binu (a'a kiyi hakuri), ba zamu kara ba" Farida ta fadi.
"Ni kam zan cigaba". Hakeem ya fada yana dariya.
Abun ya bata mata rai sosai, sai ta ja tsaki ta bar wajan. Tana tashi, Farida da Mummy suka kalli Hakeem, Farida ta ce "shikenan ka ja mana wani masifan, kai baka san aunty Mide sai da rarrashi ba, ga shi ban dau nyt wear dina ba" ta fada kaman zatayi kuka.
"Ni kam Farida ki daina damun mu da maganan night wear, ba zaki rasa adaki na ba. Kai kuma Hakeem, ka san yanda zaka lallabi yayar ka, ta daina fushi, dan kai kaja komai".
Ya ce "toh" yana wani hura hanci.
"Amma Mummy kin san ba zata saurare ni ba yau, sai dai gobe in Allah ya kai mu".
"Allah ya kaimu". Mummy ta fada.
"Amin" Hakeem da Farida suka amsa.
Aranan, ran Olamide abace tayi barci.
```Ya kuka ga wanan salon?
Allah yasa dai kunji dadin shi.```
Thanks for reading, karku manta da sharhi, saboda sharhi is life🤪🤪🤪🤪🤪.
*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*
*T.W.A*
*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_
MARUBUCIYAR
*-RAYUWAR HUSNA*
- *MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_
3️⃣&4️⃣
```Dedicating this page to those who commented on the first chap, I love you guys loooooooooooods.```
_Bismillah_
Around 3:30 am na dare ya tashi, yayi sallan dare, yana yi har lokacin Fajr yayi, ya yi raka'a taini fajr, sanan ya fito parlor, suka hada hanya da Abba, suka je masjid.
Da suka dawo kuma, tunda yana da dutyn safe, ya fara shirye shirye.
"Ya ilahi, gaskiya I need a wife. Da ina da mata, duk wannan shirye shiryen ita zata mun. Kawai sai dai inji tana tashi na, ta ce qalbi ka tashi kayi wanka, ta cire mun kayan da zan sa, ta sa mun coat dina da briefcase di na waje daya, ta ciro mun covered shoe dina, shima ta sa mun a one side. Ina fita kuma ta mika mun ina sawa, in ta gama dressing dina, sai tace qalbi muje dinning ka ci breakfast. Ba kaman Umma ba, da zata dinga mu fada. In kuma na gama cikin breakfast, sai ta rike mun briefcase, ta raka ni har mota, sannan ka fun in shiga, tayi hugging dina, sai in shiga mota, ta mika mun briefcase, ni kuma in diga mata flying kisses, sannan in kuna mota, ita kuma ta dinga waving dina har in bar haraban gidan mu". Ya fadi ya na wani irin smile.
"Amma gashi yanzu ni ke komai. Da ma lokacin da adda Fadi take nan ne, maybe data mun. Duk da cewa muna fada sosai, dan ita nake bi, still na san zata mun". Ya fada with frustration.
Haka ya ita surutun shi shi kadai, har ya gama shiri, ya fita ya je dinning, ya ga ba kowa. Tun dama da kyar suyi breakfast tare inba weekend ba, ko kuma ran da yake da dutyn rana. Rai abace, ya shiga kitchen. Yana son ya fara girka indomie, yaga note akan kula. " ka ci, ba dan halin ka ba". Yana ganin handwriting din, ya san na Umma ne. Sai ya saki murmushi, ya dauki abincin, ya kai dinning, ya ci. Sanda ya koshi kafun ya kwashe kwanonin, ya kai kitchen. Daya gama kintsa komai, ya je dakin Umma, ya mata sallama, ta mai adawo lafiya, da addu'oi, ya je dakin Abba, shi ma ya mai, sannan ya fita, ya kama hanyar asibiti.
Yana driving yana bin kira'an sheik Abdulrahman Sudais, sai kawai ya fara addu'an Allah ya ba shi mata, shi ya fara gajiya da irin rayuwar nan, shima yana son yayi kyau kaman Hamma Sudais. Haka ya ita tunani har ya isa asibiti.
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
Around 4:00 Am, Mide ta tashi, daman ita kadai ta kwana, Farida ta kwana da Mummy ne, dan data shiga daki, data sha masifan da bazata taba mantawa da shi ba .
Da Mide ta tashi, ta shiga toilet tayi business din ta, sannan ta yi alwala, ta fito ta fara nafls. Da lokacin raka'a taini fajr yayi, tayi, sannan tayi sallan fajr. Tana idarwa, ta fara karatun alqur'ani, tayi azkar din safe, da wasu addu'oi, sannan ta ninke sallayan, tasa a mazaunin sa, kafun ta fita taje dakin Mummy. Ta shiga da sallama, Mummy da Farida suka amsa. Data shiga, ta tsuguna, ta gaida Mummy, Mummy ta amsa, ta sa mata albarka. Sai Farida ta ce "aunty mi (aunty na), e dakun(please) ki yi hakuri, bazan kara ba". Tayi magana kaman za tayi kuka.
Olamide ko tayi kaman ma bata san tana yi ba. Ta tashi zata fita, Mummy ta ce ta dawo. Cikin respect, ta dawo ta tsuguna gaban Mummy, dan daman Mummy da Farida na zaune ne akan sallaya, Farida na ma Mummy karatun ta da aka masu a islmiyya, ita kuma Mummy tana gyara mata.
Da Olamide ta tsuguna agaban Mummy, Mummy ta ce "wai ni wace irin zuciya gare ki?
Ba yafiya kwata kwata a zuciyar ki. Ya zaki kwana da mutum azuciyar ki, baki tsoron ki mutu, ko kuma shi wanda kika sa arai ya mutu?
Fisabilillah! Ai wannan ba hali bane, ko tun iwa re se (ki gyara halinki), kafun lokaci ya kure maki".
Ran ta abace, amma cikin sanyin murya ta ce "Mumny fa ni kadai kike ganin fault dina fa, baki ganin na su, barin ma Hakeem, kema dai kin ga abubuwan da yake mun, amma sai ki dinga cewa ni ke da fault". By this time, tana magana tana zubar da hawaye.
"Toh ai ke ce babba, ya za kiyi, dole ki dinga hakuri. Fushi fa ba abu mai kyau bane. Na san abubuwan da suke miki na bata miki rai, amma su fa a matsayin wasa suka duki komai".
"Toh ni bana son irin wasan. Kullum su ita tsokana na kaman kanwar su. Harda ke ma". Ta fada tana kallon Farida.
"Shekaru nawa kika san na girme ki da shi, shekaru hudu fa, amma in aka fara magana, ke kike leading. Gwanda ma Hakeem, age gap din mu ba yawa, amma ke fa. Ko shi din he has no right or what so ever to disrespect me".
Tana cikin magana, sai ga Hakeem ya shigo. Su na hada ido, ta dauke idon ta. Sanda ya gaida Mummy, sanan ya ce "Aunty ina kwana". Ta ki amsa mai. Ya kara cewa "na san na miki laifi, but I was only joking, wallahi wasa mu ke dake. Amma na ga kaman wasan mu na bata miki rai, saboda haka, ina mai baki hakuri, dan Allah kiyi hakuri, ki yafe mana".
Still tayi shuru, sai hawayen da ke zuba a idon ta. Abu kadan na sata kuka, she is always emotional.
"Haba Olami, ba zaki yafe masu ba, haba my first fruit, you were the first person who made me know how wonderful and exciting been a mother is. Ke ce first din komai na, dan Allah dari jin wan (dan Allah ki yafe masu)".
Cikin kuka, ta ce "na yafe maku, amma ku san irin wasan da zaku dinga yi da ni". Tana gama magana, ta tashi zata fita, Mummy tace ta dawo. Da ta dawo, Mummy ta ce da su, suyi group hug. Su kayi group hug dukan su, Mummy na sa masu albarka.
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
Yana isa asibiti, ya shiga office din sa, ya zauna. Kafun ku sani, har patients sun fara shigowa.
Ya na kiran next, wata budurwa ta shigo, yarinya akwai kyau ba laifi, gata fara. Tana shiga ta gan shi, ta fara gyara mayafin ta, tana gyara kayan ta. Shi ko ya riga ya gano ta, dan haka majority din yan'matan dake shigowa suke. Sai su dinga wani gyare gyare. Wasu ma har cewa suke, zasu iya samun numbern sa incase idan ciwon su ya kara tashi, sai su fada mai, it's either yayi kaman bai ji ba, yana next, wani ya shigo, su kuma su fita disappointed, ko kuma ya basu amsa rudely.
Daya ga gyare gyaren ta bai kare ba, ya ce "can you have a sit please, we still have other patients waiting out there".
Ta gyara murya, ta ce "uhmmm sorry". Sannan ta zauna.
"Toh me ke da mun ki"? Ya tambaye ta.
Ta fada mai abun da ke damun ta, ya rubuta mata magunnuna, ya bata. Ta fita kuma ya zama problem, ta ce "kaman na san ka ".
"Ya ce Allah ko"?
"Ae, dan na san ina ganin face dinnan sosai".
"Hanya kuwa, dan ni ban san ki ba".
" Okay, amma ka san Fadila Umar Muhammad yero"?
"Ae na san ta, ya akayi".
"Haba no wonder, kuna kama sosai. I think ina ganin hotunan ka awayan ta ne. Actually munyi BASUG(Bauchi state university) tare da ita ne, amma snr dita ce, dan tana level 4, ina 1, amma mun shaku sosai".
"Allah sarki, nagode".
"Uhmmmm na ce ba, kana iya bani numbern ka, kaga sai mu cigaba da zumunci ba".
"Numbern na ko na ta, dan naga ita kika sani".
"Na ka, ai ina da nata". Ta fada tana murmushi.
"Toh ai tunda kina da nata, alhamdulilah. Ita kika sani ba ni ba. Please here is the door. Next patient, ya fadi.
She was soo embarrassed, ta dau bag din ta, ta bar wajan.
Ba zata wuci 22 years ba, so ya girme ta.
Tana fita ya fashe da dariya, ya ce "ai ko mata sun kare, ba zan iya zaban ki ba. Na san mata ta na can itama ta kosa mu hadu. Ya Allah Kasa mu hadu very soon". Yana cikin addu'a, patient ya shigo. Bai bar asibiti ba, sai around 2:30 PM. Instead ya je gida, sai ya je gidan adda Wasila. Yana horning, aka bude mai gate. Mijin adda Wasila na da kudi sosai alhamdulilah. Ba ita ce first wife din sa ba, first wife din sa ta rasu, ta bar yayan ta uku, after shekaru hudu da rasuwan ta, ya auri adda Wasila yanzu shekarun su 8 da aure, yaran ta biyu, da Zaynab da Faiz. Su kuma yaran Mijin, da Jamila, Nana Hauwa, da Abdulazeem, amma suna kiran sa Azeem. Akwai zaman lafiya dosai, yaran na son ta sosai, dan bata babanta su da nata yaran ba, duk daya suke awajan ta.
Yana horn aka bude mai, gate, mai gadi na ganin shi, ya ce "a'a auta! Kai ne haka da ranan tsaka"?
"A'a bani bane, kai ne".
Yana fadan haka, shi da mai gadin, mai suna lawali, suka fashe da dariya.
"Kai auta baka gajiya da tsokana. Allah yayi dai yau ka zo Hajiya bata je wajan aiki ba yau".
"Ai na sani mallam, ba asibitin mu daya ba"?
"Awww haka ne fa". Lawali ya fada, yana sosa keya.
"Kar ka damu, in zan fita zamu hadu". Abdallah ya fada, ya je ya gyara parking. Shiko Lawali, sai washe baki yake.
Abdallah na sallama, yaran suka zo da gudu. "Oyoyo uncle! Oyoyo Uncle". Suke ta fada, suna hugging din sa one after the other. Bisa duka alamu dai yanzu suma suka dawo daga school.
Sai ya tambaye su Mummyn su, suka ce tana sama, yanzu muma muka shigo". Zaynab kenan, ta amsa.
"Toh Jebu, je ki fada mata best din ta ya zo".
Zaynab ta bata rai, ta ce "best din Ummi ko best din Zaynab".
"Toh best din Zaynab".
"Yauwa uncle auta". Tana fada ta bar wajan da sauri, kar ya buge mata baki.
"Zaki dawo ai yarinya". Ya fada.
"Me ka kawo mana". Nana Hauwa second born din gidan, shekarun ta 14, tana jss3 ta tambaya.
" Ku da kuka je school, bai kamata a kawo maku kayan dadi ba, kar yazo ya dagula maku lissafi".
"Kai! Uncle auta, ka iya zuki". Jamila babban cikin su, wanda shekarun ta 15 yanzu, kuma tana ss1 ta fada, ta bar wajan da sauri, dan ta san halin shi, yanzu zai bubbuga mata baki.
"Ai da ke da Zaynab, mai kwace ku sai Allah. Ni na maku kama da autan ku ne?
Wannan munmunan autan na ku" ya fada yana kallon Faiz.
"A'a kar ka bari mu fara, ka daina ce ma handsome dina ugly tohm". Adda Wasila ta fada.
"Ko dan gaisuwan nan babu, sai fada? Ko kema kin shiga group din su Umma ne"? Ya fada yana bata rai.
"Na isa?
Ai ban isa ba. Toh autan mu, ka zo lafiya? Ya aiki yau"?
Ya amsa mata, daga nan suka fara hira, suka ci abinci. Suna gama ci, suka kara taba hira. Suna cikin hira, ta ce "Abdallah!" yana jin yana yin yanda ta kira sunan shi, ya san akwai magana kenan.
"Na'am adda". Ya amsa.
"Yaushe zaka yi aure ne?
You are not getting any younger".
"Hmm adda kenan, zan yi, lokaci ne bai yi ba. Ko nima na kosa inyi, amma har yanzu ban samu wace ta mun ba". Ya fada.
"Kar ka tsaya ruwan ido, inba haka ba, ka kwaso nonsense. Kuma kana wani cewa baka samu kowa ba, yan'matan dake family fa?
Ga yaranan kyawawa, ga kyaun hali, amma kace baka samu ba"?
"Ba haka bane, I don't just have interest in them. Basu zauna mun a rai ba. Amma na san My wife na can tana jira na, lokacin haduwan mu ne kawai bai yi ba".
"Toh Allah yasa ahadu soon, inba haka ba, kawu Dajjo ya hada ka da wata acikin family".
"Ba amin ba, In Sha Allahu soon zamu hadu".
Bai bar gidan ba sai 5:PM.
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
"Toh goge hawayen ko". Mummy ta fadi.
Olamide ta goge hawayen ta, ta ce "Mummy ban san abun da yasa nake kuka haka ba, kuma bana iya controllimg din shi".
"Kya koya ai, in kika yi aure, zaki koya".
Olamide ta sa hannu agoshi, ta ce " Mummy abu kadan kice aure. Ni kam ba yanzu zanyi ba, kuma ma fa bani da ko mashin shini".
"Hmmm, bari in bar maku dakin". Hakeem ya fada.
"Nima haka". Faiza ta fada.
"Dawo nan munafs. Yanzu in kuka fita, ba abun da zaku yi in ba munaf ba". Olamide ta fadi
"Kul, ma ban be awon omo mi ni munafukai( kar ki kira mun yara na muna fukai)". Mummy ta fada.
"Toh alhaja Mummy". Olamide ta fada.
Ko wanan su ya fara morning duty din sa, da suka gama, suka ci breakfast, Farida ta je school, su kuma suka koma dakin su.
"Aunty Mide, ina son in danyi wani dan talk da ke" Farida ta fada.
"Ina ji, kuma ki fadi sensible thing, inba haka ba ki sha mari".
"Am serious fa". Ta fada tana making serious face.
"Toh am all ears darling Faree".
"Daman akwai wani ne, cousin din su Eyman, ya ce wai yana so na, baki gan shi ba, yana da kyau sosai fa". Farida ta fada.
"Zo, matso kusa". Olamide ta fada.
Farida ta matso kusa da ita. Sai Olamide ta taba wuyan ta, ta ce "gashi jikin ki bai yi zafi ba, toh me zan ce yana damun ki".
"Aunty fa am serious. Ai kin san Eyman, wanan kawa ta din nan yar Maid, kin san how much I love kanurai ai".
"Ki tashi anan kafun inyi ball da ke. Kina ss2, intsead ki dinga tunanin yanda zakiyi passing din third term exams din ki, kina tunanin na miji, ko ni nan banda saurayi, kuma ina 300l. Common ki tashi kije kiyi assignment dinki kafun inyi ball da ke".
Afusace, Farida ta ce "ko dan wanan halin na ki, ba zaki samu saurayi ba". Tana fada ta bar dakin.
Ita ko Olamide, maganan ya dame ta, maybe maganan Farida gaskiya ne, shi yasa haryanzu bata samu saurayi ba. Amma kuma to hell, ta san lokaci ne baiyi ba, dan in lokaci yayi, ko cikin rami aka sata, sai sun hadu da mijin ta".
Thanks for reading, ayi sharhi abeg, because sharhi na oxygen ooooohh🤭🤭🤭🤭🤭.
```Am dedicating this page to my washi Wasila, aka washi buje🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭. I love you wujiga wujiga``` 🤣🤣🤣
_Bismillah_
Abun ba wuya, yau Olamide ta koma school. Faridan data ce tama fi kosawa ta wuce, ita ta fara kuka, wai zata yi missing din ta. Kuka take sosai, har ta sa Mide ma kuka. Hakeem da Mummy ko sai kallon ikon Allah suke. Har gareji suka raka ta, nan ma sanda suka yi kuka. Daman ko man fada da argument din da zasu yi, basu iya rabuwa da juna, Farida da Mide na mugun son juna. Shima Hakeem, ya na son sisters din sa kaman ran sa. Ita kuma Mummy, kwanciyar hankalin ta bai wuci taga kan yayan ta a hade ba.