x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 15 - BANBANCIN KABILA

  • 42001 words
  • 45000 words
  • Out of 57901 words

Category: Love Stories

Views 245

25 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
office."Nabila ta fada.
Maganan ta ya basu dariya, sai Olamide tace "yayi mana highest in yaga bazai iya daurewa ba, ya shiga wani ward ya kwanta."
Duk suka kara fashewa da dariya. Da Nabila taga dariyan ba mai karewa bane, tace "toh ya ishe ku, ku daina ma heartbeat dina dariya."
"Oho dai mun dai yi." Nafisa ta fada tana mata gwalo.
Zata daki Nafisa da wasa kenan, Olamide tace "kuzo mu tafi inda za'ayi test fa, kar muzo muyi missing. Inya so ma in muka isa, sai ku ci gaba da dukan juna."



Da suka isa inda za'ayi test din, har an fara shiga, suma suka yi joining din queue, aka rarraba su, kuma ga two seats interval tsakanin dukan su.

Test din yayi hot sosai, duk wanda ya fito, sai yayi complain.
Nafisa ta fara fitowa, sai Nabila, Olamide ce last.
"Kai habibty, nayi zaton ba zaki fito ba". Nafisa ta fada.
"Ko ni, nayi zaton sai kinga karke pen din ki ne." Nabila ma ta fada.
"Ae din, koma meye." Olamide ta fada tana murguda masu baki.
"Kuga fa muje muyi sallah da wuri, saboda mu samu gaba a hall din da zamu yi wannan lectures din, kunga dai mutani dayawa sun zo test, haka za'ayi cunkoso a lectures ma yau." Nabila ta fada.
"Toh suka amsa mata."



Nasan maybe wasu are lost, basu gane me Nabila ta zo yi ba a wannan pejin.
Kaman yanda dai na fada a baya, cewa bayan bikin ta da two weeks zata dawo, domin ta ci gaba da karatu.



Da suka idar, suka nufa hanyan hall din lectures din su, suna tafiya cikin sauri. Luckily for them, sun samu space a gaba, saboda mutani basu fara shigowa ba sosai, suka samu wuri suka zauna su uku.






〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Da Abdallah ya isa asibiti, ya je yayi signing, sannan ya shiga office din sa, ya fara aiki, amma hankalin sa baya kwance, yana ta tunani kala kala, da kyar ya samu yayi aikin ranan.

Da suka yi closing, su uku (Abdallah, Farouq and Asim) suka hadu a karkashin wani bishiya, duk suka zauna a saman benci.
Sai Asim yace "Abdallah, yana ga yau din nan, kaman hankalin ka a tashe yake?"
"Gaskiya I noticed that too. I hope dai ba akan Olamide bane?" Farouq ya tambaya.
"Ni kam, tun daka hadu da ita, yau kana dariya, gobe kuma hankali a tashe." Asim ya fada worried.
"Ba zaku gane ba wallahi. Ni kadai na san yanda nake son ta, ni kadai na san yanda soyayyan ta ya gama mamaye zuciya na, wallahi ina son ta fiye da yanda kuke misali, ina son ta, ina son ta, ina son ta." Abdallah ya fada.
"Then what is the problem?" Asim ya tambaye shi.
"Exactly, meye matsalan?" Farouq ma ya tambaya.
Sanda Abdallah ya numfasa, ya ce "matsalan shi ne ban san yanda zan yi confronting din su Abba ba da wannan maganan ba, sannan ina tsoron amsan su. Wallahi ina ji a jiki na kaman ba zasu yarda ba, ina ji kaman zasu raba ni da masoyiya ta, kuma in aka yi haka, ba karamin cutar dani aka yi ba, dan koma wa zan zo in aura, indai ba ita ba, sai dai muyi auren, ba dan naso ba." Abdallah ya fada, idanuwan sa sun yi ja'a. Da mace ne, data yi kuka, amma tunda namiji ne, yana ta kokarin dannewa, saboda shi kadai yasan abun da yake ji.
"Hmmmm this is serious. Amma baka ce mana adda zee da hamma Sudais ma sun yi accepting din relationship din ku ba, then itama mahaifiyar ta ma tayi accepting, sannan kuna communicating da kanin ta, toh ai kunyi mai wuyan, am pretty sure su abba ma baza su zama problem ba In Sha Allah, ka daina damun kan ka please." Farouq ya fada.
"Yes please, ka kwantar da hankalin ka, Olamide taka ce In Sha Allahu, yanda Nafisa ma tawa ce da yardan Allah." Asim ya fada yana murmushi.
"Na gode maku sosai, Allah ya bar mu tare. Amma kun san me, ko ita ma hankalin ta a tashe yake, wai tana tsoro, and have been trying to make her cool her mind down. Kuma In Sha Allahu ran Saturday ko sunday nake son nida su hamma Sudais da adda Fadila mu fada masu, ku taya mu da addu'a, Allah yasa su yarda.
"Amin kar ka damu, In Sha Allahu zasu yarda. Kuma ka cigaba da kwantar mata da hankali ita ma." Farouq ya fada.
"Zamu taya ka da addu'a, your love will win In Sha Allah, and it will be an eye opener to other parents with this character, su abba zasu sa other parents su yi realising cewa tribe is not a fault in marriage In Sha Allah, now cheer up young man." Asim ya fada.
"Na gode maku, Allah ya bar mu tare." Abdallah ya fada.
"Amin suka amsa mai."





〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️


Da su Olamide suka tashi, driver din gidan su Nabila ya zo daukan su, ya sauke su Nafisa har gida, sannan ya wuce da Nabila gida.
Su Olamide sun mugun gaji, duk abun da suke, a gajiye suke yin shi.






```Thanks for reading.```



Comment
Like &
Share.



~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹
*BANBANCIN KABILA*
_(Short story)_
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹

*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*

*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

*-RAYUWAR HUSNA*

*-MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_






3️⃣5️⃣&3️⃣6️⃣





_Bismillah_






"Na samu wace nake so." Abdallah ya fada, kan sa a kasa.
"MashaAllah, shi ne sai ka wani kira yayyin ka?" Umma ta fada.
"Toh ai shi ne, I don't see the need for this." Abba ya fada.
"There is need for it." Abdallah ya kara fada.
"Then what is it." Abba ya tambaye shi.
"Gaskiya dai yarinyan na da hankali, ga kamun kai, ga addini, she is very loving. Ai sun hadu da adda Fadila lokacin bikin Farouq, kuma she can testify to her character." Abdallah ya fada.
"Yes I can, tana da hankali sosai wallahi, data zo gida na, kaman na hadiye ta, she is so loving." Adda Fadi ta fada.
"I don't still see the need for you guys coming here." Abba ya fada.
"Kai! Abba kai dai be patient. Amma dan Allah zan so ku duba alamarin nan da kyau kafun ku bada amsa." Hamma Sudais ya fada.
"Toh muna sauraron ku." Umma ta fada.
"Toh da farko dai ba a Gombe take ba, kuma, kuma, kuma."
"Kuma me?" Umma ta tambaya.
"Uhmm bayarbiya ce, amma tashin arewa." Abdallah ya fada kan sa akasa.
Ai umma da abba, sun ji maganan ne kaman saukan aradu. Ji suka yi kaman an zuba masu ruwan sanyi, sai kallon Abdallah suke.

Da Abdallah ya ji shuru yayi yawa, sai ya kalli yayin sa pleadingly, su ma su sa mai baki.

"Abba yana ji kun yi shuru ne, gaskiya according to what the both of them told me, tana da hankali sosai, gashi ma dana ga hoton ta, I thought ma Fulani ce, ba zaku ma san bayarbiya bace." Hamma Sudais ya fada.
"Umma! Abba! Dan Allah say something, am sure zaku so ta, tana da hankali sosai wallahi, she is every sister's dream for her brother, and she is also a gem every house hold wants." Adda Fadi ta fada.
"Me kuke son mu fada, ai wannan maganan ya fi karfin mu. So kuke a dinga zagin mu cikin family kullum, ku kenan burin ku a dinga zagin abban ku ako wani family meeting?" Umma ta fada.
"A'a, kwanciyan hankalin ku nake nema, kuma kullum ina cikin neman yanda zan faranta maku rai." Abdallah ya fada.
"Kana son ka faranta mana shi ne kake son ka kawo mana yarinya marasa dabi'a cikin gida, shi ne ka ke neman yanda zaka zubar ma mahaifin ka dan sauran mutuncin shi da familyn ku suke gani, kana son faranta mana, shi ne kake neman sa mana hawan jini?
Toh ka sani ba'a gidan nan ba." Umma ta fada ta tashi daga inda take zaune, shi ma abba ya tashi, domin shi yama rasa abun da zai ce.

Su Abdallah na ganin iyayen su sun tashi, suma suka taso da gudu. Abdallah da hamma Sudais suka je wajan abba, ita kuma adda Fadi, ta je wajan umma.
"DanAllah abba kayi magana, wallahi ina son ta, kuma tana so na, gashi tana da hankali, kuma tana da tabi'a mai kyau. Ku bata chance, zaku ji dadin ta." Abdallah ya fada.

"Wallahi umma tana da dabi'a. Ki bar ganin bayarbiya ce, tama fi wasu fulanin hankali. Wallahi umma zaki ji dadin ta, dan Allah ku ba soyayyan su chance dan Allah." Adda fadi ta fada. Da umma ta wani harare ta, ta cire hannayen ta a jikin ta, ta ce "in kika gama, ki wuce gida, ki gaida mun namesake dina da Irfan." Umma na gama magana, ta wuce dakin ta.

Shima abba, duk rokon da su Abdallah suke yi, sai shiga ya ke ta kunne dama, yana fita a na hagu, dan daman sun rike shi ne, sai ya balla hannayen su, cikin sukuni ya bar wajan.

Zai bar parlorn kenan, Abdallah yace "kar ka manta, ku kuka ce kowa na samu, indai ta zauna mun, then you guys will support my decision." Abdallah ya fada idonuwan sa jazur.

Abba bai ma bashi amsa ba, ya bar parlorn, ya wuce daki.


Su Umma na barin dakin, Abdallah ya tsuguna kasa, yaji jiri na daukan shi, ya dafa kai. Su Hamma Sudais da Adda Fadila suka zo kansa da gudu.
"Common be a man, kayi hakauri ka basu time. Kasan basu taba ganin irin haka ba a family, kai ne na farko, so they have to think, kafun su iya baka amsa." Adda Fadila ta fada.
"Gaskiya kam, you should give them time, kaman yanda Fadila ta fada, ka kyale su for sometimes, In Sha Allahu everything will be alright, yanzu kam they are in shock." Hamma Sudais ya fada.

Suna cikin lallaban shi, wayar sa ya fara ringing. Da kyar ya iya ciro wayan daga aljihun sa, ya duba screen, yaga sunan Adda Zaynab ya fito.
Da kyar ya iya daga kiran. Muryar sa kaman zai yi kuka, ya ce "assalamu alaikum adda!"
Adda Fadila ta mai signal ya sa a speaker, sai ya sa.
"Waalaikumus salaam mijin Faiza, amma ya naji muryar ka haka."
Sanda Abdallah yayi nishi, sai yace " Adda am not good at all, nothing went well. Gwanda Umma ma tayi magana, tayi objecting. Amma kin ga abba, bai ce komai ba, he just stood up and left." Abdallah ya fada idanuwan sa cike da ruwa.
"Subhanallah! Ya za'ayi kenan?
Ina hamma da Fadila ma tukun?" Ta tambaya.
"Gamu." Su biyu suka amsa.
"Me kuke yi da baku sa baki ba." Adda Zaynab ta tambaya.
"Ban gane me muke ba, ke kin tambaye shi kuma yace maki bamu sa baki ba?" Hamma Sudais ya tambaye ta.
"Kayi hakuri Hamma, amma dai you all know it that I hate to see auta miserable, that why I said that. Amma toh yanzu ba abun da zamu iya yi ne?
Ko in masu magana ne?" Adda Zaynab ta fada disturbed.
"You should, ala in suka ga kema kin sa baki, maybe su yarda. Dan yanzu kam basu ma son su ga fuskokin mu, dan umma harta sallame ni." Adda fadi ta fada.
"You should also try your luck." Hamma ya fada, sai ya kalli Abdallah, yace " we are with you, everything will be alright In Sha Allah."
"Yes we are." Adda Zee da Adda fadi suka fada.
"Nagode maku sosai, Allah ya saka maku, ya raya zuriya, ya hada mu duka a jannah." Abdallah ya fada da jajjayen idanuwan sa.
"Amin amin autas." Suka fada.

"Toh auta, anjima zan masu magana, kaga by that time maybe sun sauko." Adda Zaynab ta fada.
"Toh. Allah yasa su ji naki." Abdallah ya fada.
"Amin" yayyin sa suka amsa, adda Zee kuma tayi hanging up.

Su Hamma Sudais sun kai 30mins, suna kwantar ma Abdallah hankali, da kyar suka samu ya daidaita.

Da suka wuce, shima ya koma daki, ya hau kan gado, ya jingina da pillow, sai tunanin Olamide ya fado mai. Me zai ce mata yanzu in suna waya?
Inma ya fada mata, hanya bai zai yi loosing din ta ba?

Haka ya ita tunani, har lokacin sallah yayi, yayi sallah acikin dakin shi.

Daya idar, yana cikin addu'a, wayar sa ya fara ringing. Ya duba wanda ke kira, sai ya ga sunan Olamide (my qalbi) boldly akan screen, nan ya fara jin heart din sa na beating, yama rasa mai zai yi, ya daga ne ko ya bari.





〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️



Sanda Nafisa ta bari bayan 30mins, sai taje kusa da Olamide akan katifan ta, Olamide na ganin ta, ta juya fuska. Yanzu kam tama daina tunanin yanda iyayen Abdallah zasu yi reacting, haushin Nafisa take kawai, saboda ita baza ta iya fada mata haka ba, ko suggesting din shi baza ta yi ba.
Da Nafisa taga ta juya kai, sai ta juyar mata da kai tana kallon ta, tace "Allah sarki habibty, wallahi I care for you, I care about everything about you, bana son ganin hawayen ki. Kuma na fadi hakan ne saboda I really care about you. Kuma indai kin saurare ni da kyau, toh bance kuyi breakup ba, cewa nayi da baki son shi yanda kike son shi haka, dana ce maki kuyi breakup."
"Toh naji ki, sai da safe." Olamide ta fada, ta juyar da fuskan ta zuwa dayan gefen.
"Haba habibtyn Fisa, I really care about you, shi yasa kika ga na fada haka. Wallahi na tsani inga kina cikin damuwa, balle azo ga kuka, amma ina mai baki hakuri, kiyi hakuri da wannan stupid friend din naki, bazan kara ba." Nafisa fada.
"Toh naji." Olamide ta fada.
"Baki ce kin hakura ba." Nafisa ta fada.
"Ban hakura ba." Olamide ta fada.
"Haba habibty na, wallahi I care about you, kin ga idan kika ci gaba da haka, education din ki ma zai yi slacking. Bana son situation din da zaki dinga slacking a komai." Nafisa ta fada.
"Toh naji na hakura, shikenan?" Olamide ta fada ta juya kai tana kallon ta.
"A'a, ina son ki hakuran gaske, ba irin wannan ba." Nafisa ta fada a shgwabe.
"Wani irin hakuri ne yafi wannan, har ina amsa maki, toh na hakura, amma I don't want to talk to you." Olamide ta fada, ta tashi ta zauna.
"Haba habibty, so kike inyi ciwo, ya zaki ce kin hakura, amma baki son yin magana da ni, ki tuna fa I love you more than you can imagine, your happiness is my, and your sadness worries me too." Nafisa ta fada kaman zata yi kuka.
"I know you love me, and I also love you too, you mean a lot to me, but you should have consoled me, bawai ki dinga bani irin advice din nan ba at that moment. Wallahi alokacin nan, comfort nake so, ina bukatan ki kwantar mun da hankali ne. Ko kin san idan iyayen sa basu yarda ba, hakan na iya zama sanadiyan rabuwan mu, so I need comfort, not that type of advice. You can advice me that any day, banzan yi fushi ba, but I was hurt when you deed it at that time." Alokacin Olamide tana magana tana kuka.
"Ban san abun daya sa nake da saurin kuka ba, amma this is me." Olamide ta kara fada.
Nafisa bata san lokacin da ta yi hugging din ta ba, ta ce "am very sorry habibty, bazan kara ba, I just said it, ban yi tunani ba, danAllah kiyi hakuri." Nafisa ta fada.
"Nayi, amma Fisa na dauke ki as sister ta, ko kin mun laifi, bana iya fushi dake." Olamide ta fada.
"Am very sorry, banzan kara ba." Nafisa ta fada.


Da suka gama koke koken su, su dan yi hira, Nafisa ta ita kwantar mata hankali, su kayi barci.



Da suka tashi da safe, suka yi dutyn su, suna ta hira, ranan ya kasance Saturday, gashi basu da lectures, so suna ta huta duka gajiyan da suka yi tun monday. Ana cikin haka, Abdallah ya kira ta, ya sanar mata da cewa bayan asr zasu fada masu Abba, tun lokacin mood din ta ya canza, amma tana ta kokarin danne shi, not to make anyone around her worried.



Around 3 data ji shuru, sai Nafisa ta bata advice wai ta kira shi, da tana ta contemplating. Sai bayan sallan asr ta yi concluding kawai ta kira shi, kawai ta kira shi.





〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️


Sanda wayan ya kusan tsinkewa, ya daga.
Daya daga bai yi magana ba, sanda ta ita sallama, kafun ya yi clearing din muryar sa kafun ya amsa.
"Baka amsa mun ba tun dazu ina
End Ads