"A'a adda Fadi, bazan yarda kina dukan mun ya ba. Ina yi aure, zan zata fara samun saida, saboda yau tana nan, gobe tana can, dan haka ki rike amana kafun lokacin".
"Toh Abdul".
"Yauwa". Sai ya kalli Afra, ya ce ki tafi daki zanyi magana da Mummyn ki".
"Toh Uncle, amma baka kawo mun choclate da bobo ba yau". Ta fada kaman zata yi kuka.
"A'a, kar ki sa hankali na ya tashi, kafun in wuce, zan siya maki".
"Owk Uncle, mi yatti". Tana fadan haka, ta wuce daki.
"Kaga ma ko tayin ruwa ban maka ba". Adda Fadila ta fada.
"Toh ai nayi zaton baza'a bani ba".
"Ai ban isa ba, bari in kawo maka drink, ko ruwa zalla kake so"?
"Toh kaji jikar Dajjo, ki kawo mun duka biyu. kuma na san baza'a rasa small chops ba, ahado mun, dan nasan ina gama magana, zan bukace su".
"Shikenan an gama my brother." Ta tashi, zata bar wajan, dan ta ya rike mata kafa.
Kai! Irfan, kar ka fadar dani fa, kaje wajjan addan ka, nima ka bari nayi attending to my brother".
"Wannan dan ki mai ido kaman mage zai bar ki ne?
"Kai bro, ka daina zagin heartbeat fa". Ta fada, sai ta duki Irfan, ta tafi kitchen da shi a hannu.
"Ni kam na ga ikon God yau, naga yanda zaki kawo mun abubuwan nan da shi ahannun ki". Ya fada.
Daya bayan daya ta kawo mai drink, da snacks ta sa mai agaba. Data gama jera mai komai, ta zauna akan kujeran da ke opposite da Abdallah, ta sa Irfan akan kafan ta.
"Toh me kake son fada mun"? Ta tambaye shi tana daga mai gira.
Sanda ya numfasa, sannan ya ce "Daman akan Kawu zanyi. Gaskiya abunda yake ma Abba mu ba kyau kwata kwata, ya bi ya raina mana iyaye". Abdallah ya fada ran sa a bace.
"Hmm bari kawai brother, abun na kona mun rai sosai wallahi". Ta fada, ta dafa goshin, tana jijjiga kai.
"Wallahi fa, yana bata mun rai. Kin san abun da ya ma Abba mu ne jiya"?
"Sai ka fada. Amma kuma kardai wani rashin mutuncin ya masa, kasan meeting ya kusa, yana neman abun da zai yi disgracing din iyayen mu ne". Adda Fadila ta fada.
"Ai kuwa, saboda su samu abun fada ba. Yace ma Abba wai yaushe zanyi aure, Abba yace lokaci ne baiyi ba, ya hau Abba da fada, wai baga yara a family ba, mai ya sa bazan zaba daya daga cikin su ba. Kuma to be frank, keh ma kin san basu game ni ba ko kadan. Abba yace bai sani ba, sai yace wai Abba bai bamu tarbiya ba, dukan mu da salon mu muke zuwa,maganganu dai na rainin hankali. Wallahi Fadi, sai kin ga yanda Abba yake magana, zaki san ransa ya baci sosai ba ka dan ba. Daya fada mana ma, keh ma dai kin san Umma, ta fara magana, nan suka ce mun wai I shouldn't be in a hurry, Allah zai bani in lokaci na yayi, kuma ba dole sai bafulatana ba, ko bahaushiya ce, zan aure ta, kuma ko kawu ya ce shi bazai yarda a mai taro agida ba, toh a zo gidan mu ayi". Yanda Abdallah ya ke magana, kasan ransa ya baci sosai.
Ita kuma Adda Fadila mai saurin kuka, har idanuwan ta sun kada. Sai ta kira Afra, ta bata Irfan, su ta fi daki tare, kafun ta yi magana. "Wai ni ya zamu yi ne mu karban ma iyayen mu yancin su a cikin family, ae mun yarda Abban mu is not flowing in dollars, amma bai taba zuwa gidan ko wannan su roko ba, amma sun bi sun raina shi saboda wannan azalimin da yake babban gidan Yero Family. Shifa in bai ga kana flowing in naira's ba, toh fa kai ba kowa bane, kuma rainin hankali kala kala zai dinga ma. Wallahi ko ni am in support, Allah ya baka bahaushiya, alokacin zai san bawai Abban mu bai san abun da yake yi bane, kawai barin sa yake. Amma kasan abun mamaki brother, suna mugun son hamma Sudais, adda Bilkisu da adda Wasila. Kasan shi hamma, duk da cewa baya biye mai, amma ya auri yar family. Ita kuma adda Bilkisu, saboda abubuwan da take basu, inta dawo daga dubai, in suka zo hutu. Ita kuma Adda Wasila, saboda mijin ta akwai kudi, kuma tana masu kyauta, sannan sun maida ta money making machine, suna washe mata baki anyhow, suna wani bata girman karya, ita kuma abubuwan na ruda ta". Ta fada, kaman zatayi hawaye.
"Toh ai shi ne, wallahi adda Wasila na bani mamaki sosai. In fada maki, yanzu dai daga gidan ta nake". Abdallah ya fada.
Nan ya kwashe mata komai, ya fada mata.
Adda Fadila bata san lokacin data fara kuka ba, ta ce "wani wata irin zuciya gare ta, adinga raina maki iyaye, amma ki ce su din kike so".
"Ki daina kuka adda'am, komai mai wucewa ne, kuma In Sha Allahu, sai na karban ma iyayen mu yancin su. Kar ki damu kin ji masoyiyar auta, mai ji da shi, amarya a gidan Sadiq, Mummy Rukayya da Irfan, yar gaban goshin Goggo Khadija". Abdallah ya fada yana murmushi.
Sai ta goge hawayen, kalaman, su kwantar mata da hankali. Duk da cewa shi ke bin ta, basu wani fadan nan na masu bin juna, instead, suna nuna ma juna soyayya ne sosai, basu taba son ganin bacin ran wani daga cikin su. Har yan'biyu ake kiran su, saoda shekara daya Fadila ta girme shi dashi, ga kaman da suke, kaman identical twins.
"Kin san me adda Fadi"?
"Sai ka fada autan mu".
"Auran Farouq fa saura sati biyu".
"Sati biyu?
Ba bayan yarinyar ta gama first semester dinnan za'a yi ba"? Ta tambaya surprisely.
"Ae, amma wai sunce ayi in two weeks time, kuma kaman za'a mata transfer ne ta dawo nan".
"Hmmm, toh Allah ya kai mu, kace kana da zuwa journey kenan, ga shi kai ne babban abokin ango, sai kai ma ka bude ido ka neman mana wata a kano, amma fa banda yar bleaching, duk da nasan kowani gari akwai masu yi, amma na kanawa is just too extraordinary".
"In Sha Allahu, kar ki damu". Abdallah ya fada.
Suka fara wani sabon hira kuma, bayan sallan Asr, ya bar gidan, ya koma gida. Nan ya sami Abba da Umma, suna hira, yayi complain din gajiya, Umma ta yi mitan ta, Abba kuma yayi supporting din sa. Yayi route din sa, sannan lokacin barci yayi, yayi barci.
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
"Madam ki tashi, an mana fixing din lectures fa". Nafisa ta fada tana tada Olamide.
"Keh! Wani irin lectures kuma, ba ana registration ba har yanzu"?
"Ae anayi, amma ai this is not the first week, third week fa kenan ". Nafisa ta amsa.
"Toh sai me, ni ki kyale ni, barci nake ji". Olamide ta fada.
"Okay in kyale ki ba, salon in kika tashi ki mun masifa ba, ai baki isa ba, you must wake up". Nan Nafisa ta ita jijjiga ta, tana "wake up sleepy head, wake up sleepy".
"Ohhhhh, keh fa habibty, disturbance din ki na iya sa sabon ciki zubewa haba". Olamide ta fada.
"Oho, ko tsofon ciki ne, ni dai ki tashi, by 11 mu ke da lectures din zuwa 1". Nafisa ta fada, still tana jijjiga ta.
"Mo daran(na shiga uku)! Dan Allah ki kyale ni. Me ta ma yanzu?
Indai 9:30 bai yi ba, toh ki bari inyi barci har 9:30, I promise kina tada ni zan tashi". Olamide ta fada.
"Yanzu dai it's 8:15. Kinyi promising, kar kiyi breaking din shi, ina tashin ki, ki tashi". Nafisa ta fada seriously.
"Ba wanka na da shiryawa ne kike tsoro ba, ai na chanza yanzu, bana bata lokaci kuma". Olamide ta fada.
"Allah yasa. Bari in bar ki kiyi barci ko habibtyn Fisa"?
"Yauwa habibtyn Fai'za". Olamide ta fada.
9:30 dot Nafisa ta tada Olamide. "Ki tashi, it' 9:30 now".
Da'a zata yi masifa, sai ta tuna ita tayi alkawarin zata tashi alokacin. Olamide ta tashi, ta shiga toilet, tayi wanka, sannan ta dawo ta shafa mai, ta sa wani red colour satin, mai belt. Data sa kayan, ta daura belt.
"MashaAllah, babibty, yau kam na yarda kin chanza. Within 30mins har kin shirya, keda almost 1 hour kina shiri. And yes, nima irin wannan zan sa". Nafisa ta fada tana tura baki.
"Kina wani tura baki, ba ni ya kamata ayi ma shagwaba ba. Ki sa mana, wani kaya zaki sa da'a. Kema kin san indai we both have the dress, we wear them on the same day". Olamide ta fara ana demonstrating da hannun ta.
"Yauwa kin ga wanka kawai nayi, na kara sa night wear, bari in sa nima". Nafisa ta fada.
Sharp sharp, sun gama shiri, suka shafa powder, da lip gloss a lebe, sannan suka dauki Black hijabs, suka saka, suka sa black flat shoes, sai suka dauki red side bags, suka yi slinging din shi a shoulders din su. Suna gama shiri, suka fito, nan suka hadu da su Hafsat da Halima, su ma zasu shiga school, suka tafi tare.
Suna sauka a adaidaita, suka raba hanya da su Halima, dan su sun zo ida registration din su ne, su kuma suka wuce inda zasu yi lectures.
Suna zaune, wata black beauty, ta shigo, taje inda suke zaune, tayi taping din shoulder din Olamide.
"Ore'mi(kawata) yarinyar ta fada.
"Hahhhhh, ashe kin zama bayarbiya bamu sani ba". Nafisa dake ta ciki ta amsa, saboda Olamide ke ta baki, shi yasa tayi taping din ta.
"Su Bila beauty, an shigo yau". Olamide ta fada.
"Ni dai ku masa mun in zauna, kafun ku tsare ni da surutu, kar adinga kallo na". Nabila ta fada.
"Awww, bari in matsa, kema habibty sai ki matso ko"? Nafisa ta fada.
"Butan kashi, wato ni in zauna a tsakiya, akan wannan karfe, toh naki". Olamide ta fada.
"Kai Ore, kin san fa ke ce siririyar cikin mu, kuma ai karfen baya tokarin mutum". Nabila ta fada.
"A'a, naki, ban ki in zauna ata baki bakin nan ba, amma naki in zauna aciki". Olamide ta fada tana wani murda baki.
"Toh yana iya dake, matsa mun in shiga". Nabila ta fada.
Olamide ta tashi, Nabila ta samu ta shiga, sannan Olamide ta zauna a baki bakin. Da suka gama balance, Nabila tace "daman ina son mu hadu ne, kafun in maku wata magana, saboda zan so ace muna tare, shi yasa ban fada maku ta waya ba". Nabila ta fada.
"Toh muna sauraro ko habibtyn Fisa"? Nafisa ta tambaya.
"Ae habibtyn Fai'za".
"Toh daman kun san biki na, is suppose to be done after this semester is finished, amma Baffan mu, yace wai ayi yanzu, that is two weeks to come, kuma iyayen yaya Farouq sun yarda". Nafisa ta fada ta na rufe fuska, wai ita nan mai kunya.
" Ashe abun ya matso, ina ankon"? Nafisa ta tambaya.
"Kai habibty, ai ba maganan anko zaki fara mata ba, ai kya ce Allah ya sanya alheri tukun. Yauwa Bila, don't be shy. Amma ina da tambaya. Toh in kika yi auren, ya batun school, ko zaki bar mu kenan"?
"A'a, zan cigaba anan, kin san cousin dina ne, so anyi magana da iyayen sa, ance inayi kaman two weeks acan, sai indwo. Amma zan dinga zuwa once in a while. Ga shi kinsan asalin mu yan gombe ne, so zan hadu da familyn mu da yawa". Nabila ta fada tana murmushi.
"Toh amarya Farouq bada kan ki asare". Nafisa ta fada.
"Toh ai ta riga ta bada. Am soooo happy ore, at least zamu cigaba da haduwa da Bilan mu aunty Bils". Olamide ta fada. Itako Nabila, sai ta rufe fuskar ta da hannun ta.
"Am soooo happy for you oren mu, Allah ya sanya alheri, ya kawo zuriya daiyiban. Allah sa kyawawan maza su zo, inyi wuf da daya". Nafisa ta fada.
"Amin ya rab". Nabila ta amsa.
"Amma ni habibty, me ke damun ki ne, yanzu baki da kunya"? Olamide ta fada.
"Toh me ke ciki, ni kam ki tsaya awajan, zaki ga nayi wuf da wani, ke kina nan ". Nafisa ta fada.
"Ai kuwa, babban abokin yaya, handsome ne sosai, kin gan shi ne, gashi shima doctor ne".
"Wow mashaAllah, kice dai in fara shiri, because am ready to do za wuf with him". Nafisa ta fada.
"Gaskiya kam ki shirya, sai kuyi wuf da juna. Ke Olamide ba zaki yi wuf da wani ba, ina fa da handsome cousins". Nabila ta fada.
"Wa zai yi wuf da yar yarbawa, sai dai kuyi wuf da juna, nima in jira yoruba prince dina yayi wuf da ni". Olamide ta fada.
"Kai habibty, ni kam in kika koma gida, ki tambayi Mummy, hanya ba karere kuke ba, saboda kina kama da fulani tooo much. Kuma me ke ciki in kika auri bafulatani, ai Allah ya halice mu duka". Nafisa ta fada
"Gaskiya kam, Allah created us all, kuma bai banbanta mu ba. Wallahi da muka fara haduwa da ke ko, I thought fa ke fulani ce, sai lokacin da kika fada mun yoruba name din ki, na yarda ke yoruba ce". Nabila ta fada.
"Haka ake cewa, amma nasan I claim Niger state kawai, because that's where we know, ba mu ma san hanyar garin yarbawa ba". Olamide ta fada.
"Toh it's maybe possible maybe garin yarbawan ma kunje ne. Saboda duk wayanda kike nuna mana as family, suna kama da fulani ne, especially cousin din ki din nan, aunty Hasinah". Nafisa ta fada.
"Oho, mu kam abun da aka fada mana zamu yarda da shi".Olamide ta fada.
Aiko tana rufe baki, lecturan su ya shigo.
Ana gama lectures, suk fita. "Yauwa my ore's, yaushe zaku fitar anko ne, kun san kune manyan kawaye fa". Nabila ta fada.
"Ko gobe ko jibi". Nafisa ta fada tana kallon Olamide.
"Ae hakan yayi. Kuma mu sanar ma yan dept din mu, da kawayan mu". Olamide ta amsa
"Toh mashaAllah. Ba zaku zo gaida hajiyar ku bane". Nabila ta tambaya.
"Ai gaisuwa ya zama dole, ala ma mu biki yau ko habibtyn Fai'za". Olamide ta tambayi Nafisa.
"Hakan ma yayi". Nafisa ta amsa.
*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*
*T.W.A*
*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_
MARUBUCIYAR
*-RAYUWAR HUSNA*
*-MAHAKURCI MAWADACI (2020)*
```Dedicating this chapter to my jikoki, Fatima and Ayusha (Jiks 1 and 2)🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭. Your comments make my day.```
1️⃣1️⃣&1️⃣2️⃣
_Bismillah_
Suka fita daga school premises, suka nemi kekeh da zai kai su anguwan su Nabila.
Da aka sauka su awani dan madaidaicin gida, amma fa gidan akwai kyau sosai, tun daga wajan gidan har ciki, akayi decorating din shi da flowers, so flowers din sun fito da kyaun gidan sosai.
Nabila ta kwankwasa kofar, aka mude masu.
"Sannu baba" suka fada a tare.
"Yauwa sannun ku, kunzo lafiya"? Ya tambayi su Olamide.
"Lafiya kalau". Nafisa da Olamide suka amsa.
Cikin wani kofa suka shiga, nan suka cire takallaman su, sannan suka shiga parlor da sallama.
Suna shiga, suka samu mahaifiyar Nabila, kanwar ta Safina da yayan ta Faeeq.
Da sallam suka shiga, Hajiya Hajara na ganin su, ta ce "sannu ku da zuwa my daughters".
A kunyance suka tsuguna a gaban Hajiya, suka gaishe ta. Ita kuma Safina, ta rungume su, ta ce "nayi zaton ko ba zaku zo kuga autar Hajiya bane".
"Mun isa"? Nafisa ta tambaya.
"A'a bamu isa ba" Olamide ta fada.
"Toh ni baza ku gaishe ni bane?
Especially wannan bayarbiyar". Yaya Faeeq ya fada.
"Ina wuni yaya Faeeq. Ni dai na gaishe ka, saura yoruba princess din ka".
"Tab!! Allah ya kiyaye".Olamide da Yaya Faeeq suka fada tare
"Ni kam Faeeq ka bar mun ya'a fa. Zo ki zauna kusa dani yar'lele ta". Hajjiya ta fada. Da sauri Olamide taje ta zauna kusa da ita.
"Ni wallahi Ummi shiyasa bana son zuwa gidannan in yaya Faeeq na nan". Ta fada a shagwabe.
"Ki kyale shi. Ni nasan yana son ki ne, kuma bazan bashi ke ba". Hajiya ta fada tana murmushi.
Duk yanda yaya Faeeq yake da keyi da Olamide, dukan su ke noticing. Abun kadan sai yayi maganan ta, ko tana nan ko bata nan. Ga shi yanayi da yake mata magana ma ya bayyana.
"Allah ya kiyaye, me zanyi da ita". Yaya Faeeq ya fada.
"Nima Allah tsare ni nayi soyayya da kai". Olamide ta fada tana hararrar sa.
"Ki shiga hankalin ki dani, ki bar ganin ke ba muharama ta bace, zan dake ki ne black and blue". Ya fada yana ya making serious face.
"Kai!! Wani baku gajiya ne?
Kullum ku dinga fada kaman cat and dog. Yaya Faeeq mun san kana son Olamide ne, ba sai kamana corner corner ba. So ka fada mata kawai,