x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 19 - BANBANCIN KABILA

  • 54001 words
  • 57000 words
  • Out of 57901 words

Category: Love Stories

Views 244

25 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
wayar ta ya fara ringing. Ta dauki wayar akan bedside drawer, ta duba mai kiran ta, taga sunan Abdallah. Tana ganin sunan, taji rate din da heart din ta is beating, was too fast. Sanda ta saki wani irin numfashi, sannan tayi bismillah, kafun ta daga still heart din ta na bugawa 3³. Taji dadi ma Farida bata cikin dakin, tana caan dakin mummy.
"Assalamu alaikum!" Olamide ta fada.
"Waalikumus salaam. Kin tashi lafiya?" Abdallah ya tambaye ta.
"Lafiya kalau. Kai fa?" Itama ta tambaya.
"Not too good. Anyways that's not why I called, ina da maganan da nake son muyi, kuma ina son ni da ke muyi accepting din haka as qadr din mu." Abdallah ya fada.
"Ban gane muyi accepting din shi as qadr mu ba." Olamide ta fada confusedly.
Sai wani idea ya shigo mata, ta kara cewa "na gane yanzu. Wato iyayen ka basu yarda ba ko?" Ta fada wasu zafafan hawaye na fita a idon ta.
Sanda yayi wani irin numfashi, kafun yace "bazan maki karya ba, iyaye na basu yarda ba, amma ina son ki san ina so...." Olamide bata bari ya gama magana ba, ta kashe kiran.
"Inalillahi wa'ina ilahil rajiun! Ya zan yi da kai na, ya zan yi da zuciya na?" Haka ta ita tambayan kan ta questions kala kala tana kuka.




〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️



Tun ran da Abba ya ma Abdallah Allah ya isa, Abdallah ya rasa yanda zaiyi. Ya fada ma yayyin sa, suma suka ce ba wani mafita, ya fada ma Mide kawai. Shi kuma ya kasa fada mata kai tsaye, shi yasa within those two weeks, yake ta mata abubuwan da zai dinga bata mata rai, maybe soyayyan sa zai ragu a zuciyar ta, amma yaga ina, abun sai karuwa yake. Shi yasa yau din nan ya yanke decision zai fada mata.
Kafun ya kira ta ma, sanda ya ita practicing din words din sa. Ya san in ya fada mata, zata shiga wani irin hali kuma ba ita kadai ba, ko shi zai shiga wani irin hali. Bale ma shi ya riga ya shiga tun da dadewa, maneji kawai yake.




Daya kira ta, suka dan gaisa, kafun ya fada mata reason har ta fada. Nan yaji wani irin zafi a zuciyar sa. Yama kasa fada mata abubuwan daya so ya fada, saboda ga bisa duka alamu, kuka ma take.
Gashi he wanted to tell her words that will make her calm, but she cut the call.

What sort of life is this, me yasa ba wanda yake son yayi supporting din shi ne, instead kowannan su na kara mai zafin da yake ji a zuciyar sa.



Ya kira Olamide ya fi sau goma, amma ta ki dagawa. Tana gani bawai bata ganin ba.




〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️



Olamide nata kuka, ta rasa wa zata fada ma damuwan ta.
Sanda ya bari ta gama son shi, sanda ya bari ta gama planning din yanda future din su will be, shi ne yanzu ya ce su hakura da juna, ai ya cuce ta.
Kuka take na fitan hankali.

Ana cikin haka, wayar ta ya fara ringing. Tana dubawa taga Abdallah ne, sai tayi tsaki.
Ya kira ta sau goma, amma taki dagawa. Daya ishe ta da kira, ta kashe wayar ta.

Baa fi 5mins ba, sai ga Farida ta shigo.
"Aunty gashi yaya Abdallah yana son yin magana da ke. Farida ta fada.
Ki ce mai bana son inyi magana da shi. Olamide ta fada kan ta a kasa, saboda bata son Farida ta ga hawayen ta.
"Yaya tace bazata yi magana da kai ba." Farida ta fada.
"Kin san me?" Abdallah ya tambayi Farida.
"A'a." Farida ta amsa.
"Ki sa wayar a speaker, ki sa kusa da ita, sai ki fita please." Abdallah ya fada.
"Okay toh." Farida ta amsa, sai ta sa wayar a speaker, sannan ta sa a kan bedside drawer, ta fita.


"Na san kina jina. I want you to know that is was never my choice, kuma Allah na da reason din sa daya sa hakan ya faru da mu. Let's take this as qadr din mu.
You are my first love, and you will always be the only woman I will love with all my heart for the rest of my life.
Although zaa hada ni da wata, koman son da zan mata, bazai taba kaiwa wanda nake maki ba.
I may be with another woman, but my heart belongs to you Abdallah's qalbi, kece zuciya ta, kuma zuciya daya muke dashi, and my heart belongs to you Mide, you are my heart." Abdallah ya fada a lokacin shima ya fara hawaye.
Alokacin kuma Olamide tana kuka sosai, sai taji kaman ranan mahaifin ta ya rasu.

Cikin kuka ta ce "bazan so ace ka saba ma iyayen ka ba saboda ni, sam sam bazan so hakan ba. Ka bi umarnin iyayen ka, kuma In Sha Allah zaka ga dai dai. I pray this will be the best for me and you. I also love you, and my heart belongs to you too. Goodbye ifemi, have a great life ahead." Olamide ta fada tana kuka mai cin rai.
"I love you too yide'am, I love you soooo very much qalbin Abdallah. If there was another word that is more than love, then I have that for you qalbin Abdallah. Please take care of my heart for me, ko bamu zama daya anan ba, I pray Allah makes us one in jannah. I love you soooo much yide'am, I love you soooo much qalbin Abdallah. Goodbye." Abdallah ya fada yana kuka itama tana kuka, sai Mide ta kashe wayar.




Olamide ta ci kuka, kuka ta ke na fitan hankali. Shikenan ta rasa Abdallah, she wish she was with Nafisa, at least she will have a shoulder to cry on. Bata son ta fada a gida, kar hankalin mummy dana kannan ta ya tashi.




〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️



Da Olamide ta kashe wayar, shima ya fara wani shafin kuka. Ya ci kuka kaman ran sa zai fita. Zai bi umarnin iyayen sa, amma yasan ko ya nuna mata so, bazai taba kaiwa wanda zai nuna ma Mide ba.
Yana cikin kuka, wani idea ya shigo ma sa, sai ya dau wayar sa, ya kira Nafisa, ya fada mata komai still yana kuka.

"Inalillahi wa'ina ilahil rajiun! Wannan kuma wani irin damuwa ne?
Allah sarki habibty na, abun da take tsoro kenan, amma muka bata assurance cewan hakan bazai taba faruwa da ita ba. Man proposes, but God disposes. This is you guys destiny, kuyi accepting din shi, Allah ya hada kowannan ku da rabon sa, ka daina kuka, it's breaking my heart wallahi. In kai kana irin wannan kukan, habibty na fa, ya zata yi. Allah sarki, I wish we were together, I would have consoled her. But any ways, this Saturday zamu koma school, and today is Wednesday, so it's not too far." Nafisa ta fada.
"Please console her even from the phone, saboda qalbi na is going through alot wallahi. Ina son abi na, amma iyaye na basu so, bazan iya bijire ma maganan iyaye na ba. I hope she forgives me for giving me her heart, but I hope she keeps my heart for me. Thank you for been a good friend to my heart, Allah ya saka maki da jannah." Abdallah ya fada sai ya kashe wayar.




〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️


Olamide na cikin kuka, taji wayar ta na ringing. Bata so dubawa ba, amma her heart was giving her to check it.
Tana dubawa, taga sunan Nafisa.
Ta daga da sauri. Tama kasa mata sallama, ta kara fashe da kuka, tana cewa "shikenan nayi lossing din ifemi, shikenan ni da shi har abada?
Wallahi I can't love anyone man other than him. Na shiga uku na, me zan fada ma mummy?
Mummyn da she is really happy about these whole thing, me zan fada mata?" Haka Olamide ta ita maganganu tana kuka.

Da kyar Nafisa ta samu tayi consoling din Olamide, tayi shuru.
Amma tana kashe wayar, ta cigaba da kuka.




Har 10:30am Olamide bata fito ba, tun mummy bata yi magana ba, har tazo ta je dakin su Olamide da kan ta.

Mide na jin foot step na zuwa towards dakin su, Olamide ta tashi ta shiga toilet, ta bude tap.

Mummy na shiga, ta ji alamun ruwa a toilet.
Bata fita ba, ta zauna akan gadon Olamide.
Olamide na fita, ta fara mata masifa.
"Kinin seyo na (meke damun ki ne wai)?
Tunda safe baki fito ba, wa kike son ya dafa maku breakfast?
Wannan wani irin dabia ne?
Wato ke kina nan kina barci, mu kin bar mu da yunwa." Haka mummy ta ita ma Olamide masifa.
Allah sarki Olamide ta ma kasa ce mata komai in ba mummy kiyi hakuri ba.
Mummy taja wani irin tsaki, har tana hararan Mide, sai tace "if you like stay there, sorry din ki zai dafa mana brakfast."
Mummy na gama magana, ta fita ta bar dakin.

Tana fita, Mide tasa hannun ta a kai, tace "yau kam na ga ta kai na. Dame zan ji, da mummy ko heart?".






```Thanks for reading, zeexee love y'all.```



Comment
Like &
Share.


~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹
*BANBANCIN KABILA*
_(Short story)_
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹

*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*

*🔱(( Home of Expert and Telented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

*-RAYUWAR HUSNA*

- *MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_





4️⃣6️⃣&4️⃣7️⃣






_Bismillah_





Har Allah yayi yau Saturday, Olamide zata koma school, ita kadai ta san irin dadin da take ji, at least she will have a shoulder to cry on. Saboda within Wednesday to this Saturday, ita kadai ta san abun da ta ji. Ko zata yi kuka ma a boye take yi, saboda bata son yan gidan su su sani.
Kana ganin ta, ka san abu na damun ta. Ko su mummy ma sunyi noticing, da suka tambaye ta, ta ce bakomai, tana jin ciwon kai ne, aka sata dole ta sha maganin ciwon kai.
Jiya which was Friday, da Mummy taga yanda Mide ta rame, ita da daman ba wani jiki gare ta ba, ta kara ramewa, sai wani uban kan daya karu.
Mummy was so disturbed, ta tambaye ta abun da ke damun ta, ko bata jin dadi ne bata fada ba. Sai tace ma mummy wai maleria kedan damun ta, amma ai tana shan magani, ta samu maganin maleria a cikin first aid box din su.
Mummy tace ko zata bar zuwa school zuwa next week, saboda a mata treatment mai kyau, da sauri tace a'a, bawai ciwon na wani damun ta bane, ta san abu kadan ke ramar da ita.
Mummy tace haka ne. Amma Hakeem ya kasa yarda da maganan, shi yasa jiyan da daddare, ya je dakin su ya same ta cikin blanket, daman Farida bata ciki, yayi sanda, har ya isa inda take, sai yaji shashakan kuka, ya yaye blanket daga kan ta, a zabure ta tashi, tana goge hawayen ta.
"Dan Allah Hakeem me haka?
Baka san meye knocking bane ko sallama, ko kuma rashin hankali ke damun ka." Olamide ta fada mai kan ta a kasa, a dole tana rufe mai fuska karya ga hawayen ta.
"Koma meye, shi ke damu na. Ance maki ban san karya kike ba?
Tun ran Wednesday nake ta noticing change in you. Tun ranan fa idanuwan ki a kunbure suke, kuma suyi jazur. Na san mummy ma ta san karya kike, ta kyale ki ne kawai.
Yanzu dai ina son ki fada mun tsakanin ki da Allah, kar ki mun karya. Ni dan'uwan ki ne na jini, kuma baki da yan'uwan da suka wuce ni da Farida.
A matsayin ki na babban yaya wanda bata taba son taga bacin ran kanne ta, ki fada mun abun dake damun ki." Hakeem ya fada hannayen sa akan shoulders din Mide.
Maganan sa yayi touching din heart din ta. Truely bata da wanda yafi su, ko Fisa ma a bayan su take. Ta kara fashewa da kuka, sannan tayi hugging din kanin ta.
Ta kasa fada mai komai, inba kukan da take ba.
Da AbdulHakeem yaga wannan kukan ba me karewa bane, sai yayi thinking of an idea din da zai iya sa ta bar kuka, ya ce "ko kina da ciki ne?" Hakeem bai gama rufe baki ba, yaji saukan mari.
"A'a ciko nake da shi." Olamide ta fada tana hararan shi d jajjayan idon ta.
"Am very sorry aunty ta ta kai na, I hate to see a strong woman like you cry. Me ke damun ki ne please?" Hakeem ya tambaye ta disturbed.
"Hmm Hakeem, abun dake damu na ba kadan bane, amma karka dau wani mataki, and promise me bazaka fada ma mummy ba." Ta fada.
Olamide ta san idan ta fada ma Hakeem, yana iya kiran Abdallah ya mai rashin mutunci, kuma gasiya bata son hakan ya faru, dan koba komai sunyi soyayya, kuma har yanzu suna son juna, kaddara ne dai kawai.
"I promise." Hakeem ya fada.
Nan Mide ta fada mai komai.

Hakeem yayi fushi sosai, yace mata sai ya kira Abdallah, daya san a familyn su baa yarda a auri wani kabila, me yasa yace yana son ta, wato ya san hakan zai faruwa, amma ya zabi yayi breaking din heart din sister din sa.
Da kyar Olamide ta samu tayi calming din shi down, sannan ta tuna mai da alkawarin daya dauka.


So a gidan su, Hakeem kawai ya san abun daya faru.


Da sassafe Hakeem da Farida suka raka Olamide tasha, inda zata hau motan kano.
Hakeem ke driving. Farida kuma nata fada mata how much she will miss her, duk da cewa ba randa baza su yi fada ba.





〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️



Tun ran da Abdallah ya fada ma Mide abun nan, ya dawo kaman marasa lafiya.
Ran Thursday ma daya je gurin aiki, da kyar yake attending to patients, sai ya rubuta medication, sai ya kara gogewa, saboda rubbish kawai yake rubutawa.
Ko kuma inya tambayi patient abun dake damun su, in suka fada mai, kafun ya rubuta medication, sai ya manta abun da suka ce ke damun su, sai kuma ya kara tambaya.
Daya isa wajan aiki ran Thursday, ya fada ma abokan sa komai, duk sun tausaya masa.
Farouq yace Nabila bata sani ba ne, data fada mai maybe.
Yace ai jiya abun ya faru, kuma shine ma ya fada ma Nafisa.
Asim yace toh kar Allah ya sa Nafisa ma tayi fushi tace bata son shi.
Abdallah yace mai, karya damu hakan bazai faru ba, ai ba banbancin komai a tsakanin su. Suma din kaddara ce ta fada akan su.



Yau Saturday, dutyn rana gareshi, so by 8:am, ya je kitchen, domin ya taimaka ma umma da arranging din breakfast a kan dinning table.


Umma da Abba sunyi noticing din chanji game da shi, amma suka yi ignoring din sa, saboda daman bukatan su ya biya, ya bar soyayya da yar yarbawa.



Da suka gama arranging din komai, suka zauna, suka ci breakfast. Suna gama ci, Abba yace Abdallah ya kai plates kitchen ya dawo, suna da magana.
Abdallah najin haka, heart din sa ya fara beating da karfi. Allah yasa dai lafiya.

Da Abdallah ya gama clearing din dinning, ya koma ya zauna.
Sanda Abba yayi clearing din muryar sa, yace "nayi magana da Alhaji Madaki, kuma ya yarda, ba matsala. Kuma tunda gobe ranan hutun ka ne, kana iya zuwa gidan sa gobe dan ku gana da Safiya." Abba ya fada.
"Kai MashaAlla, naji dadi sosai." Umma ta fada.
"Banga use din zuwa na gidan ba, tunda ku iyayen kun riga kun gana, ku sa date kawai." Abdallah ya fada.
"You are very stupid for saying that. Kuma in ka cika kai dana iska ne, kar ka je. Ku kuke sa mutum yake fade fade. Mtchww." Abba ya ja tsaki ya bar wajan a fusace
"Kaga irin ta ko?
Duk dan daya ki bin umarnin iyayen sa, duk abun daya faru shi yaja ma kan sa." Umma ta fada, itama ta tashi ta bar dinningn.


"Na shiga uku na, wani laifi na ma su Abba ne a rayuwar nan?
Ya ilahi, gani gare ka.
Kun ce in rabu da zuciya na, na rabu da ita, amma still kun ki bari na.
Bakomai, zan bi umarnin ku, saboda naga daidai a rayuwa na." Abdallah ya fada da hawaye a idon sa.
Sai ya kara cewa "koya qalbi na take oho, Allah sarki qalbin Abdallah, I hope you will forgive and learn to move on, and lastly keep my heart save." Abdallah ya fada da hawaye still a idon sa.


Daya share hawayen sa, shima ya tashi ya tafi dakin sa.
Daya shiga dakin sa, ya hau kan gado,
End Ads