Olamide, ga shi har 9 din dare yayi. Maybe kawai ya kira ta, sai ya dinga canza magana idan zata yi tambayan abun da su abba suka fada. Amma gobe inta koma gida, sai ya fada mata cewa sun ce zasu yi tunani akai.
Haka ko aka yi. Ya kira ta, yayi wishing din ta best in all the exams she wrote, in taso ta tada maganan, sai ya canza topic, har suka gama wayan, bai bata opportunityn da zata tada maganan ba.
"Allah sarki my qalbi, Allah ya ga bana son in maki karya, amma yana iya, iyaye na basu son union din mu. Duk da cewa basu san ki ba, sun bi sun sa tsanan ki a zuciya, saboda *BANBANCIN KABILA.* Amma karki damu, zan san yanda zan yi dasu.
Haka Abdallah ya ita tunani, har barci ya dauke shi.
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
Tunda suka tashi around 4, ba wace ta kara runtsawa. Suna ta shirye shirye. Suna idar da sallah, suka karanta qur'ani, suka yi addu'an safe, Nafisa ta fara shiga wanka, Olamide ma tazo ta shiga.
Suna gamawa, kowannan su ta shirya, suka rurufe ko ina, su ka kashe duka sockets, sannan kowannan su ta dauki jakar ta, sanan suka yi sallama da sauran mutan gida, kowannan su ta nemi keken da zai kai ta tasha, nan suka yi hugging din juna, kaman baza su bar juna ba, kafun suka shiga, suna waving din juna.
Olamide na isa tasha, luck was on her side, saura mutum daya motan ya cika.
Ita kuma Nafisa, saura mutani hudu.
"Madam what are you looking at, have been calling your name."
Olamide ta ji tap din mutum a shouldern ta, tana jin muryar, tasa this is definitely her mum. Da sauri, ta juyawa tayi hugging din ta.
"Mummy mi, nayi missing din ki sosai."
"Me too. Muje mu shiga mota. You look tired baby girl." Mummy ta fada.
"Muje. Kaman kin sani mummy, na mugun gaji." Olamide ta fada.
Da suka isa gida, Farida ta fito da gudu, tayi hugging din Olamide, itama Mide tayi farin cikin ganin kawan wata.
Duk sunyi complete, amma banda Hakeem, sai next week zai dawo.
Ta shiga dakin ta, taga an gyara ko ina, sai ta kwanta saman gadon ta, ta ce "wow home sweet home." Ta dan huta akan gadon, kafun taje ta shiga toilet, ta dan watsa.
Sun dade suna hira, aka maida Mide yar'lele. Da suka gaji da hira, mummy ta wuce dakin ta, Mide ta Farida ma suka tafi nasu.
Farida ta kwanta a nata gadon, Mide ma ta kwanta a nata, tana kwantawa, taji idanuwan ta na rufuwa, tama manta da zance iyayen Abdallah, saboda tsabaragen gajiya.
Asuba ta gari.
Da suka tashi da safe, suka yi morning routine din su, suka yi wanka, suka hadu a dinning, suka yi breakfast. Suna gamawa, ta ki Nafisa, Nafisa ta gaisa da mummy da Farida, itama Mide, suka gaisa da Ummi da abba. Nafisa ta tambaye ta ko Abdallah ya kira, tace ae, amma lokacin tayi barci, so zata kira shi idan sunyi hanging up.
Sun dade suna hira, kafun suka yi sallama.
Da suka gama waya da Nafisa, Olamide ta koma dakin ta, nan ta kira Abdallah.
" Assalamu alaikum ifemi"
"Waalaikumus salam yide'am. An tashi lafiya, kin same su lafiya?
Ya gjiyan hanya?
"Fyn alhamdulilah. Kaima ka tashi lafiya?" Olamide ta tambaya.
"Lafiya kalau." Abdallah ya amsa.
"Baka je wajan aiki bane?" Ta tambaye shi.
"A'a, yau ina afternoon duty ne." Abdallah ya amsa.
"Okay toh, Allah ya kaimu afternoon." Olamide ta fada.
"Amin amin yide'am." Abdallah ya amsa.
Sai kuma shuru ya biyo baya kafun Abdallah yayi breaking din silence din.
"Akan maganan nan, na fada masu." Ya fada zucuyar sa na bugawa.
"Okay, me suka ce toh, I hope it's not what am thinking."
"Nope it not. Kin san this is the first time this is happening in our family, toh wai zasu yi tunani akai." Abdallah ya fada yana runtsa idanuwan sa, yana astagfirullah a zuciyar sa. Allah yaga baya son karya, amma at this point, this is the only way out.
"Hmm toh shikenan, at least basu zage ni ba, kuma basu ki ni ba Alhamdulilah, Allah yasa suyi thinking positively. Kaga sai anjima, yanzu mummy zata fara kira na, inta ga na dade ban fito daga daki ba." Olamide ta fada.
"Okay bye qalbi'am. Abdallah ya fada, sannan ya kashe wayar.
```DanAllah kuyi hakuri da kuka ji ni two days shuru, I was kind of busy ne, shi yasa, amma am back now💃🏽💃🏽💃🏽.```
```Thanks for reading and always been patient, zeexee loves you guys 75, 50, 100%🤭🤭🤭🤭.```
*🔱(( Home of Expert and Telented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))*
*T.W.A*
*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_
MARUBUCIYAR
*-RAYUWAR HUSNA*
- *MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_
4️⃣1️⃣&4️⃣2️⃣
_Bismillah_
Bayan sati biyu, kowa ya dawo, gidan mummy ya cika jif, it was a complete home.
Around 5:pm, Olamide da Farida suna daki, suna hira, sai wayar Olamide ya fara ringing.
"Duba mun wake kira na." Olamide ta fada.
"It's yaya Abdallah. Amma bakin ce yau bazaki yi picking din calls ba?" Farida ta tambaye ta.
"Meya dame ki, bani abu na, kuma ki fita." Olamide ta fada.
Farida ta mika mata.
"Toh ki fita." Olamide ta fada tana nuna mata hanyar kofa da hannu.
"Ni kam bazan sa kunni a conversation din ku ba, just please let me stay." Farida ta fada tana mata puppy face.
Olamide taja tsaki, sannan ta daga wayar.
"Assalamu alaikum!"
"Waalaikumus salaam Olami." Abdallah ya fada.
"Toh ya kake, har ka dawo daga wurin aiki ne?" Ta tambaye shi.
"Lafiya kalau, ke fa?
Na dawo fa, amma na bi na gaji wallahi." Abdallah ya fada.
"Nima lafiya. Allah sarki, sorry. Wannan aikin na ku is very stressful wallahi." Olamide ta fada.
"Bari kawai qalbin Abdallah, aikin is very very stressful." Abdallah ya fada yana mika kaman tana ganin shi.
"Allah sarki ifemi, may Allah make it easy for us all." Olamide ta fada.
"Amin amin yide'am. Kina cikin mutani ne?" Abdallah ya tambaye ta.
"A'a, nida Farida ne kawai, ya aka yi?" Olamide ta tambaye shi.
"Daman akwai wani magana mai mahinmaci da nake son muyi ne, kuma I will need your full attention. So in ba damuwa, ina son ya zamanto ke kadai ce, so that zaki bani full attention din ki." Abdallah ya fada stressed.
"Okay toh." Ta fada, sannan tama Farida signal da hannu ta fita.
Rai abace, bakin nan a zungure, ta fita.
"Toh am alone. Amma lafiya kuwa?" Ta tambaye shi.
"Lafiya ba lafiya." Abdallah ya fada.
"Ni kam ifemi ka daina tsoratar dani." Ta fada hankali a tashe.
"Karki tsorata please, wannan maganan da zan maki, na fahimta ne, zan so mu fahimci juna ne." Abdallah ya fada yana shafa kai.
"Dole na tsorata ai, the way you are talking is not pleasing at all. But anyways ina jin ka." Olamide ta fada.
"Toh ki kwantar da hankalin ki." Ya fada.
"Toh naji. Me kake son ka fada." Olamide ta fada.
Sanda yayi wani irin numfashi, kafun ya ce "Olami, kin san this is the first time din da irin abu haka zai faru a familyn mu kenan, kaf cikin familyn mu, mutum daya ce kawai ba bafulatana ba, matar kawu Dajjo kenan, amma ita ma she is from the North. Amma namu is different, we come from different parts, so it's really hard to come to a conclusion." Ya na son ya cigaba, Olamide ta katse shi.
"What do you mean, just go straight to the point please." Ta fada muryar ta na rawa, kana ji ma, zaka san a tsorace take.
"It's really hard for my parent, kafun ma akai ga Uncle dina. Harga Allah, ina son ki, kuma so fisabilillah. Kuma wallahi bazan iya son wata ya mace kaman yanzda nake son ki ba." Ya kara shuru.
"Just go straight to the point please." Olamide ta fada.
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
"I have made my decision and that's final. Zan hada ka da yar Alhaji Madaki ne. Kuma I don't want to hear anything about that yoruba girl again." Abba ya fada yana huci.
"Allah sarki umma ta ki sa baki mana, kar ki bari a cutar dani mana, danAllah ki ba Abba hakuri." Abdallah ya fada da hawaye a fuskan sa.
"Me kake son in fada ne?
Me kake son in fada. Kai da aka baka chance, amma kayi misusing din chance din ka?
In ma tambaye ka, wai mata sun kare ne a arewa?" Umma ta tambaye shi.
"Allah sarki umma, ita ta zauna mun, ai ta ma fi wasu yan arewan natsuwa." Abdallah ya fada.
"I can see you are sick. Abban ku ya riga ya yanke decision, kuma bani da ja akan decision din sa. Then kar ma ka fada ma yayyin ka, saboda zaku bata lokacin ku ne." Umma ta fada.
"Ka tashi ka fita mun kafun in maka abun da baza ka ji dadi ba." Abba ya fada.
Jiki a sanye ya tashi ya bar wajan, ya koma dakin sa.
"Wato shikenan zasu raba ni da masoyiya ta, yanzu kam kasancewa na da masoyiya ta ba tabbas".
Daman bai yi asr ba, sai ya shiga toilet, ya yo alwala, sannan yazo yayi sallah. Ya dade akan sallaya yana addu'a, Allah ya kawo mai mafita.
Daya gama addu'a, ya ninke sallayan, yasa a mazauin sa, sa ya zauna akan sofa, ya fara tunanin mafita, sai wani idea ya shigo masa, ya dauki wayar sa, ya kira Olamide, to him that will be the best decision to make.
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
"To be sincerely speaking, su Abba are still having doubt, har yanzu basu yarda ba, kin san irin haka bai taba faruwa a familyn mu ba, so suna doubting akan decision din su." Abdallah ya fada.
"Atakaice dai basu sona ko?" Olamide ta fada da hawaye a idon ta.
"Ba haka bane, waye zai ki ki a rayuwar nan, ai ke abun so ce. Kawai dai suna kan tunani ne. Gashi kin san babban familyn mu kaf ma nada nasa matsalan, so sai sun shirya sosai." Abdallah ya fada.
"Toh naji. Amma why am I not believing these, ina ji kaman karya kake mun, ina ji kaman sun ce basu so na ne, and you are just covering up." Olamide ta fada.
" So you don't trust me, what is the use of a relationship without trust ?" Abdallah ya tambayi Olamide rai abace.
"Nifa bance I don't trust you ba, amma ina ji ne kaman you ain't saying the truth. Amma ba komai, kayi hakuri in na bata maka rai."
"Sai anjima." Abdallah ya fada, ya kashe kiran.
Jiki a sanye, Olamide ta kalli wayar ta, wasu zafafan hawaye suka fito mata.
Tayi kuka ta gode ma Allah. Abdallah bai taba fushi da ita ba, amma yau yayi, gashi kuma to be sincerely speaking, with the way he is talking, kasan karya yake, he is trying to cover up.
Ana cikin haka, lokacin sallah yayi, ta tashi ta shiga toilet ta yo alwala, ita ma Farida ta shigo, ita ma taje tayi alwala.
Tana son ta tsokane ta, taga yana yin ta, sai tayi shuru, tasan ba lafiya.
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
Frustration ya kama Abdallah, sai yaji ma baya son yin magana da kowa. Shi dai yasan a yanayin yanzu kam, da kyar idan zasu yi aure da Olamide. Gashi baya son saba ma iyayen sa, amma a yanda yake son Mide, hanya bazai saba masu ba?
He was feeling very frustrated that he could do anything at this moment. Sai hawaye yake shar Shar kaman karamin yaro. Who said men don't cry?
Men do cry, but not in front of people, they are also humans, they have hearts.
Ana cikin haka, lokacin sallah yayi, ya shiga yayi alwala, yana gamawa, ya fita ya tafi masjid shi kadai, yaki jiran Abba.
Da Abba ya fito, yayi knocking din kofar sa, ya ji shuru, sai ya bude kofar, yaga baya nan, ya jijjga kan sa, yace "wato dan na hana sa yarinyar nan, shi ne yaki tafiya da ni masjid ko?
Hmm kar ma ya bari in sa next week ayi auren nan." Abba ya fada. A fusace ya bar wajan, ya ce "zamu gamu ai."
Da suka dawo daga masjid, Abdallah ya shige dakin sa, ya rufe dakin sa.
Daman daya fito daga masjid, bai jira Abba ba. So da Abba ya jira ya jira, sai ya koma gida. Yana shiga, yayi sallama, Umma ta amsa mai, ya ce "ina Abdallah?" Ya fada ran sa a bace.
"Na ji shigowan sa, kaman ya wuce dakin sa. Lafiya?" Umma ta tambaya.
"Ba lafiya. Ba lafiya saboda Abdallah ya raina ni, Abdallah ya maida ni dan sa, ya manta ni na haife sa. Amma kar ya manta, decision na hannu na ne, I can do and undo in this house. Wallahil azim, inya bani haushi, sai ayi auren sa da yarinyar nan next week Friday." Abba ya fada yana huci.
Aiko Umma na jin haka, ta tashi daga saman kujeran da take zaune a fusace, ta je dakin Abdallah, ta fara knocking.
Yana jin knocking din ta, ya ki tashi, sanda yaji abun yaki karewa, ya tashi, ya bude kofar.
Yana budewa, ta finciko shi, ta ja shi har parlor inda Abba yake zaune yana fushi.
"Ka tsuguna ka ba mahaifin ka hakuri yanzun nan." Umma ta fada.
Sai ya tsuguna a gaban Abba, ya bashi hakuri.
"Wallahi! Kaji nace wallahi, inka sa wasa, next week Friday zaa daura auren ka da Safiya. Mahaifin ta bayi da matsala, yanzu zamuyi komai, inje in fada ma Baffan mu, sharp sharp zaayi komai." Abba ya fada.
"Dan Allah Abba kayi hakuri." Abdallah ya fada.
"You better be careful with me. Ka shiga hankalin ka ka bari mu yi abun nan yanda nake so. Kuma ban yafe ba in na kara ji kayi magannan yarinyar nan. Kuma inma ka kara magana da ita, it should be that you will be telling her ku rabu." Abba ya fada, ya tashi ya bar wajan.
"Kaga irin ta ko?" Umma ta tambaye sa.
"Aya umma ba laifi na bane, amma hukuncin daku ka yanke mun bai yi ba ne, na rasa inda zan sa kai na." Ya fada da hawaye a idon.
"Mtchwww umma ta ja tsaki ta bar wajan.
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
Olamide na idarwa, tayi adu'a, tana ta rokon Allah yasa ba dai karya yake mata ba. Tana gamawa, ta ninke sallaya, ta dau wayar ta, ta kira Nafisa, ta zaiyana mata komai.
"Toh tunda yace maki it's been hard on them, you should believe that. Truly this is new to them, baa taba hakan ba a family din su. Just pray for the best, and believe him." Nafisa ta fada.
"Toh naji Fisa, but am scared. Ni fa mahaifiya ta bata dau time ba, ta ce toh, then why is it hard for them?
Ai muma yarbawa muna da kishin yaren mu, muma bamu cika auren wanda ba yaran mu ba. Amma mummy ta yarda. Bakomai dai, let's hope for the best kawai." Olamide ta fada.
Thanks for reading. Kuyi hakuri kun ji ni shuru, waya ta ta fada a ruwa shi yasa.
*🔱(( Home of Expert and Telented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))*
*T.W.A*
*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_
MARUBUCIYAR
*-RAYUWAR HUSNA*
- *MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_
4️⃣3️⃣&4️⃣5️⃣
_Bismillah_
*BAYAN SATI BIYU*
A ranan Mide ta tashi bata wani jin dadi, ji take kaman an mata rasuwa. Tunda ta tashi, tayi sallah, ta gaida mummy, ta koma dakin su, ta fara jin wani iri, kwata kwata ba abun dake mata dadi.
Within this two week, ita da Abdallah suna soyayyan su, amma ba kaman da ba, basu wani dadewa suna waya, gashi ta riga ta fada a tarkon son sa. Kullum in suka yi waya, in ta ga bada tone din daya saba mata magana yake ba, in tayi kokarin fada mai, sai yaji haushi, ya ce she is not appreciative, he is trying everything possible just to love her, even though soyayyan su is a forbidden one for now.
Wani sain, in suka gama waya, sai tayi hawaye, saboda ba Abdallahn data sani ne wannan ba. Unkown to her that he was breaking his parents rules just to be with her.