x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 12 - BANBANCIN KABILA

  • 33001 words
  • 36000 words
  • Out of 57901 words

Category: Love Stories

Views 238

25 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
masjid, ita kuma Umma, tayi a dakin ta.
Da suka dawo dinning suka tafi straight, Abdallah ya shiga kitchen, ya taimaka ma Umma, suka yi setting din dinning, kafun suma suka zauna, Umma tayi serving din su, suka ci abincin su silently. Da suka gama Abdallah ya kwashe kwanuka, ya kai kitchen, sannan suka koma parlor, suka fara wani sabon hira. Sanda Abdallah yaga sun yi nisa cikin hiran, yace " Abba Umma, kun san me?"
"Ya zamu sani in baka fada mana ba?" Umma ta fada, shi ko Abba inba dariya ba, ba abun da yayi.
"Daman akwai wani aboki na ne, da muka gama secondary dashi, amma muna communicating, shi ne yau muka hadu, sai yace mun wai shi ya samu wacce yake so, amma matsalan wai bayarbiya ce, kuma family din su, suna iya barin mace ta auri koma waye, amma mazan su kam, daga fulani sai fulani, shi ne wai in ba shi shawara, ni kuma na rasa abun da zance masa."
"Hmmm this is serious. Amma idan iyayen sa are very understanding, zasu iya bari. Amma in tambaye ka mana?" Abba ya fada.
"Toh Abba na." Abdallah ya fada.
"Ya fada ma iyayen sa ne, kuma me suka ce?"
"Gaskiya kam, ya kamata ya bi umarnin iyayen sa." Umma ta fada.
"Gaskiya bai fada masu ba, yana tsoron amsan su."
"Ya dai fada masu, sai yaji opinion din su koba haka ba hajiya?" Abba ya tambaya ya na kallon Umma.
"Haka ne. Amma kuma yabi umarnin iyayen sa, dan a hakan zai samu nasara a rayuwa." Umma ta fada.
"In Sha Allah zan fada masa, nagode." Abdallah ya fada.
"Bakomai autan mu." Abba ya fada, yana ja'a mai kumatu."
"Awwsh Abba, zaka cire mun kumatun ai." Abdallah ya fada a shagwabe.
"Sannu auta na, bazan kara ba, kaga daman babu kumatun, kar azo kuma ya cire, ana neman cuko." Abba ya fada.
"Ko kai ka fada. Mutum siriri haka?
Dama ana iya kyautan kiba ne, dana ce yayyin ka su baka, duk da dai suma ba wani kiba gare su ba, amma sun fi ka, but still banda Fadila, dan itama gata ga irin ta." Umma ta fada.
"Hahhhhhhhhhh, kai hajiya baki da dama. Wato dukan su ba auki, ai in kika duba, haka yan gidan mu suke, ko wannan fitinan nan tsohon nan ma haka yake, kaman a hure, amma fitinan shi, ya fi most fatest person kiba." Abba ya fadi.
Abdallah da Umma suka fashe da dariya.
Haka suka ita hira. Sun dade suna hira, dan har 10:30pm suka kai.

Da Abdallah ya shiga dakin shi, yayi realising din time, yasan ko ya kira qalbin sa, ba zata daga ba, dan he is pretty sure tayi barci. Shi ma yayi shirin barci, ya yi azkar kafun yayi barci.
Asuba ta gari.






```Thanks for reading, Allah ya bar kauna, zeexee ma na son ku.```




Comment
Like &
Share.



Zeexee ce πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar FightπŸ’œπŸ’–: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹
*BANBANCIN KABILA*
_(Short story)_
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹

*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*

*_πŸ”±((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

*-RAYUWAR HUSNA*

*-MAHAKURCI MAWADACI (2020)*





```Dedicating this page to sis Khadija (Hadiza). Nagode sosai da encouragement din ki, Allah ya bar dankon kaunaπŸ’œπŸ’œπŸ’œπŸ’žπŸ’•.```






2️⃣3️⃣&2️⃣4️⃣





Da suka shiga, Afra ta ita rarraba ido tana kallon su, Adda fadi tace da ita "baki iya gaisuwa bane?"
Sai tace "ina ini".
"Ina gajiya, ya kike?" Nafisa da Olamide suka fada tare.
"Lafiya kalau alhamdulilah". Ta amsa.
Aunty Fadi tace ku zauna mana". Ta fada tana murmushi.
Da Abdallah ya shigo, Afra taje wajan sa da gudu, tayi hugging din shi, tana fadan "oyoyo uncle'am".
Shi kuma chewing gum din mummy, ya je ya boye a ta kafan Adda Fadi.
Abdallah ya daga Afra sama, tana ta dariya, sannan shima ya nemi wuri ya zauna. Ya ce "ni kam meye ruwa na da kai, kaje can ka karata da Mummyn ka".
Adda Fadi tace "oho dai, my son ya fi ka kyau, ko Irfi?" Shi kuma ya kada kai.
Adda Fadi ta tashi, ta je kitchen, ta kawo masu chilled drinks da ruwa, da snacks, tasa masu a gaba.
Sai tace "banda pulako fa, ku fara taba wannan".
Nafisa tace "toh".
Abdallah yace da Afra, "kinga amaryar uncle and future mummyn ki In Sha Allah."
"Wacce acikin su uncle?"
"Kiyi guessing, zan baki dairy milk".
"Allah zaka bani dairy milk?" Ta tambaye shi excitedly.
"Uncle ya taba saba alkawar?"
"A'a. Bari in nuna maka ita toh."
All this while, Olamide nata satan kallon su, tana son irin wannan relationship din su, bisa duka alamu, Ife(love) nada son yara, so he will make a good father In Sha Allah.
Tana cikin tunani, taji hannun Afra cikin nata, tace "ita ce wannan ko uncle?"
"Very good, saboda wannan task din da kika yi passing, zan siya maki packet din dairy milk."
"Woo" ta fada exictedly.
Sai ta kalli Olamide da Nafisa, tace "kuna da kyau sosai kaman uncle dina".
Kunya ya kama Olamide, Nafisa ko tace "ki dai fadi gaskiya, kice tana da kyau kaman Uncle din ki " ta fada tana pointing din Olamide.
"A'a tana kama dani dai, ai nafi Uncle kyau, ko Uncle?" Ta fada tana kallon Abdallah.
Duk suka fashe da dariya. Shiko Irfan, ya bi ya makale da mummyn sa.
"Ku ci fa." Adda Fadi ta fada tana pointing din abun da tasa masu agaba.
"Ai In law din ki akwai kunya." Abdallah ya fada.
"A'a, kima cire kunyan nan, dan ba inda zaki in baki ci ba."
"Zan ci." Ta fada a kunyance.
Da kyar ta bude ruwan, ta sa a cup ta fara sha, Nafisa sai kallon ikon God take, ashe habibty nada irin kunya nan.
"Ya kuke ya school?" Adda Fadi ta tambaya.
"Alhamdulilah." Suka amsa tare.
"Wallahi da ba dan bro yace mun ke bayarbiya ce ba ko, wallahi da fulani zan kira ki".
Sai Olamide tayi murmushi, tace "haka ake cewa".
"Gaskiya kam, dole afada. Amma ke kam fullo ce ko?" Ta tambayi Nafisa.
"Ae daga Bauchi."
"Ashe ma bamu da nisa. Gaskiya in law, kin shiga mun rai sosai, am sure su Abba ma will be excited ta accept you In Sha Allah. Bari in kira maku Abban su Afra ku gaisa ko?"
"Toh" suka amsa.

Da Adda Fadi ta bar wajan, sai Abdallah yace "qalbin Abdallah, dan Allah ki sake kin ji?"
"I will". Ta fada tana murmushi.
"You should please. Adda Fadila bata da matsala wallahi, kuma in kika sake, zaki ji dadin ta. Inma so kike in bar ku tare ne anjima inzo in dauke ku, am okay with that, I just want you to be comfortable."
"No, ba sai ka bar gidan ba, In Sha Allahu zan yi kokarin sakewa. Kuma tunda ina tare da habibty, sakewa kam ya zama dole."
"That's good. Habibty ki sa ta sake sosai please."
"Baka da case ai." Ta fada tana murmushi.
Sai Afra ta zo kusa da Olamide, tace " kece wife din Uncle, wai kunyi dinner ne?"
Maganan ta ya basu dariya, Nafisa ta ce "Afi bama aure ba, dinner suka yi."
"Ae, ai dinner shi ne aure, ko Uncle?" Ta fada tana kallon Abdallah.
"Ni kam ban san wannan ba Afin uncle, amma maybe qalbin uncle ta sani." Ya fada yana kallon Olamide.
"Sunan ta kenan qalbi?"
"Ae sunan ta kenan qalbin Abdallah, amma zaki iya kiran ta qalbi." Ya fada still idon shi na kan Mide.
Sai taje kusa da Olamide kuma, tace "qalbi ai dinner shi ne aure ko?"
Olamide ta kalli Nafisa, ta kalli Afra, ta kara kallon Nafisa, ta kara kallon Afra.
"Ki fada mata mana, tana jiran amsan ki qalbi." Nafisa ta fada.
Olamide taji kunya sosai. Data ga still Afra na kallon ta in a way that says I need an answer.
"Amm Afra baby, dinner ba shi ne aure ba, dinner is just a party which takes place during wedding functions. Shi kuma aure, is the coming together of two different people, to become one."
"Okay toh. Amma kuma zaku yi dinner?"
"A'a" suka hada baki.
Sai kuma suka kalli juna suka yi dariya.
"Toh aure kawai zaku yi kenan?"
"In Sha Allahu." Abdallah ya amsa.
Sai ta kara komawa wajan Nafisa, tace "kema sunan ki qalbi ne?
Kema zaki auri uncle ne?"
"A'a ni kam sunana Nafisa, kuma wani uncle din zan aura In Sha Allahu ba wannan ba. Ai wanan na habibty ne ita kadai." Nafisa ta fada tana taba kumatun ta.
"Wacece habibty kuma?" Tayi tambaya confusely.
"Aww sorry, amma qalbi habibty ta ce, kuma qalbin uncle din ki."
"Toh naji."
Suna cikin hira, Afra na masu questions, su kuma suna amsawa, Adda Fadi da mijin ta suka yi sallama.
"Ina ini" Olamide da Nafisa suka fada tare.
Sanda ya zauna, yace "an yi ni lafiya"
"Lafiya kalau. Mun same ku lafiya?" Su biyu suka fada.
"Lafiya kalau alhamdulilah. Kun zo lafiya, ya gajiyan biki?"
"Lafiya kalau alhamdulilah." Suka amsa.
"Toh MashaAllah. Ina amaryar mu acikin ku, ko bata zo ba ne?" Mijin Adda Fadi uncle Isah ya tambaya.
"Kai love, wannan kuma wani irin tambaya ne. Ga amaryar nan mai jallabiya bakin nan."
"Haba dan Allah! Wannan ai bafulatana ce." Ya fada in shock.
"Kai ma dai zaka fada. Wallahi da Abdallah bai fada mun asalin ta ba, da ban yarda ba."
"Ni dai haryanzu I find it hard to believe. Zan baki dan wani assignment amaryar mu, ki yi tambaya agida, afada maku asalin ku, dan ko kawu Dajjo ya gan ki, kuma ba'a fada masa yaran ki ba, bazai sani ba."
"Haka ake cewa, kuma munyi tambaya, duk wanda muka tambaya, suce mu yarbawa ne".
"MashaAllah. Shi yasa discrimination ba kyau, Allah mai yanda yake so da bawan sa. Allah ya kai mu lokacin auren ku."
"Amin"Abdallah ya fada da karfi.
"Kai auta ko kunya" Adda Fadi ta fada.
"Toh kunyan me zan ji, addu'a aka yi kuma na amsa.
"Toh yayi". Ta fada tana hararan shi.


Haka suka ita hira, suna dariya, har Olamide tazo ta sake. Cikin hiran ma suna ta tambayan ta questions, kuma alhamdulilah tana amsawa yanda ya kamata. Sun ci sun sha, saboda Adda Fadi bata bar su ba, sanda taga suna ci, kuma suna shan duk abubuwan data kawo masu.


6:pm nayi, Olamide ta ma Abdallah text, wai ya koma da su, yasan dai gobe zasu koma, so they are things they will like to do before going back. Yana ganin message din ya share, yayi kaman bai gani ba, ya dago kai suka hada ido, ya dauke idon sa. Ta kara mai wani message din, yaki.
Sanda tace "ammm Adda Fadi, zamu wuce, kin san gobe zamu koma, ya kamata mu dan zauna da kawar mu kafun mu koma, kuma zamu shirya wasu abubuwan mu."
"Baki yi karya ba, amma why not ku bari anjima?"
"Haka nima nace, amma ta ki." Abadallah ya fada.
"A'a ba wai taki bane, gobe fa da sassafe zamu koma, kun ga ya kamata mu tafi yanzu." Nafisa ta fada tana murmushi.
"Toh in kuka koma, sai kuma yaushe?"
"Yaushe?" Olamide ta tambaya, sai tayi wani irin murmushin da dukan su suka yi dariya.
"Sai anyi auren kenan ko?" Adda fadi ta tambaya.
"A'a fa ban ce ba." Ta fada a kunyance, tana wani rufe ido, muryar ta kasa kasa, amma sunji ta.
"Oho dai, mu dai munsan maanan haka." Adda Fadi ta fada.
"Allah ya kaimu lokacin, ya daura ku akan duk wani makiyi, ya sa iyayen mu su yarda, kar suma su nuna banbanci, su yarda da wannan union din, saboda hadin nan In Sha Allahu zai yi kyau." Uncle Isah mijin Adda Fadi ya fada.
"Amin" kowa acikin parlorn ya amsa.
"Toh Adda zamu wuce". Abdallah ya fada.
Ai suna jin haka, suma suka tatara jiki suka tashi tsaye.
"Gaskiya ban ji dadin wucewan ku din nan ba, amma na ji dadin zuwan ku sosai alhamdulilah. My prayer is also for this union to happen wallahi, saboda kin gama mamaye zuciya na qalbin Abdallah. Allah ya sa iyeyen mu su yarda, kinga alokacin, zamu dinga haduwa anyhow. Gashi kema Fisa, idan Allah yayi, kema nan zaa kawo ki, wato three three kenan kuka yi. Allah yasa ayi auren ku kuma, ku zo Gombe, ku dinga zuwa wajan wannan addan ta ku, maybe ma by that time mun saba da Nabila, dan nasan Farouq zai kowa ta wajan fav sis din su." Ta fada tana murmushi.
"Toh Allah yasa." Olamide ta fada.
"Mu tafi." Abdallah ya fada.
Zasu fita, Adda tace ku jira ni ina zuwa, bari in sa hijab. Tana barin wajan Olamide ta mika ma Afra leda, na thank you, cike da sweets da chocolate, wafers, da dai sauran su. Tana mika ma Afra, ta gani, tace "yay chocolate, nagode sosai qalbin uncle da adda Fisa." Ta fada tana hugging din su.
Abban su ma yayi godiya, sai ga Adda Fadi ta shigo, itama da leda cikin hijab, ba zaka gane ma ba, sai ka kare mata kallo, ta ce "muje."
Duk suka fita waje, Abdallah ya bude gate, sannan, ya fita da motan sa, alokacin Adda Fadi ta jawo hannun Olamide, tace "In Sha Allah, me and him, zamu san yanda zamu yi da family members din mu, dan Allah kema kiyi kokarin convicing din mummyn ki, wallahi ban taba ganin kani na yaso wata ya mace ba haka, kuma daga bisa duka alamu, kema kina son shi. Wallahi zuwan ki yau yasa nayi clearing kai na and my thinking akan tribalism. Am soo happy I met you wallahi. In Sha Allah I will always put you guys in my du'a. Kar ki ce a'a, dan Allah ga wannan." Ta mika ma Olamide.
Olamide ta amsa, ta mata godiya. "Adda nagode sosai, Allah ya saka maki, ya raya maki yara. In Sha Allahu zan fada ma mummy, moreover, nasan ta wajan mummy bakomai, but still zan fada mata and thanks for accepting me, I can't thank you less wallahi." Olamide ta fada, bata ma san lokacin data yi hugging din Adda Fadila ba, har da wayen ta.
"A'a kar ki mun kuka Abdul ya gani yace na fada maki abu ne." Adda Fadi ta fada tana goge mata hawaye, suka ji ana horn, sai Adda tace "ga wannan ki ba habibtyn ki, mu je kafun ace ina tsungulin ki." Dariya su biyu suka yi, sannan suka fita, Olamide ta shiga gaba, daman Nafisa ta riga ta zauna a baya.
Data shiga, suna ta waving din juna, har suka bace ma juna.







```Thanks for reading.```


Comment
Like &
Share.



~Zeexee ce~ πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ

[8/30, 1:21 PM] Abokiyar FightπŸ’œπŸ’–: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹
*BANBANCIN KABILA*
_(Short story)_
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹

*TAMBARI WRTER'S ASSOCIATION*

*_πŸ”±((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

*-RAYUWAR HUSNA*

*-MAHAKURCI MAWADACI (2020)*







2️⃣7️⃣&2️⃣8️⃣



Anyi sallah lafiya, Allah Ya maimaita mana. Haryanzu dai ba wanda ya bada goron sallah, but am still waiting lol. Allah ya naimaita mana, may we witness more and more eid's to come.

Like I promised, nace zan rubuta suran pejin nan bayan sallah, toh alhamdulilah, gashi yau na cika alkawari.
Asha karatu lafiya, kar ku manta da sharhi, because it's like an oxygen of a writer.




_Bismillah_






4:am alarm din Olamide ya fara ringing, cikin barci taji karan shi, gashi ta sa shi kusa da kunne ta, so har cikin kwakwalwar ta take jin Kara. Da sauri ta tashi, ta kashe, sannan tayi addu'an tashi daga barci, ta sauka daga kan gado, ta shiga toilet, tayi business din ta, tayi brush, sannan tayi alwala, ta fito ta tada Nafisa.


Da suka idar da sallah, suka karanta qur'ani a islam pro app, suka yi addu'an safe da maraici, kafun Olamide ta fara shiga wanka, sannan Nafisa ma ta shiga.

Suna cikin shiri, Nabila tayi sallama ta shigo, tace "kaman kun san nazo duba ku ne ko kun shirya, gashi Allah yayi kun shirya. Amma yaya yace sai kaman 7-7:30 zai kai ku park. So in kuka gama dressing, akwai kwai a kitchen, ku soya, jiya yaya ya siya maku bread, kuma akwai kayan tea, then ku duba store ma, akwai sardine." Nabila ta fada.
"Toh mama Nabila. Amma ko gaisuwa?" Nafisa ta fada.
"Allah sarki kuyi hakuri, tun jiya maganan nan ke rai na, shiyasa, amma amun afuwa, ina kwanan ku."
"Ina gajiya, ya gajiyan jiya, ya dawai niya da mu?
Allah ya bada lada, ya baku zaman lafiya, ya kawo zuriya dayiban." Nafisa ta fada.
"Kalau, gajiya kam akwai shi. Amin amin, nagode sosai kawayen albarka. Kuma Allah yasa muga naku, nima in kai ku dakunan ku."
End Ads