x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - GAYYA CE

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 37291 words

Category: Love Stories

Views 75

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
amin ce wa amma daga bayya ya Amince. " Ya ce ai wannan abu kuwa she ake kirah da GAYYA CE!!.

Nan fa na koma dakin matar Dad Hajiya Maryam naga ta haihuwa yar ta mace an tafi da ita dakin huta amma yar ta rasu, nasan yanda suke matuƙa kaunar haihuwa dan haka na dauki Jamal na saka musu, na saka aka ɗauki gawar aka kai ta mutuwa re.
Nan ma ina fito wa naga wata mata tana tafe tana kuka na tambaye ta lafiya ta ce haihuwa tayi 'yar babu rai.
Na ce baiwar Allah ga wani jahadi idan zaki iyya wannan bebyn ta hannun na wata yarin ya ce ta haife ta ta gudu, wai ashe irin yaran nan ne 'yan gaba da fatiha, dan Allah baiwar Allah ki tallafi yarin yar nan ki rike ta a mai makon yarki, da taki amince wa amma daga baya ta Amin ce da batun na karɓe yar hannun ta wadda ta rasu na bata rayayyiya ita ce Jawahir babbar su. Sannan na bawa matar kud'in ma su yawa mukayi sallah ma batare da nasan ina zata nufa ba, su kuma na bar musu karamar ita ce jalila.

Na koma d'akin na yiwa Doctor Aminu sallah ma na tafi sbd bana so mu hadu da Al Hassan.

Ya karasa maganar cike da haki aka kawo masa ruwa ya sha.


Ya mika wani katin ATM ya ce wannan shi ne bankin da Al Hassan ya tura kudin dan banyi amfani da ko naira biyar ba.

Wannan kuma recoding nayi a lokacin da muke karah tattauna maganar. Gani ga shi ga Doctor Aminu.

Bai k'arasa maganar ba wani mugun damkar da papa ya masa yana karaji wato ni zaka rabawa yara har kana ikirarin wai jina na ne shege, ya fara dukan doctor su Ahmad suka yi saurin rike shi.

Ya nata wata fuzgye fugye wai sai ya kashe Doctor, sai da kotu ta daka masa tsawa sannan ya hankalta.

Doctor Adam ya ce na gode wa Allah daya sa kaji d'acin abin da na aikata mata kamar yadda kai ma ka aikatawa ɗan uwan ka mafi soyuwa a gareka ba shi wa wani abin so bayan kai, Alhmdllh.

Kotu ta kirah Doctor Aminu ya tabbatar da hakan, sannan a kace a na san papa ya tabbatar da hakan shima.
Dan babu karya a zan cen doctor Adam .

Mamy ciki kuka ta zu gaban papa ta ce ka sake ni Al Hassan ka sake ni kai ba mutum bane a she kai ne ka raba 'yayan ka da 'yayan ɗan uwan ka, mai ne ɗan uwan ka bai maka ba a duniya? Dama irin sakayyar da zaka yi masa kenan Al Hassan dama rashin imani ka ya kai haka, Tom wllh Allah ya isa tsakanin da kai bazan taba yafe maka ba, zalunci da kai mun nayi asarar rayuwa ta da har na kare ta a tare da kai, kai din kaga dabba mai manta wa da halaccin. Wllh sai ka sake ni na gama zama da kai na ce, ka sake ni, ya yi mata banza ya kasa ce wa komi.
Baiyi aune ba sai ji ya yi ta sauke ma shi wasu lafiyayyon maruka a fuskar shi, ya dago kuwa yana kallon ta, "ta kuma ce wa ka sake ni dabba" ta daga hannun zata kuma sauke ma shi wani marin papy ya rike mata hannu rai ɓace ya ce karki sake mai mai ta kuskure, sa'adatu ɗan uwa na ba abun rai nin ki ba ne, akan ido na zaki mare shi akan idon 'yayan shi ki dinga kiran shi da duk kalmomi da suka zo bakin ki, to wllh karki karah idan ba haka ba kotu ce zata raba ni da ke.

"Papa ya dago ido sa taf da hawaye ya ce na cancanci abun da ya fi haka daga Sa'adatu dan haka ban ga laifin ta ba, kiyi iya marin da zaki min in dai zaki huce, na kasan ce ni mai laifi ne a gare ki, sam bakiyi sa,ar miji ba dan Allah ki yafe min kinji!! ya tsuguna a wajen ya fashe da kuka jawahi ce ta k'arasa wajen ta rike shi tana lallashin shi".

Ita kuwa Mamy da Jamal tausayi shi na gamun gafarah ya dauke a idon su sai ma wata tsantsar tsana da suka ƙarah yi mashi.

Papa kuma ya tabbata da abun da su doctor suka faɗa daga nan kotu ta ce zata yanke mushi hukunci shi da doctor.

Ammy kuwa ta kasa magana gaba daya sai mamaki ta keyi ga hawaye wani na biyo wani
Ku biyo ni dan jin yadda zata kaya



✍️✍️✍️💥💥💥
*GAYYA CE!*




*Written by*

*Fatima alaramma lafazi*
*(Falaramma)*



https://youtube.com/@fatimaalaramma?si=v_EK6JyH_nkqroPZ


*Sadaukar kar wane ga iyaye na da 'yan uwa na 'yayan Alaramma baki d'aya ina alfahari da su*



💖✨✨✨💞💋💋

Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina rukun Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane zasu amfana dashi wannan kenan.



✨✨✨

Wannan labarin na musamman ne ba gama garin labari bane, GAYYA CE! kuna ji kun San abun sai Wanda ya karan ta, labarin ban dariya da kuma soyayya, tsan tsar cin amana da kuma Butulci, San zuciya da kuma hassada, duk acikin book din GAYYA CE! kunaji kun San ba karya littafin, ina alfahari da ku ges nagode.





PG 2️⃣7️⃣&2️⃣8️⃣

.................... Babu wani b'ata lokacin aka yan kewa Papa hukuncin shekaru 5 a gidan yari tare da tara ta Naira miliyan hamsin. Ina faɗa ma shi ya kuma fashewa da sabon kuka, ya na cewa ni n na jawowa kai na nayi abin da hafi hakan ma, kuma na cancanci fin wannan hukuncin da zaku san abun da na aikata, papy ya rufe ma sa baki yana kuka yana bawa ɗan uwan na sa hakuri.
"Ka dena kuka ya kai ɗan uwan na wllh abun da nayi na cancanci fin haka, ni ne ya lalata maka Company ka na tsawon shekara da shekaru, ni ne nake bibiyar Jawad saboda na kashe shi, duk wani hatsari da kake samu ko Jawad ke samu ni ne na haɗa shi. Dan Allah ka yafe mun ɗan uwan na, papy ya rufe masa baki ya ce ya isa haka.

Shi kuwa doctor Aminu kotu ta ce zai biya su jamlah Naira miliyan biyu saka makon yana gani bai sanar ba. Ko ya yi gidan yari na shekara biyu.


Shi kuwa doctor An yanke masa hukumcin shekaru uku a gidan yarin da tara Naira miliyan hamsin shima.

A wajen wani Brister ya ce yana ne marwa Doctor beli aka ce an bayar, Amma banda na papy.


Mom din jamlah kuwa tuni an wuce da ita hospital sbd tashin hankali anan ta haifi 'yayan ta biyu mace da namiji.

Zu kuga farincikin wajen Dad, dama an ce wanhanun ga Allah bayyiwa ne. Ga shi yau cikin da kike gudu shine gatan ki.

Bayan kwana biyu tuni an bada belin doctor ya cigaba da al'amuran rayuwar shi . Har ma zai koma America nan da sati daya.

Papy kuwa tun daga wannan rana aka kasa gane kan shi, farincikin gaba daya ya dauke wa ruhin shi, cikakken abinci ma ya dena ci.


Jamal tun da mom ta haihu kullum tana hospital ita ke kula da mom da jarirai bata wani nu na wani abu.
Ammy da Mamy ma kullum suke zuwa sai bayan magari ba su Jawad suke dau ko su.

Jawad ba karamin kudi ya kashe ba wajen siyawa bebys kayan, kowa ya yaba kokarin shi da karamar shi.

Duk da suma su jalil da su Ammy da Mamy ba,a barsu a baya ba.


Yaya Yusuf ma sosai yake zuwa wajen yaran, a yan zu ya fahimci yana san Jamla sai dai tayi masa ni sa ya sani ni.

Satin mom ɗaya a hospital din aka sallame su, suka koma gidan su dake sharad'a.
Tare da Jamla dan har yanzu Ammy bata ce komi a kanta ba.


******
Farouk shi ma ya zo gidan aka faɗa masa komi ya yi matukar farincikin kwanan shi 5 a gidan sannan suka koma Kaduna shima mom aka bar Fatima a gidan dan yan zu tana da d'aki ita da jalil a gidan.


A yanzu Fatima ba tada Aminiyar da ta kai jalila suna mugun kaunar junan su bata barin dakin sai taga yaya jalil ya shigo sbd wani irin kunyar shi takeji a cikin su.


Ita kuwa Jawahir koda yaushe tana wajen mamyn ta sbd sosai take san mahaifiyar ta ta.

Kuma a wannan zaman da takeyi da Mamy tsakuwa mai karfi ta shiga tsakanin ta da Jawad, ita kan ta Mamy har mamakin lamarin na su take, saboda yadda Jawad ke wa jawahir da kuma nuna mata kulawa da tausaya wa .
Jalilah yar gidan su ce a hannun Ammyn shi ta girma amma baya nu na mata soyayya haka, duk da jawahir yarin ya ce mai biyayya.

Shi kam Jamal ba shi da aiki kullum yana hanyar sharad'a wajen Jamla, dan tare suke rai nan su. Ayyan da Ayyana sosai suke nuna masu kauna. Mom ta ce gaskiya suke zasu yi maku zaman d'aki, Dad kuwa tuni ya dena jin kunyar sa ya saki jikin sa da lamarin Jawad din.

*Bayan watanni biyu*

Tuni kowa ya koma kan aikin shi amma har yanzu su Jamal basu koma Kaduna ba sbd papy ya hana, Ammy kuwa daga sun Farah magana sai kuka shiya sa ma suka hakura da maganar.

Inna da Babba wani madaidaicin gida dake kusa dasu papy ya basu kyau ta suka ci-gaba da rayuwar su mai daɗi kuma kullum su Jamal sai sunzo gidan tunda harda d'akin su a gidan. ina tuni rayuwa tayi masu dad'i komi ya zama Tarihi.



******
Papy kuwa kullum a zuwa kotu yake akan maganar papa amma har tsawon wannan lokaci bai taɓa samun ganin shi ba.
Da aka samu wani Brister ya tsaya musu, haka aka ragewa papa shekaru tare da karawa papa wasu kudade ya ce yaji ya gani.

Daga haka dai aka bar shi zaiyi shekara ɗaya.

*Bayan kwana biyu*

Yau aka bawa papy damar ganin papa dan haka da wuri ya shiga gidan yarin cikin farinciki ganin 'yan uwa na shi. Ko da aka fito masa dashi jikin shi har rawa yake yi ya karasa gaban shi ya rushe da kuka sbd ganin yadda papa ya koma, papa ya yi ba'ki ya rame kamar mai wata cuta.
Ga wani gashi da ya yi yawa a jikin shi kasan ce war su masu jawan suma.
Haka shi papa ya rungume papy suna koku sai da sukayi mai isar su, sannan ya shiga ba shi hakuri da naiman yafiyar shi yana ba komai, a haka azo akace lokacin ya yi zai koma kuma sai wani lokaci.
Papy yana kuka haka ya bar dan uwan nashi, shi kuma yana riƙon shi alfarmar idan sun tashi zuwa nan gaba su zu dukkan su.


Koda papy ya koma gida babu wata walwala Ammy ce ta shawo kan shi ya ɗan dawo dai dai daga nan komi ya yi daidai.


Bayan shekara ɗaya
After one years


Abubuwa da dama sun faru a tsakanin waɗan nan shekarun inda su Jamal suka koma ƙasar waje dan cigaba da karatun su irin na Jawad, wato kasuwanci.
Duk da shi Jawad har karatun lpy ya yi kuma ya yi suna akan hakan ma.


Fatima sun koma Dubai ita da jalil yana karatun sa duk da ita ya hana ta. Sai dai har zuwa wannan lokaci Fatima ko B'ari bata taɓa yi ba.
Kullum suna addu'ar samu sbd duk kan nun su masu san yara ne.

A yanzu duk wanda ya kalli Fatima yasan tana hutawa tayi kiba tayi haske sosai. Ga kuma wata kauna da soyayya da Su Ammy da Mamy da papy kan shi suke nuna mata.
A yan zu sun koma kano da zama ma gaba ɗaya.

A yau ne su Jamal suka samu hutun watan ni huɗu a makaranta dan haka gobe shida Jamal da jalil da Fatima zasu koma gida.

Washe gari karfe 11:00 am suka sauka Jawad ne da jawahir suka zo daukan su, kai tsaye gidan papy suka wuce suka huta kafin da yamma suka wuce gidan su.

Fatima suna ta hira da Aminiyar ta Jalil wadda ba,a taɓa jin tsakanin su.

*Bayan sati ɗaya*

Jawad ne da Jamal suka zo gidan Jalil a zaune suke suna hira hada Fatima saboda suma suna kaunar ta kuma suna ganin girman ta duk da yarin ya ce karama.


"Jawad Bebyn Jalil dama haka su ke ce mata.
"Ta ce na,am yaya Jawad".

" Kina ganin babu matsala ni da Jamal idan muka yiwa papy maganar auran mu da su Jawahir, sbd kinga papa ake jirah kuma papa shiru gwara muyi auren mu sbd gaskiya mu a shirye muke wata biyu muke so a saka".

" Dariya Fatima ta yi tace hakan ya yi babu matsala koni ma ai zanyi farincikin hakan tun kana nima zaman kad'aici ya ishe ni idan 'yar uwa ta ta zo."
Duk ka suka ware ido suna kallon ta da mamaki.

"Jawad mai me kike nufi? Kina nufin a gidan nan zamu zauna?".

"A'a ina nufin idan yar uwa ta tazo mana".

"Au jalil aure zaka yi bamu sa ni ba".

"A'a wllh ni ma bani da masaniyar hakan."

"Fatima yaya Jawad zaka auri jawahir, yaya Jamal zai aure Jamla. shi kenan ita my dear Jalila ba zatayi aure ba? To ita ma tare za,ayi zata auri my love."

Gaba ɗaya ji sukayi jikin su ya yi wani mugun sanya, a kuma ɓangaren Jawad ya yi farincikin amma bazai nuna hakan ba.

"A'a bebyn Jalil ba za,ayi haka ba ta ce ai kuwa haka za,ayi.

Jalil ya yi shiru ya kasa magana ya ce wato ni bani da zaɓi na sai abun da kullum aka zab'a mun.
Amma bazai iyya yiwa Fatima hakan ba sbd ita din mace ta gari ce.

Haka sukai ta bata bakin kartayi haka ta ce anyi ma. Daga karshe suka mata sallah ma suka tafi jiki ba nauyi.


Suna fita jalil ya juyo ya ce wannan zaɓin ki ne amma ni bazan wa matata kishi ya ba. Ya shige ya barta a falon tana murmushi.

Shin jalil zai Amin ce da wannan haɗin a karo na biyu?




✍️✍️✍️💥💥💥
*GAYYA CE!*




*Written by*

*Fatima alaramma lafazi*
*(Falaramma)*



https://youtube.com/@fatimaalaramma?si=v_EK6JyH_nkqroPZ


*Sadaukar kar wane ga iyaye na da 'yan uwa na 'yayan Alaramma baki d'aya ina alfahari da su*



💖✨✨✨💞💋💋

Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina rukun Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane zasu amfana dashi wannan kenan.



💥💥💥

Wannan labarin na musamman ne ba gama garin labari bane, GAYYA CE! kuna ji kun San abun sai Wanda ya karan ta, labarin ban dariya da kuma soyayya, tsan tsar cin amana da kuma Butulci, San zuciya da kuma hassada, duk acikin book din GAYYA CE! kunaji kun San ba karya littafin, ina alfahari da ku ges nagode.




PG 2️⃣ 9️⃣💥3️⃣0️⃣


Fatima ta dad'e a wajen tana tuna ni kafin daga bisani ta meke ta bishi dakin shi.
A kwance ta same shi ya daga kan shi sama da alama ya yi nisa a tuna nin da ya keyi, a hankali ta zauna gyefen shi sannan ta jawo hannun shi.
Ya kuwa d'ago da kan shi suka haɗa ido sai ya yi kasa da idon shi fuska ba bu annuri.

"A hankali ta kama hannun shi tana murzama cikin wani rin salo da wata kallar murya Fatima ta fara magana" my dear Husband ta kira sunan shi ya dago yana kallan ta alamar yana bi bata re da ya ce komi ba.
Idan Allah ka hauri Jalila wallah mutuniyar kirkice ga addini da san 'yan uwa.
Yan zu ka duba kaga ya kamata su yaya Jamal su jewa papa da wannan maganar ba yan ita yarsa bata samu ba, kai ne mijin jalila my dear kawai Ubangijin ya saka ni a tsakanin ku ne amma kai ne wanda Allah ya bata in sha Allah.

Kasan yadda papa ke san beby wllh hakan da zakayi zai karawa papy da Ammy kaunarka.
Kuma ka duba kaga ko acikin su sun fisan ka kuwa soyayyar da suke maka ya kasa boyuwa kuma suna yin hakane sbd kai din mai biyayya ne da nuna masu kauna.
My dear dalilin san da su Ammy ke maka ne yake tabbani, ko da basa san abu na saka baki a ciki sun hakura da lamarin yadda na faɗa haka zasu yi haka ta dinga bashi baki tana masa wani irin abu da hannu ta a jikin shi wanda hakan ya kashe masa jiki sosai ya rungumo ta kawai a jikin shi. Murya a sanyaye ta ce dan Allah kayimin wannan Alfarmar my dear.

Kasa bata amsa ya yi dan tuni ya faɗa wani shafin ita kuma tana taya shi ya yin da take dad'a rikita shi.

Cikin wata irin murya mai cike da galaba ita da lamarin da take masa ya ce "na amince da batun ki my wife.
Bai iyya furta koda uffan daga haka ba ya faɗa cikin salon matar tasa.



***** ** Da yamma ta shirya ita da jalil suka hufi gidan papy tayi masa
End Ads