x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 5 - GAYYA CE

  • 12001 words
  • 15000 words
  • Out of 37291 words

Category: Love Stories

Views 86

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
Kamar kuwa Jalil yasan mai yake sakawa axuciyar shi, sai kawai yajiyo Muryar Jalil yana tanbayar ina aka bar jamlah, dad ya yi murmushi yace sorry Jamal tana maka sannu gobe da safe zata zo, Ni zan kai mom Asibiti ne sbd ita ba bata jin daɗi, " kallan ta sukayi cike da tausaya wa suna jirah mata ya jikin.


Sun jima suna hira daga baya sukayi sallah ma. Sakamakon ko inna basu haɗu da ita ba sbd ita da jawahir da yamma suke tafiya.



Mom jamal ce ke gaban doctor inda take mata bayanin abinda yake damun ta sosai doctor Amini ke kallon mom fuskarta dauke da murmushi, " inda ta ce wa mom bazan ce maki komi ba Hajiya Maryam amma bari nasa ayi miki text dan tabbatar da zargina". Haka kuwa akayi mata text inda ganta keta faduwa dad yana ta kwantar da hankali ta in sha Allah ba wata matsala ba ce.



ku san mitina 30 suka dauka sannan aka dawowa da doctor Amina result din ta kallah " ta ce zargina ya tabbata. Dad ta kallah tace Alhaji ina tayaka murna dan Hajiya na dauke da ciki wata biyar ajikin ta, mom kuwa cikin damuwa da fargaba take kallan doctor "tace cikin kuma doctor da girma na haka kin san rabona da haihuwa kusan 20 years kenan, bata kai ga wata maganar ba dad ya rufe mata baki rai a bace ya ce haba Hajiya Amina Maine haka. Ni ina matukar farincikin da wannan cikin a gaban ta yayi wa Ubangiji sujjada, ta farincikin tare da bawa doctor kyau ta sannan ya jata suka tafi.



Ni kuwa nace Ubangijin ya azurta ku da naku mom.



Tun a mota dad kewa mom nasiha sbd gaskiya bata wani ji dad'i wanna cikin ba dan ta gama haihuwa. Amma a nasihar da dad ya mata sai ta gamsu kuma ta godewa Allah.



Fatima ce yau ta Farah zuwa hospital da kayan breakfast din su, dakin ta shigo dan kuwa lokacin yayi wanka ya shirya shaf ga wani farih da ya karah da kibah sbd yana matukar samun kullah wa ta ko,ina. Yana san a sallah me shi amma fafur doctor yake dan kullum tare suke kwana da shi da Jalil a gurin sa.



Bakin ta ɗauke da Sallah ma ta shiga ya amsa mata fuska a sake sbd yarinyar tana matukar burgeshi sbd nutsuwa ta. "Yaya Jamal ya jikin naka", ina fatan da sauki dan mom ma tana gaida ka". Da sauki Alhmdllh Fatima ya mom na fatan tana lpy?" Lpy lau take yaya Jamal.



Haka dai suka dinga hira sama sama, inda tayi saving na shi ta mika mashi, " ya barb'a tare da mata godiya.


Yaya Jamal ina yaya Jalil yake naga ban gane shi ba?,


Yaje kai jamla makaran ta ne.

Amma nasan anjima zai dawo bazai dade ba in sha Allah.


Shiru ce ta biyu baya. Kusan 10 minit.

Sallah mar yaya Farouk ce ta saka su amsawa, fuska ɗauke da murmushi duk kan nin su.


Doctor Farouk ya zauna gefen Jamal sannan ya farah jirah masa tambayoyi yi kamar yadda ya saba, yana bashi amsa.


Bro Farouk dan Allah ka sallameni ko badan niba ka duba kaga yadda Jalil yake ta wahala shi kaɗai duk ya yi baki ya rame.



Pulet din hanun Fatima ya karba da cup sannan ya farah kaiwa bakin shi yana murmushi, Bro jiyafa ina kallan ka yadda ka kurah wa Jalil ido kana kallon shi, karka damu har yanzu babu wani banbanci a tsakanin ku, amma nayi maka alkawarin zan sallame ka nan da kwana biyu.

Suna kai wa nan Jalil yayi Sallah ma shida Jamla.


Guri ta nema ta zauna sannan ta gaida su ɗaya bayan ɗaya ta kuma yiwa Jamal sannu da jiki, daga haka bata kara cewa komi ba amma abu d'aya ne ya bata haushi yadda Fatima ta dare suna ta kwasar hira ita da Jamal, dan har zuciyatar ta zafi take mata tayi matukar kewar Jamal ɗin.


Fatima da doctor Jalil ne suka fita zuwa office din doctor.


Yana fita jamla ta sauke wata ajiyar zuciya mai karfi. Tare da dage rikaf ɗin dake fuskarta.


Tashi tayi ta jawo pulet ta hau zuba mashi sakwarah da miyar Agushi wadda taji na ma kawai kan shi take yi. Ta miƙa mashi batare da tace nashi kallah ba.



Kallan ta yake cike da mamaki ya rasa mai yasa yake jin mutuwar jikin indai yana tare da ita. "Yaya Jamal gaskiya ka ce sbd yau ton asubah na tashi nake haɗa maka naso dashi zaka karya amma babu yadda na,iya.


Tana maganar ne ranta a matukar bacce, dan ya tabbatar da abinda yake gani a idonta ne yasa ya ce,"to ai hanuna ne yake mun ciwo bazan iyya ci da kai na ba ya kare zan cen yana wani kyakkyawan murmushi.


Matsawa tayi gaf da shi ta ce maza bude bakin na baka, "cikin tsoka na yace babba dani zaki bani abincin a baki," hade rai tayi ka bude ina jiran ka. Haka ta dinga bashi yana ci yana kallan fuskarta ciki da santa da kaunar ta.


Yaci abincin sosai sannan ya ce mata ya koshi, yana ta yaba daɗi abincin, sai daɗi ta keji,


Tsokanar ta yake wai dama haka kika iyya badah abinci a baki ban sani ba?.


Tana jin shi ta mai banza dan ta fahimci tsokanar ta yake yi.


"Zo kiji" taji Muryar shi daga sama.


"Wai ni yaya Jamal baka san sunana bane?.

Ohhhhh sorry Noor, ta k'ara so inda yake, mai yasa yau bakiji makaranta ba?.

Kasa tayi da kanta sannan ta ce nace yau zan zo na duba ka ne, shiyasah ban je ba,

"Tom bakuda lecture ne?

"Eh babu, duk wanda muke dashi ready na iyya"


Hira su keyi cikin nutsuwa inda yake addu,ar kar Allah ya kawo wani yaga jamlah dan bai shirya wa tashin hankali yanzu ba. Ya jiyo Muryar inna tana ce wa yanzu na zo Farouk.


Ta d'urah hanunta kan Handel din k'ofar, nan ma hankali shi ya karah tashi dan bai san yadda zai yiwa Jamal maganar ta maida likaf dinta ba.

Typing 📲


GAYYA CE!
*Free page*




*Written by*

*Fatima alaramma lafazi*
*(Falaramma)*



https://youtube.com/@fatimaalaramma?si=v_EK6JyH_nkqroPZ


*Sadaukar kar wane ga Sadiq Abubakar CEO din lafazi Allah ya Kara masa lpy, da nisan kwana mai albarka, godiya ta musamman*



💖✨✨✨💞💋💋

Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina rukun Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane zasu amfana dashi wannan kenan.



✨✨✨

Wannan labarin na musamman ne ba gama garin labari bane, GAYYA CE! kuna ji kun San abun sai Wanda ya karan ta, labarin ban dariya da kuma soyayya, tsan tsar cin amana da kuma Butulci, San zuciya da kuma hassada, duk acikin book din GAYYA CE! kunaji kun San ba karya littafin, ina alfahari da ku ges nagode.




Pg 13-14


........Cikin hanzari ya ce ashhhhhh tare da haɗa fuska kamar wanda wani ciwo ya taso ma shi.


Cikin sauri ta karah so inda yake tana tanbayar shi ko lafiya, da sauri ya riko ta ya sauke likaf din cikin dabarah batare da ta fahimci hakan ba.


Sannu yaya ko na kirah ma doctor ne, ya d'aga mata ido alamar eh, har zata fita yace amma dan Allah karki karah daga likaf din nan.


Abakin kofar su kayi karo da inna inda har kasa ta tsuguna ta gaida ta, cikin girmama wa, sannan tayi gaba abin ta, inna cikin mamaki da kad'uwa ta ke kallan ta sbd jin Muryar ta tamkar jawahir din ta data baro a gida. Jiki ba nauyi ta shiga d'akin baki dauke da Sallah ma, ya amsa cikin sakin fuska tare da nuna mata guri ta zauna, ya gaida ta ta amsa tare da tambayar jin nashi, "yace Alhmdllh".


" Nace jamalu wannan yarin yar da ta fita Ni kam wacce ce ita?, jiyayi gaba shi ya faɗi dan jin kalmar ta amma ya ɗan dake yace inna Jamal ce fa yar gidan Alhaji. "Ohhhhh Ni dai yarin yar tamun yanayin murya da jawahir wllh", ta kare maganar cikin jimami.

" Kai inna abu ne naku na tsufa amma yan she zaki haɗa ta da yarki. Ya faɗa cikin salon tsokana.

"Inna to yar yawa bata fita komi ba jamalu, na tabbata da ace jawahir ke samun kulawar yarin yar nan da tuni tafi haka kuma sai an kalleh ta an kuma kallan ta. Dariyar Jamal ya yi sbd yasan dama za,ayi haka, yace kai inna banda sanka fa. Nan dai suka dinga yi.


Fatima ce zai ne gaban Jalil wai nace yaya Farouk taya kake banbance yaya Jamal da yaya Jalil, Ni dai gani nake kamar bazan iyya gane suba. Dariya ya yi mata Sannan yace nima fa ba sosai ba nake gane su Fatima, Jalil ne ya juyo yace kina so kidinga kage mu, tom kawai ki zauna ki fahimce mu sosai zaki gane mu, sai kuma kaf d'in su kasa dariya.


Akwan a tashi ba wuya a wajen Allah gashi yau watan Jamal biyu da Sallah mushi a hospital. Sosai yan zu Farouk ya zama abokin su Jamal dan har zuwa gidan su Farouk suke su sha Shira da mom musamman Jalil, wanda a wannan lokaci sukayi wata muguwar shakuwa da Fatima. Inda ita kuma bikin ta kullum yake karah matsowa inda yan zu saurah sati Daya.

Sukuwa su Jamal tuni chanji rayuwa ta same su dan yanzu Allah har gida faruk ya bawa su Jamal kyau ta, suke zaune.

A yanzu idan kikaga Jalil da Jamal zaki dauka wasu masu faɗa ajine ne dan ko suturar da suke sawa ta chanza. Sosai suke kama kuɗi sbd Jalil ma ya koma kasuwa mom Farouk ta d'urah shi kan duniyar ta sbd ta yadda da amanarsa inda shi kuma Jamal ya koma kan sana,arshi ta funichace dan sosai yake samun kasuwa dan bai yarda ya zauna kasan wani ba.


Inda Jamal yakoyawa jamla mota sosai ta iyya dan yanzu da kanta take zuwa makaranta ga kuma wata matsananci yar soyayya data kullu tsakanin su, sai dai babban tashin hankali Jamal shine kada dad ɗin jamlah ya hana shi ita. Amma a zahirin gaskiya yana matuƙar kaunar ta. Koda yaushe yana san ya sanar da ita halin da ake ciki na kamar su da jawahir kan war shi amma ya kasa, sbd gudun abinda zai faru.


Jamal ce ke shirya wa cikin wata shaddar Farah wadda Jalil ita ce yasa da safe kafin ya fita ya saka, tayi masa matukar kyau, sannan ya fito zuwa falo inda ya tadda su Farouk da Jalil yasan fa yanzu zasu ce zasu bishi dan haka ya haɗe rai yace. Jalil ya bashi mukulin Babur zai fita, wani kallo Jalil ya watsa mashi sannan ya ce wllh yau duk inda zaka kafarka kafarmu sai muje Farouk ya ce bako shakka duk da nasan ba bazai wuce wajen jamla ba, wadda yake ta raina mana hankali wai basan yake ba, wanda nid'in na dade da sanin hakan.

Banza ya musu ya fice suka bishi inna da ta shigo falon yanzu ta bisu da Allah ya tsare.


Shi kuwa da'yar ya yarda suka tafi tare musu iyyakar inda zasu tsaya. Suka ce sunji ba komi zasu tsaya a inda ya ce, amma a zuciyatar su basu Amince da hakan ba.

Bakin k'ofar gidan su jamla sukayi parking sannan suka shiga, tafiya sukayi kaɗan ya ce ku tsaya anan, na shiga na fito. Bai k'arah sa maganar ba ya hango ta tana doso su, inda shi kuma Jalil ya tsirah mata ido shida Farouk suna kallan ta.


Tabbas ita ce wannan jawahir ce, sautin Muryar ta ce ta dawo da su cikin hayyaci su, baki na rawa yace jawahir mai ya kawo ki nan kuma.

Fuskar ta ɗauke da murmushi tace yaya Jaml dai. Dan shi bai ma kawo wata jamlah ba ce.


Jamal ne ya jawo su yace ku dalla can wannan ce fa jamla, kawai suna kama ne, dan Allah malam ka kama kanka ya ce wa Jalil.


Ko kallah shi Jalil bai ba yaje gaban ta ya tsaya ya ce. Ki faɗa tsakani da Allah ke ba jawahir ba ce. "Baki da mamaki ta ce Allah yaya Jalil jamlah ce ni. Cikin sanyin jiki ya farah mata baya ni inda ta gamsu da maganar sa, ta kuma yi masa alkawarin zata zo gida taga jawahir da wannan sukayi sallah ma dan kan shi ya farah masa ciwo.

Kai tsaye gida suka koma inda kawai kwanciya ya yi sannan sukayi sallah ma da Farouk dan shima jikin shi ya yi sanyi.



*KANO*

A yanxu wani takun sak'a ne ya shiga tsakanin papy da Jawad dan sosai ya gane halin shi da kuma san, cutar da shi da yake ƙoƙarinyi, cikin wannan week din ne ma yasa aka tsinka mashi birkin mutar shi da'yar Allah ya taimake shi ya fita lpy daga mutar, kuma yasan wanann Baya rasa nasaba da papyn dan yanzu baki d'aya ya tsane shi.


Ita kuwa Bebyn papa bata san duk abinda yake faruwa ba kuma Jawad bai canza mata ba sbd ya fahimci tana san cigaban sa dana mahaifinsa dan haka shima ya bata girbi na daban a zuciyar sa.

Shi kan shi papa ya rasa mai ke damun d'an uwa nashi, gaba ɗaya.

Nasara kam sosai ake samun ta, inda papa yake gina wani k'atan family Hausa wanda yake ta cinye mashi kud'i, kuma a yan zu ya na gaf da kammala shi.


Ina da sukuwa su Ammy rayuwa suke ta farincikin da jin dadi sbd ɗan ta ya samu farincikin duk da har yanzu bai wani fiye magana sosai ba amma haka ma ta godewa Allah.



*Kaduna*

Yau kwana biyu da zuwa gidan su jamla inda tun daga wannan rana Jalil ya fita daga lamarin Jamal.


Shi a tunaninshi babu wani abu da ɗan uwan na shi zai boye mashi amma sai yaga sabanin hakan. Dan haka ya kama kan shi.


Shi kuwa jikin shi duk ya yi sanyi, shi kan shi yasan bai kyautawa ɗan uwan na shi ba, amma ya yi hakan ne dan gudun abinda zai je ya dawo.


Yau ma yana shigowa d'akin ya tashi zai fita ya rike mai hannu, Jalil dan Allah ka saurareni, dan Allah kayi hakuri nasan ban kyauta maka ba amma kayi hakuri kaji.


"Ummm idan ka gama ka sake ni zan tafi malam.


Haka dai ya yi ta bashi hakuri Sannan ya ce bakomi Allah ya sa haka ne yafi Alkairi, tare da fice wa ya barma shi dakin.


Gobe ne ya kasan ce dauren auren Fatima.

Da Jalil da Jamal ake yin komi, sai dai a daren ne Fatima ta kira Jalil tana kuka tana faɗa mashi ita ta fasa auran shi, sakamakon wani video da aka turu mata nasa. Shima kuma da yaga ni yace karta damu zaizo gidan yanzu in sha Allah.

Sanar da Jamal ya yi halin da ake ciki sannan suka fice zuwa gidan su Farouk din dan samun abokin na su da maganar.


Cikin sa,a suka same shi inda sufa Farah tattaunawa kan matsalah. Abun ba karamin batawa Farouk rai ya yi ba dan sunyi binciken halin shi amma basu gane komi ba.


Tuni mom ta san da batun dan haka a falo suka same ta ta zagba tagumi. Gaida ta sukayi kamar yadda suka sabba, sannan suka shiga jajanta lamarin inda mom kallo ɗaya zakayi mata ka fahimci ta shin hankali dake tattare da fuskrta.


Take ta kira kanin mahaifinsu suka sanar da shi bai jima ba yazo da yake ba su da nisa, haka dai sukayi ta tattaunawa, da jimanta lamarin wannan shine karo na biyu da aka fasa auran Fatima, sunata tattaunawa daga baya kanin mahaifin na su ya tafi shi kan shi ya rasa maka ma.


Wani sabon hawaye ne suke zuwa kan kuncin mom nan da nan hankalin su ya k'arah tashi, Jamal ne yace mom dan Allah ki dena wannan kukan komi zai daidai ta da izinin Allah.

Fatima ce ta she go falon idon ta ya yi jajur duk ya kunburah, gaba ɗaya ta basu tausayi.

Gaban Jalil ta tsaya cikin kuka ta ce yaya Jalil kaga abun da kebi ya yi mun ko, ta kuma fashe wa da sabon kuka.


Komawa tayi ta rungume mom suka fashe da sabon kuka kowa ya kasa furta komi acikin su.


Mom ce ta dago murya na rawa tace Jalil, "na,am. Mom sai kuma tayi shiru, tashi yayi ya koma inda take yace ina jinki mom.

"Dan Allah jalil kayimin wata alfarma mana, dagowa ya yi jikin na rawa yace. Ina jinki mom.

Dan Allah ka auri Fatimah!!!

ka tausaya min nida 'yata kaji tausayi na. Tana kaiwa nan ta kuma fashewa da kukan.


Gaba daya jin shi da ganin sa sun ɗauke shida Jamal, hatta Farouk abu ya bashi mamaki dan bai taba zatan haka daga gare ta ba.


Innalillahi wainnailaihiraju,un!!! Abun da suke furtawa shida Jamal kenan.
Kuna ganin zai amince da wannan auren.

Typing 📲


GAYYA CE!
*Free page*




*Written by*

*Fatima alaramma lafazi*
*(Falaramma)*



https://youtube.com/@fatimaalaramma?si=v_EK6JyH_nkqroPZ


*Sadaukar kar wane ga Sadiq Abubakar CEO din lafazi Allah ya Kara masa lpy, da nisan kwana mai albarka, godiya ta musamman*



💖✨✨✨💞💋💋

Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina rukun Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane zasu amfana dashi wannan kenan.



✨✨✨

Wannan labarin na musamman ne ba gama garin labari bane, GAYYA CE! kuna ji kun San abun sai Wanda ya karan ta, labarin ban dariya da kuma soyayya, tsan tsar cin amana da kuma Butulci, San zuciya da
End Ads