hotel dake unguwar surulure. Nan dalaal ta sanarwa Ummy. Itama Ummy ta gayawa Alhaji saifuddeen. Nan take Alhaji saifuddeen ya gayawa judge din da yai alkawari. Cikin kankanin lokaci aka fara aiwatar da bincike.
Sannu ahankali cikin tsukukun nan Dalaal ta shiga rayukan ahalin Alhaji saifuddeen baki d鈥檃ya. Kowa sonta yake yana yabawa kyakkyawan halin ta. Ga wata shakuwa data sake kulluwa tsakanin dalaal da Habeeb. Gefe d鈥檃ya dai zuciyar ta dalaal bata mance fuskar saurayin data ceto a korama.
Tana daga kwance ta mike tana gyara gashin ta. Tunanin sa ne kawai ke addabar zuciar ta tarasa meyasa. Daganin sa bakon shan giya ne saboda sunga masu irin cases d鈥檌nsu da dama a asibiti.
鈥淔uskar sa ce kemin yawo a kai... Da idanu?! Why? Ya kamata ace ka fita daga zucia ta....鈥�
Cikin haka Ummy tashigo ta same ta
鈥淜e da wa kike magana?鈥�
鈥淶ance ne ni d鈥檃ya Ummy.鈥�
鈥淜ina magana a zuci zaki ce. Ta fito fili ko?鈥� Wani abun ne ke damun ki?鈥�
Har zata gaya mata sai kuma tayi shiru tana girgiza kai. Tarasa dalilin dayasa ta kasa fadawa Ummyn, Dubada bata boye mata komai, Itace tamkar babbar kawarta a duniya.
鈥淚na abokanan aikin ki na can? Da yama sunan sa?kuna waya?鈥�
鈥淢uhannad? Mun rabu ai Ummy. Yanada yaudara da yawa.鈥�
鈥淎llah zai kawo mijin ki duk a inda yake. Kila yana garin nan, Ko unguwar nan. Kila yana wani garin. Ko baya kasar ma gaba d鈥檃ya. Allah kadai masani. Allah zai baki miji wanda zai soki ya kaunace ki har karshen rayuwar sa.鈥�
鈥淎amin Ummy! Ni fa ba aure nakeso yanzu ba鈥�
鈥淎i dole kiyi Hayateey, Da lokacin ki yazo zaki yi. Yawwa Baban su habeeb yacemun anata tattara shedu. Da an kammala komai sameer zai zo hannu.鈥�
鈥淯mmy! Banason a masa komai fa.鈥�
鈥淜akki damu hayateey! Ko babu komai kanin mahaifin ki ne, Tamkar mahaifi yake agurin ki. Dole a bashi darajar sa. Kawai hakkin ki zaaa karbo miki.鈥�
鈥淭oh Ummy!鈥�
Hira suka zauna suna yi. Kan dalaal na kan cinyar Ummy tana shafa mata har tayi bacci. Ranar Ummy a wajen dalaal ta kwana kamar ko Yaushe Idan Alhaji saifuddeen ba abangaren ta yake ba.....
***HAFEZ***
Dawowar sa kenan daga Gym wayar sa tayi kara. 鈥楴K鈥� shine sunan mai kiran. Tsayawa yai yana amsa wayar a hankali kamar ko yaushe . Saboda shi baya da hayaniya. Kuma mutum ne shiru shiru da abun duniya bai dame shi ba, Yanada kawaici sosai da kauda Kai a abunda basu shafe shi ba. Matsalar Hafez d鈥檃ya, Zurfin ciki da barin damuwa a zuciyar sa. Baya iya sanarwa wani nasa damuwar sa sai ta kai ma鈥檏ura. Sannan shi damuwar wanin sama sata yake a zuci taita cin sa. Shi yasa yake a wahale kullum ba lapiya.
Yana tsaye yana goge fuskar sa da k鈥檃ramin towel, Dayan hannun kuma yana waya da shi. A nutse yake amsa wayar yana dan murmushi,
鈥淭hank you bro! Allah bada sa鈥檃.鈥�
Yana gama wayar ya katse yana mai mayar da ita aljihun gaban wandon sa.. kai tsaye ya shige cikin gida bakin sa dauke da sallama. Yana gayda su papa ya haye sama yai wanka. Da ga nan ya kwashi su bushra ya kaisu wajen lilo. Anan suka huta sannan suka dawo gida. Ya haye dakin sa yana mai cigaba da research din da yake a computer!!!! Dr. Hafezullah kenan, Mazan fama馃槝鉂わ笍
*DALAAL: A new world 鉂わ笍鉂わ笍*
***
*_鈽� AL-茦IBLA_*馃挊
_Na Safiyya Huguma_
*_鈽� MABU茒IN ZUCIYA_*馃挅
_Hafsat Rano_
*_鈽� DALAAL_*馃挐
_Na Miss xoxo_
*_鈽� UBAYD MALEEK_*馃挀
_Na Mamu gee_
*_鈽� MAKAUNIYAR 茦ADDARA_*馃挃
_Na Bilyn Abdull_
Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nisha蓷i馃拑馃徎馃拑馃徎馃拑馃徎馃拑馃徎.
**8Tana tafe akan hanya tana tsince tsince a bola. Sanye take cikin cikakkun kaya riga da zani na atamfa da babban mayafi wadatacce. Idan baka lura da yanayin yadda take magana ita kadai ba tana hawaye, Hade da tsintsar kayan bola, zaka kwakwaso rantsuwa ka dire hade da buga tsallen albarkar cewar lapia k鈥檃lau take. Sai dai kash, Da ka sake matsawa kusa da ita zaka harbo jirgin.
Masu kula da ita a sirrance na biye da ita a baya. Kowanne zaka dauka harkar sa yake. Amman a zahiri kula da ita suke, Ciki harda wata mace da itama ke tafiya nesa da ita. Ta gama tsince tsincen da zata yi a bolar ta koma gefe ta rafka tagumi tana hawaye.
鈥淎mshi... Zo ku amshi kowa ya dau d鈥檃ya nace. Kunji? Ko sai nasa bugu, Sakar masa mana.鈥�
Ta fada a tsawance tana mai rafkawa wata bishiya bulala. Kai kace da wasu take.
鈥淵auwa! Yan albarka.. To bara na samo ma ku wani abincin.鈥�
Mikewa tai tacigaba da tafiya. Tarin kayan bolar data dauka na hannun ta ta rike su. Can ta durkusa ta dauki wasu kwalaye. Ta goya a bayan ta tana jijjigawa.
鈥淭oh! Ya isa, ..鈥濃€�
Ba ita ta dena dauka da ajiyewa ba sai kusan gabannin magriba. Ta nufi hanyar gidan su kamar wata mai cikakken hankali. Sharbaceciyar mace, Sambaleliya tamkar ita tayiwa kanta halitta dan kyawu. Lalle Allah yayi halitta. Kyakkywar babbar mace jajir da ita, Tamkar ka tsaga jikinta jini ya fito don tsananin kyawun fatar jikin ta. Doguwa, Mai dauke da 鈥榢ira mai kyawu. Kana hango kanannadden gashin kanta baki wuluk na fulanin jaubawa.
鈥淢aimunatu kin dawo?鈥�
Wata tsohuwa da kallo d鈥檃ya zaka mata kasan jininta ce ta tambayeta alokacin data shigo tana zubar da kayan hannun ta. Kad鈥檃 kai tayi kamar gaske alamar Eh. Ta nemi waje ta zauna tana gyaggyara kayan bolar data kwaso.
鈥淪annu diyar albarka, Allah ya dube ki ya baki lahia.鈥�
Can ta mike ta shige daki da kayan hannun ta na bola ta shiga adana su kai ka dauka abubuwan arziki ne.
Tsohuwar ta share hawayen daya zubo mata tana kallo dakin da maimunatun ke faman ha鈥檇a shirgi.
鈥淎llah ya baki lahia diyar albarka. Allah yasa mu na da rabon ganin samun lahiar ki, Shekaru nata ja. Allah sarki rayuwa. Allah kai kadai ka barwa kanka sanin wannan baiwa.鈥�
Mikewa tai dakyar ta shige cikin dakin girki ta dakko kwano, Tuwo ne na dawa da miyar kuka, kamshin man shanu sai tashi yake yi. Kofi ta dakko ta ebo mata ruwa a randa mai sanyi. Gidan tsaf tsaf dashi. Gida na na marasa k鈥檃rfi haka, Amman dai akwai wadatar zuci. Dakuna ne guda uku. A jere. Guda biyu kulle suke da kwado. Da alamun masu dakin basa kusa. Gidan ko鈥檌na a tsaftace. Ga rijiya a gefen wata bishiya dake tsakar gidan. Sai bandaki a gefe.
Ya sha siminti gidan, Da na 鈥榢asa ne aka gyara shi ya koma na bulo. Dai dai karfin zaman talaka. Gwaggo Haule. Ta shiga daki wajen Haj Maimuna. Ta ajiye mata tuwon a gabanta. Tana kallon yadda maimunan ke kwantar da kwalaye akan gadon karfen mai rumfa kamar 鈥榙an jaririn gaske.
鈥淪hid鈥檕 bisa nan, Amshi ga abinci nan da zahin sa.鈥�
Ina tamkar da gunki Gwaggo Haule take, Haka takarashi maganar ta kamar koda yaushe, Wai dai gwadawa take yi. Ko Allah zai yi baiwar sa tayi magana. Gwaggo Haule na ficewa. Haj Maimunatu ta ajiye kwalayen hannun ta. Ta sakko da sauri tana kallon tuwon. Hannun ta tasa ta shiga ci tana korawa da ruwa. Tana gama cinyewa tayi katuwar gyatsa tana shafa cikin ta.
鈥淜in cinye? A dad鈥檕?鈥�
Gwaggo Haule ta 鈥榙aga asaberin dakin, Tana mai tambayar Maimunatu kamar zata amsa ta.
Jijjiga kai Haj Maimunatu tayi tana mai bararrajewa akan tabarma. Ta sheke da dariya tana tafa hannaye ita kadai. Gwaggo Haule ta girgiza kai kawai ta saki asaberin ta koma tsakar gida tana jan carbi.
鈥淲ai ina tsahare ta shiga ne? Daga zuwa gangaren makarantar Malam shine ta jima haka?鈥� Ta karasa fada tana mai sauke bahaguwar ajiyar zucia cike da takaici.
***Tun daga nesa kake jiyo kururuwar tsahare, Tana tafe tana jan hannun dan ta Habu. Dayan hannun kuma ta rike roba da ruwan tofi aciki.
鈥淐urgal, Cirgal.. cangali cangali, Cillar cillau..鈥� Wasu yara suka leko ta saman katangar wani gida suna tsokanar Habu dake cangala kafar sa ta hagu.
Da sauri tsahare ta juya tana zabgawa yaran harara, Fasa tafiyar tayi ta juya ta shige cikin gidan. Da sauri yaran suka gudu cikin daki suna doko kyauren tagar.
鈥淚na lamunde? Zan iya cin kan kwal haka kaza ta butar kan uban shegun 鈥榶ayan ki. Sai na tasgada shege ko shegiya cikin su. Keda Ayuba (mijin lamunde) zan hada naci kwal uban ku baki d鈥檃ya. Yau ga buroaba kau.鈥�
Lamunde ta ja tsaki tana mai cigaba da sakatar hakoran ta. Fuskar nan tasha jar hoda kamar bazawarar akuya. Bakin nan yasha jambaki. Ga gira taja kamar zata hade da idanun ta.
Tsahare ta sake jan tsaki tana bubbuga kafafunta a kasa.
鈥淎鈥檃 ha! Yo ki dena man tsoki.鈥�
Lamunde ta bata amsa tana mai choge ture kaga tsiyan kanta gaba. Diddigaggen gashin kanta ya bayyana.
鈥淵o sai naci kan butar buhun uban ki. An maki tsokin. Shegiya kau, Shi ya saka Ayuba ya yo maki abiyar zama (kishiya/abokiyar zama) Banza mi dauyin hammata kau.. Idan iyalin ki suka sake kiran Habu da cirgal, Sai na tasgada kafafun shegu.鈥�
鈥淎 hayye! Sena ci ma ki kan abun uba ki. Shegiya..鈥�
Jin kalaman lamunde, Hakan ya sake tunzura Tsahare taja dogon tsaki tana mai ajiye robar hannun ta. Hade da debo ruwan zagi ba surke ta d'urawa lamunde. Ta nannade hannun rigar ta, Ta kwakwaso zanin lamunde Ji kake tis, Bas, Wakacau, Das.. Sunata dambatuwa. Makota na kusa dana nesa dik matayen sun lek鈥檕 suna kallon gulma. Kowanne yana ihun zuga wanda ya fiso.
鈥淵auwa timata kasa. Naushi ruwan cikin shegiya. Yo haka zaki. Sumar ta Tsahare. 鈥�
Dak鈥檡ar wasu daga ciki suka iya raba lamunde da Tsahare da suka yiwa junan su dukan tsiya.
Tsahare ta rik鈥檕 hannun Habu suka koma gida tana mita. Tana shiga Gwaggo Haule ta shiga mata fadan rashin dawowar ta da wuri. Gwaggo Haule itace mahaifiyar Bala mijin tsahare. Habun kuma jikanta ne. Daya samu matsalar allurar polio kafar sa ta nakasa guda d鈥檃ya.
鈥淵anzu haka fada aka gama yi da ke. Shiya saka baki dawo da azama ba.鈥�
鈥淵o gida biyu ne kawai fa Gwaggo. In hi鈥檇i maki, D鈥檃ya matar malam ce muka buga match da ita yar renin hankali, Sai lamunde. Jemammiyar matar ayuba mai kayan miya. Yar haka kaza ta uba. Shegun yayan ta ke tsokanar habu wai cirgal.鈥�
鈥淭oh Allah shi saukaka. Mi malam yace?鈥�
鈥淵ace Kamar yadda ake mata kullum a kara mata a ruwan sha tasha a shafe mata jikin ta dashi.鈥�
鈥淭oh angode ma shi, Allah shi albarka. Kema angode.鈥�
Gwaggo Haule ta mike da tofin a hannun ta tayi daki. Itama Tsahare ta dakko makulli ta bude dakin ta ta shige.
**** Kamar koda yaushe bayan tayi bacci mai nauyi. Gwaggo ta shasshafe mata jikin ta da ruwan tofin ayoyin Allah. Cikin bacci ta sauke ajiyar zuciya hade da juyawa ta gyara kwanciyar ta tana sakin jariran munshari d鈥檃ya na bin d鈥檃ya.
Gwaggo ta fice da sand鈥檃 tayo alwala ta koma dakin tana sallah, Kana jiyo sautin kukan ta a sujjada tana rok鈥檕n Allah samuwar lapiar hankalin Maimunatu. Tana idarwa ta shiga jan carbi tana wasu addu鈥檕in sosai. Kwalayen magungunan asibitin Maimunatu ta dudduba. An zazzana k鈥檃idar yadda maimunan zata sha, Kowanne da alamar zanen kara d鈥檃ya ko uku wato sau uku a rana. Ganin an bata tasha na sha ta hadiyi na hadiyan. Sai gwaggon ta kakkauda su gefe. Domin irin tsofaffin nance ita marar tara shirgi. Ko鈥檌na tsaf. Maimunan na kan gadon karfe me rumfa. Ita kuma gwaggon na kan katifa yar k鈥檃rama irin ta yan boarding, Ta rage hasken fitila mai lagwani. Sannan taja zani ta rufe kanta tashiga bacci mai dadi. Bayan ta tofe jikin ta dana Maimunatu da addu鈥檕i...
***WASHE-GARI****
Da farar safiya Hadizalo yar Gwaggo Haule ta karshe ta dawo daga birni wajen girkin yan makarantar kwana da suke yi. Bazawara ce, Auren ta ya mutu. Yaran ta biyu suna wajen baban su. Bayan ta gaida gwaggo ta bude dakin ta da mukulli ta shiga tana hantse baccin da bata yi ba. Malam Bala ya sayo koko da kosai ya kai wa Gwaggo bayan ya gayshe ta. Gwaggo taci nata tana mai ajiyewa Maimunatu nata ita da Hadizalo.
Haj Maimunatu 鈥榶a ce awajen Gwaggo Haule. Domin tun tana kankanuwa iyayen ta suka rasu. Kuma ita kadai suka haifa. Sai rikon ta ya dawo wajen Gwaggo haulen. Gwaggo haulen kanwar mahaifiyar Maimunatu ce. Uwar su d鈥檃ya uban su d鈥檃ya. Da Gwaggo haulen itada su Maimunatu tun kafin su yiyyi aure har ya zuwa auren nasu kafin rasuwar mijin ta a tare suke da kishiyoyin ta guda biyu. Ita ta cikon ukun su. Sai amarya ta hudun su. Gwaggo Haule, Yayan ta biyu kacal da marigayi Aliyu mai faskaren ice, sauran gaba d鈥檃ya sun rasu. Sunyi zama na mutinci da girmamawa da kishiyoyin ta biyu. Hamdiyya da Zaitunah. Kafin a auro musu kubura. Shigowar kubura gidan itace ta tarwatsa zaman lapian da suke yi da kishiyoyin ta. Kawu na suka rabu. Daga baya ma suka hade kai aka ware gwaggo Haule. Abubuwa da dama sun faru lokacin da suke gida d鈥檃ya. Irin gidan nanne babba na da. Kowacce da dakin ta. Ga yaran Kowacce mata. Babu abunda ba鈥檃 sayarwa agidan nan. Gidan marigayi Aliyu mai faskaren ice shine gidan daya fara samun arzikin talabijin din kallo a kauyen, Tun daga kauyuka ake zuwa ganin abun kallon. Allah yayi masa arzikin kauye lokaci d鈥檃ya. Bai da鈥檇e da samuwar arzikinsa ba rai yayi halin sa. Aka raba gado kowacce tagama gaban ta. Shine Gwaggo Haule da yaranta biyu suka samu wannan gidan da suke ciki a matsayin rabon su.
***. ***. ***.
鈥淜u hito ki riko hannun ta. Kar muje mu tarar da layi. Wancen zuwan da mukai yace muzo da wuri Idan zamu dawo don yai mata gwaji.鈥� Cewar Malam Bala, Babban 鈥榙an Gwaggo Haule.
Hadizalo dake fente fuskar ta da hoda me ruwa (foundation) taja tsaki ahankali tana dadira jambaki a bakin ta. Sai kallon kanta take a mudubi tana mai yaba kyawunta.
鈥淕a ni nan fitowa, Gwaggo kin shirya ta ko?鈥�
鈥淢i? Yo wani shiri kuma banda wanda aka gama tun dazu.鈥�
鈥淲allahi Y鈥檃r 鈥榢urkurar har tazo.. 鈥�
Tsahare ta fada tana leka tagar dakin Hadizalo.
鈥淜eda kin cika minahinci Tsahare. Ina ganin ki ta wutsiyar idanu na.鈥�
Futowa tai daga dakin tana hararar Tsahare ta wasa. Ta shige dakin Gwaggo tana sake gaysheta.
鈥淭aso muje Addah Maimunatu! Allah ya baki lahia.鈥�
鈥淎llahumma Aamin鈥�
Gwaggo ta fada tana kallon Maimunatu.
Haj Maimunatu na gefen katifar Gwaggo, An shiryata cikin riga da zani na atamfa, Ga yalwataccen hijabi har kasa. Idanun ta sun sha kwallin da Gwaggo Haule ta rambada mata. Mikewa Gwaggon tayi. Ta mikar da ita. Har waje ta rakasu ta sakata a yar 鈥榢urkura (Adaidata sahu/Dan sahu/tricycle/velocipede)
鈥淭oh Allah ya dawo daku lahia, Allah ya bada nasara. Ku hidi masa likitan fa, tana yawan firgita ko taita wannan kukan da take. Amman babu fashe fashen da take a baya. Kuma wani lokacin bata fita ma, Yauwa ku hid鈥檌 ma shi takan kad鈥檃 kai ko girgiza shi wasu lokutan idan an tambayeta.鈥�
鈥淭oh Gwaggo! Sai mun dawo.鈥�
Dan kurkura yaja, Gwaggo na daga musu hannu, Hade da bin su da adduar dawowa lapia dama dacewar warkewar Haj Maimunatu. Cikin gida ta koma tana mai cigaba da adduoi. Tsahare na tsakar gida tana tular wanki. Data gama ta zuzzuba ruwa a mazubin sa. Ta share ko鈥檌na tas. Sannan ta koma dakin ta ta janyo littafin hausa tana karantawa.
Suna zuwa asibiti, Likita ya fara tambayoyi yana duban Haj Maimunatu dake wasa da kasan hijabin ta. Sosai ya ga alamar samun saukin ta akan zuwan su na baya. Hadizalo ta sheda masa maganar Gwaggo. Likitan yayi rubuce rubucen sa a takarda. Ya dago ya dube su baki d鈥檃ya yana mai mi鈥檏awa Malam bala takardar.
鈥淎kwai sauran kudaden gwaje gwaje da basu kare ba, Mai gida ya sake aiko da wasu. Yanzu ku tashi ku je da takardar dakin gwaje gwaje ayiyyi mata seku dawo.鈥�
Mikewa sukayi, Suka fice. Hannun Haj Maimunatu na cikin na Hadizalo.
鈥淪hi dai baya gajiya?鈥滳ewar Malam Bala
鈥淢ai shariah ai baze gaji da hidimar Haj Maimunatu ba, K鈥檃una ce daga Allah. Allah dai ya bata lapia. Ya hada kawunan ta da iyalin ta.鈥� Hadizalo ta bashi amsa.
鈥淭oh Aamin ya rabbi..鈥�
K鈥檃rasawa cikin dakin gwaje gwajen suka yi. Cikin lokacin da bai wuce awa da rabi ba, aka kammala kowanne gwajin. Suka koma wajen likitan da sakamakon. Karba yai yana duddubawa fuskar sa k鈥檜nshe da fara鈥檃.
鈥淭oh Alhamdulillahi! Allah ya tabbatar mana da alkhairi.鈥�
鈥淎meen likita.鈥�
鈥淲ato cikin ikon Allah da qudirar sa. Babu wata sauran matsala akanta. Sauran gwaje gwajen ma komai ya nuna ba matsala.鈥�
鈥淢asha Allah! Alhamdulillah! Ana kuma hada mata da adduoi da tofi a gida. Duk asuba akwai makarantar almajiran dake sauke mata qur鈥檃ni.鈥�
鈥淒ama ai kai da kaga wannan sakamakon kasan bana na-saa-ra (turai)bane kadai. Allah yasa mu dace. Toh kowane irin lokaci. Ko da yaushe, Hankalin ta zai iya dawowa jikin ta. (Dementia/Alzheimer's disease) Sannan zata fara iya razana ko furgice idan tana bacci. Domin komai zai rika dawo mata ne daki daki. Ko kuma lokaci d鈥檃ya. Allah ya tashi kafad鈥檜n ta. Ya dawo mata da hankalin ta da nutsuwar ta. Idan hankalin ta ya dawo, Duk abunda yafi soyuwa agareta inma mutum ko abinci a temaka a kawo mata shi. Kar a dau lokaci mai tsawo.鈥�
鈥淚nsha Allahu likita. Allah ya saka da alkhairi鈥�
鈥淎amin! Ga wadannan magungunan a bayar a pharmacy na nan cikin asibitin zasu baku magungunan kamar ko yaushe. Idan akwai ragowar wasu a gida azubar kar ai amfani dasu.鈥�