zasu komi, wannan kenan.
Yau take sallah Alhmdllh, sunyi tsaf sun fito dan zuwa masallaci dan gabatar da sallah iddi, alokacin Noor tuni ta dawo gidan sarki, sarki garin fahad, da wazir anata masu busa kafin su tafi masallaci, Ammy da ita da fatima sai Noor a gyefen Ammy sai tazar sarki fahad da yaransa guda biyu, an kai raka,ar kashe ne kowa ya ɗago za,ayi sallama, amma ƴar tshowa bata ɗago ba, har aka idar da sallah, ana idar wa, Ammy ta ɗaura hanun ta kan jikin ƴar tsohuwa, gaba ɗaya ta faɗu jikinta, Innalillahi,wainna'illaihi raju,um!! Tuni sukayo kanta suna dubata, suna kuka, yayinda wata dattijuwa tazo wajen ta taɓata tace Allah ya gafarta maki baiwar Allah!! Sai dai kuyi hakuri ai tarasu, nanfa suka cigaba da kuka inda awajen akasamu hirami aka rifeta akasanar wa dasu Abu da sarki fahad, dasu muhmd, suna sunji mutuwar sosai, inda muhmd ya sanarwa dasu dad, ba,awani, jimaba aka maidasu gida, sannan danan akayi mata sutturah, aka kirasu suyi sallah ma da ita, sannan akafita da ita, nanfa akayi mata sallah, akakaita ga makwancin ta, kullinafsun za,ikkatul mauta, Allah ya fabar ta masi, Hauwa halinki nagari ya biki, sosai sunji mutiwar ta, inda kalamanta suka dinga dawowa Ammy da fatima wannan kenan.
Da misalin ƙarfe 4:00 ne jirgin su Abu zai tashi dan haka harfe 3:00 suka gama komi, inda sukayiwa su dad sallah ma, dansu sai nan da sati zasu dawo.
"Su sarki fahad dasu dad sukayi masu rakiya har airpot sannan suka wuce gida su dad", yayinda har lokacin mutuwar ƴar tsohuwa na dukan su,wannan kenan.
A gida suka cigaba da zaman makokin su bayan sati ɗaya kuma kowa ya watse, amma har lokacin basu ɗena mata sadaka ba.
*GARIN KANO*
"Tuni su dad sun dawo sun cigaba da gabatar da karatun su, da kuma ayyukan su "inda mom tasa a nemu mata ɗan uwanta uncle ɗin su fatima tunda an rashi gaba ɗaya", anan ne ake faɗa mata ya rasu, tun tafiyar su Turkiyya amma ba,asan ɗan uwan su bane tunda haɗari yayi, tayi kuka sosai harta fawwalawa Allah, ta mashi addu,a, takuma yimasa saraka, wanna kenan.
*GARIN TURKIYYA*
"Bayan wata biyu" yau ne fatima ta tashi batajin daɗi hakan ne yasa yau ko falon bata fitaba, duk da dama dai tunda cikin ya shiga watan haihuwar shi, bata iyya tafiyya sbd girman shi yayi yawa, wani lokacin sai ta zauna tayita kuka, wai itta alallan dule cikin ya dameta haka farisi zaita bata hakuri yana lallasar ta, yanzu har ta kai ko wajen Ammy bata iyya zuwa sai dai Ammy ita tazu, Abu ma yana zuwa wani lokacin shida Ammy, suma sosai suke tausaya mata yanayin girman cikin.
"Noor albushi rinki" "farisi daya shigo gidan yanzu yake kiran ta" yana faɗa, ɓeganta a falon ba dan haka yayi ciki abunshi, innalillahiwa,inna,ilaihirraju,un!!! Noor ya kira sunan ta cikin gigitacciyar muryar sa, wannan kennan.
😭🙆🙆 WAI SHIN NENE NE YASAMU NOOR?
TAKU HAR KULLUM
FATIMA AKARAMMMA 😍😍😜
INA SANKU MASO YANA NAGODE SOSAI,
BYE💃💃💃
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️
____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*SANADINTA NE* *Takun karshe*
*Written by fatimaalaramma* *( falaramma)*
*Sadaukar wani ga maryam ibrahim, marubuciyar BARA,AKUFAI, Allah ya ƙara maki lpy sis mery*
*Comment and share fisabilillah*
Bismillahirrahamanurrahi
-Pg 59- 60
"Noor daman bakida lpy baki sanar dani ba" ya ƙasa gabanta cikin gigita tareda da riƙota, ita kuwa tuni hankalinta ya fara fita daga jikin ta, ɓeƙara gigita ba, sai da yaga wani jini da take zubarwa ga kuma, jikin ta daya saki sosai, daukan ta yayi yafice daga ɗakin da ita cikin gudu, yana fitowa harabar gidan faɗawa suka farah take mashi baya, bai jira akawo mashi muta ba, ya fara gudu da ita, yayin da yayi wani ɓangare na gidan, sosai yake gudu iyya ƙarfin shi, yayin da motaccin kuma suka take mashi bayya dan sun fahimci inda ya nufa, "wani bafaɗe ne yazu gab dashi a mota" yace mu karasa ranka ya daɗe, "ko kallanshi beba ya cigaba da gudun shi da matar sa, kafin ya ƙarasa an buɗe wajen dan haka da gudu, yashi, kai tsaye wani daki ya wuce da ita ya kwantar da ita akan wani gadon asbiti, ya rufe dakin sannan yadawo kanta ya fara aiki ya shiga dubata cikin nutsuwa ta reda kiran sunanta ahankali.
Tuni an sanarwa da Ammy abinda yake faruwa, dan haka kai tsaye ƙaramin clinic ɗin gidan suka nufa, cike da tashin hankali, tuni sun kira dactor Maryam sun sanar da ita halin da ake ciki, sannan suka ƙarasa asbitin hankalinsu a tashe.
Aiki yake cikin ƙwarewa sosai dakuma maida hankali inda yasamu nasarar dawoda ita cikin hayya cinta, sannan ya farar mata magana, Noor kiyi nishi insha Allah bebyn mu, zai fito, yana faɗa wani hawaye na fitowa daga idanun sa, ɓe ankaraba ya ji tarike shi sosai, sai kukan beby yaji, ya yi kasan da sauri ta rike shi nan ma ta ƙara kankameshi, da ƴar yasamu ta sake shi ya dauki bebyn, namiji ne ya shiga yanke mashi cibiyar yayin da ita kuma wani sabon ciwan ya zumata wanda yafi na dah, bayan ya aje bebyn ne ya karasa bakin ƙofar ɗakin ya mikawa Ammy bebyn wanda suka shigo yanzu, sannan ya koma ɗakin, kanta ya koma ya cigaba da taimaka mata, take takuma sanbulo bebyn ta, mace, bekai ga ɗaukan yarin yar ba, yaga wani kan bebyn ya tahu, cikin ikon ubangiji, shima ya fito, namiji ne shima, shikuwa besan sanda ya fara godiya ga Allah ba, tare da daukan ƴaƴan ya fita dan ya kaiwa, doctor maryam ta shirya su, ya koma ɗakin, Abu a wajen yayi sujjada ga Allah, sbd wannan babbar kyauta dayayi masu, shikuwa kan matar shi ya komi yacigaba da kula da ita, yayi mata abubuwa da yawa sannan ya yi mata injections, sannan ya yimata ɗinki, sannan ya shiga toilet ya shiryamata ruwan wanka da kanshi ya shigar da ita ya mata sannan ya fito da ita ya gwera wajen, sannan ya bude dakin, sbd amma nata faɗa yace shi babu wanda zai shigo yaga matarsa, maine anfanin karatun likitan dayayi indai sai an taimaka mashi a wajen haihuwar matar sa, wannan kenan.
"Zukuga farinciki wajen Abu da Ammy", nan fa aka shirya yarah, aka fito dasu, masha Allah sukaga ƴaƴan kana kallan macen kaga ba,indiya, yayan da mazan kana ganin su kaga larabawa, ana fitowa da ƴaƴan, Ahmad na doko sallahma cikin hosbital ɗin da sauri ya ƙaraso wajen ya karbe dayan dake hannun doctor maryam, wow ya furta a hankali, kana kallan yaran kamarshi ɗaya da mahaifin shi, yayin da ɗayan kuma ke kama da Ahmad wato kunga maman shi yayi, ton da fatima kamarsu ɗaya da Ahmad, ya kawo mata ruwan tear tasha sannan ya ƙarasa gab da ita ya subbace goshinta sannan yace, ngd miki matata, kibani abinda bazan iyya bawa kai na ba, ngd sosai my Noor, ina ƙaunarki, ɗan Allah kice min wani abu ko naji ɗaɗi my, Noor, dan tunda aka kawota hosbital ɗin batace komi ba har kama yanzu yayi yayi da itta amma taki magana, can kuma ta faɗa jikinshi ta fashe da matsanan cin kuka, rasa mai zaiyi yayi dan haka shima ya fashe da kukan sai da sukayi mai isarsu sannan, ya ɗago yace haba Noor menene nayi miki dahar zaki ƙiyimin magana, sallamar su Abu ce hanashi ƙarasa maganar, "Ammy ta rungumeta tana mata sannu" yayin da "Abu shiya yake ta jero mata, sannu tare da zuba mata addu,oi, dakuma neman dacewa duniya da lahirah",wannan kenan.
"Caraf yaji an riƙeshi, ya ɗago da kanshi yana kallanta ta sakar mai wani kayyataccen murmushi", sannan tace, ngd farisi, shima besan sanda ya mayar mataba tare da kama kun nan ta yana faɗa mata, magana, tana dariya, ya ƙara da cewa kinsan da kiƙiyimin magana, gwara in be karasa ba ta rufe bakin shi, tace yanaga baka farinciki, yace inayi mana, amma na kasa bayyana shi sbd rashin jin muryarki, dariya tayi sannan tace ina sanka mijina ina alfahari da kai ina san kasance wa dakai, nima ina kaunarki my Noor, gaba ɗaya sun manta da su Abu dasuke ɗakin, yayinda sukuma hankalin su nakan bebys, wannnan kennan.
Batayi aune ba taji an rufe mata fuska ta baya, ahankali ta furta Ahmad tana dariya, shima dariyar yake ya juyo ya rungume ta sannan yace conguratuletion my sis, murmishi kawai ta mashi, bakaramun jin daɗin ganin ɗan uwan nata tayiba, nanfa, farincikinta ya ƙara ƙaruwa, jinta take tamkar sarauniya, gamijinta gakuma ɗan uwan ta, wanda take jin sa, a ranta, tashi yayi ya karbo ƴaƴan shida Farisi, yayin da Ammy ta kawo ɗayan da hannun ta, kasa tayi da kanta yayin da Ammy ta dora mata shi kan cinyar ta, tacce gafa yaya ki farah dashi, masha Allah my zarah Allah ya baki lpy Ameen Ammy na, bari naje na hado maki abinda zakici da kai na, tafice tare da yimata kissa a goshi.
"Shi kuwa Abu tuni ya kira dad ya sanar dashi yayinda yaketa kiran ƴan uwa da abokan arzuƙi", "har sultan ya kira ya sanar dashi dan lokacin shima baya gida", yaje wani gari duba wani company su, Abu yama rasa ya zaiyi dan haka yace, asanar da haihuwar a ko inna, wannnan kenan.
Ahmad ne ya fita ya fito daga ɗakin bayan doctor maryam tazu ta yimata sannu tare da yimata barka, sannan tace, yarima ya kamata ace yanzu, abasu susha, sbd kaga zasukai 30 minit da haihuwa, ko fima, kaga wannan bebyn tanajin yinwa, dan ta fahimci akwai san zuciya a tsakanin iyayen guda biyu, sun fi sun kansu feye da ƴaƴan, sanna ta fice abun ta, yayin da Ahmad shima ya goya mata baya, wannan kenann.
'ƳA'ƴan guda biyu suna hannun farisi yayin da babban yake hanun ta, tayi ƙasa da kanta, my Noor ɗago kiga bebyn nan kamasu daya da mom, ɗagowa tayi ta kallin yarin yar bata san sanda wani san bebyn nata yakamata ba, aa aisunfi kama da Ammy, dariya yayi yace ai duk ɗaya, sbd Ammy da mom basu da banbanci, sukayi murmushi a tare, "wannan kuma kamarsu ɗaya da fariai na", "cewar Noor", "shiyasa naji sanshi ya kamani, lokaci ɗaya", "tafaɗa tana murmishi", "nikuma wannan kamarshi ɗaya da Noor ɗita shiyasa na kasa badashi, wannan kuma kamarta ɗaya da mom ɗina, sosai zasu birgeka inkaga yadda suke hira a tsakanin su, yayin da dukan su ya dora mata su kan cinyarta yace bari na maku pic, sbd na dinga kallah ina jin daɗi, ya masu sannan ya dauki biyu haɗa aka masu tare, abun gwanin sha,awa, wannan kenan.
"Ammy ce ta shigo dakin ɗauke da sallah ma", yayinda bayi suke biye da ita, kululin hannun su suka ajoye, sannan suka gaidasu suka masu barka, hadima ce ta fatima ta ƙaraso wajen tacce sannu ranki ya daɗe Allah ya rayya, nan tashiga yimasu addu,a sannan fatima ta mike mata bebyn ta karba sannan ta miƙa tana ƙara addu,a, sannan suka fice daga ɗakin, "Ammy tacce wai anya kuwa my Zarah an bawa yaran nan, mama, ƙasa tayi da ƙanta alamar kunya, take ran Ammy ya ɓacce, ta farah faɗa tace Anoor ai lefin kane kasan komi bazaka gayamata idan ita bata sani ba ai kai ka sani, nanfa Ammy tayita faɗa saida tayi mai issarta sannan tace bata babban ta bashi, sannan sai ka bata ƙaramar da karamin, "tom insha Allah Ammy, ya miƙa mata shi sannan yace kifarah bashi ayyi mashi bismillah, ya faɗa yana murmushi sbd tunawa dayayi dawani kalamanta abaya data faɗa mashi, "Ammy tace bazaka tayata ba shine zakayi baya" ɓaiyi aune ba yaji ta fashe da kuka, Ammy ta ɗago tana kallanta, ta ƙaraso gab da ita tace haba my zarah, menene haka kuma kingafa yinwa sukeji, dan Allah ki taimaka ki basu badan muba, tana kaiwa nan tafice ta barmasu ɗakin, wannan kenan.
"Farisi ne yashiga lallashin ta, sannan yace ɗan Allah ki basu nima tundazu nakesan yi maki magana kawai bana son kiyi kuka ne", "nifa bazan iyyaba tafaɗa cikin shagwaɓa, ɗan Allah my Noor, sosai yashiga lallamata sannan ya taimaka mata ta bashi, yana farawa ta fashe masa da kuka tacce zafi, yanata bata hakiri duk da kai tana bashi tausayi sbd gabaɗaya ta rame lokaci ɗaya takuma wani yi fari sosai, dayar yasamu ya gama ana ceremashi ya fashe da kuka yayin da itama ta fara kukan wai, ita tagaji, dakyar dai yasamu suka gama sannan yadinga shi mata albarka, sbd duk sunyi barci, ringtorn ɗin wayar shi dayaji ne yasa, shi ajine, beby girl ɗin ya ɗauki, wayar dad ne ya dauka cikin jin daɗi suka gaisa dad yashiga yimashi, murna sannan ya miƙawa Noor ta karɓa tanajin muryar dad ta fashe da kuka, dadyna, "na,am mamana, sai kuma tacigaba da kukan, "haba mamana menene haka Allah yamaki wannan kyauta keda zakiyi dariya amma kike kuka" dad ɗan Allah kazo,sai kuma tayi shiru, "zanzo mamana karki damu, naga yara masha Allah' Allah ya raya mana su, batace komi ba", amma azuciyar ta amsa 😂😂😂 nikuma nace wato Noor gulmace ta hanaki amsawa.
😂 "dad insha Allah nan da kwana biyar zamuzu insha Allah", haka dai sukayita hira wannan kenan.
Alhmdllh yau kwanaki Noor, biyar da haihuwa, ina da tuni su dad sun bayyana anata murna da farinciki musamman dad wanda farincikin shi ya fi na kowa.
"zugaka kyautut- tuka wanjen dad" da abu da farisi har mom da Ammy ba,a barsu a baya ba.
Yau ta kama ranar suna, inda yau yara suka tashi da sunayen su, inda babban ya tashi da sunan dad da kuma na Abu dana baban shi, wato (muhammad), Inda macen ta tashi da sunan mahaifiyar ta, (faɗimatu ) "nikuwa nace sunan matar sa ya mayar sbd daɗin zama",😂😂 inda shi kuma ƙaramin ya tashi da sunan (Abdallah ) wato sunan Abdallah ƙanin fatima, waɗan nan sunaye sun samu asali ne a wajen mahaifin yaran wanda hatta itta kanta fatiman bata san da sunayen ba, sai ranar, "zu kaga murna gurin su Abdallah da farinciki wai yayi takwarah, harda Abban ramadan ma murya yaringa yi.
Ansha liyyafa sosai, sannan kowa ya watse zuga gidan shi da babbar kyauta cike da farinciki da jin daɗin walimar sunan.
Kwanan su dad biyu a garin Turkiyya, bayan su na suka koma zuwa garin su Nageria, inda kowa ya koma kan aikinshi.
Maijego kuwa Alhmdllh tacigaba da wankan ta, alhmdllh tana samun kulawwa ta kowanne ɓangare, Alhmdllh, satin su uku da haihuwa, Bilal da matar sa sukazo yiwa fatima barka, da kayan su niƙi-niƙi, zukaga murna gun Fatima, dan ƴar Bilal ta girma sosai tayi wayo.
Satin su Bilal ɗaya a garin Turkiyya suka koma gida, yayi daidai da ranar da fatima tayi arba'in. bakaga yadda fatima tayiwa ƴar Bilal siyayya. Tayi masu godiya sosai da addu,ar Allah ya ƙara haɗa kansu, wannan kenan.
💖💖💖💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💖💖💖💖💋
*BAYAN SHEKARA BIYU*
Acikin waɗan nan shekarun abubuwa da dama sun faru, tsakanin kano, da Turkiyya.
"Mamma kiyiwa Haisam magana wllh tun dazu yake tsokana ta" cewar wata jyakkyawar yarin ya data shigo ɗakin yanzu, gani nayi ta ɗago da kanta "ta ce jiki kiramin shi" "mamma ai ya gudu ban garen su Ammy", "to rabu dashi zaizu ya sameni" tsaf na tsaya ina kallan Mamma😂 Noor ce tayi bala'in kyau sosai, kana ganinta kasan tana hutawa, taɗan ƙara ƙiba kaɗan da tsayi, sai wani haske data ƙara sosai. "Zarah ɗan Allah kidinga hakuri da Haisam karki manta shiɗin ƙanin kine haba my zarah" "murmushi yarin yar tayi tace tom na hakura Mamma na," "yauwa jeki kirawo min, mai martaba", sunan da suke kiran muhmd dashi kenan, "tom mamma" yarin yar ta fice cikin nutsuwa, wannan kennan.
Gyefe na hango farisi na sau kowa daka kan sterf a hankali, har ya ƙaraso gaban Noor bata sani ba, sai da ya hura mata iska a ido sbd ya fahimci tun sanda yafara sauko wa, ta manta me takeyi sbd kallan shi, "Abba ka sauko ta faɗa cikin basarwa" "eh na sauko yakk ya gajiya ya faɗa yana murmushi", "banza ta ma shi sbd ta faminci inda ya dosa", "sannan ta nisa tace ya kamata kayi breakfast yanzu kaga lokaci yana kurewa," "Tom shikenan madan my Noor haka suka zauna kan table din suka farah breakfast sunayi suna hira abun su harsu ka kammalah wannan kenan.
Suna gama wane, zarah da maimarba ta suka shigo falon, kai tsaye wajen su, suka nufa bayan yaran ya gaida su ne, "sannan ya kalli maman tashi yace mamma ance kina kirana" "eh bawani abu bane", "dama break fast zakayi dan haɗima tace mun bakai ba", "kaga Shurem dan Allah ka ɗinga cin abinci kaji", "kaɗena wahalar da hadimarka haka" "Ace kai kullum sai anyi faɗan abinci da kai haka kaga