hannun Baraka tayi daga jikinta tana nuna ta da d'an yatsa Tace Kar ki kuskura ki sake tab'a jiki na kin gane ko? Sannan Kar ki kuskure ki sake tako min gida da irin wannan maganar in ba Haka ba wallahi zan had'a Miki jini da majina."
Mamakine ya kama Baraka murya jabrawa Tace " Amma Nana kin gane da wa kike magana kuwa? Baraka ce fa aminiyar ki Ni kike fad'awa irin wannan maganar"
A tsawace Tace "To hell with you Baraka ke d'in banza ke d'in wofi ke kanwar uwata ce da bazan fad'a Miki Haka ba? Na Gaya Miki Kar ki sake Tako min gida munafuka anna mimiyi"
Rai a b'ace Baraka Tace " Dani kike zancen Nana wallahi sai na tuna Miki a Siri zan Kira Abban Yesmin na fad'a mishi Duk abubuwan da kika Shukka hatta bin mazan da kikeyi"
Nana dariya ta Shiga yi kana Tace " idan kin fasa fad'a mishi kinji tsoro"
Baraka Dariya ta Shiga tayi Tace " Allah sarki har na hango ki akan titi kina bara don na tabbata idan iyayen ki sukaji abinda kikayi sai sun tsine Miki sunyi Allah wadai da halin ki"
"ko kad'an hankali bazai tashi ba in hakan ta Faru Dani idan na gyara tsakanina da ubangiji na ya wadatar dani"
" Wani ubangijin Kenan? Ubangijin da kike had'a sa da wani? Kar ki manta Allah baya yafe Wanda ya had'a shi da wanin sa"
" Ummmn, Allahu gafururahim, na tabbata zai yafe min in dai nayi tuban gaskiya, Kuma laifin da nayi Masa tsakanina dashine kawaii,ki sani idan na koma Kan titi ke Kuma Zaki koma gidan yari Ina da video da recording na kisan Kan da kikayiwa Mahaifiyar Asiyah,Anisah Kai harda Sadiq Ina da komai da komai,Kinga nice da riba sabida Allah baya yafe laifin wani was wani"
" Ina da kud'in da zan wanke kaina Kuma wallahi sai na Kira shi na fada masa,tun wuri Ina Baki shawara kizo mu had'a Kai mu d'aura daga inda muka tsaya" tana maganar tana kokarin rike hannun ta.
Wata gigitacciyar mari Nana tayiwa Baraka har Saida ta fad'i akan sofa dake gefen ta.
Baraka rike kuncin ta tayi da hannu biyu Tace "Kai kai kaaii Kika an mare Ni?"
"An mare ki"
'dago was tayi da sauri ta nufe ta da niyar Rama Marin da ta Mata,Abban Yasmin dake tsaye tun shigowar Baraka ya nufu inda suke da sauri, hankad'e Baraka yayi ya shafa Mata maruka guda biyu masu kyau sannan yace "This should be the last time da Zaki sake shigan min gida kina jina ko?"
Ba Baraka kadai ba hatta Nana ta tsorata don Bata San sanda ya shigo gidan ba, Murmushi baraka tayi ta mike Tace "Baka San me ya Faru bane Amma bara na baka Labari kad'an daga cikin abubuwan da wannan munafukar matar ka take yi ta kasance tana cin amanar ka da maza,itane gidan boka,itane lesbian"
" Uhmn sai Kuma me Ina sauraron ki" hard'e yayi Yana kallon ta,jikin ta jikin tane yayi sanyi har ta kasa magana a Karo na biyu Tace "Kinyi shiru Shikenan ko Akwai wani Abu?"
Murya chan ciki Tace "Shikenan."
Had'a hannun sa yayi guri guda yace "to nagode sosai thank you for informing me, yanzu ki fice min daga gida ko in kashe ki yanzun Nan,Kuma kin sani Sarai idan na kashe ki na kashe banza"
Jiki na rawa ta fice daga gida tana mamakin yanda bai d'auki maganar ba "ko dai asiri ta Masane?" Shafa kumatunta tayi Tace "To wallahi sai Kun San Kun mare Ni" ta jaa motar ta ta wuce hotel d'in da sukayi zasu had'u,Yana ganin ta ita kad'ai ya tambaya ina kawartata take ta Fara Masa kame kame ba 'bata lokaci ya Koreta daga d'akin, Hakan ya sake hassala ta tana driving sai huci take ta ce "Wallahi wallahi sai nayi ajalinki" cikin wannan tunanin ta koma gida.
Safiyya tunda tayi sallar Maghriba ta yi wanka ta ci kwalliya,abaya tasa pink an Masa kwalliya da stones ruwan Bula (Royal blue) tayi Rolling da d'an kwalin rigan ta sanya takalmi irin Mai igiyi Shima kalan ruwan Bula,tayi kyau matuka dama Safiyya Kyakkyawa ce kawaii dai halin uwa ta biyo,Duk da dama Safiyya, Anisah da Asiyah kamanin su d'ayane kamannin Mahaifin su Sadeeq, tana ji a jikin ta Dole Hashim zai Zo tunda dai Yana son Asiyah.
Baraka na zaune a parlor ga dai TV a kunne Amma hankalin ta ba a Kai take ba sai kunce wa take ta warwareww, Sallama Safiyya tayi ta zauna ganin hankalin mummyn nata baya gunta tab'e Baki ta Shiga boga game a wayan ta.
"Hashim kasan Allah da Kai na kwana a Rai na, Yarinyar Nan shaid'aniya ce gata karama yarinya Yar ss2 kam me ta sani a zamanin mu Amma ka duba kaga makircinta ko mace Yar shekara arba'in baza tayi ba"
Murmushin takaici yayi yace "Ni kaina abun na bani mamaki Faisal,Amma ya zanyi Ina son Asiyah Ina so na San a wani hali take ciki Dole nayi yadda take so"
" Kasan mene ne, hashim? Duk yanda za'a yi ka nuna Mata ita d'in kake so kayi ka nuna Mata baka son Asiyah,Dole game zamu buga kamar yadda take so"
" Kamar ya Kenan fa ban fahimce ba"
" Abin nufi zaka tura gidan su,ayi komai da komai, Kan ranar auren Kai ma ka nuna Mata in dai Bata fad'a maka inda Asiya take ba zaka fasa by then Bata da option Dole ta fad'a maka sabida kaga a wannan lokacin lokaci ya kure Mata sun gayyaci Yan uwa da abokanan arziqi babu yadda zatayi Dole ta fad'a maka idan ka tabbatar da hakan ka ganta sai ka fasa"
Murmushi Hashim yayi Wanda shi kansa ya manta ranar da yayi yace " hakan za'a yi Abokina nagode sosai"
" Kar ka damu yanzu ka tashi Muje masallaci Naga Ana Kiran sallah daga Nan sai mu wuce gidan nasu."
Hakan kuwa akayi suna idar da sallan Kai tsaye suka wuce gidan su Safiyya horn sukayi aka bud'e musu gate dake ta sanar da sabon Mai gadin da zuwan su, tana Jin horn ta tashi jiki na rawa da niyar zata fita.
A tsawace Baraka Tace "And where are you going to?"
Murmushi tayi Tace "Mummy bako nayi"
Cikin rashin fahimta Tace "bako? Daga Ina?"
Murmushi tayi Tace "Mummy kiyi hakuri idan na dawo zan fad'a Miki komai." Tana Kai Nan ta fita da sauri.
Baraka na kiranta Amma Bata juya ba bare ta ji me zata ce, kad'a Kai kawaii tayi ta cigaba da mugun Shirin ta.
Faisal yace "Kirata Mana"
"To ai bani da number ta"
"Kamarya baka da number ta dame kukayi waya?"
" Uhmn hiding number tayi"
Kama Baki Faisal yayi yace " Lallai yarinyar Nan ta wuce tunani na,Allah ya kyauta."
Ya amsa da "ameen, Bari na aiki Mai gadin ya Mata magana kawai" har ya sauke kafa d'aya sai ya hango ta ya waiga ya kalli Faisal yace "gata chan ma tana zuwa"
Da sallama ta Kara so inda suke, da Murmushi d'auke a fuskarta ganin su biyu ne sai taji wani iri,Tace " Sannun ku da zuwa"
A tare suka amsa da "yauwa sannu"
"bismillah ku Zo mu Shiga ciki"
Babu wanda yace Mata komai,kawaii fita sukayi suka bi bayanta, Faisal murya kasa kasa yace "Mutumina yarinyar Nan fa karshe ne gun kyau wallahi ta had'u"
Hararar da Hashim ya Masa ne yasa yayi saurin Kay da kansa.
Maganar da yayi ya sauka Akan kunnen Safiyya Aiko tana jin hakan ta canza tafiya sai yauki take,a parlor da ake saukan bakin ta ajiye su, Yar aikin gida tasa ta kawo musu drinks, Faisal ya sa hannu ya d'auki exotic ya Fara Sha,gyaran murya hashim yayi yace "Abokina kaga gimbiyar tawa ko?"
Murmushi Faisal yayi Yana kokarin had'iye exotic da ya cika bakinsa da shi don dama shi masoyin exotic ne, sai da ya had'iye yace "Na ganta Abokina tabarakallah Masha Allah,sannu Amaryar mu."
Safiyya wani irin dadi taji rufw fuska tayi da hannu biyu Tace "yauwa sannu abokin mu,da fatan kana lafiya?"
"Lafiya lau,ya gida yasu hajiya?"
" Suna lafiya Lau"
" Masha Allahu."
Hashim gyara zaman sa yayi yace " My princess gani nazo,ya ake ciki?"
Cikin muryar shagwab'a Tace " So nake cikin satin Nan kazo neman aure na"
Murmushi yayi yace "shine kawaii?"
Ta d'aga Kai alamun "eh"
Murmushi irin na Zaki Raina Kanki yayi yace "Consider ita My Sofiyat"
"Wow Amma naji dad'in sunan Nan"
" Dan Allah dagaske kike?"
" Eh dagaske nake har cikin Raina naji shi"
" To in ko Haka ne yanzu Kika Fara Jin dad'i don yanzu na Fara kirin ki da sunaye masu dad'i"
Murmushi tayi tace "Nagode sosai,Allah ya bar mu tare"
Ya amsa da Amin Amma a iya baki ya tsaya.
ASIBITI
"Asiyah inaso ki kwantar da hankalin ki ki saurare ni,Kuma ki fahimce Ni kinji?" Dr Badiyya ke maganar Nan cike da tausayin Asiya, Asiyah ta amsa da "Toh Aunty Ina sauraron ki"
"Baba Mai gadi Yana Asibitin Nan"
Tashi tayi ta zauna tana Murmushi Tace " Baba ya dawo Alhamdulillah, ina yake?"
Nan ta fad'a Mata tun ranar da aka kwantar dashi Bai tashi ba,bare ma aji ya samu aunty Rukayya ko Bai same ta ba.
Kuka ta Shiga tana fad'in "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Ya Allah me nayi me nayi da chanchanci irin wannan laifin, Allah na tuba ka yafe min"
Dr Badiyya rungumarta tayi Tace " Ki daina fad'in haka Zaki yi sabo Allah ya na gwada bayin sa ne Wanda take so,ki d'auki wannan a matsayin kaddarar rayuwar ki,insha Allah komai zai wuce Allah ya Baki ikon cin jarrabawar nan, kiyi hakuri Asiyah Dole ki bar asibitin nan don na tabbata zasu Kore ki yanzun ma nice ma roka aka barki Kuma private hospital ne"
Fashewa tayi da kuka Tace " Na Shiga uku Ni yanzu Ina zan je,idan na koma gidan mu kashe Ni zasuyi"
"Ki daina kuka Asiya baza ki Koma gidan Nan ba, nayiwa Mahaifina maganar ki,Kuma ya amince ki dawo gidan mu da Zama kamun a samu mafita"
Godiya ta Mata sosai,da yamma suka wuce gidan su Dr Badiyya,Amma kamun Nan sai da ta biya d'akin da baba Mai gadi yake,gidan nasu Ba wani babba bane Kuma ba masu kud'i bane ba kawai dai sun da rufin asirine dai dai gwargwado.
"Nayi farin ciki sosai Nana hakan da kikayi ya tabbatar min da cewar kin tuba ne dagaske,idan shaid'aniyar Jan ta Kuma zuwa gidan nan ki sanar Dani nasan matakin da zan d'auka a kanta"
Ta amsa da to,kashe mata Ido yayi yace "Ya to mu haura sama na Baki sako" ya haura sama abunsa
Murmushi tayi dake ta gane abinda gogan nata ke nufi sai ta mara Masa baya,Niko da na leka Naga abinda yaso yafi karfin idona na jawo musu kofar nayi gaba.
Hira suka Sha sosai kamar dama tun chan Yana Sona ta,karfe Tara saura suka you Sallama suka wuce, Faisal yace "Abokina ban San haka kake ba Ashe zaka iya yaudara jibi yadda ka sake kamar dagaske kana sonta"
Murmushi yayi yace " Toh idan ban yi hakan ba bazan samu abinda nake so ba, I'll do whatever it takes to make Asiyah mine,sabida Ina sonta Ina Kuma kaunara ta"
"Allah ya tabbatar Mana da Alhairi yanzu ya maganar turowan?"
"ai yanzu ba anjima ba muna Isa zan sanarwa hajiya ta Kar a b'ata lokaci gurin wannan abun"
"Hakane ka dai bi hankali yarinyar Nan abin tsoro ce"
" Toh insha Allah,zan kiyaye" gidan su Faisal suka biye ya ajiye shi kama ya wuce gidan su,Yana zuwa ya samu hajiya na parlor tana kallon film,a gefen ta ya zauna,bayan ya gaishe ta bai sake cewa komai ba,kallon sa tayi Tace "Son Dan Allah ka fad'a min me yake damin ka,idan baka fad'a min matsalar ka ba wa zaka fad'awa?"
Riko hannun ta yayi yasa shi a cikin nata Yana d'an Wasa dashi yace "Mom,aure nake so"
'dan zaro Ido tayi Tace "Aure son a Yanzu?"
"Eh Kuma so nake a cikin satin Nan aje a nema min auren"
Zare hannun ta tayi tace " bazaiyu ba Hashim,kasan kana son aure Kuma kaki karb'an aiki? Yanzu Haka company ya daina tafiya yanda ya kamata ka sani mahifin ka ya tura ka kasar waje kayi karatu be don ka rike kamfanin bayan ransa ba zaman kashe wando ba daga Nan zuwa chan ba,idan kaga kayi aure to ka Zama cikakken mutum ne akasin haka Kuma to wallahi ba da yawuna ba."
Tana Kai nan ta bar gun ta barshi bakina bud'e Yana mamakin yanda ta d'auki maganar da zafi haka,Kiran Faisal yayi ya Sanar Masa Yanda sukayi da mom, Faisal yace "ai kaji Kuma Ana wata sai ga wata, Kai ma Hashim baka Jin shawara nasha fad'a maka ka koma company ka karb'i aikin Nan Amma ka bar bare akai yanzu wa gari ya waya?"
" Faisal na Kira ka ne ka ne don ka kwantar min da hankali ba ka kara min tashin hankali ba"
" To am sorry yanzu me abunyi?"
Iska ya hura Mai zafi kana yace "zan Fara zuwa aikin"
Mamakine ya kama faisal anfi shekara uku Ana bin say ya karb'i aikin Nan Amma Taki kwasam Rana d'aya ya amince tabbas Yana kaunar yarinyar Nan sosai.
"Toh hakan yayi Amma ka Fara Samar da hajiya tukanna kaji me zata ce"
" Okay insha Allah zanyi hakan,sai da safe"
A tare suka katse wayar.
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
PLEASE VOTE AND COMMENTS
NOT EDITED
" To am sorry yanzu me abunyi?"
Iska ya hura Mai zafi kana yace "zan Fara zuwa aikin"
Mamakine ya kama faisal anfi shekara uku Ana bin say ya karb'i aikin Nan Amma Taki kwasam Rana d'aya ya amince tabbas Yana kaunar yarinyar Nan sosai.
"Toh hakan yayi Amma ka Fara Samar da hajiya tukanna kaji me zata ce"
" Okay insha Allah zanyi hakan,sai da safe"
A tare suka katse wayar.
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
"Gaskiya nana al'amarin mutummin Nan ya fara bani tsoro yau ki manin sati biyu kenan Yana bacci sannan babu Wanda yazo neman sa"
" Abban Yesmin Nima abin na damina ,ace babu Wanda yazo neman sa,Allah dai ya bashi lafiya"
Ya Asma da "Ameren"
Faisal da Hashim na gani zaune,Hashim ya bugu uban tagumi,Faisal Ne ya dafe kafad'ar sa yace "Take it easy man,komai yayi zafi maganin sa Allah"
Huci yayi Mai zafi kana yace "yazanyi Faisal,wallahi duk duniyar ta daina min dad'i,na tsani yarinyar Nan na tsane ta and now I have to pretend Ina son ta duk bugun numfashina soyayyar Asiya ke karuwa a zuciya ta a yayin da kiyayya da tsanar Safiyya ke karuwa a Raina,wallahi wallahi idan wani Abu ya same ta sai na ga gatan su wallahi sai na say a d'aure ta da ita da uwarta"
"Allah shi kyauta,Amma ya kukayi da mummy ne ta amince da maganar auren kuwa?"
" Bata amince ba" Yana maganar ya d'auki juice dake gaban sa ya tsiyaya a glass cup sai da yayi sipping kana ya d'aura da fad'in "Na rasa yanda zanyi yau da two weeks Kenan,Ina gudun Kar Safiyya ta gane cewar game muke"
"Kar ka damu insha Allah baza ta ganeΒ ba,Kai ma dai Hash baka jin shawara wallahi,tun da ka dawo daga kasar waje ake ta binka ka Fara zuwa company kaki zuwa ka bar bare akai baka san rayuwar Nan tamu ta lalace
ba mutum ba abin yarda bane ba"
"A wannan halin zan Fara aiki? Ta ina zan Fara bazan ma iya concentrating ba"
" Hakane Amma Ina da shawara,Ina ga shine kad'ai mafita da ya rage Mana"
Ajiye glass cup d'in dake hannun sa yayi yace "uhmn Ina sauraron ka"
Magana suke kasa kasa Wanda na kasa ji, (nace idan tayi tsami zanji)
Murmushi Hashim yayi yace "Kai Alhamdulillah nagodewa Allah da ya had'a Ni da aboki irin ka hakan kawaii za a yi"
" Toh yanzu kaga bamu ga ta Zama ba,tashi zakayiΒ Muje mu nemi mafita"
Tashin su ke da with wayar Hashim ta Fara ringing Ciro wayar yayi daga aljihun sa Yar karamar tsaki ya jaa like, Faisal ke kallon sa irin kallon wa ke Kiran ka?
Chan ciki yace "yarinyar Nan ta dame ta takurawa Rayuwata"
Cikin kallon rashin fahimta Faisal yace " Wace yarinya Kenan fa?"
"Badiyya Mana ban San me take nema a guna ba,kwanaki ta daina kirana yanzu kusan sati uku Kenan take damina kullum sai ta Kiran Sam Bata da zuciya wallahi mtsww"
Murmushin gefen Baki Faisal yayi yace " Haba Kai kuwa sati uku fa kace? Kuma baka damu da kaji Kiran da take maka ba?"
" Ban damu ba,bana son ta ita Kuma ta makale min,Ni ban San meyasa matan yanzu Basu da kunya ba,Wai ace su Rika bin na miji da wanne zanji Dan Allah,da shaid'aniyar Nan Safiya zanji ko da ita?"
" Duk da hakan dai Badiyya Bata chanchanci Haka daga gare ka ba, yarinyar Nan ta nuna maka so iya so sabida laifi kalilan da ta maka sai is d'auki Karan tsana ka d'aura Mata, Allah da kansa kullun cikin sab'a Masa muke kuma yake yafe Mana,kayi hakuri ka saurare ta ko da kuwa baza ku cigaba da soyayya ba"
Huci Hashim yayi yace "Amma Faisal kasan babu macen Dana so a Rayuwata kamar Badiyya,naso ta irin son da ban tab'a yiwa wata 'ya mace a duniya ba,Amma taci amanata"
" Na sani, na sani Hashim let the bygones be gone please kamanta da duk wannan ya kamata ka saurareta kaji me ke faruwa"
" Toh naji zan kirata Amma ba yanzu ba"
" To ba matsala take your time but jar fa ya wuce yau d'in Nan"
" Naji naji mu tafi ko?"
Murmushi kawaii Faisal yayi yabi bayan Hashim.
Kwance take ajikin Sa suna kallon American film Mai suna RUSH HOUR, wayar Abban Yesmin ke ringing tun d'azu ankira yafi sau uku,ganin sabon number shiysa bai d'aga ba,Nana ganin Kiran yayi yawa Tace "Ya kamata ka d'aga Kiran Nan Naga Mai Kiran a matse yake"
Yar karamar tsaki yayi yace Miko min please" tashi tayi Mika Masa kana ta koma ta kwanta a jikin sa, kwanciyar ta yayi dai dai da shigowar wata Kiran, duka biyu ya d'aga da "assalamualaikum"
Daga d'ayan 'bangaren aka amsa da " wassalam am sorry to disturb you sir"
"Is ok who am I talking to?"
Ya amsa da "Dr Hassan from Doma hospital"
" Oh am so sorry,how may I help you?"
"Good news sir, the person you brought to our hospital just woke up"
Abban Yesmin min baisan sanda ya ture ta ya zauna ba yace "Are serious? When did he woke up?"
"About an hour ago"
" Okay okay am on my way now"
Sai da ya katse wayar yaga ya ture ta har kasa ita kuwa sai