yanda yarinyar Nan ta tafi da imani na bane ba, kasan wani irin shock da naji kuwa?"
Tunda Hashim ya Fara magana Faisal yake kallon Adams Baki a bud'e hannun sa Kuma a Kan goshin sai sai da ya Bari ya ida maganar dake bakin sa kana yace "Hashim Kenan kana da abin mamaki, naga Kaine kullum kake fad'in baka da lokacin Mata Kuma baka ga yarinyar da zaka bud'i Baki kace kana sonta ba?"
"Eh Haka nace Amma yau na gani tunda gashi ka gani na Mata magana Kuma na fad'a Mata Ina sonta"
Dariya Faisal ya Shiga yi Yana tafi yace "kaji mahauci waya ce maka Haka ake tinkarar mace daga had'uwa sai kace kana sonta, meyasa baza ka bari na saka a hanya ba?"
Tsaki Mai Kara yayi sannan yace "Amma ai kaga sanda na fita ko?"
"Ina na gani ji nayi kawai na buge goshina"
"Ina zakaji ka tsaya kana sana'ar chatting da Emmata"
Murmushi Faisal yayi Yana shafa kasumabar sa sannan yace "Alhaji baka San d'adin chat da Mata bane wallahi shiysa"
"Kai ware dalllah, Ni yanzu Taya za a yi na sake ganin yarinyar Nan?"
"Oh Allah Kai Kuma abin ta Kan kwaila ka Fara"
"Eh d'in kasan yarinyar Nan tafi Wannan mahaukaciyar budurwar ka"
Kama Baki yayi yace "Babyn tawa kake Kira mahaukaciya?"
"To mene ne in ba mahaukaciya ba, yarinya tayi kwalli kamar Mai aljanu?"
"Lallai Hashim one zero kaci tuwo a kaina Amma ba komai zan Rama"
Dafe Faisal Hashim yayi sannan ya Shiga girgiza shi had'e da fad'in "am sorry am sorry yanzu dai please help me out, ya kake ganin za'a yi?"
Kau da fuskar sa yayi ya d'an yi shiru kana yace "Let's follow her muga gidan su, don alamu sun nuna a unguwar Nan take"
Cikin murna yace "Good advice" Nan ya murd'a key suka bi bayanta.
Asiyah tunda ta bar gun bata daina gudu ba har sai da ta Isa bakin gate na gidan su, Kan ta dai daita nitsuwata sannan ta bud'e karamin gate ta shige Ciki.
Hashim da Faisal sai dube suke Amma Shiru kake ji basu ganta ba Yar karamar tsaki Hashim ya ja had'e da buga steering motar sa kan kana yace "Kamar aljana ta b'ata baat?"
Yana maganar Yana leka waje.
"To wa ya sani ko aljannar ce , don nayi mamakin yanda ka damu da ita a lokacin guda haka in......"
Hararar da yayi Masa ne yasa Faisal ta kasa karasa maganar da yake.
Sauka yayi a Kan titin yayi parking a gefen, Faisal yace "Kar ka damu tunda dai tana zuwa islamiya ta kwana gidan sauki gobe ba sai mu dawo ba?"
Murmushin samun nasara yayi yace "Thanks Abokina" Nan ya tada motar suka bar unguwar dropping d'in Faisal yayi Kan ya wuce gida bai tsawon lokaci ba ya Isa gida dake gidan nasu ba nisa.
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
Kuyi hakuri da wannan, sabida na Koma maranta.
Wattpad bana ganin vote an Comments d'inku alamu sun nuna Baku Jin d'adin book d'in sabida zan daina d'aurawa kawaii.
π¦π¦ *MATAR UBA* π¦π¦
_(A True Life Story)_
*Short story*
```Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)```
Follow me on Wattpad @Milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0
π *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION*πποΈ
_'kungiya d'aya tamkar da dubu_
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayiwa Yan Uwa Mata nasiha,Allah ya bani ikon gama shi lafiya kamar yanda na Fara lafiya ameen.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* Much Love.
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
Not Edited
CHAPTER 9
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
...........Asiyah da Sallama ta shiga amma babu Wanda ya amsa tab'e Baki tayi alamun ko a jikinta, ganin safiyya a zaune ne a Kan sofa abin ya Bata mamaki cike da mamaki take kallon ta Tace "Safiyya Ashe dama kina Nan kina ji Ina Sallama ba ki amsa ba?"
Shiru ko kallon ta ba tayi ba bare ta amsa mata kad'a kai tayi Tace "please Safiyya idan wani abun na Miki tell me bana Jin d'adin sabon halin da Kika Fara min daga jiya zuwa yau"
Wani irin muguwar kallo ta Mata Kan ta Tace "Idan kin gama tambayoyin naki mummy na neman ki."
Sai ta cigaba da kallon da take.
Asiyah kanta ne ya d'aure a zuciyar ta Tace "ko dai maganar shamsiyya gaskiya ce Anya ba mummy ba ce ta Shiga tsakanin su? In ko hakane ta cuceta ta cutar da Safiyya" cikin Wannan tunanin ne ta karasa kofan d'akin mummy tasa hannu zata kwankwasa kofar sai ji tayi Baraka na dariya har da buga kafa hakan tasa ta d'an tsaya don Jin abinda take fad'a "ke dai qawata bari, Shiyasa nake son ki kw d'in ta dabance na yi yanda kikace nasan Dole ita da kanta zatace ta hakura da makarantar."
Dariya ta sake yi kana Tace "Haba ai Asiyah kamar kwallo take a hannu na ko ince kamar waina duk inda nasi zab juya ta gamar yanda na juya Ubanta, Qawata na so ace na kashe ta kamar yanda na kashe Anisah da Uwar su, Amma she is my next target."
Asiyah dafe kirjin ta tayi ki tayi duniyar na juya Mata kanta Kuma ya Shiga tsarawa kamar zai tsage gida biyu, ganin tana kokarin fad'i wa ne tayi saurin jingina jikinta a jikin bango, ta d'auki tsawon lokaci a haka, a hankali ta nufi d'akin ta babu abinda ke Mata yawo a Kai da Kuma zuciyar ta sai kalmar da taji "Na so ace naΒ kashe. Ta kamar yanda na kashe Anisah da Uwar su" cikin Wannan tunanin ne ta zauna a bakin gado tare da have Kai da gwiwa "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un ashe itace sanadiyar mutuwar Mummy na,farin cikina Kuma sanyin idanuwata? Me suka Miki da har suka chanchanci mutuwa" kuka ta saki Mai cin Rai kuka take sosai Wanda tunda take Bata tab'a irin sa ba Jin ana kwankwasa kofar tane yasa tayi saurin mikewa had'e da share hawayen ta bud'e kofar ganin mummy ce tayi saurin gaishe ta Bata amsa ba, kallon ta take nason fahimtar abinda ke damin ta Amma ta kasa ta ce "Ke kukan uban me kike?"
Cikin shakewar murya Tace "Ba kuka nake ba"
Taking ta Yi sannan Tace "Safiyya Bata fad'a Miki Ina neman ki ba?"
"Ta fad'a min so nake na cire uniform sai nazo"
Tab'e baki tayi ta Mika wata leda had'i da fad'in "ki kaiwa Maman Yesmin" tana mika Mata ta juya zata tafi Asiyah Tace "Mummy kud'in machine fa?"
Wata muguwar harara ta Mata sannan Tace "me amfanin wad'an Nan?" Tana maganar tana nuna kafar Asiyah.
Asiyah ita ma kallon kafan nata tayi sannan Tace "Tafiya" "good to dasu Zaki tafi bani da kud'i"
Cikin sanyin murya Asiyah Tace "Mummy gidan fa da nisa gashi yanzu Maghriba ta kusa zan yi dare a hanya"
"Wannan Kuma ke ta shafa"
Kai a kasa Asiyah ta shige d'akin ta.
Canza Kaya tayi tasa abaya sannan ta d'auki hijab Wanda ya d'an rufe mazauninta kad'an sannan ta fice daga gidan, tafiya take ta na zuba saurin don Kar dare ya Mata a zuciyar Tace "In ba mugun ta da rashin imani ba ga motoci a gida sannan ga driver ai za'a ce ya kaini" maganar da d'azun ce ta sake dawo Mata tafiya take tana kuka ganin bazai amfane ta ba ta Shiga yin addu'o'in da duk suka Zo bakin taΒ a Haka har ta isa estate nasu Nana (Maman Yesmin) tana Isa Taki ana kiraye kirayenΒ sallah da sallama ta Shiga Yesmin ce ta amsa ganin Asiyah ce da gudu ta nufo kofar ta rungume ta tana fad'in "Oyoyo aunty Asiyah yau kece a gidan namu?"
Nana Jin an ambaci sunan Asiyah yasa tayi saurin fita daga kitchen a tsawace Tace "Ke Yesmin ba ki da hankali ne? Sau nawa nake Miki warning a Kan ki daina Shiga har kar mayyar yarinyar Nan?"
Yesmin kai a kasa sai ta Shiga Wasa da yatsunta hanun ta.
Asiyah cikin girmawa ta gaishe ta kamar bata ji haushin maganar ba, cike da gadara ta amsa gaisuwar Kan Tace "Yesmin karb'i ledan hannun ta" cikin sauri ta Mika Mata sannan ta nuna Asiyah da Yar yatsa Tace "Get out from here Jaka kawaii"
Murmushi tayi sannan ta ce "Sai da safe mummy" sai ta fice daga gidan, Nana a zuciyar ta Tace "Wannan Wace irin yarinya ce da Bata da zuciya ko kad'an duk abinda ka Mata baya b'ata Mata Rai"
Murya Yesmin ne ya dawo da ita daga tunanin da ta Lula "Na'am me kikace?"
Nana ke yiwa Yesmin tambayar nan, a Karo ja biyi ta kuma cewa "Mummy cewa nayi meyasa kukeyi Mata hakane ko tausayin maraicin ta ba ku ji?"
"To sannu uwata, kina jina Yesmin daga yau idan Kika Kuma Shiga harkar da ba naki ba sai na karya Miki hakori,wuce ki bar Nan" Yesmin turo Baki tayi had'e da bubbuga kafa Tace "Ku dai Rika Sara Kuna duba bakin gatari don wallahi Allah bazai Bar Ku ba"
"Lala lala Yasmin Ni kike fad'a wa hakan?" Ganin tayo kanta hakan yasa ta shige d'akin ta da gudu had'e da rofo kofan ta Ciki, cikin b'acin Rai Tace "Yau Ni da ke a gidan Nan Yesmin" har wani huci take.
******
"Son Dan Allah ka tashi kaje kayi dropping d'in Addar ka a gida"
Turo Baki yayi cikin shagwab'a yace "Mami Wai Dan Allah meyasa ake so a Maida Ni driver d'inta ne? Ta Kira mijinta Mana yazo ya d'auke ta, kuma ai tana da motar ta ko?"
Murmushi irin nasu na manta Mami Tace "Hashim Kasan halin Fadeelah Sarai ba ta fiye son tuki ba Dan Allah tashi ka kaita kaga karfe takwas harta wuce"
Ba don yaso ba ya tashi ya fita ta d'auko key ya nufi parlor, Da gudu yazo ya rungume shi shafo kansa yayi had'e da d'aukan sa yace "Adnan bakayi bacci ba?"
"Eh uncle Hashim Kai muke jira ka Maida mu gida da Momy"
"To gani nazo Ina Islam take?"
"Gata chan a bayan Momy tana bacci" Yana nuna inda Fadeelah ke tsaye kallon su take tana Murmushi, Kai yasa ya fice ba tare da ya Mata magana, Sallama tayi wa Mami sannan ta bi bayan su.
A sit na Mai zaman banza ya ajiye shi sannan ya zago ya Shiga gun zaman diver tana Shiga ta tada motar Mai gadi ya bud'e musu gate suka fice, Adnan da Hashim ne ke Hira yayin da Fadeelah ke sauraron hiran su, suna Isa ya musu sai da safe ya juya abin sa, ya nufi hanyar gida.
Asiyah sauri take sosai ganin wuri ya Fara duhu gashi gun Shiru ba kowa sai motoci dake wucewa d'add'aya, a kan wata kwana Taji ance "Ke Ina Zaki?"
A tsorace ta juya ganin wani jibgegen na na Miji ne yasa ta juya da sauri ta Kara speed din ta, Bata Ankara ba taga wani ya fito a gaban ta Dariya yayi had'e da Sa hannu a aljihu Kan yace "Saurin me kike ne?"
Cikin Rawar murya Tace "Gida zani"
A hankali ya nufo ta ta juya baya da niyar gudu ya chafko ta ihu ta saki Mai Kara tana fad'in "Dan Allah Kar ku cutar dani kuyi hakuri ji marainiya ce" d'aya daga cikin su yace "ta kwaana gidan sauki Nima maraya ne" d'ayan ne ya kyal Kyale da dariya kana yace "Shikenan mutumina kunyi anko" Kana Jin Muryar san a shaye yake.
Tsaba ta yayi a wuya tana ihu tana neman taimako Amma Shiru kake ji, wani uncompleted building suka Shiga da ita.
Motar Hashim na gani ya tsaya kashe kid'an da yake ji yayi ya d'an yi shiru a fili yace "Kamar muryar kukar mace nake ji?"
Sai ya kuma Jin ihun hakan ya tabbatar Masa da akwai Wacce take cikin matsala, fitowa yayi da ga cikin motar sai Kuma ya daina Jin kuka, yasa kafar sa d'aya cikin motar ya Kuma jiyo muryar da sauri ya juya ta inda yake Jin Muryar sai ya hango maza biyu d'aya na gaba d'aya na baya sannan da alama mace ce a kafad'ar sa, cikin sauri ta nufi inda suke.
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
Mu had'u a page ba gaba
Please vote and comments
Milhaat ce
Yar Terawa
π¦π¦ *MATAR UBA* π¦π¦
_(A True Life Story)_
*Short story*
```Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)```
Follow me on Wattpad @Milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0
π *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION*πποΈ
_'kungiya d'aya tamkar da dubu_
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayiwa Yan Uwa Mata nasiha,Allah ya bani ikon gama shi lafiya kamar yanda na Fara lafiya ameen.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* Much Love.
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
CHAPTER 10
NOT EDITED
Motar Hashim na gani ya tsaya kashe kid'an da yake ji yayi ya d'an yi shiru a fili yace "Kamar muryar kukar mace nake ji?"
Sai ya kuma Jin ihun hakan ya tabbatar Masa da akwai Wacce take cikin matsala, fitowa yayi da ga cikin motar sai Kuma ya daina Jin kuka, yasa kafar sa d'aya cikin motar ya Kuma jiyo muryar da sauri ya juya ta inda yake Jin Muryar sai ya hango maza biyu d'aya na gaba d'aya na baya sannan da alama mace ce a kafad'ar sa, cikin sauri ya nufi inda suke.
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
.........."Dan Allah kuyi hakuri Kar ki cutar Dani"
Hannu yasa a Baki yace " Ssshhh ki daina ihu baza mu cutar da ke ba zamu ji dadine mu jiyar dake dad'i"
Yana maganar yana tangadi alamun a shaye yake, a kasa ya ajeyi ta suna kokarin raba ta da kayan da ke jikin ta,Β takure kanta tayi guri guda tana kuka tana rokon su amma Basu kukata bare suji tausayin ta.
Cikin sauri Hashim ya karasa gun bugu d'aya ya Masa ya fad'i Kun San mashaya idan shaye shayen yayi musu yawa yana tafiya da karfin su, abokin tafiyar tasa ganin an bugi abokin sa ya saketa ya arce da gudu,da kyar ya mike ya bi bayan sa.
A hankali yake tafiya kusanta ganin ya kusanto ta tayi saurin mikewa ta Ruga da gudu ta fice daga gun, kad'a Kai yayi har ya juya zai tafi sai Kuma ya hango hijab d'in ta Murmushi yayi Wanda ya bayyana kyawun fuskar sa, cikin tafiyar sa Mai Kama da takama ya karasa gun ya sunkuya ya d'auka ya dad'e Yana kallon hijab d'in had'e da murmushi Wanda shi kansa Bai San Yana yi ba, shinshina hijab d'in yayi had'i da Jan dogon Numfashi idon sa a rufe a hankali ya bode idanun saΒ kana ya fice daga gun,motar sa ya fada kana ya jaa motar da speed ya bar gun.
******
"Idan shegiyar yarinyar Nan ta dawo Kar ka kuskura ka bud'e Mata gate kana jina ko?" Baraka ke maganar Nan tana nuna shi da d'an yatsa had'i da rike kunnen ta alamun gargad'i.
Cikin Rawar murya yace "Toh toh Hajiya"
Hararar sa tayi Had'i da tsaki ta juya ta shige Ciki.
Da gudu Asiyah ta karaso tana bubbuga gate tana kallon bayan ta gani take kamar sun biyo ta, da sauri ya fito Yana kallon ta cikin tashin hankalin da son gane abun da ke damin ta had'i da leka bayan ta don ganin me ya biyo ta, gashi kanta ba ko d'ankwali yace "Asiyah lafiya me ya faru? Wa ya biyo ki?"
Cikin kuka Tace "Baba habu ka Bari na Shiga daga Ciki tukunna Wallahi zasu cutar dani"
" Su waye?"
" Wasu ne" tana maganar tana kokarin kusa kanta Ciki ta gefen sa, da sauri ta dakatar da ita, Kai a kasa yace "Kiyi hakuri asiya yau baza ki kwana a gidan Nan ba?"
Cikin tashin fahimta Tace "kamarya ban fahimce ka ba?"
Kan ya yi magana suka tsinkayi muryar Baraka na fad'in " Kamar yanda nace" Tafiya take tana jaan kafa hannayen ta duka biyu a kwankwaso Tace " Daga ina kike?" Cikin tuhuma take maganar.
Cikin sanyin murya Tace " Daga gidan su yesmin"
"Yi minΒ shiru Munafuka, na kirata ta tabbar min da cewar kin bar gidan tun Kan ayi sallar Maghriba"
" Mummy Wallahi daga chan nake wasu ne suka tare Ni a hanya Kinga abin....." Kan ta karasa maganar dake bakin ta Tace " Dakata Munafuka just Zaki Raina was hankali, yoo kin Saba Basu Kanki ya za'ayi baza su karb'a ba, kin ga ki bar nan gun ko yanzun Nan na nad'a Miki na jaki, Kai Kuma wuce ka rufe min gate" tana kai Nan ta juya ta shige Ciki, baba habu tausayin ta ne ya kamashi Amma babu yanda ya iya Dole yayi yanda yace sabida yasan Baraka Sam Bata da mutunci duk da a haife zai haife da hakan baya Hana ta yi Masa rashin mutunci da aikin ya dogora Wanda ya ke ciyar da kansa da Matar sa.
******
Kofan ta Shiga bugawa tana Kiran sunan mummy da baba habu Amma Shirin kake ji, ta ci kuka sosai Saida tayi Mai isarta kana ta bar gun da saurin gaske.
Bata tsaya ko ina ba sai kofar gidan su
Kawarta shamsiyya, da gudu ta karasa kofar gidan ta Shiga bubbuga kofan gida, cikin tsawa Mai gadi yace "waye"
Cikin kuka Tace "Baba Hassan nice"
"KeceΒ wa?"
"Asiyah"
Chan kasa yace "Asiyah da Daren nan?"
Da sauri ya bud'e kofar ganinta a haka ya yi bala'in tada Masa hankali, "daga in kike haka me ya same ki na ganki a haka?"
" Baba Dan Allah gun shamsiyya Nazo ka barni na shugay daga Ciki?"
" Bismillah shigo shigo" Yana wangale Mata kofa, wata ajitar zuciya ta sauke Mai Karfi had'i da sungunawa kamar tayi ruku'u alamun gajiya Numfashi take saukewa a Kai kai, Tace "Dan Allah baba Ka Kira min Shamsiyya"
"Zo Muje" tafiya yake tana buyer dashi jaaan kafan take sabida yanda kafafunta suka Mata nauyi, cikin nitsuwa ya danna door bell d'in gidan, cikin Sa'a shamsiyya yace ta fito tana ganin Asiyah a haka hankalin ta yayi mugun tashi da sauri ta karasa inda take ta rike hannayen ta, cikin tashin hankali Tace "Asiyah what happened? Me ya same ki?"
Asiyah kasa magana tayi sai kawaii ta fashe da kuka, hakan ya sake tada Mata hankali, baban Hassan ne yace "Ku Shiga daga Ciki Mana shamsiyyatu sai kiji ko mene ne ko?"
" To baba"
" Yauwa to sai da safe ko? "
Shamsiyya yace ta amsa da " Ameen baba"
********
Suna Shiga Kai tsaye d'akin ta suka nufa, ruwan wanka ta had'a mata Mai d'an dumi sannan ta Shiga tayi wanka, ta shafa Mai sannan ta bata sleeping dress