d鈥檌yar albarka, Mai gidan naki yace idan muka koma zai dakko kwararren likita ya sake duba ki, Tunda nan din kinga likitocin sunce ba gado kuma asibiti ya cika. Sunce kin rigada kin haihu lahia me za鈥檃 zauna a musu. Kina ganin tun dazu suke aikowa mu tafi鈥�
Ciccije lebe kawai take tana dan dafe kasar marar ta. Gwaggo na goye da Habeebullah yanata baccin sa. Hadizalo da su Iya Ramma aminiyar Gwaggo, su suka temakawa Haj Maimunatu ta gyara jikin ta. Aka zura mata hijabi.
Saifuddeen ya dakko shatar mota ta debo su suka koma gida. Yana ta mata sannu. Ita dai dauriya kawai take. Da dare jiki ya kara tsananta. A dole aka kara daukar ta suka nufi babban asibitin cikin birni. Duk likitocin basa nan. Sai nurses su kuma sunata yanga. Suka dura mata ruwa suka bata gado. Ciwo nata cinta tana salati. Haka ta kwana d鈥檃ya tana sallallamin sabon ciwo. Likitocin basu zo kanta ba ganin ai ta haihu wai zazzabi ne kawai. Sai da sukaita roko tukun sannan wani babban likita yazo washegari. Yana dubata yace ai wata haihuwar ce. Kowa ya cika da mamaki. Yabi likitocin da nurses ya zage su tas. Domin da da akwai karar kwana data rasu.
Gashi ta jigata tana ta salati, Can ta janyo surah ta shiga Karantawa tana kuka. Takasa haihuwa da kanta. Daga karshe likita yace mijin yasa hannu ayi aiki a ciro. Saifuddeen nata tsiyayar hawaye haka yasaka hannu aka shiga da Maimunatu dakin tiyata tanata karatun alqur鈥檃ni tana kuka da karfi. Basu dau lokaci sosai ba aka fito da katon jariri.
鈥淚na mahaifin sa, Gashi nan kayi masa huduba, Zamu dan yi masa checkup dan shi bai zo da lapia ba gaskia.鈥�
Hannun Alhaji saifuddeen na rawa ya karbi jaririn yana hawaye. Huduba ya masa yana mai matsa masa ruwan dabinon daya tofa a baki.
鈥淶aku iya ganinta.. Dan zamu mata allura ne. Batada lapia sosai.鈥�
Duk suka dunguma suka shiga cikin dakin. Tana kwance tana hawaye. Bakin ta dauke da karatun qur鈥檃ni tana yi a hankali. saifuddeen ya karasa kusa da ita yana dan nuna mata jaririn.
鈥淢aimunatu nahh! Ashe yan biyu ne. Mun kara samun albarkar wani 鈥榙an namiji. Tsiran su kwana biyu da wuni. Na rad鈥檃 masa MUHAMMAD HAFEZ. HAFEZULLAH!, Hafizin qur鈥檃ni ne Insha Allahu, Saboda haihuwar sa mai abin mamaki ce. Da karatu a bakin ki kikai nakudar sa.. Allah ya raya mana su. HABEEBULLAH DA HAFEZULLAH!鈥�
Jikin ta gaba d鈥檃ya sai ya soma rawa. Tana mika hannunta ya bata. Tana karba ta saki wata kara. Kafin tai wulli dashi gefe. Kowa ya dimauta da ganin abunda ya faru. Likitoci sukai kanta suna bata taimako. Ashe wata sabuwar jijjigar ce. Tasha wahala ainun. Jaririn ma daukar sa akayi aka shiga bashi temako, Babu abunda ya same shi na buguwar da yayi. Sai dai yazo da ciwon zuciya mai tsanani..
鈥�
Furgigit ta farka tana gumi duk kuwa da iskar fankar dake kad鈥檃wa, Ga kuma sanyin ruwan sama.
鈥淕waggo... !Gwaggo鈥�
鈥淣a鈥檃m diyar albarka.鈥�
Gwaggo ta farka da sauri daman batada nauyin bacci kwata kwata.
鈥淕waggo! Ashe yan biyu na haifa? Gwaggo ina Hafez? Hafezullah dana haifa daga baya bayan kwanaki biyu da haihuwar tagwan sa Habeebullah? Gwaggo suna ina? Habeeb da Hafez? Suna ina Gwaggo? Ina saifuddeen? Mahaifin su?鈥�
Gwaggo ta sauke ajiyar zucia tana hamdala.
鈥淟abarine mai tsawo Maimunatu. Shekaru da yawa a talatin kadan ne babu. Sannu ahankali sai yanzu Allah ya ida nufin sa hankalin ki da tunanin ki suke dawowa....鈥�
Wani kuka ne ya kufcewa Maimunatu mai tsuma zuciar duk wanda ya saurara. Haba shi yasa mutane suketa zuwa mata murna. Kuka ta shiga yi sosai harda shessheka. Gwaggo Haule ta mike ta janyo ta jikin ta tana rarrashin ta.
鈥淶an sanar da ke komai... Idan kika kammala tuno duk abubuwan da suka shude diyar albarka. Yanzu kije kiyi alwala kiyi sallar godia ga Allah daya azurta ki da wannan baiwa. Domin ko acikin mutanen duniya masu irin matsalarki da wuya suke warkewa. Likitoci da dama suna mamakin warkewar ki. Sai dai komai na duniya fararre ne kararre ne. Allah bai saukar da ciwo ba sai da yayi maganin sa. Kedin mai karatu ce. Shi yasa ubangiji Allah ya warkar dake... Sannu diyar albarka. Tabbas kinsha jinya.鈥�
Mikewa Maimunatu tayi bayan ta gama goge hawayen ta, Taje ta kama ruwa tayo alwala. Ta shiga sallolin godia ga Allah. Duk yan gidan kowa ya fito jin motsin su gwaggon, Nan Gwaggo Haule ta shiga basu labarin abunda ya faru na kwanciyar yau da Maimunatun tayi.....
****MADRID***
Yana daga kwance bayan yasha maganin ciwon zuciar sa. Bacci na neman daukar sa wayar sa tashiga kara. Ganin me kiran yai saurin dauka. 鈥楤NK鈥� (Baba kano) Gaisawa sukayi sosai. Alhaji saifuddeen nata tambayar jikin sa. Basu wani jima ba sukai sallama. Ba dadewa kuma Habeeb ya kirashi. 鈥楾B鈥� (twin brother)
Dauka yai nan ma suka sake gaisawa dashi bayan wayar da suka yi dazu. Amman wannan karon video call suke ta Skype.
鈥淯hm!Yanzu mukayi waya da Baba ma...鈥�
鈥淵eah yacemin zai kira ka ai... kasha maganin?鈥滺abeeb ya fada yana mai kallon fuskar Hafez ta waya.
鈥淵eah na sha..鈥�
鈥淭oh ya jikin? Allah Kara sauki鈥�
鈥淎amin!! Da sauki鈥�
鈥淭ohm bara na ky鈥檃le ka kayi bacci. A gayda su Aunty.鈥�
鈥淭ohm! Zasu ji, Okay! Goodnight鈥�
Katse kiran yayi. Ya ajiye wayar. Ya dora kansa akan pillow yana lumshe idanun baccin dake fusgar sa..
***Shima Habeebullah a nasa bangaren ya ajiye wayar ahankali yana murmushi. 鈥楾BH鈥� (Twin brother Hafez) Haka yai saving sunan tagwan nasa da shi.
鈥淢ammaa! Allah ya Kara baki lapia, Yasa muna da rabon ganawa da ke. Allah ka cikawa Hafez da ni burin mu na ganin Mamma..! Allah kuma ya kara hada kawunan mu ya toshe duk wata 鈥榖araka da zata taso..鈥�
Cike da farin ciki ya janyo files din gaban sa yana mai dudduba su.....
鈥⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€�
Ni kai na Nana Hafsatu sai dana matse hawayen farin ciki, Allah ya raya mana ku. MUHAMMAD HAFEEZULLAH SAIFUDDEEN IBRAHIM SANDAMU DA MUHAMMAD HABEEBULLAH IBRAHIM SANDAMU...!!! 馃挐馃挐馃敟馃敟馃敟馃敟 YAN GIDA DAYA, YAN BIYU MASU KAMA DAYA, MASU HALI MABAMBAMTA馃馃鉂わ笍鉂わ笍
Tab ruguntsumi 馃Ya zata kaya ne?馃槀馃挃Waye zai hakura.... ?馃檰馃徑鈥嶁檧锔忦煓咅煆解€嶁檧锔廤ohoho馃槀馃槀馃敟
鈥⑩€�
Ba lalle na cigaba da posting kullum kamar yadda na fara ba, Zan dan dinga hutawa kamar na zafafan baya. Ido ya fara matsawa.
Muna godia da kaunar books dinmu da kuke鉂わ笍
*_鈽� AL-茦IBLA_*馃挊
_Na Safiyya Huguma_
*_鈽� MABU茒IN ZUCIYA_*馃挅
_Hafsat Rano_
*_鈽� DALAAL_*馃挐
_Na Miss xoxo_
*_鈽� UBAYD MALEEK_*馃挀
_Na Mamu gee_
*_鈽� MAKAUNIYAR 茦ADDARA_*馃挃
_Na Bilyn Abdull_
Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nisha蓷i馃拑馃徎馃拑馃徎馃拑馃徎馃拑馃徎.
*Abdul-rahman (sudais) is a young boy who's so passionate about putting the Holy Qur'an into memory. Please help this little boy grow his YouTube channel *ABDUL-RAHMAAN* you got nothing to lose in sha Allah thank you and Jazakumullah khair馃檹馃徎
https://youtu.be/WWIGq5Jbtb0
Do subscribe please...
*DAN ALLAH A SHIGA A DANNA SUBSCRIBE DON GANIN DUK SANDA AKA DORA BIDIYON SUDAIS YANA KARATU, HAFIZIN YARO NE DAYA TASO DA ZUCIAR SON KARATUN ALQUR鈥橝NI. *
*JAZAKUM ALLAH KHAIRAN AS YOU SUBSCRIBED鉂わ笍鉂わ笍*
*DALAAL*
*Tana* kwance akan cinyar Ummy. Ummyn na shafa mata kanta, Sai lumshe idanu take bacci na son daukar ta. Can ta daga kai tana duban Ummy.
鈥淯mmy! Habeeb yacemin yanada brother da baya gidan nan da a Morocco wai yake. Toh kuma ni a Spain na taba ganin wani me kama da Habeeb din. Amman kawai yanayin fuskar sa da sajen ne sai tsawon da yanayin jikin. Saboda banga kwayar idanun sa ba. Lokacin yana sanye da glasses.鈥�
鈥淣a鈥檃m hayateey! Zahiri. Tabbas Hafezullah kanin Habeebullah ne, Yan biyu ne. Shi Hafez din yana wajen k鈥檃nwar mahaifin su dake aure acan, Ko sanda aka auro ni gaskia banzo na tarar da shi ba. Sun dai taba zuwa wai Shi da Haj ziyadan, Lokacin ni kuma naje kaduna. Tabbas a madrid Alhaji yacemin suke da zama.. Ai kuwa suna kama sosai.鈥�
Shiru Dalaal tayi na dogon lokaci. Gaba d鈥檃ya ta rasa kalmar da zata furta. Ashe dai idanun ta ba gizo suke mata ba? Ajiyar zuciya ta sauke.
鈥淎llah sarki...鈥�
鈥淢enene Hayateey?鈥�
鈥淏abu komai Ummy! Kawai ina mamaki ne ashe yan biyu. Gaskia suna kama. Dan dai wancen yafi wannan hasken fata.. Wacece maman su to?鈥�
鈥淚dentical Twins ne tabbas, Mahaifiyar su bata gidan nan ai, Haj Binta itace marikiyar Habeeb. Ita kuma Haj Ziyadah itake rikon Hafez. Mahaifiyar su kauyen su d鈥檃ya da babansu Habeeb din. Sunan ta Haj Maimuna..鈥�
鈥淎llah sarki! Da an sani ba鈥檃 raba su ba..鈥�
鈥淭oh ya za鈥檃i? Akwai dalili shi yasa.鈥�
鈥淭oh Allah rufa asiri.鈥�
鈥淎amin Hayateey. Ya zancen yajin aikin?鈥�
鈥淢onday me zuwa za鈥檃 tafi.鈥�
鈥淪aboda hafsatu ta ishe ni, Da zuwan ki.鈥�
鈥淶anje Insha Allah.鈥�
Hira suka cigaba da yi. Gwanin ban sha鈥檃wa. Dalaal kawai dai dauriya take. Amma lamarin ya d鈥檃ure mata kai. Gashi kwanan nan tunanin sa na neman birkita mata lissafi.
***SANDAMU***
Haj Maimunatu gaba d鈥檃ya cikin tsukukun nan ta kasa cin abinci sosai, Gaba d鈥檃ya maganarta d鈥檃ya biyu akan yaranta suke. Data fara tunani kuma kanta zai soma ciwo.
鈥淕waggo na kasa tuno komi fa, Abunda na iya tunowa shine kamar na dan fara shayar da su suna jariran ko? Toh ni dai iya nan na iya tunowa. Kayan Habeebullah na jarirai shud鈥檌 ne, Shi kuma na Hafezullah kore ne...鈥�
Gwaggo Haule na daga gefe itada Hadizalo. Hadizalo na gyaran kayan miya, Ita kuma gwaggon tana goga goro a magogi. Gwaggon ta nisa tana mai zura goran data bare a dan tofin dake cikin ta.
鈥淶ahiri....Anyi haka diyar albarka, Kin shayar da Habeebullah da Hafezullah kusan kwanaki nawa nema idan ban mance ba. Suna jariran. Alokacin bayan kin haiho Habeeb mun dawo gida ruwan mama bai zo maki ba. Saifuddeen ya hiddo kudi aka siyo madara aka damawa Habeebulla. Daga nan ma ciwo ya dawo sabo, Ashe nakudar Hafezullah ce. To bayan kin haihe shi. Sai jijjiga tazo miki. Kin sha wahala ainun. Har takai kinyi jifa da Hafezullahi.鈥�
Haj Maimunatu ta rintse idanu tana hawaye, Hade da jijjiga kai tana salati.
鈥淕waggo ki bar zancen nan.鈥�
Hadizalo ta fada tana zubar da hawayen itama.
鈥淎鈥檃h Gwaggo cigaba inason ji., Dan Allah karki b鈥檕ye min komai鈥�
Gwaggo ta fyace hanci tana mai cigaba da cewa.
鈥淭oh sai likitoci suka shiga baki temakon gaggawa, aka duba Hafez aka ga buguwar batai masa komai ba. Sai dai kwana biyun da yai da yini, Bayan kin haihe tagwan sa. Da jijjigar da kika yi. Da wasu bayanai dai da likitan ya fada. Shi Hafez sai yazo da ciwon zuciya. Dan gaskia har ranar da zasu karb鈥檈 su ma sai da aka kaishi asibiti.鈥�
鈥淕waggo! Meyasa aka karb鈥檈 su.鈥�
鈥淢aimunatu dole a karb鈥檈 su. Tunda kinga matsala kika samu. Har takai ki kanyi jihwa/jifa dasu karo na biyu kenan. Akan kuma idanun baffannin shi saifuddeen da kannen mahaifiyar sa mata. Matsala ce data samu kwakwalwar ki da tunanin ki. Tunda kowa mance shi ki kai. Yaran ki kai jihwa dasu bayan an dawo gida kina basu Mama. Shi kanshi saifuddeen idan yazo ganin ku daukar abu kike ki je hwa masa...鈥�
鈥淗auka dai nayi sosai Gwaggo.鈥�
鈥淒iyar albarka... Ki godewa Allah! Domin kinsha jinya gaskiya. Domin ni da kannen mahaifiyar sa mu kayi shawara kan lalle ya karo aure. Idan yaro ya isa yaye ya bawa matar shi. Ko ita ta shayar da shi. Domin kinga ni na manyanta ba zeyiwu na shayar dasu ba. Ga ki ke babu dama sai a cutar dasu. Shikenan sai akace akwai kanwar sa datayi aure da dadewa bata taba haihuwa ba. Nan mukai shawara kan sai a bata d鈥檃ya itama.鈥�
鈥淶iyadatuh?鈥�
Haj Maimunatu ta tanbayi Gwaggo tana mai goge hawayen fuskar ta.
鈥淭abbas itace kau! To dai gaba d鈥檃ya sai aka cigaba da basu madara. Da akan kawo sunan din Idan kina bacci a sakala musu maman su sha. Idan kika farka sekita bori kina fashe fashe. Daga karshe ma duk sanda Za鈥檃 kawo su ko idan shi saifuddeen din yazo sai abin naki yayi tsamari ki wuni kina kuka bakyason ganin su baki d鈥檃ya. Har kwana yake a bakin kofar gidannan sau ba adadi yaron kirki. Na kira Alhaji Aminu nace ya nemi manyan saifuddeen din kan ya sawwake miki. Domin aure ba zai yiwu a haka ba.
鈥淒ak鈥檡ar dai ya iya shikar ki, Shika d鈥檃ya ya miki. Yara kuma aka bawa ziyadatun Hafez, Shi kuma Habeeb wata gwaggon su ta karb鈥檈 shi. Basu shekara biyu ba saifuddeen din aka daura mishi aure da wata diyar abokin baban sa. Toh yarinyar kirki dai wallahi ita ta cigaba da shayar da Habeeb har Allah ya temaka aka yaye shi. Shi kuma Hafezullah yaki amsar maman Ziyadatun, Har wajen mutane ukku duk yaki amsa. Sai madara suka cigaba da bashi. Dakyar yake iya karbar maman, Daya karba zai saki. Inaga sau biyu akace yasha na ita ziyadatun. Dake Allah ya sanya mai garin jiki ne kuma mai kwana agaba ne sai Allah ya raya shi.
鈥淒a anan garin kanon ita ziyadan take. Kullum sai takai Hafez wajen Habeeb har suka taso suna tafiya da magana. Sun yi sa鈥檃r marik鈥檃 gaskia. Sun rike su da amana. Duk sanda za鈥檃 kawo su wajen ki to fa ranar ke ba Lahia kinta yage yage kina doke abubuwa. Ganin haka yasa nace saifuddeen ya dena kawo su. Nan gaba zasu kawo kansu idan sunyi wayo. Gida da komai haka saifuddeen ya bamu a kano kan mu koma, Nace a鈥檃h! Ya dai barmu nan din. Har Allah ya baki lahia ki koma dakin ki idan kin amince.
鈥淭oh ana haka. Jikin Hafez sai ya matsa lokacin yana shekaru hudu ne ko uku. Bazan mance ba saifuddeen ya kara zuwa yana sanarmun kan su ziyadan zasu bar kasar kuma da Hafez zasu tafi Zai dinga ganin likita acan. Toh hakan akayi. Suka tafi kasar Morocco acan ya zama hafizin gaske har ya haddace qur鈥檃ni cikin kankanin shekaru ko nawa ne na manta. Amman dik hutu sai yazo shi wajen tagwan sa. Shima tagwan yakan je wajen sa. Toh haka dai suka cigaba da rayuwa.
鈥淪hi Hafez na can kasar Shi kuma Habeeb yana nan, Har Allah ya azurta marikiyar sa da haihuwa itama. Tafara haihuwa, Yayanta ko nawa ne an fada na mance don munje radin sunan ma. Toh Shi dai Habeeb ya kanzo nan din a boye don Karki gani. Shi kuma Hafez yana can yana ganin likitoci. Sun zagaya k鈥檃rashe da dama. Itama marikiyar tasa na neman haihuwa. Daga karshe ma dasa mata akayi. Ta haifi mace bayan Hafez din ya girma abadan ma. Sai suka koma kasar turawa kuma nan ma aka kuma dasa mata wani cikin ta sake haihuwar mace. Ance bata kara zuwa an dasa mata ba, yaran nata na nan kanana guda biyu.
鈥淪hi Hafez gaskia Saboda yanayin raunin zuciar sa ba鈥檃so yaga halin da kike ciki Shiysa mahaifin nasa ya hana kowa ya kawo shi wajen ki. Nima kuma na goyi bayan hakan ganin shid鈥檌n bame lahia bane. Amman dai Habeeb har wasu yasaka a boye suke duba lahiar ki Idan kin fita. Sannan shi mahaifin nasa yana mana aike gaskiya sosai, Ya samawa wannan dan (Malam Bala) aiki acikin birni. Sannan marikan Habeeb da Hafez din suna kokarin aiko kayan abinci da suturu a kawo miki. Hajiya binta marikiyar Habeeb wallahi har kayan abinci da kudi a boye take bayarwa akawo.
鈥淎mman dai Hafez saboda yanayin ciwon sa shi bai kara sanya ki a idanun saba. Habeeb yacemun Saboda hakan ne ma yake fushi dasu duka. Kan boye masa da ake. Amman yanzu Alhamdulillah za鈥檃ita baki dafa鈥橧 kicigaba kuma da shan magungunan ki na asibiti. Likitoci na kara duba ki. Ga sauka ana miki da yardar Allah komai yazo karshe. Saifuddeen dinma yace zasu zo. Idan kika huta. Nake jin har Hafez dinma dan ance ya kafe sai ya dawo kasar nan. Ki godewa Allah Maimunatu, Yaran ki nutsattsu ne, Sun tashi a hannu na gari, an rike su kamar 鈥榶a鈥檡a. Ba suyi maraicin uwa ba . Sun samu uba nagari jajirtacce. Habeebullah babban lauya ne na fannin shari鈥檃. Shi kuma Hafez din ance dakta ne na ilimi fannin kwamfuta... Alhamdulillahi.鈥�
Haj Maimunatu ta matse hawayen farin ciki,
鈥淕waggo shekarar su nawa yanzu?鈥�
鈥淏asu kai talatin ba. Amman dai a deb鈥檈 namu na hausa. Muga..鈥�
Ta shiga irgawa da hannu tana lissafi can ta cigaba da cewa,
鈥淎 turance 28 suke, A debe na hausa sunyi 29.鈥�
鈥淎llah ya raya su..鈥�
鈥淎amin Yaa rabbi.. Aamin.鈥�
鈥淕waggo kina ganin zasu yafemin?鈥�
鈥淵afewa wacce iri? Me kikai musu? Ke din da ba a sane kike komai ba, A haihuwar tasu fa kika ha鈥檇u da wannan lalurar diyar albarka.鈥�
鈥淭oh Gwaggo ku yafemun..鈥�
鈥淏abu abinda kikai mana diyar albarka. Sai da ma ince dake ki yafeni saboda ni ce na bada shawarar a dauke su. A kuma raba auren naku zuwa sanda zaki warware.鈥�
Hawaye ta shiga gogewa tana salati. Sai da tayi kukan ta mai isarta sannan tace da Gwaggo
鈥淕waggo shawarar da kika basu itace wadda tafi dacewa, Ko nice nan kwatankwacin haka ya faru da wani nawa shawarar da zan bayar kenan. Alhamdulillah! Allah na gode maka. Allah ka yalwatawa bayin ka lahia ingatacciya.鈥�
鈥淎llahumma Aamin diyar albarka, Hadiza sauke ruwan wankan nan ki sirka ki kai mata bayi. Diyar albarka tashi ki wanka ko kyaji dadin jikin ki. Kizo ga tofi Malam ya aiko almajirin sa. Idan Kinci abinci kuma ki hadiyi magungunan ki.鈥�
鈥淭oh Gwaggo.鈥�
Bata musa ba ta mike ta zura hijabi ta cire kayan jikinta ta daura zani. Hadizalo ta kai mata ruwan wankan, Bayi ta shige ta fara wanka. Tana yi tana hawaye...
***MADRID***
A nutse ya karasa parking din motar a parking lodge. Ya shige cikin gida bakin sa dauke sallama.
鈥淜a dawo Hafez? Duk kowanne ya shiga鈥�
鈥淣a dawo Maa! Eh kowanne yayi. A daren yau ma za鈥檃 sasu a jirgin da zai tafi lagos direct.鈥�
鈥淢asha Allah! Kaga ai mun samu sauki, Sai yan kayayyakin da suka rage kawai. Yaya kuwa ya kira wo ka?鈥�
鈥淎鈥檃h!鈥�
鈥淥h okay...鈥�
鈥淲ani abu ya faru ne?鈥�
Murmushi Haj Ziyadah tayi tana mai girgiza kanta,
鈥淎bun farin ciki ne, Nasan ko shi bai gaya maka ba, Habeebullah zai