Nana na ganin ya Shiga TaceΒ "Baraka Taya Za'ayi mijin ki zai ce miki kar kiyi kuka,kiyi kuka sosai har sai hawayen ki sun kafe"
Cikin rashin fahimta tace "kamar Yaya? Nayi kuka ban fahimce ki ba?"
"Eh Mana Taya zaice Kar kiyi kuka bayan shekara d'aya d'aya har uku baki samu ciki ba, zuwa gidan bokaye da malamai cikin Nan ya samu ya lalace Kuma yace Kar kiyi kuka?"
A tsawace Tace "Me yasa Baki da hankali ne Nana ke Wace irin qawace? Ke yanzu ba Kya Jin tausayina?"
Yar karamar dariya tayi Tace "Ke ai ba abinda tausayi bace ba Sadeeq ne abin tausayi" tashi tayi Tace "Anyways Naga jikin naki da sauki tunda har kina iya masifa Kinga tafiya ta" tana Kai Nan tayi ficewar ta.
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
https://www.wattpad.com/1027106095?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Milhaat&wp_originator=uyxpR83O%2BJUyICY7Jr%2F9ofp0ACXRgT4vHI5%2Fc7gGafd0OzHEvHJPC0mzEOA5avXT10q7uF8MK4FsdOZJnwW3r5VX9NY2LSyN%2FwxotkHH7Ty1QwqMWaCJ8pB6r4NmqV2h
PLEASE SHARE AND COMMENT
MILHAAT CE
YAR TERAWA
CHAPTER 5
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
.............Asiya tun da ga Wannan ranar ta daina cin girkin Baraka idan ta bata zubarwa take idan tayi bacci sai ta Shiga kitchen ta girki indomie ko taliya Kan tayi bacci wasu lokutan Kuma da yunwa take kwana.
Baraka kullum cikin mamaki take taya za'a yi tana cin abincin Kuma babu abinda ke samin ta hakan yasa ta hakura ta d'auki alwashin gana mata azaba ba dare ba rana in yaso ta gudu ko Kuma wahala ta kashe ta.
Daddy Kuma yasa Ido sosai a lamarin Asiyah don ya lura tana cikin damuwa, gashi yarinyar na da zurfin ciki hakan yasa yake bata kulawa na musamman in dai Yana gida ta tana makale a jikin sa, Baraka Kuma tayi ta Mata Hidima kamar zata goyata Amma da zaran ya fita sai ta Zama kamar dodo.
*BAYAN WATA SHIDA*
Baraka ta samu Ciki, Daddy kullum cikin tarairayar ta yake yana bata kulawa, Asiyah Kuma ko da Wasa Bata tab'a fad'a masa abinda ake Mata ba.
Kamar kullum suna zaune a parlor shi da Baraka aka Kira wayar sa, Yana picking daga d'ayan b'angaren akace "Sir munyi baki Kuma sunce suna bukatar ganin ka yanzu"
Jin suwaye bakin hakan yasa ya Mata Sallama ya fita.
Bayan ya gama abinda yake yi a office din a hanyarshi ta komawa gida yayi hatsari, Baraka na zaune da cikin ta d'an wata shida aka kirata aka Sanar da ita ba ta tsaya b'ata lokaci ba ta fita tana zuwa asibiti ta Samu Yana emergency kuka ta shigayi ganin yanda yaji ciwo, kafan sa na dama karaya uku Haka ma kansa bandeji ne hannun sa na dama ya karye, riko hannun ta yayi da hannun hagunsa Murmushi yayi sannan yace "Baraka ki daina kuka kinji?"
Cikin kuka tace "Taya za'ayi na daina kuka ka duba kaga yanda ka ji ciwo wallahi tausayin ka ne ya kamani Allah ya tashi kafad'ar ka"
Ya amsa da "Ameen Amma Baraka Ina ji a jikina kwanaki na sun Kare Dan Allah Baraka ki kula da Asiyah ki rike ta tamkar Yar ki kisani cewar marainiya ce, dukiya ta duk sunan tane akai sannan Kema akwai naki kason da abinda ke cikin ki, Dan Allah ki sata a makaranta tayi karatu ta Zama likita sannan ki aurar da ita ga miji na gari" ya Karasa Maganar Yana kuka, cikin kuka Tace "Insha Allah Kai zakayi Mata duk wa'annan, insha Allah Kai Zaka aurar da ita"
Kallon ta yayi idon sa cike sa hawaye yace "Na so nayiwa Asiyah kallon karshe Amma nasan bazaiyu ba"
"Dan Allah Sadeeq ka daina fad'in haka"
Murmushi yayi yana ciza leb'en sa,shi kad'ai yasan abinda yake ji yace "Ki taimaka min da Ruwan sha"
Cikin rashin nitsuwa ta fita don sayo ruwa.
Tana shigowa d'akin ta ji likita na cewa time of death 6:46" Yana kokarin rufe Masa fuska, yatsar da pure water hannun ta tayi, ta d'aura hannu a Kai ta kwala ihu tana fad'in "Na Shiga uku" da sauri likitoci sukayi kanta Nan take ta fad'i sumammiya.
Nan ta Fara bleading dakyar suka samu suka tsayar da jinin, Asiyah na gida ta kasa bacci sai safa da marwa take duk hankalin ta ta kasa kwanciya.
A Rana ita kad'ai ta kwana, a asibiti aka sallace shi ta Kira abokan nan sa na gida da gun aiki aka Sanar da dangi na kusa da na nesa anan aka sallace shi, Aunty Rukayya ce ta d'auko Asiyah don ta ganewa idon ta don sanda ta fad'a Mata Taki yarda cikin kuka Asiyah ke fad'in "Karyane Daddy Yana Raye Bai mutu ba, Daddy bazai min Haka ba, Daddy bazai barni a duniyar Nan Ni kad'ai ba"
Rukayya Taji tausayin ta sosai, Yarinya Yar karamar ta zama marainiya ba Uwa ba uba, duk yanda za a yi Dole ma ta d'auki Asiyah ta dawo gunta" tana maganar Nan ne acikin zuciyar ta.
Sai da ta ga mahaifin ta a kwance cikin likafani ta Fad'i sumammiya, Nan aka tafi da gawar aka kaishi makwancin sa, mutanen gun duk sai da sukaji tausayin Asiyah wa amda suke da saurin hawaye Kuma sai da suka Mata kwalla ganin halin da take ciki.
Kwana ta yi ta wuni a sume farkawan ta ta d'auka mafarki take Nan ne fa bud'e sabon shafin kuka.
Tun daga Wannan ranar Rayuwar Asiyah ta canza ta lalace, Baraka abin nema ya samu gaba ki d'aya ta Hana ta zuwa makaranta makarantar ma ta Hana ta zuwa Islamiyya kuma sai ta ga dama ta Barta ta tafi Sam Bata damu da mutuwar Mijin nata ba ita dai dukiyar take so Kuma yanzu ya shigo hannun ta sai yanda taso tayi dashi.
*BAYAN WATA UKU*
Baraka ta haifi 'yar ta ta mace kyakkyawa ce kamannin ta sak kamar Anisa, Baraka ganin kamannin Anisah ce ta tsorata da farko ganin ba amfani ta sake jikin ta, ta cigaba da kula da 'yarta Wacce aka sawa suna Safiya.
AFTER FIVE YEARS
Safiya na gani zaune Akan koshin ta yi Hannun ta rike yake da remote, fitsari ne ya dame ta hakan yasa ta tashi ta Shiga toilet dake parlor d'in bayan ta fito ga mamakin taga TV a kashe Remote ta d'auka ta danna switch bottom Amma yaki yiΒ Β a fili Tace "Na Shiga uku Kar dai na sake lalatawa, yau Mummy zata kashe Ni" ta karasa Maganar had'e da goge hawayen da ya zubo Mata.
Asiyah na ganiΒ ta Shigo parlor jikin ta duk kura da alama shara tayi ganin safiya tana kaiwa ta na kawo wa yasa ta karasa inda take Tace "Ya dai Safiya me ya faru na ganki kamar kinaΒ cikin damuwa? Kuma harda kuka lafiya kuwa?"
Cikin kuka Tace "Aunty Asiyah na Shiga uku yanzun Nan nake kallon TV sai na Shiga ban d'aki don nayi fitsari sai na dawo Naga TV ya d'auke"
Murmushi tayi Tace "ki daina kuka Bari na duba" Asiyah tayi duk abinda taga zai iya Zama matsalar Amma yaki kawo wa, huci tayi Tace "Inaga fa yaci fuse ne Dole sai an kai shi gyara."
Safiya ta fashe da kuka Tace "Yau na Shiga ukuΒ nasan yau Mummy sai ta kusa kashe Ni"
"Ki daina kuka Safiya kinsan bana son kukan ki ko?"
Cikin kuka Tace "Aunty Asiyah Dole nayi kuka idan mummy tasan nice nasan sai ta kusan kashe Ni."
"Ki kwantar da hankalin ki ba Mai kashe ki kinji?"
Jaaa da baya safiya tayi Tace "kamar ya? Kar dai yau d'in ma zaki karb'i laifin da ba naki ba?"
"Safiya bana so mummy ta dake ki sabida Haka Kar ki fad'a Mata kinji?"
Safiya Tace "a'a Ni gaskiya yau Kam bazan yarda ba kullum cikin karb'an laifina kike mummy ta Rika dukan ki bana so"
Murmushi tayi Tace "Muje muyi sallah" rike hannun ta tayi suka haura sama.
Bayan ta dawo daga yawon ta, ta zauna a Parlor ta d'auko remote tayi kallo Amma yaki yi ta duba sosai Amma yaki yi murmushin gefen baki tayi tace "Lallai yarinyar Nan wato na hanata tab'a TV Nan Amma Taki ji Zaki gane kurenki" Nan ta Fara kawala Kiran sunan su,cikin sauri suka sauko cikin girmamawa ta durkusawa Tace "Mummy welcome" Rai a b'ace Tace "Sau nawa nace Miki ki daina cemin mummy Ni ba mamarki bace ban haifi mayya ba" Kai ta San kasa sai Baraka ta d'aura da fad'in "uban wa ya tab'a TV Nan tsakanin ke da safiya?"
Kallon Juna sukayi a tare suka ce "Ni ne"
Tab'e baki Baraka tayi Tace "I knew it kece Kika b'ata ke mayyar Ina ce haka? Duk abunda Kika tab'a sai ya b'aci ke Kuma safiya nasha fad'a Miki ki dai na kokarin Kare ta in ba Haka ba zan.b'allaki"
Cikin kuka Tace "Mummy wallahi ba itace ba nice na b'ata."
A tsawace Tace "Safiya fice min daga nan ko na Zane ki"
Cikin kuka Mai sauti da tausayin Yar Uwarta ta haura sama da gudu.
"Ki yi kneel down Kuma yau a Haka Zaki kwana" Bata Musa ba tayi yanda Tace, Baraka ta Fara kalle kalle a fili tace "Ina yarinyar Nan take? Altine!!! Altine!!!" Daga nesa naji ta amsa daΒ "Na'aaam" altine itace sabuwar 'yar aikin Baraka.
Cikin girmamawa Tace "Sannu da dawo wa hajiya" a tsawace ta dakatar da ita "Dallah Malama ban kiraki don ki gaisheni ba, Ina Kika je har Kika bar mayyar Nan ta lalata min TV?" Tana maganar tana nuna Asiyah da Yar yatsa.
Cikin Rawar murya Tace "Hajiya Ina kitchen ne Shiyasa Amma fa safiya ce take kallon cartoons d'azu ban San ya akayi ba"
A tsawace "Would u shut up ur dirty mouth, by the way yau a Haka zata kwana Karki kuskura ki b'ata Abinci idan Kika Bata Kuma kin San sauran a bakin aikin ki bayan na ci mutunci ki" tana Kai Nan ta haura sama.
Altine tana matukar tausayin Asiyah hakan yasa ta bar gun, safiya sai da tabbatar Baraka tayi bacci ta fito, ga mamakin ta Asiyah na parlor Bata tashi ba.
Cikin tsand'a ta karaso Tace "Aunty Asiyah Dan Allah ki tashi Muje mu kwanta."
Asiyah duk ta galabaita jikin ta ya jike sharaf duk da AC dake d'akin Bai Hana ta had'a zufa ba,cikin Rawar murya Tace "A'a Safiya so kike mummy tayi fushi dani?"
"A'a bana so Amma kin San daii bakya Mata gwanin ta komai kikayi ba dai dai bane a gunta to me amfanin yi? Dan Allah ki tashi"
Ta na Maganar tana jaan hannun ta Amma Taki tashi har ta gaji cikin sanyin murya Tace "Kina Jin yunwa ko?"
Kai kawaii ta d'aga alamun eh, safiya Tace "Sannu tun breakfastΒ da kikayi ba kici komai baΒ kin wuni aiki Nan maΒ two slice of bread kawaii Kika ci bari naje na kawo Miki abinci"
Murmushi tayi ta d'aga kaai alamun to, tana fita ta shigo kitchen ta d'auko plate ta zuba spoon d'aya sai ji tayi ance "Safiya" a tsawace, a razane ta waigo ganin altine ce yasa ta sauke Numfashi a hankali.
Altine tace "Ke me kikayi anan?"
Ba tsoro tace "Abinci naxo d'eba wa aunty na"
Murya kasa kasa "Baki da hankali ne? So kike ki jaa min masifa ko?"
"aunty altine please ki barni na d'eba Mata ko da kad'an ne"
Wacce aka Kira da Altine a tsawace Tace "Ki fita" a razane ta fita, tana kuka.
A ranar Asiyah a kneel down ta kwana, sai da aka Kira sallar asuba Baraka ta fito a tsawace Tace "Ke mayya tashi ki fice daga nan, in kin so ki sake b'ata min wani Abu sai kin kwana kin wuni kina kneel down " tayi tsaki ta fita, safiya ta shigo parlor da alama ita ma batayi baccin ba, riko hannun Asiyah dakyar ta tsaya kafafuwanta sun kumbara timm, tana tafiyaar tana kuka da taimakon Safiya Asiyah tayi wanka da Ruwan zafi ta gasa jikin ta tayi alwala a zaune tayi sallah sabida kafufuwan ta sunyi tsami baza ta iyaΒ tsayawa ba sabida irin azaba da gwiwowinta ke yi.
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
Please wattpadd bana ganin Vote dinku da Comments.
Kuyi hakuri fans kwanaki kusan shida ban samu nayi muku typing ba, Kun San an koma makaranta Zama sai ya gagareni gashi Kuma ban gane karfin jikin nawa ba Ina Mai Baku hakuri.
Mu had'u a page na gaba
Milhaat ce
Yar Terawa
π¦π¦ *MATAR UBA* π¦π¦
_(A True Life Story)_
*Short story*
```Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)```
Follow me on Wattpad @Milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0
π *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION*πποΈ
_'kungiya d'aya tamkar da dubu_
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayiwa Yan Uwa Mata nasiha,Allah ya bani ikon gama shi lafiya kamar yanda na Fara lafiya ameen.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* Much Love.
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
Not Edited
CHAPTER 6
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
......... altine na gani a kitchen tana shara had'e da rawa da waka, wakar ado gwanja take Mai taken fad'in Alhairi gaskiya jari.
Baraka ta shigo tayi tsaye akanta tana Mata kallon sama da kasa a tsawace Tace "Altine!!! What do you think you're doing?"
A razane da Yar da tsintsiyar dake hannun ta ta fara tsotsa kamar wata Mai kwarkwata, cikin Rawar murya Tace "Hajiya Ina kwana"
Fuska a tamuke Tace "Yi min Shiru which stupid song are you singing?"
Washe Baki altine tayi Tace "Madam ba stupid song bane kin San yanda ake yayin shi a kauyen mu kuwa? Umm ado gwanja ne fa Kum......"
A tsawace ta dakatar da ita Tace "Shut up, ke bakya gajiya da surutu"
Altine hannu tasa da sauri ta rike bakin ta.
Baraka Tace "Me kikeyi a kitchen d'in?"
"Babu komai Hajiya"
"Okay maza ki min breakfast Ina jiran ki a dinning"
Ta amsa da "to Hajiya"
Har ta Kai kofan fita ta dawo da baya Tace "Yauwa daga yanzu na raba muku aiki da Asiyah tunda bata da abin yi sai lalata min Kaya"
Cikin kuka altine Tace "Hajiya me na Miki? Me na Miki hajiya da Zaki rage min albashina Kuma kike cewa mu raba aikin da 'yarki?"
Baraka tunda altine ta fara Maganar take aikin kallon ta Baki a bud'e sai da Kare maganar sannan Baraka Tace "ke wawuya ce, inaga gadon wauta kikayi, a Ina kikaji na ambaci na rage Miki abashi?"
Sosa keya ta shigayi Baraka Tace "Useless girl, hurry up and bring my breakfast" tana Kai Nan ta fice.
Altine turo Baki tayi a fili Tace "Kanki ake ji Ni banji me kike fad'a ba sabida Haka Kan ki Kika zaga,Mata sai mugunta sai kace mayya aniyar ki ya biki da dukkanin sharrin ki"
Sai ta cigaba da aikin ta, bayan ta gama had'a breakfast din,ta jera a dinning, Irish ta soya tayi source.
Asiyah na d'akin ta tana nad'e kayan da ta wanke, Sai taga shigowar Safiya Murmushi tayi Tace "Safiya ba Sallama?" Ba tare da ta kalli fuskar ta ba, Jin tayi Shiru ta d'ago Kai a hankali Tace "Safiya what happened why are you crying?"
Cikin muryar kuka Tace "Aunty Asiyah it has happened again?"
Cikin rashin fahimta Tace "What happened again?"
"I tempered with mummy's wrist watch"
"Ya Salam!!! Haba safiya meyasa kike tab'a abin ta,Wasa kike dashi ya lalace ko Kuma me?"
"A'a na d'auka ne kawaii sai ya daina aiki, na rasa me yake damin hannu na duk abinda na tab'a sai ya lalace"
"Kiyi hakuri ki daina kuka, bazan bari wannan yasa mummy ta tsane ki ba"
"A'a Aunty ya Isa haka ya kamata mummy tasan nice Wacce nake lalata Mata abubuwa ba ke ba"
"Kar kiyi hakan kinji yanzu tashi Muje mu karya" nan ta riko hannun ta suka Fara cin abinci bai dad'e ba Baraka ta sauko ita ma ta Fara cin nata abincin tana cikin cine wayar ta ta Shiga ringing cigin girmamawa da kaskantar da Kai ta amsa da "assalamualaikum Sir" ta d'an yi Tace "Okay sir yanzun Nan zan Zo na Riga nayi wanka Kaya kawaii zan sa"
Sai ta katse.
Safiya kirjinta ne ke dukan uku uku don tasan dole mummyn ta zata yi amfani da agogon, cikin sanyin murya Tace "Mummy Ina Zaki je?"
"Gun aiki ana nema na urgently"
"Ha'aah I thought ba Kya zuwa ranar juma'a?"
"Eh ta kamane,Bari naje na shirya" ta shafa Kan safiya said ta haura sama cikin sauri.
Safiya ta kalli asiya tace "yau kashi na ya bushe"
"Kar ki damu ki ci abinci"
Bayan sun gama ci suka koma d'akin Asiyah.
B'angaren Baraka ta gama Shirin tsaf ta d'auko a gogon Nan zata sa sai ta ga bayayi a fili Tace "Me kuma ya faru da agogon Nan"
Rai a 'bace ta Fara Kiran sunan "Asiyah, Safiya ina yaran Nan suke?idan na biye musu zasu haukatani"
Cikin zafin nama ta Shiga d'akin a Tsawace Tace "acikin ku Wace ce ta tab'a min agogona"
Safiya tayi saurin cewa "Nice "
Asiyah Tace "Safiya ki daina karb'an laifin da ba naki ba mummy nice"
Wata mahaukaciyar mari tayi wa Asiyah had'e da fad'in sau nawa nake ce Miki ki daina kirana da mummy Ni ban haifi mayya ba" Asiyah Marin da ta Mata ya gigita ta har sai da ta Fad'i a Kan gado, Baraka ganin hakan ta hau Ruwan cikin ta sai aikin dukan ta take, Safiya Kuma na kokarin riko ta.
Sai da ta yi Mai isarta ta fice daga d'akin, tana fita ta d'auko makullin mota, Mai gadi na gani a zaune hannun sa rike da wayar sa Yana kallon film Wanda na kasa gane wane iri ne lashe la'b'ban sa yake had'e da rike wandon sa sai lumshe Ido t
Yake.
Baraka Tace "Audu d'ako min jakar Nan da ake sa petir Kuma ka bud'e min gate" sai ta shige mota ganin bai taso ba hakan yasa tazo ta bayan sa ta leka Ashe film d'in basa yake kallon kad'a Kai tayi had'e da ciza Baki wata muguwar rankwashi ta Masa yayi saurin mikewa had'e da tare gaban sa, Tace "Wawa soko a Haka zaka Kare kana kallon blue film, jibi yanda Wando ka ya jike, da wata akwalar chaina phone ka d'ako jarkan Nan kasa min a mota"
Sai hakuri yake ta Bata,yayi saurin d'auko jarkan yasa a bayan mortar sannan ya Koma ya bud'e gate d'in,saita fice.
Safiya kuka take sosai tana bawa Asiyah hakuri Amma Asiyah ta nuna Mata hakan ba komai bace.
Audu na gani da Altine a Kan gado Yana zaune daga shi sai gajeren Wando ita Kuma zani kawaii ta d'aura a kirjinta Jin nayi tace "Yau ta bazan baka ba, sabida ban yarda da Kai ba nasan ba Sona kake ba"
Langwab'e Kai yayi yace "Kar kimin haka wallahi ina sonki"
'daga kafad'a tayi Tace "ita Kuma Mai ayabar Nan da kullum sai tazo gunka in fatan ba sonta kake ba?"
"Haba my altine,Ina dake me