kenan Allah ya maku Albarka" suka amsa da Amin tare suka difa duk kanin su a mota ɗaya inda suke ta tattaunawa da fafi akan agreement din da sukayi da masu kwangilar, sosai abun ya ƙarah burge papa tare da yabawa kwazan su, bayan sun sauka office ne kuma kowan ne yayi ɓangaren sa.
"Jamal wai mai yasa wannan yarin yar jamlah kullum fuska ɗauke da liƙaf sai ka ce wata tsohuwar munafuka" "Ummmm jalil wai yau she ka koma haka ne ban sani ba ina ruwanka da yarin yar muta ne ni wllh ma ta burge ni da take yin haka sbd makaranta ba abun wasa bane," Amma dai ai yakama ta muma mu sani kodan watara na" dallah rufewa mutane baki" cewar jamal, jamal ce ta ƙaraso wajen da sauri ta gaida su kamar yadda ta saba sannan ta shige mutar abunta, yau ma kamar kullum jamal take kallah ta gefen idan ta sosai wannan bawan yake burgeta, ku ma abun da har yau yake bata mamaki guda ɗaya ne ba,aga ne jalil da jamal sbd babu ban banci a tsakanin su amma ita basa taɓa haɗe mata koda kuwa kaya irri ɗaya suka saka, wannan kenann, ku ma jamal shi ne mutum na farko da take ɓata lokaci wajen tuna nin shi komai yasah?
Haka shima ɓan garen jamal din yafi jalil muradin ganin jamlar komai yasa? bawai yana zuwa gidan bane dan ya raka jalil kaita makaranta yana zuwa ne dan ya ganta, sbd ganin nata yana karah masa nutsuwa, Bakin makaran tar suka tsaya amma babu wanda ya ankarah tsakanin jamal da jamlah jalil yayi mangana har yayi shiru yana kallan su can dai ya taɓa ɗan uwan nashi yace jamal lpy kuwa? sai lokacin ya dawo tuna nin shi yace lpy lau tare da haɗe rai, ita kuwa jamlah wannnan maganar tashi ce ta dawu mata da tunanin ta, ta buɗe ƙofar jiki a sanyaye ta fito Suraiyya ce ƙawar ta wadda ta jima take jiran fitowar ta hangota kuwa tana fitowa ta nufu surayyan har ta tafi taji an ce baki jiba cikin tsananin mamakin wanda yayi maganar ta juyo tana kallan su jamal ne yace kikulah kinji, tsabar mamaki kasa magana tayi sai kawai ta ɗaga mashi kai. tare da tafi ya a bunta wannan kenan.
Me kuke ganin zai kasan ce a wannan labarin mai suna gayya ce.
*Sadaukar kar wane ga Sadiq Abubakar CEO din lafazi Allah ya Kara masa lpy, da nisan kwana mai albarka, godiya ta musamman*
💖✨✨✨💞💋💋
Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina rukun Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane zasu amfana dashi wannan kenan.
✨✨✨
Wannan labarin na musamman ne ba gama garin labari bane, GAYYA CE! kuna ji kun San abun sai Wanda ya karan ta, labarin ban dariya da kuma soyayya, tsan tsar cin amana da kuma Butulci, San zuciya da kuma hassada, duk acikin book din GAYYA CE! kunaji kun San ba karya littafin, ina alfahari da ku ges nagode.
Pg 9- 10
Alhmdllh su inna zaman lafiya sosai suke da Baba yana iya bakin kokarin shi wajen kulawar da su, ɓangaren su Jamal ma kuwa ba shida wata matsala. dan sosai suke ganin girman shi da darajar shi.
Jawahir a zahirin gaskiya bata wani kukan maraici sbd inna bata rage ta da komi na rayuwa ba, bata da wata matsala dan ko suyar Awarar ma ta dena.
"Jamal! Kasan wani abu kuwa" a'a sai ka faɗa Jamal ya bawa Jalil Amsa.
"Na rasa mai yasa jamlah maganar ta ke matukar kama da ta jawahir. wllh wani lokaci idan tayi magana har gabana faduwa ya keyi.
"Ni kuma na rasa mai ne matsalar ka da yarin yar nan da har ka saka mata ido haka". Ban san sanda ka lallace ba Jalil.
Allah Jamal bawai haka bane kawai nidai ina muradin ganin yarin-yar nan.
"Jamal! Rai a bace yake magana Jalil in dai magana ce kan yarin- yar nan karka karah yimin ita, na barka lpy.
Cikin mamaki da al'ajabi Jalil ke kallan dan uwan na shi. Anya kuwa shi ne? to mai yake damun shi?. Ko dai santa ya keyi?.
Ya rasa mai bashi wannan Amsar dan haka ya yi shiru abun shi.
KANO
Jamal ne ke ta sauri zuwa officer din Tahir.
Sallah.
Kawai ya yi.
ba tare da izinin ba ya shiga duba computer din shi. Rai a matukar bace, sbd ya rasa daga ina matsala take.
Tahir! Ne ya fito cikin daga Toilet ya xubawa ogan na shi ido.
ko bai faɗa ba yasan abun da ya ke dubawa, dan ko bai zuba shi zai je.
"Tahir! mai nake gani haka a cikin wannan Company nin wane ne ya zari wannan kuɗin haka". "Wallahi Jawad yadda ka gani nima haka na gani, kuma yan xu nima nake shirun zuwa na sanar ma", amma wani hanzari ba gudu ba kasan wane ya ciri wannan kuɗin? Papy ne ya cire su ta wani sabon account da ya buɗe yan zun nan na gano haka.
Amma bari na nuna maka, take ya nuna mashi rai shi ya kuma bacci ya kasa furta ko uffan kai wai ya fuce.
Kai tsaye officer din papa ya wuce rai bace.
Sallah ya yi ya bashi damar shigowa, gaida shi ya yi.
Ya amsa. Tare da tambayar sa ko lafiya ya ganshi haka. "papa kayi hakuri da abinda zan faɗa maka, "bakomi ina jinka"
Papa mai yasa papy baya sanka? Mai yasa kullum muradin shi ya dinga tuzar ta ka? Mai yasa baya san ganin ci-gabanka? Mai yasa kullum muradin shi ya tarwa tsaka?
Kafin ya kuma wata maganar tuni papa ya da ka mashi wata gigitacciyar tsawa. Ya ishe ka haka Jawad ka she baka da mutum ci? Ni xaka kallah ka dinga zagin dan uwa na a gaba na.
Na san abun da kake san sanar dani Jawad ka kiya ye dan zan iyya komi sbd dan uwa na, kuma ko Company nan zai tarwatse babu ruwan ka da shi kayi aikin ka, ko kuma ka koma wani Company nin.
Jawad ya shiga bawa mahaifin na shi hakuri tare da fice wa ya barshi.
Yau da wuri suka shirya dan fita kai Jamal makaran. A bakin comput din gidan suka tadda ta da alama su take jiran, tayi shigar ta kamar yadda ta saba.
Mota suka dauka suka fito da ita.
Dai dai lokacin kuma dad ɗin ta ya fito ya ce dan Allah Jalil ka kai Jamal makaranta Jalil xamu fita tare zai kai ne airport kuma ina sauri ne kaga sai ya dawo da mutar.
" Tom shikenn ba damuwa dad tare da gaida shi".
Motar ya shiga. Ita ma tabude gaban motar ta shiga da mamaki ya ke kallan ta amma bai yi magana ba.
Suka dauki hanya "dago wa tayi ta kalle shi a nutse sannan ta ce yaya Jamal ina kwana. " kallan ta yayi kafin ya ce kin tashi lpy, lpy kalau Alhmdllh yaya Jamal.
Daga wannan babu wanda ya kuma ce wa kowa komi har suka kusa kara so wa makarantar. Wata iska ce ta taso da guguwa wadda gaba daya gari yayi duk abun ka da lokacin damuna. Jamla cikin tsoro da gigita ta fada jikin Jamal ta saka kanta a kirjin shi jikin ta na mugun rawa, to ni likaf din dake fuskantar ta ya fice ya kama gaban shi. Shi ma tsaida muta ya yi sakamakon baya ganin hanya.
Cikin ikon Allah iskar ta Farah lafawa. Alhmdllh gari ya farah haske. Jamal ya dago idon shi ya sauke su kan jamla data rungume shi ta kuma saka fuskantar ta a kirjin shi. Kasa mata magana ya yi ko ya ce ta dago har gari ya yi haske kowa ya farah cigaba da tafiya.
Cike da sanyi murya ya farah magana, kina so ki makarah ne. Kawai abinda ya ce mata kenan.
Cike da jin kunyarsa ta dago kanta daga kirjin shi, cikin rudewa ya ke kallan ta amma ya kasa furta ko uffan, innalillahi,wainna illaihiraju ya kafar maimai tawa cikin zuciyar shi. Ya zuba mata ido sai kallan ta yake yi, tuni ida nun shi sun canza da bari zuwa jah, ya kuma kasa furta ko da alifun.
Cikin nutsuwa ta dai-dai ta zamanta sannan ta kalli hanya.
"Yaya Jamal! ta kirah sunan shi dan Allah kayi hakuri kaji.
Bai iyya furta mata ko uffan ba ya yi karfi halin cigaba da tafiya a bakin school din su ya ajeta.
Jiki ba nauyi ta fita sbd ta tsorata da yanayin nashi a tuna nin ta sbd ta rungume shi ne.
Har ta shiga makarantar ida nun shi kanta, tabbas wannan ba jawahir d'un su bace sbd fatan ta ma ba iri ɗaya ba ce amma tabbas suna matukar kama, tabbas akwai wani boyayyen Al,amari a tsakanin su.
Tom ko dai ya tabbata jawahir wannan yar uwar tace, to kuma akai mama ina? .
Shi kaɗai yake kiɗan shi yake rawar shi.
Tun da ya koma parking motar kawai yayi ya kama gaban shi, zuwa gida sbd kan shi da ke mai wani dan karan ciwo wanda da'yar yake bude idon shi.
Ya na shiga gidan kwanciya ya yi wani zazzafan zazzaɓi ya rufe shi wanda jikin shi har rawa yake yi.
Dad ya sauka garin Kano lpy ya dauki hanyar Company su. Ba jimawa suka gama cike-cike da komi sannan aka tura su kan fanin papy dan tabbatar da Agreement din. Shi da Alhaji Ahmed.
" A mota ne Alhaji Ahmed yake sanar da shi kallan karamcin ( J. U.J) company har yake ba shi labarin papa da papy ranar da suka bashi tsoro bai san 'yan biyu ba ne, dad yana ta dariya.
Cikin ikon Allah sun samu tarba ta musamman inda su ka gama tattaunawa akan komi kafin daga bisani papa ya kira Jawad dan shaida masu yadda komi ya kasan ce idan ya amince da hakan. Saka makon yau Bebyn papa bata zo ba.
Ba kuwa wani jimawa ko bata lokaci, ya shigo d'akin bakin shi dauke da Sallah ma.
Dad ne ya dago da sauri dan ganin mai sallah mar idan ba kun nan shi gizo ya masa ba yake jin kamar Muryar Jalil.
Cikin firgice da tsanani mamaki yake kallan Jawad, tabbas wannan Jamal ne babu wani banbanci ko tan ta ma.
Ya mike tsaye jikin na rawa yake kiran sunan shi Jamal, mai ya kawo ka nan kuma
Typing 📲
GAYYA CE!
*Free page*
*Written by*
*Fatima alaramma lafazi*
*(Falaramma)*
*Sadaukar kar wane ga Sadiq Abubakar CEO din lafazi Allah ya Kara masa lpy, da nisan kwana mai albarka, godiya ta musamman*
💖✨✨✨💞💋💋
Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina rukun Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane zasu amfana dashi wannan kenan.
✨✨✨
Wannan labarin na musamman ne ba gama garin labari bane, GAYYA CE! kuna ji kun San abun sai Wanda ya karan ta, labarin ban dariya da kuma soyayya, tsan tsar cin amana da kuma Butulci, San zuciya da kuma hassada, duk acikin book din GAYYA CE! kunaji kun San ba karya littafin, ina alfahari da ku sister's nagode.
Pg 11-12
...............Kallan shi Jawad ya ke cikin nutsuwa ba tare da ya ce mai ko kalah ba. Cikin sanyin Murya ya farah mashi magana, Alhaji ka zauna muyi magana cikin nutsuwa da fahimtar juna.
Haka Dad ya zauna jiki ba kwari sai dai abun har yanzu yana cikin ran shi dan ya kasa saita kan shi. Ya kuma zubawa Jawad ido yana ta mashi Kallan k'urillah dan so yake ya gane wannan ba jamal da gaske bane.
Cikin nutsuwa suka Farah magana inada Dad ke sanar dashi labarin su Jamal, da kuma yadda suke kama.
Bayan sun gama magana ne papa ya ce ba komi ai kowa ne bawa ance kalar shi 7 ce dan haka babu, mamaki.
Shi kuma dad yayi alƙawarin kawo musu su Jamal dan su tabbatar da abin da yake faɗa, dan yaga basu ɗauki zancen da mahimmanci ba. Haka dai suka gama kowa ya kama gaban shi.
Shi kuwa bangaren papy duk jikin shi yayi sanyi da jin wannan mummunan labarin, yana ta addu'a Allah ya sa ba,abinda yake tuna ni bane. Gashi yau tsawon shekaru goma kenan raban shi da doctor Aminu.
............. Jalil ne ya shigo d'akin bakin shi dauke da Sallahma bai karah furta ko uffan ba sbd hango ɗan uwan shi da ya yi cikin wani mawuyacin hali. Da gudu ya karah sa gaban shi yake tan bayar shi mai ke damun sa amma ya kasa magana, fita ya yi ya samu Napep aka dauke shi zuwa wani privet hospital, ba kuwa b'ata lokacin aka shiga dashi.
Kusan 10 minit ba wani labarin.
Ya kai wajen 30minit wani doctor ya fita ya ce ya biyo shi office.
Suka zauna kusan a tare, doctor ya zubawa jalil ido yana kallan shi yana sakar mai murmushi kafin ya farah magana. Jikin na shi da sauki sosai munyi masa injection kuma in sha Allah zai farka nan ba da jumawa ba. Ya kare maganar fuska dauke da murmushi.
Nagode sosai doctor, Amma ina katin magungunan yake, doctor ya nuna mashi takardar gaban shi da hannu, sannan ya ce karka damuna biya komi. Jalil ya kalleshi da mamaki amma kafin ya yi magana ya ce na kasan ce ina matukar san 'yan biyu a rayuwa ta sbd nidin ma 'yan biyu ne lokacin da muka girma d'an uwa ne ya rasu, wannan aikin da nake ma nashi ne nake mashi sbd ina matukar girmama ra,ayin shi idan babu damuwa ina san muzama Abokai ko in ce Aminai, ya kare maganar murya a kausashe.
Tom shikenn babu damuwa Ubangiji ya sa muzama Alkairi ga junan mu na gode sosai fa, ya mike dan fice wa dan hankalin shi na kan ɗan uwan shi.
Doctor faruk ne ya rako shi har d'akin in da sukayi sa,a kuwa ya farka, tare suka Farah jerah masa sannu inda ya dago fuska dauke da murmushi yace ai Alhmdllh naji sauki ma ina ga zamu iyya tafiya dan yasan bawani kuɗi ne a hanun Jalil ba. Doctor ya karah matsowa kusa da shi yace yanzu mai kake ji, ya ce ba komi Alhmdllh, "ma sha Allah Ubangijin ya baka lpy my bro, batun sallah ma kuma ka ajeta dan bazan sallameka yan zu ba sai na tabbatar da samun lafiyar ka.
"Jamal doctor sam bana san zanman hospital din ne fa, doctor ya dafa shi tare da rike hannun shi, dan Allah ka kwantar da hankali ka, Ni she is my brother zan kulah da kai kuma ina san lafiyarka. Haka dai suka cigaba da tattaunawa har Jamal ya yadda da maganar Farouk da kuma abotar su dan ya fahim mutum ne na mutumci kuma ya fahimci d'acin da yake ji na rashin dan uwan na shi.
Jalil ne ya koma gida dan sanar da su inna hankali su yayi matukar tashi inda Jalil ya kwantar masu da hankali sannan suka tahu Hospital din.
Jikin nashi da sauki Alhmdllh suna ta hirah da shi inda minti 15 biyar duk ya na shigowa yaga jikin Jamal ɗin da, ga kuma tsantsar nuna soyayya ga Alhalin nashi.
.............. Alhmdllh an faka kasuwanci mai kyau tsakanin ( J U J ) company, da (M K J) company inda su Dad zasu dawo gida Kaduna.
Inda shi kuma dad ya dawo da kudirin kawo su Jamal dan ganawa.
Da misalin ƙarfe 11:30am.
Dad ya sauka garin Kaduna zuciya cike da faraciki ya dawo gida Kaduna, a airport ya kirah Jalil dan yazo ya dauke shi, yace gashi nan zuwa.
Ba kuwa b'ata lokacin yazo ya dauke shi inda yake faɗa mashi ai Jamal ne bashi da lafiya yau kwana 2 yana kwance a hospital, sosai Dad yaji rashin jin dadin hakan inda ya ce da yamma idan ya huta zai zo duba shi, dai dai nan kuma parking a comput d'in gidan, inda ya raka shi har babban falon gidan sannan ya yi masa sallahma.
B'an garen Jamal kuma sosai yake samun kulawa baga 'yan uwan sa ba baga doctor faruk ba wanda har mom din shi da kanwar su sunzu duba shi, ya kuwa ji daɗin hakan sosai dan kuwa yadda Alkairan su suka zo, inda Fatima kanwar shi take yaba kyauwun shi da kirkisa yaya Farouk yake tsokar bar shi kaga ka bro Jamal Fatima ta faɗa.
Dad be samu damar shigowa wa hospital ba sai washe gari da safe. Yazo yaga jikin na shi da sauki Alhmdllh inda yace zai dawo da yamma in sha Allah shida su jamlah su duba shi. Amma abin da ya bawa Jamal mamaki shi ne yanda dad keta ƙalilan shi ' shi da Jalil kamar yau ya farah ganin su.
Hakan ce kuwa ta kasan ce dan daddare dad ya kawo su suka duba shi sosai mom ke jerah mai sannu sbd ita masifar kaunar su Jawad, yau ma harda abincin ta inda tace kullum za,adinga kawo musu. Sai dai shi Jamal gaba daya hankali shi nakan ya tambaye su jamlah amma ina kunyar dad yake ji.