ban san da wacce fuskar zan kalli zarah ba, nayiwa zarah abubuwa da yawa wanda wasu bazasu faɗu ba, tabbas zarah one in million ce, yarin yace nagar tacciya, gakuma mahaifin ta, "karki damu uktih insha Allah duk zasu yafe maki kibar wannan zancen ya isa haka, kitashi na rakaki ban garen da mijin ki yake kije ki kwanta dare yayi, aa Ammy dan Allah ki barni nan gurin ki, aa wllh kitashi mu tafi nima wajen mijina zan kwana, 😂😂😂 sbd na tayashi farincikin wannan rana, mai tarin tarihi a cikin ta, wannan kenan.
💖💖💖💖💖💖💖💋💋💋
Ɓangaren su noor da farisi, wai noor meke damun kine, ki tashi muje wajen su dad suna son ƙara ganin jikin naki, nifa na faɗa maka baza ni ba tafada tare da juya wa, ido falda hawaye, sbd bazanje, sai kuma tayi shiru, nasan yanzu an riga anfaɗa masu komi, nidai baza ni ba, sai kuma ta fashe da kuka, "noor mene hakan" wai dan Allah mene matsalar ki ne Noor, faɗa wa tayi jikin shi ta fashe da sabon kuka, mamaki abun ya bashi duk da dai ya fahimci inda ta dosa, nan yashiga rarrashin ta yana bata baki, daƴer yasamu tayi shiru, to yanzu faɗamun kinji maman beby, wata harara ta yimashi sannan tajuya kanta gyefe wannan kennan.
yau ne su Anty zee suka sauka garin turkiya da asuba yayin da tuni angama shirya masu komi, an kawo su gidan sarki wazir, "sunyi farincikin ganin junan su" dan kowa ya hallarah a fallon amma banda Noor da Farisi, sosai suke mamakin ganin Amemy amma basu ce ƙala ba, suka zubawa sarautar Allah ido wannan kenan.
Bayan su gama ne, "mom ta shiga labartawa Zee abun da ya faru batare da ta ɓoye mata komi ba, ita da Abdallah, sosai Anty zee ke kuka tace haƙiƙa yaya bamuyi sa,ar mahaifiya ba dan Allah kuyi hakuri da abun da inna Barira ta aikata maku, nasa ni ba mai laifi baci a gurinku amma dan Allah kuyi hakuri, sosai Anty zee ke kuka tana basu hakuri, "Ammy ce ta ɗago ta tace haba ƴar uwata" mene kika yi mana, da kike ta wannan kukan ai bakomi yanzu haka ma nace ane mumana yaya sbd kin san shima ta haukatar dashi sbd yana ne mana, nan ta saƙe fashe wa da wani kuka, suka ƙara jawota jikin su, tom yanzu ina alfanin abun da inna ta aikata, ace ɗanka ma baka barshi, kai wannan wacce irrin jarrabawa ce, haka dai sukayita bata baki tayi shiru suka shiga bata labarai masu dadi, shikuwa Abban Ramadan tuni ya fita wann kenan.
Noor ce da farisi suke saukowa daga steff ɗin bene, suci wata peenk shadda ta matuƙar daukan su, dukan su sai zuba kamshi suke duk dadai ita Noor hijabi ne ajikin ta wanda baikai ƙasa ba fart ɗin ABU suka faɗa dan sun' san anne zasu same iyayen nasu maza, riƙe yake da hannun ta sukayi sallah kofar falon, akayi masu iso sannan suka shiga har lokacin hannun su riƙe dana juna, noor nata ƙwace hanun ta amma ya rike da kyau wannan krnan.
Har ƙasa suka tsuggun na suka gaida su yayin da suka amsa cikin sakin fuska, "Abu ne yace wa noor ƴata dawo ƙusa dani" ki zauna ya jikin naki "da sauki Abu na" ta faɗa a kunya ce yayin da ta ƙarasa gab dashi ta zauna shikuma farisi ya zauna ta bangaren da dad yake suka saka Abu a tsakiya, sosai "Abu ke kallan su cikin farinciki da jin daɗi" ya jawo su duka jikin shi yace haƙika kuɗin nan kun zamemin wani haske a rayuwa ta, haƙika kuɗin bango ne arayiwa ta, kune sanadin farinciki na, ina sanku ina alfahari daku har karshen rayuwa ta, a yanzu bani da wani abun so bayan ɗaya guda ɗaya, sai kuma Noor da mahifinta haƙika ina sanku ina ƙaunarku har karshen nun fashi na naƙarshe a duniya bazan dena sanku ba, haƙiƙa shidin ya zamemen tamkar mahaifin shi dana rasa a baya, yanuna dad, ita kuma tamkar cikon gurbin ɗana Anoor ce, sosai dad kejin daɗin kalaman Abu, yayin da ita kuma noor kaunar Abu ya ƙara mamaye ta'ta kwantar da kanta akan kafadar shi sosai ina kallan shi tamkar dad ɗinta itama, wannan kenan.
"Shikuwa dad farinciki ne ya ƙara lulluɓeshi yana farincikin ko yanzu Allah ya ɗauki ranshi yasan yabar masu kulamashi da ƴar tashi wadda yake jinta AZUCIYAR shi sosai yake godewa Allah bisa ni'imar dayayiwa ƴar tashi wanna kennan.
Sallamar su Ammy ce ta katse shurun ɗakin wanda suka shigo suka zazzauna, inda basu ƙarasa ba su Ramadan da noor suka shigo suna dariya dasu Abdallah da Ahmad wanda tun safe suna bangaren su mejor faisal suna nunu namasu wajajen wasan ni na gidan, sbd sosai yaran sun ɓurge su dayake kuma babu yara a gidan wanna kenan.
Lahhh!! "Dama Anty kinzo" Noor ta faɗa tare da ƙarasawa inda suke eh wllh dazu da asuba nazu ai, sai akace mun bakijin daɗi, ƙasa tayi da kanta alamar kunya tacce a zuciyarta wato itama angaya mata, aa yaya dai mamana Anty zee ta faɗa aa bakomi Anty sai anane taahiga gaida su ɗaya bayan ɗaya, inda ta ƙarasa gaban Ammy tana gaida ta, ta amsa tare da jawota jikinta sosai tana tanbayar ta jikin nata tace da sauƙi, wannan kenan.
"Abban su Ramadan ne" ya doka sallah ma ya shigo shima nan fa ta gaida shi yashiga mata tsiya mamana rabona dana ganki a gida na tun haihuwar maimoon, sai kuma bikin ki, ko kirana ma kinde nayi, murnushi tayi tace kayi hajuri uncle insha Allah zanzo dad ne yace mani bakwa garin ne, tom Allah ya kawoki lpy Ameen uncle, sannanfa falu aka shiga tattauna wa baki ɗaya ana hira yayin da aka nunawa Ammy takwararta maimoon ƴar Anty zee aikuwa bakuga daɗin dataji ba yayin da tayi mata kyautar wani ƙaramun conpany na takalman yarah, wannan kenan.
Sosai ɗakin yacika da farinci kana kallansu kasan sunajin daɗi da farinciki sai hira suke gwanin bansha' awa yadda kasan abokan juna, inda Abban Ramadan yake cewa Abu tom yaushe ƴaƴan na zasu koma gida Nageria ne wani kallo ya watsa mashi alamun wasa yace ai waɗanan sunzu gida tusa a banɗaki, gaba ɗaya ɗakin suka ɗau dariya wannan kenan.
"ABU ne ya dauko wasu tulin takardu"ya zuɓesu gaban farisi yace kadu ba wannan sbd da baka nan ne aka kirkire su sababun conpany ne duk suna under Nageria ne kuma duk anyisu ne sbd kai amma nayi kyau tar guda ɗaya ga wata baiwar Allah datayi musabaƙa alqur,ani wancen shekarar wato fatima muhmd ibrahim, zaka gani a nan, noor ce ta ɗago ta kalleshi tace" ABU ai ni ce!" Allah noor wllh Abu masha Allah ashe ƴata ma na bawa duk ɗakin sukayi murmushi wannan kenan.
Nan yashiga dubawa yana jerowa abu tanbayoyi game dasu harya kammalah komi wasu naga ya ware a gyefe guda wasu ma gyefe guda sannan naga ya haɗe ragowar ya kai daki sanna ya dawo ya zauna kusa da dad ya miƙa mashi takardun guda uku, dad ya karba yace wannan fa maibabban suna, eh abbu naka ne, halak makal kacigaba da kulawa dasu sbd nan din abubuwa sunyi yawa aa maibabban su na bazan karɓa ba, haba dad ai abun duk ɗaya ne, Abu ya faɗa shima sosai akayi fama da dad kafin ya karba tare dayiwa su Abu godiya sbd yayi mashi bayanin yanda abubuwa kanfani ya masu yawa shiyasa, wannan kenan.
Ya jugo ga Noor yace kema my wife ga naki amma su na kasar nan ne, wannan gift din beby ne da kika bani, da kuma Allah ya azurta mu dashi, wannan babban conpany ne na kayan mata kinga komi zaizama kasan ci, ya kuma miƙa mata na biyu yace wannan kuma na takalman man yane da ake fita dasu ƙasashe, nabaki ne sbd kaunar da nake maki, aa kabar nan ma ya isa dan Allah, "Abu ne ya katse ta da cewa Allah yasaka da alheri" Allah yataki riƙo ƴata aiba,amaida hannun kyauta baya, ko dan gaba, aa "Abu abubuwan sunyi yawa yakamata a bar wancan conpany aa dad babu ruwanka dad kazuba ido kayi kalli kawai ai matar sace bakomi duk ɗaya ne wannan kenan.
"Muhmd ne ya jawo Abdallah jikin shi yace wai mai yasa gaba ɗaya abokina kade na sona ne ko nemana kadena yi ma, aa yaya ba haka bane wllh naga kayi busy ne shiyasa na barka ka huta, kuma kaga kullum ina bangaren su yaya faisal, gaskiya nima yaya soja nake san zama kamar mejor faisal, Allah Abdallah insha Allah to Ubangiji ya zaɓe abun da yafi alheri Ameen yaya, karɓe wannan yaya kakarɓa mana wannan ƙaramun conpany ne da yake kano na safufine naka ne halak malak gashi nan da sunan kama, ngd yaya Ubangiji yayi jagorah ya ƙara arzuƙi wannan kenan.
yau satin su dad ɗaya a gidan su farisi, sosai suke jin daɗin gidan duk da kullum sai sunce zasu tafi Abu ya hanasu, wannan kenan.
"yaune su dad ke haɗa kayansu shida mom" dasu Anty zee da mijin ta zasu wuce family hause dinsu , amma su Abdallah duk suna gidan da Ahmad da su Ramadan da noor karama, dan susunci sunga gida ABU dakan shi yasa akayi mashi shiri suka ɗauki hanya dan raka su dad gida muta guda sukayi sbd daga nan ma akwai wani waje dasuje susha iska, nan da nan gari ya dauka sarki ya fito shida iyalan shi akadinga mashi hamdalah, wannan kenan.
Gurine mai matuƙar kyau da tsaruwa dan haka kowa ya huta kuma ya shakata ance ansha gakuma rabon wasu gift da abu yasa akayi masu yace na murnar samun jika wand kowa ɓesan mene a ciki ba, wanna kenan.
Yayin da dare ya farayi aka wuce da su dad family hause ɗinsu, tare dayi masu godiya sosai sannan suka wuce sukuma zuwa gida abun su, Abdallah yana mutar mejor faisal sai zuba hira sukeyi, har suka isa gida ko lunch basuyi ba sbd kowa a koshe yake suka wuce dakunan su, Abdallah da Ahmad da Ramadan suna ɗaki daya, noor kara kuma Ammy tayi ɗakin ta da ita wannan kenan.
Tun a bakin ƙofa Farisi ya ɗauki noor ya shige ɗaki da ita bai kaita ko ina ba ya shige toilet da ita yayi mata wanka tare da saka mata kaya marasa nauyi sannan shima ya faɗa toilet ɗin ya watsa ruwa saka makon ready sunyi sallah tun awaje, tsaf ya shirya ya haye gado ya kwanta tare da jawo matarsa jinkin shi, ita kuma ta lafe sosai dama abun nema ya samu, tun kafin bayyanar cikin nan tafahimci son jikin ta yayi mata yawa musamman idan farisi yana kusa da ita sai kawai taji bata jin daɗin indai ba'ajikin shi ba, daga nan wani daddaɗan barci ya ɗauke ta, sbd jin daɗin abun da mujin nata kemata, wannnan kenan.
NIMA NAN NATAFI NAWA BARCI 😂😂
I LOVE YOU MASUYA NA
TAKU HAR KULLUN
FATIMA ALARAMMMA 😍
BYE 😂😂
*_LAFAZI ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️
____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*SANADINTA NE*
*Takun karshe*
*Written by fatimaalaramma* *( falaramma)*
*Sadaukar wane ga Sadiq Abubakar CEO Allah ya Kara daukaka Allah yayi jagorah*
*Comment and share fisabilillah*
Bismillahirrahamanurrahi
Pg 55- 56
washe gari bayan farisi ya dawo daga sallah asuba ne, ya shigo ɗakin dan tashinta itama tayi sallah, amma ga mamakin shi sai yaganta kan sallah ya tana ta tasbihi ga ubanhgiji ta, cak ya tsaya yana kallan ta kafin daga bisa ni yaga ta ɗaga hannayenta samma tana addu,ar, sosai, tana kuka, bayan ta gama ta mike dan koma wa gandota ta kwanta, cak taji anɗagata an kwantar da ita a gadan, batayi mamaki ba, sbd turaren shi ya riga ya isar da zuwansa wajen, sai dai tundazu da takeji bata ɗauka shiɗin bane, ta ɗauka kawai sabo da sakawa ne ɗakin ya dauka, wannan kenan.
"Morning my dear" ya tsinci kallamar daga bakin ta, sosai ya zuba mata ido batare da yace komi ba, ya ɗan murmusa sannan yace tom ban karɓa ba, banasan wannan bari kiga ni na gaidaki, sauri tayi ta kauda fuskar ta, tana dariya, riko ta yayi, ya yi mata lafiyayyun kiss a kowan ne sashi na fuskar ta, wanda jikinta shima saida ya amsa, sannan ya ɗagota yace ya kika gani, hatta beby yasan da wannan gaisuwar ya faɗa yana murmushi tare da kashe mata ido ɗaya, ita dai jiki duk yayi la,asar😂, wannan kenan
✨✨✨✨
"Mom ce ke gaban dad idon ta yayi jah sosai" da alama kuka tasha, shikuma dad ya zuba mata iɗo yana kallanta, "khadija ya kirata da wata irrin murya", ɗagowa tayi tana kallanshi batare da tace komi ba, "kisa ni' ni muhmd ban taɓa kwana da bacin ranki batare da nayafe maki ba, kisa ni ban taɓa jin wai zan'iyya kullatar ki ba, wllh khadija na yafe maki duniya da lahira, ina koma ruƙon Ubangiji na daya yafe maki mata ta, kuma haryanzu ina sanki, bazan dena sanki ba har karshen nunfashi a duniya khadija, wannan kenan.
Sai musalin 11: 30 shaɗaya da rabi na hangi noor na mutsawa akan gadan da alama tashi zatayi, kaɗan kaɗan na farajiyo muryarta tana addu,ar tashi daga barci kafin naga ta bude idan ta, tafara dudduba gefenta amma bata ganshi ba, ummm kawai tace wato ya tashi tundazu ni kuma ya barni hummm.
Shikuwa farisi duk abinda take yi yana kallanta ta tap din dake hannun shi, sosai suke hira da mahaifin nashi amma muntina bayan munta na ya duba tap din dake gabanshi sbd kar noor tatashi besa ni ba, wannan kenan.
"Abba bari inje na dawo" farisi ya faɗa yana mikewa, "tom shikenan ina jiranka cewar Abu" kai tsaye ɗakin ya nufa da sauri ya shige, tare da sallah ma, ta ɗago ta zubamashi ido, can kuma ta ɗauke ta juyar da fuskar ta, "ya ƙaraso wajen yana murmushi" yace sorry beby kimun afuwa naga barcin yana maki daɗine shiyasa ban tasheki ba, kuma ga "Ammy tace indinga barinki kina hutawa" pls mana, sai lokacin ta saki fuskar ta tace, ina fatan ka tashi lpy my husband, "lpy lau kamar kyakkyawan kumatun ki, yanzu tashi na raka ki kiyi wanka ko na maki da kaina, tayi saurin girgiza kai, yace tom tashi ma za, dan nasan gaba ɗaya bebyna yunwa yake ji, ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya, wanna kenan.
Bayan sun gamane ta shirya tsaf sannan suka koma falon ɗakin inda ya shiga bata abinci a bakinta har saida ya tabbatar ta ƙoshi sannan ya barta haka, ta huta sannan suka fito dan gaida Ammy ta big falo kuwa ita da Abu dan haka take fatima ta ƙarasa falon ta zube gansu tare da gaida su, Ammy ce ta ɗago ta tace, Noor bana san irin wannan gaisuwar kinji dan Allah ki dinga kula kodan lpyr bebyn mu, wannan "gaskiya ne Abu ya faɗa" shima, Ammy ce ta dawo da ita gefenta ta zaunar da ita sannan tace muyi hira my daught, ya labarin aikin naki, farisi ne ya ɗago da sauri yace Ammy dan Allah kibar wannan maganar saboda Noor bawani aiki da ,zatayi a yanzu ko nan gaba, "wannan gaskiya ne cewar Abu", kinsan nima haka akayimun shikenan aikina ya sharuwa, Abu to dan Allah menene anfanin aikin ku bashida anfani shiyasa bama bari ko Anoor, eh wannan gaskiya ne, haka dai hira ta balle tsakanin su, wannan kenan.
"Bayan sati ɗaya: Yanzu komi ya daidaita inda su farisi angama kammalah masu komi na ɓangaren su da zasu koma, an kuma shirya ranar da za,ayi walimar komar tasu, anshirya ƴantattun bayi waɗan da za,ayi tarewar dasu, komi yana tafiya yadda ya kamata, wannan kenan.
Ƴar tsohuwa na gani zaune kan wata katafariyar kujerah wanda gaban kujerar an cikata da kayayyakin taba wa, sosai na tsaya ina kallanta sbd mamakin yadda ta koma badan nayi mata farin sa ni ba dabazan gane ta ba, duk babu tsofan, tayi kyau abunta tamkar ba ita ba, sallah marsu Noor ce ta katse mata dogon tunanin data tafi, ta ɗago da kanta ta faɗaɗa murmushinta dan ganinsu gaba ɗaya, wanan kenan.
Sunjima sosai suna hira harma dasu Abdallah da suka biyu su, kafin daga bisani sukayi sallahma, dan zasuje gidan su dad ne, koda suka fita angama shirya komi motocima akallah zasuyi talatin na rakiyar su, banda na capding Faisal wanda shima yayi sune sbd Abdallah dan shima yau zasu koma gida dan "dad yace zaman ya isa haka", duk da suɗin bahaka suka soba musamman Abu da Ammy wanda sukeran yaran sosai, wannan kenan.
Basuyi aune ba wala lafiyayyiyar muta farah mai nunfashi ta tsaya a gaban su, tare da wanga le masu ƙofa dan su gisha, sukuwa su Abdallah da Ahmad tuni suna mutar capting, "Abu ne da Ammy suka ƙarasa wajen dan yimisu Allah ya kiyaye, sosai Ammy ke masu Abdallah godiya da fatan alkairi, "shima kuma Abu haka",