x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 10 - GAYYA CE

  • 27001 words
  • 30000 words
  • Out of 37291 words

Category: Love Stories

Views 82

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
karah faɗa murmushi sa ya ce kace 'yata ce matsu kusa da ni 'yata fadimatu Allah ya maki albarka.


Jawad ya shiga cikin ya barsu da papy dan papy mutum ne mai san muta ne jalil ne kuma ya yi irin halin shi kaf cikin 'yayan na shi.


Haka dai sauran 'yan gidan suka shigo falon gaban Fatima ya sake bugawa sbd ganin su Jamal ɗin su uku gashi sai murmushi suke sakar masu a tare.

Ammy ta rungume Fatima da mom tana ta gaida ta, ta na masu sannu da zuwa sannan ta shiga da su daki dan basu abubuwan tabbawa.


Su Jawad da Jamal da jalil suka zo suka gaida mom sannan suka tafi, Jalil ya zauna gyefe yana magana da matar sa.


Ammy ce da kanta ta zo ta masu baya ni sannan ta kai su wani daki dan su huta.


Sai misalin ƙarfe 1:30 daidai su Dad suka sauka, a kan idon papa tuni ya rungumo 'yayan shi yana ta masifar shi, ya na shiga falon ya dinga kiran jalila kizo ga 'yan uwa ki, wanda aka rabaki da su tun yarah.


Ita nan ta zo ta rike su suna ta kuka da jin tausayi junan su.


Bayan komi ya lafa aka yiwa kowa baya ni sannan Dad da papa suka ce duk basu yadda ba, dan haka suka ce kotu zasu kai, sun da har abun nasu yakai musayar yawu da fad'awa junan su bakakin magan ganu.


Ba wani bata lokaci a ka shigar da karah kotu, cikin gaggawa.

Aka basu ranar Monday domin Farah shari,a.

Daga nan Dad ya yi gidan shi da 'yarsa. Wanda ita ma ta kasa juya masa baya, tabbas tana jin tausayi Dad din ta in dai ya kasance ba shine mahaifin ta ba, sbd ya dauki buri na duniya ya daura a kan ta.

Su kuma su inna ba wani abu da suka ce dan zan cen na manya ne.

Duk da Jamal ya samu Babba ya ce kadda su lamun ce ya ce shima yarsa ce.

Kuma su a gidan aka basu guri suka zauna.


Inna kuwa ta lamun ce da su Jamal ba ya'yan ta bane, sbd daga zarar ka kalli papy kasan shine mahaifin su ko shakka babu.
Amma abu guda daya daya ke bata mamaki shi ne to ina ɗan da ta haifa, ina cikin da taje Hospital da shi?.


Ta lamun ce sbd ta fahimci shi papy mutum ne mai sauƙin kai da hakuri. Ko da wannan abun ya faru, ce mata yake inna karki damu ko a yanzu 'yayan ki ne su Jamal haihuwa su kawai mukayi amma komi kune.
Ubangijin ya saka maku da mafificin Alkairi daniya da lahira, shida Ammy sun rasa ina zasu saka inna.

*Mamy*

Lokacin da ta dora ida nun ta kan su Jamal ta tabbatar da waɗan 'yayan ta ne ko ba,a faɗa ba.

Sosai su jawahir da jamla suka zuba mata ido suna kallon ta ya yin da ita Mamy tayi ƙasa da kanta ta fashe da wani marayan kuka mai taɓa zuciya.

Su jawahir da jamla ne su karah sa gaban ta suka rungume ta suna lallashin ta basu taɓa jin wani dad'i da nutsuwa ba irin na yau da suke jikin mahaifiyar su.
Take suka Farah bata hakuri suna lallashin ta har tayi shi, jawahir ta kwanta a jikin ta tanajin wani dad'i na ziyar tatta ta ko inna.

Ko bayan da aka gaba jawabi bin Mamy sukayi gidan ta suka dinga mata hira suna kwantar mata da hankali.
Har daga bisani suka dawo gidan Ammy.

Tun da wannan abu ya faru Mamy ta kasa ce wa komi, duk wanda ya kalli mamy ya kalli su jawahir kasan mahaifiyar su ce.

Amma ita duk wannan abun daya faru bata rasa nasaba da papa.
Sbd papa mugun mutum ne Mamy ita kadai ce tasan zahirin halin sa sai Jawad, kuma tayi shiru ne badan komi ba sbd yadda taga papa ya daga hankali shi, ita ke bawa su Dad hakuri ma, kuma ita ce ta cewa Jamla tabi Dad din ta, da Amincewar Mamy tayi komi.
Duk da a zahiri gaskiya Mamy tasan waɗan nan jinin ta ne daka jikin ta suka fito.


*B'an garen Dad*

Koda su Jamal suka koma gida su dake garin kano, Dad cikin tashin hankali ya wuce gidan wanshi ya sanar da shi halin da ake cin. Sosai Abban Yusuf ya jinjina lamari amma ya cewa Dad zan baka wata shawara karkayi faɗa da wannan family ɗin ba zaka iyya Shari'a da suba.
Amma fafur Dad ya ce sai yayi haka ya barshi tare da musu addu'a.
Sun dai dai ta lamarin shi da Jamla in da su ka kifad'awa mom gaskiya sbd a yan zu ta shiga watan haihuwar ta ba,asan wata damuwa a tattare da ita.

Kuma Jamla tana ta kwantar wa da Dad hankali harya sa mu ya nutsu sosai.

Su kuwa su Fatima da jalil wata sabuwar babin soyayya suka bude, inda kuma ko umm ta ce sai Mamy ta tambaye ta mai take so.
Hatta mom Fatima mamakin yadda Ammy ke kaunar Fatima take. Ga kuma kullum idan suka fito falo suka haɗu da papy ya dinga wa mom godiya kenan.
Har kunya kamata take yi sbd godiya da papy da Ammy ke mata, kuma tuni ta kirah Farouk ya sanar da shi komi yace zai dawo nan da kwana biyu.

*Bayan kwana biyu*
An shiga kotu, an Farah tattaunawa akan komi.

Inda kowa yake kawo hujjojin shi, ma su kwari.

Gidan Radio da TV da jaridu da newsperper sun naɗa tuni abu ya farah yawo a duniya.


*America*

Doctor Adam ne ke kwance jikin na shi da sauki sosai yan zu an tabbatar da kansa ce ta kama shi kuma taci ƙarfin shi sosai.

Ahmad ne ya shigo d'akin ya kuma TV da ke mak'ale A ban gon dakin.

Nan da nan suka Farah kallan labarin duniya a nan ne aka sako labaran su Jamal.
Toni Doctor ya tashi zau ne jiki na wara, ya ke kallan Shari'ar ya ce tabbas haka ne sune komi ya bayya na Alhmdllh yan zu lokacin koma wa gida Nageria ya yi.


"Ya juyo ya kalli Ahmad da Muhammad ya ce, yau she ne zamu koma gida".

" Ahmad Ya ce nan da wata daya".

"Kaji ka samu doctor Mubeen ka faɗa masa ina so na koma Nageria nan da sati daya".

"Saboda me Abe".

"Ayi abin da na ce kawai "

*KANO*

Nan kutu ta ce nan ba su nan da karshen wata su je su kawo shedun su. Na komi, daga nan kowa ya shiga bincike asibiti da akayi komi, dan bincika wa.

Kowa kuwa law yan shi ya je kan bayan nin ba,a samu na kowa ba, amma tabbas an samu shedar shigar su Hospital, amma an rasa fayal din su.

Haka nan ma aka dawo koto ba tare da wasu kwararan sheduna daga nan kota ta ce daga zanman karshe na wata mai kama wa in dai har ba,a kawo man yan shedu ba tom zasu kori karar kowa ya riƙe ɗan dake hanun shi.

Duk wannan gumurzu da akeyi akan idon Doctor kuma yana kallon komi.
Kuma nan da kwana biyu zai dawo kamar yadda ya tsara.

Kwana biyu da haka kuwa doctor ya dawo gida Nageria ya shiga haɗa komi na shi, da duk wani baya nai da ya sani, sannan ya zauna jiran ranar da za,a shiga kotu.


Haka kuwa ranar 1 ga watan July suka shiga kotun, nan ma aka Farah fafatawa daga nan, Alkali ya ce wannan bai gamshe shi ba yana gaf da korar Shari,ar Doctor ya shigo.
" ya ce ya mai girma mai tsari,a ina da magana".
An baka umar ni.


GAYYA CE!
*Free page*

*Written by*

*Fatima alaramma lafazi*
*(Falaramma)*



https://youtube.com/@fatimaalaramma?si=v_EK6JyH_nkqroPZ


*Sadaukar



💖✨✨✨💞💋💋

Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina rukun Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane zasu amfana dashi wannan kenan.



✨✨✨

Wannan labarin na musamman ne ba gama garin labari bane, GAYYA CE! kuna ji kun San abun sai Wanda ya karan ta, labarin ban dariya da kuma soyayya, tsan tsar cin amana da kuma Butulci, San zuciya da kuma hassada, duk acikin book din GAYYA CE! kunaji kun San ba karya littafin, ina alfahari da ku ges nagode.





PG 2️⃣5️⃣&2️⃣6️⃣


Guri ya nema ya zauna saka makon ba shida karfin tsayiwar, 'ya'yan shi da suke bayan shi rike da jakun kuna a hannayen su suka miƙa masa.

Papa ne ya kurah masa ido yana kallon shi amma ya manta a inda ya san shi.

Doctor ne ya taso zuwa gaban papa wanda a yan zu baya kasa banbance su, sbd baya manta wa da mummunar fuskar papa, wadda ta zama bak'ar razana a gare shi.
Su kuwa su Jamal kallan doctor suke da mamaki sun san shi farin sani amma yan zu kima nin shekara 9 kenan raban su da shi.

"Doctor ya dafa Jawad ya ce yaya Jawad, ya dafa Jamal ya ce mai bin Jawad, ya dafa jalil, ya ce auta jalil, wannan shene karamin ku".
Gaba ɗaya suka zuba ido suna kallon shi.

Nan take jikin papa ya farah rawa dan sai yan zu ya fahimci wannan wane, tabbas kashin shi ya bushe, tabbas yau karya ta kare, wani gumi ya dinga keyto masa yana saka hanun shi yana gogeshi, shi kuma Doctor ya yi murmushi.

Ya kara so gaban su jawahir, ya ce yaya Jawahir, mai bin ta Jamla sai auta jalila Ubangijin ya yiwa rayuwa albarka.

Ya mai girma mai shari'a waɗan nan 'yayan jawahir da jamla da jalila duk 'yayan Al Hassan ne.
Ga sheda ta kamar haka, ya mika musu wani fayal aka shiga duba shi.


Brister Rabi,a ce mai kare Dad ta ce ina da tambayar idan ba damuwa.

Kotu ta baki dama.


Nan ta shiga jerawa Doctor Adam tambayoyi yana bata amsa.

Kafin daga bisa ni ya ce zan bukaci wasu mutane a nan idan kotu ta bani dama.

Aka ce an bashi.


"Ina san ganin Al Hassan da Al Hussaini Dad da kuma mama zulai, da Babba Ibrahim, sai Hajiya zainab, da kuma su Jamal da su Jamal.

Kaga kuwa duk suka hallara a gaban shi, amma ban da mama ai zulai saka makon Allah ya mata rasuwa.


Nan ma ya karah bude wata jakar ya mikawa koto fayal sannan ya ciro wata waya da A T M .

*Asalin Labari*

Wata ranar juma'a bayan an sako daga masallaci juma,a misalin ƙarfe 4:30 na shiga hospital dan duba marasa lafiya kamar yadda na saba.
Ina shiga asibiti na Farah zuba marasa lpy, daga karshe na fito wajen dan hutawa, ina fitowa naga Alhaji Hussaini ya kawo mai dakin shi zata haihu saka makon a wannan Hospital din ta ke awan cikin jikin ta.
Nan danan na saka aka shiga da ita tana sha wahala sosai dan lokaci har ta Farah fita hayyacin ta ga kuma haihuwa da saura.
Mun dade a kan ta muna duba ta amma shiru daga nan na yanke shawarar zan mata aiki.

Sai dai ina fitowa sai na gaban su bakin officer din su biyu na kasa gane wanene wanda matar tasa bata da lpy.
Na k'arasa in da suke muka gaisa Sannan na faɗa mata abun da yake faruwa cikin tashin hankali suka amince da baton aikin suka saka hannu a nan ne na fahimci Al Hussaini shi ne karami kuma shine matar shi zata haihu, sannan na koma cikin dan Farah shirin aikin.

Bayan zamu shiga ne sai nazo na ce kuyi ma mana addu'a nasara zamu shiga yanzu. Al Hussaini ya ce Doctor yan zu haka an bugu min waya governer yana kiran zan cike wata ta kardar wata kwangila da mukayi da shi, kuma yanzu haka saura minti 40 ya tashi kuma dole sai naje, dan Allah ga ɗan uwan na nan da matarsa zasu zo, ka kulamin da ita kafin na dawo kaji, Ubangijin ya baku nasarah.

Sannan ya ce bari naje sai na dawo.

Ni kuma na koma d'aki dan cigaba da aikina.

Da ma ni da doctor Aminu ne babban Amini na kafin mukai ga Farah aikin ma nan take kai ya tahu, haka mukayi k'ok'ari ta haifi 'yayan ta kyawawa maza yan uku, sai dai ita kan ta batasan abun da ta haifa ba tayi doguwar suma dan haka doctor Aminu ya shiga kula da ita nikuma na shiga duba su, sbd lokacin Babba baiyi kuka ba, nan ta fama sannan na samu ya yi kukan.

Haka na fi to fuskata dauke da murmushi na samu Al Hassan na faɗa masa sannan na ce ya shigo yaga yaran. Shima fuskar sa dauke da farinciki muka shiga yaga yaran, sakamon an canzawa mahaifiyar ta su d'aki, sai da Al Hassan yana ganin 'yayan nan wani ciwo ya shige shi na hassada.

Kallo na ya yi fuska dauke da damuwa ya ce na bashi number account d'ina. Nan take na bashi ciki da farincikin, kawai sai naga wasu mugayan kudadde naira million 100 na gani.
Nan take na zaro ido yana faɗa masa abun da ya faru.

"Doctor Adam ina son waɗan nan yaran zaka dauki guda biyu ka kashe su. Sai kuma kabar guda ɗaya, dan shima na san bazai gaggare ni ba".

Doctor Adam ya zaro ido cikin tashin hankali ya ce wannan wacce kallar magana ce gaskiya kayi hakuri ba zan iyya aikata wannan abun ba.

"Ai ba shawarka nake nema ba doctor Adam, wannan abu guda biyu ne, ko dai ka kashe yaran nan ko na kashe ka da kai da 'yayan ka.

In dai bazaka iyya ba to ni zan iyya kashe ka da kai da iyalan ka.

Nan take ya dinga mun wasu mugayen bara zana.

Daga baya na Amin ce da baton sa, na dauki Jamal da jalil na fita da su, sai na bar musu babban sbd shi ne ba shi da cikakkiyar lafiya.

Ina fita na hango wata mata na ta suma sai zubar da jini ta keyi na k'araso ina tambayar Abunda ya same ta.
Aka faɗan basu da kuɗi ne gashi ba Sudan kudi a hannun su. Na ce su tafi sun ki tafi shi ne matar ta fadi a nan ta suma, mijin ta ya ce bari yaje ya samu kuɗin.

Nan take na ce a ɗauke ta a kai ta daki a fula da lafiyar ta, nan ta haihu da namiji amma dan saboda wahalar data sha dan ya rasu.

Nan take ya dauki su Jamal ya saka mata sannan ya fice.


Ya koma wajen su papa. Suka gama shirya komi sannan ya koma a lokacin har sun dawo, sunata farinci amma har lokacin ita bata farfaɗo ba.

Haka ya dinga bibiyata da abubuwa da ban da ban.

Har aka sallame su daga asibiti, sannan ya rabu dani, tare da mun kashe di mai tsauri.


Ni kuma haka na dinga zuwa wajen mama zulai ina ganin su Jamal ina kai masu tallafi saboda su din marasa karfi ne, na kuma nuna mata ina san yaran ne ina san yan biyu.

Papa wani irin rawa jikin shi yake yi ya kasa furta ko da alifun.

Ita kuma Ammy da Mamy da mom sai kuka suke yi, Babbama jiki shi duk ya yi sanyi, ya yin da papy gaba ɗaya ya kasa magana ƙwaƙwalwa sa ta tsaya cak.

Ni kuma bayan shekara ɗaya da hakan na can za layikan waya ta sannan na yi ritaya a aiki na koma, Faris da zama.


*Bayan shekaru goma da faruwar haka*

Cikin ikon Allah wata rana na zo Nageria gaisuwa yaya ta matar Dad, na yi wajen sati biyu a garin muna karbar makoki har akayi sadakar bakwai.

Ranar Monday sai kuwa na shirya dan zuwa tsohun hospital din da nayi aiki a cikin shi.

Na dauki hanyar kafin na karasa Dad ya kira ni ya sanar da ni matar shi ta Farah na Kufa nace su zo Teema clinic hospital mu hadu a can.

Da sauri kuwa na kara sa asibiti aka shiga gaida ni da bani girma wanyan likitoci da Abokai na duk sukayi farincikin gani na.

Daga nan na shiga officer din doctor Aminu sai aka ce min yana lebour room, dan haka kai tsaye na bishi ina shiga suka gaisa ya kuma ce min matar wannan mutumin ce fa zata haihuwa amma sai anyi mata aiki na ce to babu matsah bari na saka kayi ayi aikin.

Ina fita na Hadu da Al Hussaini shida dan shi Jawad a baƙin officer din muka gaisa da shi da ɗan sa nan fa ya shiga tambaya ta lafiyar matar dan uwan na shi nace in sha Allah zata huihu lpy na kuma tambaye shi Al Hassan ya ce yaje waje ne zai shigo da su Ammy. Hakan kuwa ba karamin dadi ya mun ba sannan na shige abun na, fuska dauke da farinci.

Sbd mu dama a wannan Hospital din muna da tsari, idan akai wa mace sikaini ba,a taɓa faɗa mata abun da zata haifa ko abun da yake cikin.

Mun shirya aka yima wannan baiwar Allah Tiyata aka ciro mata yar mata 'yan kuma.

Nayi farincikin sannan na fadawa doctor Aminu kudiri na yaƙi
End Ads