Cikin kuka tace "Suma tayi"Β chaak ya d'aga ta yace "Ina ne gidan ku?"
Tace "Yana chan ba nisa daga Nan" da gudu suka kaita gida Amma sukayi rashin Sa'a Baraka ta fita yawon gantalin ta da ta Saba, Asiyah ta musu godiya har parlor suka aje ta Kan suka tafi.
Ruwa ta d'ebo a roba tana sawa tana Kama Mata jiki don jikin ta yayi zafi sosai suna cikin hakan ne ta dawo tana ganin su tace "Ita Kuma wannan me ya same ta?"
"Sannu da dawo wa mummy ba ta da lafiya ne ya kamata akaita asibiti?"
Hard'e hannayen ta tayi ta ce "Asibiti? Kuma ana bukatar kud'i?"
Tace "Eh ai ya Zama Dole?"
Harararta tayi Tace "Dole? Cancer take dashi ne?"
Murya kasa kasa tace "A'a."
"Good to bani da kud'in kaita asibiti"
"Toh mummy Dan Allah ki ara min wayar ki na Kira Daddy"
A tsawace Tace "bazan bayar ba, harda wani ya Zama Dole to ta mutu Mana ina Ruwana Kun ma ci Sa'a ban d'auke ku naje na sayar daku ba, useless children"
Tana maganar tana haurawa sama.
Cikin kuka Anisah Tace "So take na mutu"
Asiyah Tace "Shhhh Karki ce Haka baza ki mutu ba Allah ya baki lafiya tashi Muje ki kwanta a d'aki."
Dakyar ta d'aga ta dake ratar shekarunsu kad'an ne Asiyah shekarunta Tara Anisah Kuma Bakwai sannan Anisah ta d'an fi Asiyah kauri, upstairs d'in su na da tsawo da kyar suka haura sabida gidan babba ne kud'i ya zauna anan.
Bayan ta Kwantar da ita ta fito ta zauna a corridor tana kuka ta had'a Kai da gwiwa tana fad'in "Mummy Ina kike Dan Allah ki dawo,mummy Kinga irin abinda ake Mana kin kasance mutumiyar kirki, mace ta gari Kuma Uwa ta gari kece irin uwar da ko wani d'a zaiyi fatan samu,ko Ina ana yabon kyawawan halin ki, Allah ya jikan ki yasa kin huta."
Sai da tayi kuka Mai isarta Kan ta tashi ta koma d'aki,yau ma da yunwa suka kwana sannan Anisah zazzab'in yaki sake ta.
*WASHE GARI*
Qawartace ta kawo mata ziyara da alama fita zasuyi.
Qawarta ta naji Tace "Ina yaran ki suke?"
Kallon ta tayi cike da b'acin Rai tace "Kya jiki da wani zance yanzu Yan iskan yaran Nan ne zakice 'ya 'yana, na haifi mayu ne?"
Suna cikin magana ne Asiyah ta sauko daga upstairs cikin sauri, Qawar bakaraka Tace "Ganan d'ayar mayyar"
Wani irin kallo Asiyah ta Mata tace "Ni ba mayya bace"
A tsawace Baraka Tace "Ke don uwarki sa'ar kice maza ki bata hakuri"
Ba don taso ba Tace "Kiyi hakuri"
Tab'e baki tayi ta amsa da "Ya wuce"
Durkusa wa tayi a gaban ta Tace "Mummy Dan Allah ki taimaki Anisah ba tada lafiya jiya bamuyi bacci ba, mukai ta asibiti ko Kuma ki bani kud'i na kaita"
" bani da kud'i"
Qawar Baraka Tace "Kaai mummy Tace Miki Kuma naji kin amsa"
Harararta tayi Tace "Kinji na amsa ne bana son rashin mutunci, kin gama ne mu tafi?"
"Eh na gama" tashi sukayi da niyar fita.
Asiyah rike kafarta tayi Tace "mummy please"
Hankad'e ta tayi ta fita.
Suna tafiya Asiyah ta fara dube dube duk ta hargitse parlor Bata ga abinda take nema ba da sauri ta shige d'akin Baraka karkashin gado da ta Fara Dubawa ta koma ta d'aga pillow, ta koma Kan wall drop ta koma gaban mirror tsaki tayi ganin bata samu ba sai ta hango wata Yar karamar purse da sauri ta d'auka ta b'ude,Murmushi Naga tayi ta zaro duba d'aya da gudu ta fita ba ta zarce ko Ina ba sai chemist Mai chemist ganin yanda ta shigo da gudu ya sa ya tsorota Yana kallon bayan ta yace "Yarinya wa ya biyo ki?"
Sai sauke Numfashi take tace "Dan Allah malam magani zaka bani"
"Maganin me kike so?"
Tace "Zazzab'i yake damun Kanwata"
"Zazzab'i da Kuma me?"
"Ciwon Kai sannan bata da Karfi tana yawan Jin jiri"
Yace "Okay" karb'an kud'in yayi ya bata maganin ya fad'a Mata yanda zata Sha tana karb'a ta fice da gudu.
Da sauri ta haura sama tana Shiga d'akin ta ga Anisah na kwance cikin sanyin murya Tace "Anisah tashi Kisha magani"
Shiru bata amsa ba ta Kuma cewa "Anisah bacci kike ne?"
Bata amsa Mata ba.
Da sauri ta nufi inda take kwance tayi kokarin d'aga ta ta kasa dakyar ta samu ta d'ago kanta idon Anisah a kakkafe tayi saurin sake ta tana Kiran sunan ta "Anisah!!! Anisah" da sauri ta rike hannun ta tace "Anisah ki tashi, ki tashi Dan Allah" hannu tasa ta rufe idanun ta sannan ta gyara Mata kwanciyar ta, tana ambatan "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un"
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
PLEASE VOTE AND COMMENTS
π¦π¦ *MATAR UBA* π¦π¦
_(A True Life Story)_
*Short story*
```Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)```
Follow me on Wattpad @Milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0
π *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION*πποΈ
_'kungiya d'aya tamkar da dubu_
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayiwa Yan Uwa Mata nasiha,Allah ya bani ikon gama shi lafiya kamar yanda na Fara lafiya ameen.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* Much Love.
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
CHAPTER 4
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
........ Da Sallama ta shigo ta tura kofan ga mamakin ta sai taga parlon a hargitse Rai a b'ace ta ce "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, me zan gani haka? Wato yaran Nan sun ga bana gida shiyasa suka hargitsa min gida?"
Rai a b'ace ta Fara kwala Kiran sunan Asiyah ganin Basu amsa ba da saurin ta tayi niyar hawa sama, sai Taji wayan ta na ringing da har kamar baza ta duba ba, ta zaro shi a jaka ganin mijin tane ta zaro Ido, gyaran murya tayi Kan ta yi picking bayan sun gaisa yace "Ya kuke da yaran?"
Kirkiran Murmushi tayi Tace "muna Nan lafiya Lau Kai fa?"
Yace "Nima Haka Ina yaran suke ne ki basu mu gaisa please"
Cikin Rawar murya tace "Na Basu wayar ku gaisa?"
Yace "Eh"
Tace "Emm...kasan bamu dad'e da dawo wa daga Shan Ice cream ba Kuma munje park sunyi Wasa sun gaji"
"Allah sarki Baraka nagode Sosai Allah ya saka da Alhairi ya Miki Albarka"
Yar karamar dariya tayi Tace "Haba me na godiya? Ai jinin ka nawa ne ba sai ka gode min ba"
"Masha Allah to basu wayar"
Cikin inda inda Tace "A a ai suna suna suna emmm d'aki suna bacci sun gaji"
"Allah sarki nayi kewar su"
Murmushi tayi Tace "Suma suna kewar ka Amma kasan nafi kewar ka fiye da kowa ko?"
Dariya yayi yace "Baraka Kenan"
Tace "Kar ka damu idan sun tashi zan Kira na had'a ku"
"To nagode Allah ya Miki Albarka."
Ta amsa da ameen, a tare suka kashe wayan.
Cikin sauri ta take tafiya tana Kiran sunan Anisah da Asiyah Amma Basu amsa ba tana Shiga d'akin ga mamakin ta taga Asiyah a tsaye ta jingina a kusuwar d'akin a tsawace Tace "Madam Ashe dama kina ji Ina Kiran ki baki amsa ba?"
Shiru bata kalle ta ba bare ta amsa sai Tace "ba wannan ba me ya faru da Parlor na" tana maganar tana kallon Anisah dake kwance tace "Ita Kuma wannar me ke damin ta? Ta kwanta bata motsi kamar matacciya?"
Kallon ta Asiyah tayi cikin kuka Tace "Eh sabida matacciyar ce" tana Kai Nan ta fice.
A hankali take tafiya har zuwa inda gawar Anisah ke kwance a hankali tasa hannun ta tab'a taji bata motsi jikinta Kuma yayi sanyi da sauri ta sake hannun ta ta fice daga d'akin tana ambatan "na Shiga uku" a cikin Zuciyar ta.
Daddy na jin Labari ya dawo da sassafe, a gaban shi akayi komai har aka kaita makwancin ta, zaune suke a parlor Yan Uwa da abokan arziki, kuka yake Sosai kamar wani karamin yaro Yana fad'in "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un ban kasance uba na gari ba, nayi alkawari wa mahaifiyar su zan kula da su Amma gashi na kasa cika alkwari.
Baraka dake zaune a gefen sa wani irin kallo take Masa na irin ko in kula idan ta ga alamun ana kallon ta Nan da nan sai ta canza fuska ta zama abin tausayi.
Kirkiran kuka tayi tana fad'in "Allah sarki Anisah ta, ta mutu ta barni bayan irin kud'aden da na kashe a gun lura da ita amma an raba Ni da ita" tana Maganar tana hararar Asiyah dake kallon ta, "Mutuwa Meyasa baki d'aukeni ba Kika d'auki yar auta ta Wacce nake Wasa da ita tana d'ebe min kewa Mai Wasa da gashin Kai na, yanzu wa zai kirani da Mummy? Bayan addu'o'in da nayi Mata ba dare ba Rana Ashe baza ta zauna ba" ta Karasa maganar cikin kuka.
Mutanen dake gun sukayi ta rarrashin ta, cikin dare Baraka ta farka a tsorace tana Kiran sunan Anisah a razane ya farka yace "Baraka lafiya?"
Sai Kiran sunan Anisah take sai yace "Ko mafarki kikayi ne?"
Ta amsa da "Eh" a tsorace, yace "kiyi addu'a mu kwanta"
Cikin Rawar murya Tace "A'a Kar ka damu ka kwanta kawaii" yayi da ita Taki sai ya hakura yayi kwanciyar sa.
*BAYAN KWANA ARBA'IN*
Kawar Baraka Mai suna Nana mahaifiyar yesmin ce ta kawo Mata ziyara, juice ta d'auko Mata a fridge ta Mata godiya tace "kamar kin San Ina bukatar hakan na d'ebo Rana"
Dariya tayi Tace "Asha lafiya" bayan ta gama Tace "Qawata ya ture ture?"
Dariya tayi tace "Nana Kenan cikin sati biyar d'in shine Zaki ce ya ture ture?"
Murmushi tayi Tace "Ya Sadeeq da Asiyah?"
"Suna Nan lafiya Lau"
Ajiye kofin dake hannun tayi Tace "Qawata yadai Naga duk kinyi sanyi ne ko kin manta maganar mune? Kin manta cewar zaki b'atar da yaran dukka su biyu ne kamin ki haifi naki? Sabida ki gaji duk abinda Sadeeq ya mallaka Amma kinyi Shiru"
Baraka langwabe Kai tayi Tace "Qawata mutuwar Anisah ya kashe min jiki, ban san Meyasa nake ji kamar Ni ce na kashe ta ba"
"Kece Kika kashe ta Mana"
Baraka gyara Zama tayi had'e da fad'in "What?"
Nana Tace "What do you mean what? Mahaukaciya,Kina so kice min Baki san cewa ke Kika kashe Anisah ba? Da ace kin kaita asibiti da bata mutu ba, Kiyi gaggawan kashe d'ayar sabida Karta hanaki Rawar gabar hantsi"
Tashi Baraka tayi Rai a b'ace Tace "Tashi ki fita" tana nuna Mata kofar fita, cike da mamaki Nana Tace "Baraka!! Korata kike a gidan ki?"
"Eh ki fice min daga gida"
Tashi tayi Tace "Aikin banza Ina nan da kafafunki Zaki nemi ni."
"Naji ki fita ko na sab'a miki"
Nana Tace "Me yayi zafi? Zan fita Amma Bari na karasa Shanye juice d'in"
A tsawace Tace "Aje Munafuka tunda ba da kud'in ubanki aka saya ba"
Murmushin takaici tayi ta fita, Zama Baraka tayi, tayi Shiru na d'an wasu lokuta sannan a fili Tace "Kuma ta fad'i gaskiya da ace na kaita asibiti da bata mutu ba, Asiyah Kema lokacin ki yayi dole na kashe ki abin da zan Haifa ya taso cikin gata."
Tashi tayi ta Shiga kitchen tayi girki dake Sadeeq na gari dole tayi girki, bayan ya taso daga gun aiki ya biya ya d'auko Asiyah a makaranta duk ta lalace ta kasa sakin jikin ta kullum cikin kuka take shi duk a tunanin sa duk sabida mutuwar Anisah ce ita Kuma tunanin ya had'u ya Mata yawa mutuwar mahaifiyar su da anisah kuma tasan cewar Baraka ce sillar mutuwar Anisah Amma ba hali ta fad'a Masa don Tace zata kashe idan ta fad'a Masa abubuwan da take musu shiyasa tayi Shiru.
Da Sallama suka shigo, tana ganin sa ta rungume shi, Tace "My Asiyah jeki cire uniform kizo kici abinci ko?" Ta amsa da "Toh" sai ta haura sama shi Kuma yace "Bari na watsa ruwa" ya haura sama.
Baraka Kuma ta komaΒ kitchen, bayan ta cire uniform ta dawo dinning table ganin ba abincin ta nufi kitchen a dai dai Nan ta samu Baraka na fad'in "Shegiya mayya idan Kika ci abincin Nan Dole ki mutu kamar yadda yar Uwar ki ta mutu guba ai ba Wasa bane" tana b'arbad'a guban akan abincin, Asiyah ta tsorata sosai ta rasa yanda zatayi a hankali take tafiya har ta haura sama.
Tana kallon duk motsin Baraka, ganin Baraka ta fita daga kitchen d'in ta Shiga d'aki da sauri ta sauko ta Shiga kitchen d'in ta zuba abincin a bakar leda sannan ta wanke plate d'in tass Kan ta sake zuba wani ta aje sai tayi saurin fita ta koma d'akin ta.
Baraka na fitowa ta Shiga kiranta a nitse ta fito Tace "Mummy gani" ganin Daddy ya fito ta shafa Kanta Zo muje kici abinci ko?" Tana Mata Murmushi itama Asiyah Murmushin ta Mata.
Asiyah taci abincin Nan sosai don tun rasuwar Anisah ba a bata abinci sabida Daddy baya gida, bayan ta gama cinyewa Baraka Tace "Kin koshi ko na Kara Miki?"
Tace "Na koshi"
"Naman fa baza ki Kara ba?"
Murmushi Baraka tayi Tace "Nagode na koshi"
Murmushi tayi Tace "toh Allah ya Miki Albarka"
Ta amsa da "ameen" kwashe plate d'in tayi ta Kai kitchen, Baraka na jira taga ta fad'i Amma shiru Nan da Nan hankalin ta ya tashi Daddy yace "Yadai Baraka ya Naga fuskan ki haka? Kina Laifiya kuwa?"
Kirkiran Murmushi tayi Tace "Lafiya Lau"
Kallon ta yake yi shi Sam bai yarda ba ta sake cewa "Kin tabbata babu abinda yake damun ki?"
Mikewa tayi Tace "Ina zuwa bari na d'auko wayana"
Yace "Okay" tana Shiga d'aki ta kira Nana, Nana na picking Tace "Nasan zaki kirani Amma ban d'auka a yanzu Zaki Kira ba"
Cikin damuwa Tace "Qawata ba wannan ba please don't mind me d'azun b'acin Raine, kin san mene ne kuwa?"
Daga d'ayan b'angaren ta amsa da "Sai kin fad'a"
"Umm yarinyar Nan nasa Mata gubar Nan a cikin abinci kamar yanda kikace Amma baiyi Mata komai ba"
"Haba haba kin San karfin maganin Nan kuwa kana cin Loma d'aya zai kashe ka"
Tace "Wallahi ta cinye abincin Nan duka ba ta rage komai ba Kuma nasa maganin fiye da yanda akace"
Nana ta ce "Ikon Allah,abin da mamaki Kam"
Baraka Tace "Ina gani fa kamar yarinyan Nan mayyace, Amma duk maitan ta na fita, Bari na Koma parlor anjima zan Kira ki" sai ta katse wayar tana saukowa daga Kan step sai ta zame, ihu ta fara yi Wanda yasa Daddy ya taso da gudu, Asiyah ma ta fito daga d'akin a tare suka nufe ta yayi kokarin d'aga ta sai yaga jini na bin kafan ta Baraka na ganin jini ta fashe da kuka Tana fad'in "My baby my baby" sai rarrashin ta yake yasa ta a mota sai asibiti ,suna zuwa likita ya tabbatar da cikin ya lalace kuka ta Shiga yi har suka dawo gida.
A ranar ba tayi bacci ba kwana tayi tana kuka Daddy yayi rarrashin duniya Taki sai ya hakura ya Kyale ta.
*WASHE GARI*
Ta Kira Nana ta Sanar mata, Nana na Jin hakan ba b'ata lokaci tazo ta tarar dasu a parlor tana kwance a jikinsa Yana ta aikin rarrashin ta Yana fad'in "Baraka ki daina kuka insha Allah Zaki samu wani cikin Allah da ya bamu wannan shi zai sake bamu kinji?"
Bayan Nana sun gaisa yace "Dan Allah Nana ki rarrashe ta tun jiya take abu d'aya"
Murmushi tayi Tace "Kar ka damu insha Allah zan Mata magana"